Showing 6001 words to 9000 words out of 102125 words

Chapter 3 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

5881

suna tahowa well organized abayan na Jameelar,da gudu sukayi cikin gida don bada sanarwa,cike da mmki Azeema tace''Jameelah dama kinsan gidan ne?wlh duk azatona sunan unguwar kawai kika sani ashe hatta kofar gidan kin sani,haba shiyasa naga ko jiransu Sagir bakiyi ba kiketa sharara uban gudu....''

Da jajayen idanu Jameelah ta dubi Azeema har saida Azeemar ta tsorata da yanayinta,''Menene ma ban sani ba akan Hafsa?inajin kawai yadda tayi rayuwa acikin mahaifiyarta kafin ta fad'o duniya ne kawai ban sani ba,Azeema kar kiyi mmki idan nace miki nasan abubuwa da dama akanta wanda shi Gidado be sani ba.....'' dan dakatawa tayi tare da sanya yatsa tana dauke guntun hawayenta,ita ko Azeema sake baki tayi tana binta da kallon mmki,ta cigaba''Azeema an gaya miki kishiya abar wasa ce?ki gode Allah ke ba'a wani takura miki kamar yadda ni aka tasani gaba acikin wannan fitinanniyar zuri'ar,Azeema ko kadan ban ta6a nadamar auren Gidado ba ammh ina meh cike da takaicin shigowa Zuri'a irin wannan,,Azeema rashin haihuwar ma ni bata wani dameni ba kamar yadda nake jin zafin yadda zan hada miji da wata gidahuma can,ayau Gidadona na shirin raba zuciyarsa da kuma gangar jikinsa gida biyu yamallakawa wata bayan ya tabbatawar dunia cewa shi din mallakin Jameelah ce ita daya,,,sister Azeema am sorry to say banajin zan iya cigaba da danne zuciyata salon na yiwa kaina illa,it's time to show dem the real me.....!'' ta ida maganarta tare da bugan sitiyari tana meh fashewa da kuka mai tsuma zuciya,sosai Azeema ta tausaya mata hadda er kwallarta,tace''Sister Jameelah pls dnt fall my hands,don Allah take it easy,,bani son ki kasance cikin sahun mata masu tafiyar da rayuwarsu akan *'KISHIN JAHILCI'* wlhy yadda kke da ajin nan kamata yayi ki tafiyar da rayuwarki akan *'KISHIN ILIMI'* ....

Sagir ne ya katse musu hirarsu ta hanyar kwankwasa motar,da sauri suka fito idanunsa ya sauka kan wasu tsirarun mutanen da suka fito lek'en en daukan amaryar,Sagir yace''Haj.jami aganina da kin koma cikin motar kinyi zamanki idan yaso su Goggo Karime tunda sune manya sai su shiga su fito mana da amaryar ammh motar taki din dai zata shiga...'' kallon uku saura kwata ta wulla masa kan tace''Amaryarka ko tamu?'' kallon ban fahimceki ba yay mata,,gane nufinsa yasa tajah dogon tsoki tana fadin''Dallah malam bani wuri in wuce sai shegen shisshigin da bbu kwarjini...!'' tajah hannun Azeema suka nufi gate din gdn,,Suraj yayi hissing cike da haushinta yace''Diz woman is an animal wlh,wai meye haka take yi ne wai don Allah?wani irin kishi ne haka?sai ka kira salandon mijin nata kace masa taki jin maganarmu...'' [dake dama shine ya basu umarnin su dakatar da ita karsu bari ta shiga gidan idan ankai],

Aiko tun kafin Sagir yakai ga latsoshi sai ganin call dinsa yay yana shigowa,da sauri ya danna receive ya kora masa bayani,hannu yasa akai yana shafawa tare da cije lips yace''Allow her,,idan har akwai sauran yadda da aminci tsakanina da matata Jameelah tou nasan she wont try doing anyting stupid kawai kokarin daga hankulanmu take....!'' ya fad'a not fully sure of himself,,ta6e baki sagir yay kawai yace''Toh Allah yasa...''

     Sai safa da marwa yake yi adakin Hajju,duk abun duniya sun taru sun masa yawa,ina ne zai soma dafawa?yana cikin wannan halin kuncin ne sai ga Hajju ta fito wanka,she was shocked to see me in tears,yana ganinta yayi saurin isa gareta ya rungumeta tare da fashewa da kuka yace''Hajju zuciyata namun zafi sosaii,,ina zan saka raina inji sanyi ne?" Cike da tausayinsa ta shiga bubbuga bayansa take fadin''Haba d'ana dena wannan kukan share hawayenka ba'a san dan sanda da kuka bafa,da jarumtaka akasanshi,,nasan da damuwarka ammah ka sani bbu abunda zan iya yi akai illa tayaka da du'a'i,ka gayawa Allah damuwarka don shine zaiyi maka maganin komi...!'' jan hannunsa tayi ta zaunar agefen gado sannan taje ta dauki kofi tadan dibi ruwa kadan aciki ta zauna ta shiga zuba addu'o'i tana tofawa aciki har dai ta kammallah sannan ta bashi yasha,nan da nan yaji wani irin dadadar sanyi ya mamaye masa zuciya,haka take masa akodayaushe idan yana cikin kunci,sai tayi masa tofi ta bashi yasha sannan ransa ke sanyi,,sallama yay mata sannan ya fita,ita kuma ta hau shiri don tarbar amarya,,akwai wani al'ada acikin wannan Zuri'ar,,wato duk matar da aka kawo aure gidan,Tsoho ne ke fara sanya mata albarka kana akaita wajen Hajju ta sanya mata tata albarkar kafin sauran,Hajju takan jika magani aruwa irin tamu dai ta gargajiya sannan ta bawa amarya tasha,yin hakan wai kariya ne agareta da kuma tsareta daga mugun nufin wani,,haka ma idan ya'ya mata zasu fita agidan wato zasu je aure,suma din takan basu *'RUWAN KWARYA'* kamar yadda ake kiransa susha don kariya agaresu,bbu wata wacce ta shigo ko ta fita da zaace ta tsallake wannan al'adar..............

     _*Tofa! muje zuwa muga ko akwai wacce zata iya tsallakewa nan gaba?muddin kuma wannan din ta tsallake aganina tana iya 6ata komi,,juz guessing oowh😄*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_

_*#KISHIN_MATA*_

_*#2020_NOVEL*_

_*#SALO_NA_DABAN*_

_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*

               🍃🍃🍃

         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT



WɾƖTҼɾ

ى

 

ASSɷ

*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_

           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   

*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA UKU...🤟*_

____________★Ba tare data tsaya neman shawara awajen manya ba ta kamo hannun Azeema,kai tsaye suka danna kai cikin gidan dauke da sallama abakunansu,gaban Azeema sai faduwa yake sosai ita ko uwar gayyar ko ajikinta,idanuwansu ne ya sauka akan enmata kusan goma zaune ah karkashin wani canopy,fuskarsu duk ah murtuke bbu ko digon fara'a,suna ganin shigowarsu duk suka mike tsaye,,kowacce ta kama kwankwaso ta hau girgije girgije,lura da hakan yasa Jameelah kallon Azeema tare da sakin wani irin shu'umin murmushi tace''Ahh lallai zuri'ar tsoho akwai munafukai sosai aciki,wato ga dukkan alamu ya nuna an kira an sanar musu da cewa ina cikin wa'enda zasu zo daukar amarya ne kuma nasan Ramlah ce tunda tana da kyakkyawar alak'a da kanwar amaryar Nabeelah...!'' cike da rawar murya Azeema tace tana kallonsu''Jaaa...meee..lah gaskia ni..fa bani qaunar rigima arayuwata kawaiiii mu koma waje mubar su goggo su shigo....!'' wani wawan kallo ta wurga mata wanda ya kusan tarwatsa hanjin cikinta tace tana hararata''Meh kike yi haka ne sai kace ba mace ba?Azeema tsoro ba nki bane tunda har kina tare ne da matar dan sanda,don haka ki kwantar da hankalinki ni bbu rigimar da zan mayi dasu ammh one word is enough for the foolssss....!'' ta fadi da jajayen ido wit full seriousness...

   ''Nabeelah wai waccece uwargidan tasa aciki ne?...'' wata mai suna Fa'iza take tambayar kanwar amaryar,ta6e baki Nbeelah tayi kan tace''Itace katuwar cikin abu kamar buhun shinkafa...'' dariya suka fasa dukah kuma iskanci ne kawai irin nata in ba haka ba Jameelah ba katuwa bace kawai she's juz chubby and sexy,kishi ne kawai suke taya yar'uwarsu Hafsah,wata mai suna Ruqayyah tace''Da wannan dariyar banzan da kuka tsaya kuna yi why not muyi saurin taransu tun kafin su karaso inda muke muci kutumar uban hegiya?''

''Tunda ita ta kawo kanta da kanta ba...'' wata Ablah ta karashe,gabaki daya su wajen goman suka nufesu,ita Nabeelar ce dai akarshe don mugun shakkar Jameelah take,agabansu suka tsaya cak!

Cike da tsoro Azeema tace''Haba bayin Allah ya haka?meya faru?

Yasin tsoron Azeema ba karamin haushi yake bawa Jameelah ba,ta kwasheta da wani irin harara tace''Azeema wlh karki bani haushi,kina ganin mutane sunci damarar zuwa wasan dandali irin dai wacce akeyi ah k'auye shine zaki wani tsaya tambaya?hanya ce dai suke neman abasu shiyasa suka tsaya mana kerere aka,,ammh abun ya bani mmki wai ace ana irin wannan wasar acikin gari kamar Abuja,kodayake na manta duk inda kaje akwai kauyawa....!'' jan hannun Azeemar tayi suka ja gefe tana mai watsa musu wani irin mugun kallon daya fadar da gabansu dukah tace''Ga hanya nan ku tafi agaida samarin dandali....!''

Sai suka ji duk kunya ta kamasu don kam gaskia ta fad'a duk wanda ya kallesu tabbas kai tsaye zaiyi tunanin dandali zasu,kukan kura Ruqayyah tayi tare da shak'o wuyar Jameelah tace''Kutmar ubaaaaa! mu zaki ciwa mutunci haka?tou kuwa na rantse da Allah sai munci ubanki da uwarki anan wurin yau tunda ke kika kawo kanki da kanki...!''

Ana cikin haka ne sai gasu Goggo Karime sun danno kai cikin gidan,ganin rikici na neman barkewa tsakanin dangin amaryar da kuma su Jameelah yasa suka nufi wajen da sauri''Kai kai meye haka ku bari,ke sakarta man...'' acewar Goggo Fatoumata,adaidai lokacin manya yan dangin amaryan suma suka nufo wajen don hayaniyar da suke ta jiyowa,bbu wanda ya kula da marin da Jameelah ta yankawa Ruqayyah sbd sauran yan'uwanta da suka rufeta,sai ji kke tass! aka rasa wanda aka mara,,Jameelah ta fashe da kuka tana fadin''Innalillahi baiwar Allah meh namiki haka ne kika mareni?'' cike da mmki ake kallonta hatta wacce ta maran don har kasa magana tayi balle tace zata rama,sauran suka had'a baki sukace''munafuka ta mareki kodai kika mareta?''

Jameelah dai bata tankasu ba sai kuka take mai ta6a rai,manyan na zuwa suka nemi jin ba'asi,anan ne ake musu bayanin cewa ai uwargidan Gidadon ne ita Jameelar,sosai sukayi mmkin yadda akazo daukar amarya da kishiyarta ahad'e ammh basu ce komi ba illa fada suka shiga yiwa 'ya'yan nasu akan don meyasa zasu taresu da fad'a? Ruqayyah sai cewa take tayi ta mareta fa ammh bbu wanda ya kulata sai cewa akayi ma karya takeyi itace ta mari Jameelar,suna ji kuma suna gani akayi ciki dasu Azeemar,Jameelah sai gwalo take ta aika musu dashi ah 6oye...

    ____________★★

Gidado ne yaje can ta bayan gida yana waya dasu Sagir donshi mmki yake yadda sukace masa wai Jameelah tasan gidansu Hafsah bayan bai ta6a kaita wajenta ba balle kwatance,lallai mata kenan yasan tabbas bincike tayi akan Hafsah,shidai addu'arsa dai aynzu shine Allah yasa karta bashi kunya,bayan yakare wayar da Sagir har zai koma can cikin gida sai yaji kamar ana magana kasa kasa ata wani lungu,ahankali yaja jiki ya lafe ajikin bango tare da kasa kunne yana sauraro,muryar Kasim d'an Baba Munniru ne ya daki dodon kunnuwansa,

    '' Don Allah ki yarda da kalaman da suke fitowa daga bakina,soyayyarki ce ke 6oye acikin zuciyata wadda ta zamo sirri tsakanin zuciyata da kirjina,hakika nayi tattalin wannan sirrin da cewa bbu wanda zan fadawa shi sai ke kadai da kika fi cancanta ah zuciyar yan mata,tabbas na zaga zuri'ar nan,ga yan mata nan da yawa acikinta ammh ko kadan banga wacce tamun ba kamarki *MUBEENAH* ,kuma na zabi fallasa sirrin zuciyata ne aduk randa Allah ya kawoki garin Abuja sai gashi ya fad'a ah bikin Hamma Gidado,plsss enmata kice wani abu man don Allah ki amince mu zamo mutane na farko da zasuyi auren dangi acikin zuri'ar nan kinji plsssss na hadaki da Allah Mubeenata ina sonki kuma ina qaunarki....''

Jikinta ne ya dauki rawa sosai,zufa ya shiga tsastsafo mata kota ina don sosai kalamansa suke neman rud'ata,da rawar murya tace''Ham..ma  ka...sim don girman Allah karka ce dani haka,,yabba (haka suke kiran babanninsu) zai mun fad'a sosai don ya hanani tsayawa da samari saina gama aji shidda wai,kuma zanso ka cire soyayyata aranka tun kafin wani yaji ma don kasan ba'a ta6a auren dangi ba ah zuri'armu tou baka ganin watakila asamu matsala idan zancen nan yyi kuskuren fita har akaji? Hamma Ka.....!''

  ''Mubeenah ki gane man! wlh Kasim ya kamu da mugun sonki kuma gaskiya wlh bazan iya hakura dake ba,insha Allahu akanmu za'a fara auran dangi acikin zuri'ar nan,kawai yanzu so nake ki tabbatar mun da amincewrki kar kiji tsoro nida kaina zanje na samu tsoho da maganar kinji?

Ajiyar zuciya ta sauke don idan tace itama din be kwanta mata arai ba tofa tawa Allahnta karya,tace''Tou shikenan naji ammh nidai muyi abunmu asirrance tukunnah zuwa nan gaba idan na kare makarantar saika fito da maganar ammh aynzu gaskia ban bada goyon baya ba....!''

Murmushi ya saki yana kura mata ido cike da zallar shaawarta,yace''Tou gimbiya yadda kikace hakan zaayi nidai amincewarki din dama kawai nake da bukata,tunda kuma kin amince ai komi mai sauki ne,yanzu dai bani lambobin wayarki wanda zamu dunga communicating ta hanyarshi idan kin koma....!''

Wani kasaitaccen dariya Baddo ta saki mai kayatarwa kan tace''Ai yabba ya hanamun rike waya wai saina gama school tukunnah,kaji fa shekaruna goma sha bakwai ammh sai cewa yake wai har yanzu ban mallaki hankalin kaina ba saina kai sha takwas tukun…'' ta ida maganar tare da cuno baki gaba,shi ko sake bin zubin halittarta yyi,komi yaji sai kace ba er sha bakwan ba,girgiza kai yay kan yace''Gaskia kam yabbanmu bai kyauta mana ba,ya zaayi ace zankaded'iyar budurwa kamarki ace bata da waya?yanzu miye abun yi?''

''Abunyi shine ka fita daga harkarta kafin watan soma cin ubanka ya matso kusa kana jina ko?'' ah firgice duk suka juyo kallonsu ya sauka akan Gidado dake tunkaro lungun fuskarsa ahad'e tamk'ar be ta6a sanin dariya ba,gaban Kasim ya shiga dukan chalugud'e,ba shiri ya jingina da bango yana fadin''Hamma Gi.......''

''Hammar kutumar ubanka?yarinya kankanuwa kamar Baddo ce ka jawo zuwa lungu kke kokarin 6atata?eyyy tambayarka nake…!'' ya fad'a cikin tsananin fusata,Kasim yace cikin tsorata''Hamma wlh ba 6atata nakesonyi ba kawai ce mata nayi inasonta da aure…!

Takaici duk yabi ya cika Gidado yace''Sonta?meh yarinya karama kamarta ta sani agame da so?in da gsk kake ma tou meyasa baka gaya mata ah filin duniya ba sai janta lungu kayi wato salon ka yaudareta da soyayyar karyarka ka 6ata mata rayuwa ko?ai duk ina la6e ina jinku kuma na rantse da Allah idan ka sake bari na ganka da ita ah ke6antaccen wuri kaji nace Allah sai kayi kwanan cell bayan na gama farfasa maka jiki da rodi...!""

Gidado yashiga karkad'a yatsun hannunsa biyu yana fadi cike da zafi''Oya tun daga wajen tsugunna ka soma tsallen kwad'o don idan ka bari na matso kusa abun bazai maka k'yau,,maza nace...'' ya ida maganarsa tare da zaro belt din wandonsa yana huci tamk'ar namijin zaki,da sauri Kasim ya tsugunna tare da kama kunnuwa biyu ya shiga tsallen kwadon kuma ta gabanshi zai bi hakan yasa duk ya kara tsorata,ita kuwa Baddo da baya baya ta soma ja tana zubar da ruwan hawaye tare da shessheka,zuciyarta fal tsoro,kallonta Gidado yay yace''Idan kika sake na sake jin shesshekarki Allah saina matso na miki duka black and blue,oya maza kama bakinki....!'' da sauri tasa hannu ta kama le6unanta ammh hawaye be bar zubowa ba,Gidado ba sauki ai saida ya shaud'a masa belt din sau biyu yana fadin''Dan iska mai 6ata yara kawai...'' shi kuwa Kasim aguje yyi cikin gida,kuka ya kufcewa Baddo ganin yana kusanto inda take,ta manne da bango ssai tana fadin''Hamma Gidado wlh shine ya jawoni zuwa nan baa son raina bane don Allah kayi haquri karka dakeni wlh banda ma lfy...!'' yanka mata wawan mari yay yana huci yace cike da haushinta''Shegiya yar iska ashe abunda kikeyi kenan acan kano bamu sani ba?ana yabonki ashe ke din tantiriyace,musa ah fuska fir'auna ah zuci,kaca ne yasa miki ah kafafu ya jawoki nan da kike cewa baason ranki bane?meyasa baki hadashi dasu Yumma,Hajju ko Umminki ba daya matsa kizo,dake kema irinsa ce shiyasa kika biyoshi lungu ku shek'e ayarku da sunan soyayyarka karya ko?''

Wani sabon kukan ne ya kufce mata jin irin mummunar zaton da yakeyi akanta,girgiza kai tashiga yi ayayin da sabbin hawaye ke ziraro mata tace cikin karyewar murya'' _*SULEIMAN…!*_ ka yarda dani wlh _*'MARYAM'*_ da _*'SHAGARI'*_ basu haifi 'yar iska ba,tsautsayi ce kurum ta kawoni lungun nan ammh bawai da nufin iskanci ba kamar yadda kke zato...!'' tana gama fadar hakan tabi ta gabanshi ta wuce zuciyarta na tukuki,shi kuwa jikinsa ne yyi sanyi da kalamanta ammh sai ya fuske tare da doka matsa tsawa yace''K…! ni sa'an wasanki ne da har zaki ambaceni da ainihin sunana kai tsaye bbu girmamawa?kai uban waye yace ma ki kira wannan sunan bayan ba kowane yake da hurumin ya ambaceni da ita ba har sai idan wannan din ya taka wani matsayi ne awajena?…''

Murmushi kawai tayi tana share hawaye ta juyo tace''Kowa ma yana da wannan hurumin ambatarka da ita sai in har bata kama ba,tou ba gashi yanzun data kaman na ambata ba tare da sanin nayi ba?'' tana gama fadar hakan ta wuce abunta ta barshi tsaye nan da tsananin mmkinta,wai shine ayau yarinya karama kamar Baddo ta tsaya tana tanka mishi magana bayan kowa shakkarsa yake acikin zuri'ar nan,ko Kasim dinma ba sa'ansa bane,ya girmeshi nesa ba kusa ba,Kasim befi 25 ko 26years ba balle ita mai 17,kwafa yayi yace''Gaskia yakamata na gyarawa yarinyar nan zama don naga tana neman rainani kafin tazo nan gaba ta bani kunya acikin jama'a…!

    

____________★

Wani abun mamki sai gashi manyan dangin amarya hadda iyayenta sun amshi Jameelah da hannu bibbiyu,aka hadasu ita da amaryar aka musu nasiha mai ratsa bargon jiki,daga karshe aka fito tafiya bayan amarya tasha kukan rabuwa da iyayenta da kuma yan'uwanta,Jameelah rike da hannunta tana ta lallashinta,,Su Nabeelah suka ce sufa basu yadda Hafsah ta shiga motar jameelah ba don basu yadda da ita ba,wasu ma sukace gaskia ne suma basu yadda ba,kalilan ne sukace sufa sun aminta da Jameelar,murmushi Jameelah tayi tace''Tou ai sai wasu su biyomu acikinku idan har baku yadda dani ba,Allah na tuba idan har naso yi mata wani abun ne ai da tuni nayi basai takai ga aure mun miji ba ammh da yake my heart

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login