Showing 24001 words to 27000 words out of 30605 words

Chapter 9 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

tambayar zata ɓata ranki haka ba insha Allahu bazan ƙara ba" riƙo hannunta Granny tayi ta share ƴar ƙwallar data zubo mata tace “ba tambayarki ce ta bata raina ba Kharimatu yanda kika damu da yaron nan Aliyu shi bai damu dake ba don Allah duk hukuncin dana yanke kada kiyimin gardama nasan kinason mijinki nima inasonki dashi zanyi ne don ƙwatar miki yancin ki"
Kallon ƙanwar Mama Yabi Granny tayi tace Saude idan anyi suna zaki tafi da Kharimatu Guru ta zauna acan duk abinda kuke buƙata zan rinƙa turo muku" amsawa Gwaggo Saude tayi da to sukaci gaba da tattaunawarsu itadai jinsu kawai takeyi tana kallon ɗan nata tana share hawayen tausayinsu daga ita harshi
Yaro kyakkyawa ya shigo rayuwar cikin yanayi mara daɗi rabonta da sanya mahaifinsa a idanunta tun cikinsa yanada wata biyu wannan wacce irin ƙaddara ce
Kwana nawa tayi na farin ciki da mijinta meye yasa ya gujeta ya daina bibiyarta.








Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Ma'aruf akayi suna na mamaki kwanaki uku da sunan suka ɗauki hanyar Guru tunda ta koma Guru cikin danginta hankalinta ya kwanta damuwarta ta ragu gata ga ɗanta yanashan gata gurin yan'uwan mamansa Baba Na'ibi ne ya rinƙa kula da ita da duk wani motsinta kullum cikin yi mata rubutu da kawo mata magungunan tsari yake domin ya fahimci bayan rabata da mijin da akayi rayuwarta ma ake farauta don dai kawai tanada ƙarfin addu'a ne kuma ƙaddararta me ƙarfi ce.
Kullum zasuyi waya da Granny zataji abinda ke faruwa Mom ma tana kiranta taji lfyr jikanta duk watan duniya Abba yana tura mata kuɗi sosai shi a burinsa ma ta koma makaranta so ya fahimci Aliyu yanzu bashida ra'ayin karatun mace hakan yasa ya tattara yabar batun karatun.
Watansu takwas a Dubai suka dawo lkcn Salma ta haifi yarta mace yarinyar tazo batada lfy ƙarshe ma ta mutu sosai sukaji mutuwar yarinyar tunda suka dawo zuciyarsa ta koma masa gurin Kharimatu musamman daya buɗe ɗakinta yaga batanan alama ma ta nuna itama ta daɗe rabonta da gdan.
Guri ya samu ya zauna daɓar zuciyarsa na bugawa da ƙarfi sai yanzu yake tuna a yanayin daya tafi ya barta da ƙaramin ciki wata uku gashi kusan watansa tara bayanan tsoro ne ya kamashi ya miƙe yace.






“To me hakan yake nufi Kharimatu nasan yanzu ta jima da haihuwa tun wata huɗu baya, me yasa ba'a faɗa masa ba? To kodai itama mutuwa abinda ta haifa yayi?" Da wannan tunanin ya lalubi numberta ya dannan kiran lkcn tana islamiyyar dake gaban gdan nasu tana koyar da matan aure taji wayar tata tana ring ta zura hannu cikin doguwar rigar atamfar tata me aljihu ta zaro wayar tana kissing Jawad dake hannunta ta ɗora idanunta akan wayar da sauri cikin faɗuwar gaba tace “Aliyu Daddyn Farooq...." Wasu hawaye taji sun silalo mata ta kara wayar a kunnenta tare da yin sallama yaja wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske yace “Kharimatu kina inane Ina ɗana ko ƴata nasan zuwa yanzun kin haihu ko me kika haifamin?" Kallon ɗaliban nata tayi da suma suke kallonta kuka me ƙarfi ya kwace mata cikin tashin hankali ya fara kiran kinga Kharimatu kada ki ɗaga hankalinki faɗamin inda kike bari nazo ko kina gdansu Granny ganinan....."
















*Oum Hairan*
[11/11, 7:50 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ41-42 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566








Ƙit ta kashe wayarta ta juya ta fice daga ajin gabaɗaya ma ji tayi zaman makarantar yayi mata ƙunci wannan tasata barin makarantar ta shiga gda tana shiga Mama Saude ta tareta da cewa “meye kuma yake faruwa Kharimatu" bata iya bata amsa ba ta shige ɗaki ta kwantar da Jawad itama ta kwanta tanaci gaba da rera kukanta tanajin wayar nata ring taƙi ɗagawa.
Mama Saude ce ta ɗauki wayar ganin sunan dake jiki yasata jan tsaki tace “Aikin banza akan wannan sakaran mijin naki kike kuka to kiran me yake miki me zakiyi masa?" Ƙasa tayi da kanta tace “nima bansani ba ina makaranta ya kirani" tsaki ta kuma ja tace “Ki daina ɗaga wayarsa kwata² ki nuna masa kema kinada gata"
Kallonta tayi cikin yanayi na damuwa ta buɗe baki zatayi mgn sai kuma ta fasa har lkcn kiran wayarta yakeyi taƙ ɗagawa ƙarshe ma Mama Saude ta kashe wayar ranar hakanan ta yini sukuku babu ƙwari sai dare ta buɗe wayarta saƙonnninsa suka rinƙa shigowa ba ƙaƙƙautawa bata bata hankalinta wajen buɗewa ba ta gogesu taci gaba da harkokinta washegari da sassafe Mama Saude tace ta shirya zasuje Patiskum taso tayi gardama ganin Mama Saude ta dage yasata hƙr suka shirya suka bar Guru Gidan wata yayar Su Mama Yabi ne da Mama Saude a Patiskum.








Bayan sun huta ne Mama Saude take bawa Hajiya Bushira labarin abinda ke faruwa
jinjina kai Hajiya Bushira tayi ta dubi Kharimatu tace “Kakar mijinki ta kawo shawara dole a cikin ido ake tsawurya duk da lamarinku akwai shiga tsakani amma shima yayi sakacin da sai an nuna masa kurensa zai gane yayi sakaci kiyi hƙr ki zauna anan har zuwa lkcn da tsohuwar nan zata buƙaci ki koma sonki takeyi shiyasa take miki gata" itadai batace komai ba domin ba gurin da zata ce ɗin bane tun farkonta tanajin tsoron masifar Hajiya Bushira shiyasa babu shaƙuwa tsakaninsu saboda bata zuwa gurinta
Da yamma Mama Saude ta tafi ta barsu sukaci gaba da zama a gdan Hajiya Bushira suna samun kulawa Hajiya Bushira akwai son yara ta kame Jawad ta goye kamar dama sun saba Itako hutawarta kawai takeyi tun tana ƙirga kwanaki harta koma ƙirga satittika tafi² har watanni biyar tama hƙr ta fawwalawa Allah ta cireshi a ranta yaronta yanata girma yana neman shekara mahaifinsa baitaɓa ganinsa ba.








Wata rana suka shirya domin zuwa duba Zahra ƙanwar Aliyu data haihu akayi mata aiki ita da Hajiya Bushira tunda suka shigo Kano gabanta ke faɗuwa suna zuwa gdan aka taresu da murna Umaimah ta ɗauke Jawad ta fice dashi sunata mamakin girman yaron da kamarsa da ubansa duk cikin yaran gdan babu me kama dashi kamar Jawad suna harabar gdan tanayi masa lilo motar Aliyu ta shigo tun daga nesa ya zubawa yaron idanu gabansa na faɗuwa dake tare take da sauran yaran suka fito idanunsa akan Jawad da keta dariya.
Yayi kamar ya wucce zuciyarsa taƙi aminta ya koma ya tsaya yana kallon yaron Umaimah ta ɗebeshi ta watsar dake dama ita ba jituwa sukeyi ba.
Bai damu da kallon da tayi masa ba yakai hannu zai ɗauki yaron daidai lkcn da Kharimatu ta fito daga parlourn tagansu tsaye yana ƙoƙarin ɗaukar mata yaro ta ɗaga murya da karfi tace “Karki bashi ɗana Umaimah!" Ba shiba hatta ita Umaiman saida ta juya bata damu da yanda ya kafeta da ido ba ta ƙarasa ta karɓi ɗanta a hannun Umaimah ta juya ta nufi sashin Granny.
Shikam Aliyu mutuwar tsaye yayi yana mamakin yanda yaron ya girma da irin muguwar canzawar da Kharimatunsa tayi cikin lkcn daya ɗauka baiganta ba








Zama yayi a kan lilon ya kora yaran ciki yana tunanin to waishi me yaja masa wannan masifar ne yana son Kharimatu Amma ya yasa gane meye yasa ya kasa kataɓus don ganin ta dawo garesa gashi har ɗan su ya girma baitaɓa sanyashi a idanunsa ba wannan abin kunya da yawa yake shikam baiga laifinta ba data hanashi taɓa mata ɗa shi kansa yanajin kunyar kansa idan ya tuna yanada wani ɗan daya kasa basa haƙƙinsa na ɗa kamar sauran ƴaƴansa.
Miƙewa yayi jiki a mace cikin rashin laka ya shiga sashin Granny suna zaune sun baje a parlourn sunata hirarsu da dariya Jawad nata haɗawa Granny shirgi tana masa tsiya babu wanda yasan dashi a tsaye saida Kharimatu ta ɗago idanunta ya faɗa cikin nasa tayi saurin kawar da kai tare da janyo Jawad ta matseshi a jikinta tasa masa nono yaron ya kama yana dukan jikinta ta lumshe idonta tare da miƙewa zatabar gurin ya kira sunanta da sauri.










Sai lkcn Hajiya Bushira da Granny sukasan wainar da ake toyawa aikuwa Granny ta miƙe da sauri tace “Kai gantalalle lfy?" Sosai kalmar Granny ta dakeshi batajin kunyar aibatashi akan lamarin Kharimatu, cikin sanyi jiki yace “Am dama inason mgn da itane" harara ta zabga masa tace “wa kakeson mgn da ita Kharimatun? Kasanta ne meye alaƙarka da ita zaka ɓacemin da gani ko sai naci mutuncinka"
Tsayawa yayi zaiyi mata magiya ta ɗaga hannu ta ɗauke shi da mari tace “Aliyu bakaiba ko ubanka Ma'aruf bai isa nabashi umarni yaƙi biba Kharimatu ta dawo gdannan inasonta a kusa dani ba makaranta ma xansa Ma'aruf ya siya mata mota ta koma...." Da sauri yace








“Makaranta kuma Granny da izinin wa?" Murmushi tayi tace “ai batada nauyin kowa a kanta aure ne nice dama nayi uwa nai makarɓiya Yabi Allah ya jiƙsnta ta ɗauki marainiyar Allah ta baka dama saida Zahra tacemin Auren sha'awa kayi da Kharimatu naƙi yarda gashinan kuwa a hankali komai ya bayyana daka samu biyan buƙatarka saika banzatar da ita to mu munaso kuma Allah yanason kayarsa daga ita har Jawad ka cire su a lissafin ahalinka Kharimatu ta rayu a gdannan iya rayuwata idan na mutu ta koma danginta na haramta maka ita Aliyu har abada zan kira iyayenka su shaida"..........
















*Oum Hairan*
[11/13, 12:33 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ43-44 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566










Wani abu yaji ya caki ƙirjinsa ya ɗago da sauri yace “Haba Granny meye yasa kike wannan mgnr wlh tallahi ban auri Kharimatu domin cutar da itaba ke shaida ce inason Kharimatu Ni kaina bansan meye yasa na watsar da lamuranta ba" ƙasa yayi ya durƙushe yace “Granny kiyiwa girman Allah ki janye wannan furucin kinsani ina buƙatar iyalina a jikina Tunda Salma ta haihu batada lfy kina gani sai me aiki na ɗauka saboda yar....."
Ɗaga masa hannu tayi ta juya tace “Ka iya tafiya wannan kaita shafa ɗannan ba damuwar Hadizatu bace" kiranta ya rinƙayi taƙi sauraronsa ƙarshe ma ta shige ɗakin da Kharimatu take zaune.
Kanta na ƙasa tana kallon yanda Jawad ya kafeta da ido tana share hawaye lkc zuwa lkc a baya ta hƙr ta cire Aliyu a ranta meyasa yanzu data ganshi abubuwa suke neman jsgule mata meye yasa ko taga laifinsa wani sashi na zuciyarta yake wsnkesa da gaske ne kalamansa shi kansa baisan meye yasa yayi mata haka ba to amma meye yasa ya haɗa harda ɗanta shima an rabashi dashi kenan?








Lumshe idonta tayi Granny na kallonta itama Hajiya Bushira kallonta takeyi cike da tausayi itakam ƴartata tana bata tausayi abubuwa sunyi mata yawa ga maraici ga rashin miji damuwa dole ta samu matsuguni a rayuwarta.
Muryar Granny ta tsinkayo tana cewa kada ki sake ki sawa kanki damuwa akan Aliyu Kharimatu inada tabbacin Allah zaiyi miki sauyi mafi alkhairi tabbas Allah baya wulaƙanta marayansa da yardar Allah duk wanda yake da hannu wajen rabaki da mijinki shima sai Ubangiji ya hanashi jin daɗin tasa rayuwar" kuka ne ya ƙwace mata ta riƙo hannun Granny tace “Wlh inason cireshi a raina na kasa Granny ki tayani da addu'a" shafa kanta tayi tace “mijinki na fari uban ɗanki ai bazai taɓa ciruwa a ranki ba saidai ki koyi dakiya da shariya Kharimatu naji daɗin abinda kikayi masa ko banza ya fahimci kinsan ciwon kanki kema kuma zuciyace a jikinki"
Sunata hirarsu da Granny da Hajiya Bushira itadai kawai kallonsu takeyi tana jan zuciya sai Magrib suka tashi sukayi sallah ta kama hannun Jawad suka fito suka nufi cikin gdan yanata yi mata gwarancinsa tana biye masa. Da sallama suka shiga Mom na parlourn tana ganinsu tayi murmushi tana satar kallon Aliyu dake kwance tun ɗazu tunaninta ma bacci yakeyi sai yanzun da taga ya buɗe idonsa akan Kharimatun tace “Au dama ba bacci kakeba kanaji ana sallah"








Tashi yayi zaune yana kallon Jawad da ya saki Maman tashi ya nufi kakarsa da tafiyarsa da batayi ƙwari ba tararsa Mom tayi ta ɗagashi ta cafe tace “Wato girmanka Jawad yana bani mamaki saikace ana buga maka iska" murmushi Kharimatu tayi tace “Haka kowa yake cewa yayi saurin girma nikam bana ganin girman nasa" dariya Mom tayi tace “Haba Kharimatu shekara ɗaya yaro kamar ya shekara biyu yaushe zaki yayeshi?" Ƙasa tayi da kanta tana murmushi tace “Waida yayi wata ashirin ko ya kika gani?" Jinjina kai tayi tace “Hakanma yayi amma ki cireshi da yayi sha huɗu saboda kinga makaranta zaki koma ga form ɗinki canma Dad ya siyo miki registration káwai zaiyi miki da ɗan abinda ba'a rasa ba saidai makarantar ba anan Kano take ba Alkalam University dake Katsina ya sama miki zaman hostel ya ganki shikuma karatu bazai yiwu da yaro ba"








Miƙewa yayi ya ɗauki wayarsa da key ɗinsa ya fice daga ɗakin babu jimawa daya cikin masu aikin gdan ya dawo ya dubeta yace “Yallaɓai ke nemanki a waje" ɗagowa tayi suka haɗa ido da Mom diririce tace “am in kaje ina zuwa" murmushi tayi tace “tashi kije ya ɗauke miki ɗa kinsan bayason jira zai iya tafiya dashi"
Miƙewa tayi ta fito yana tsaye jikin motarsa sarai tagansa ta kawar dakai tayi wuccewarta Jawad yana ganin ta wucce ya rushe da kuka yana kiran Aunty tanaji Aliyu na ƙwala mata kira taƙi ko tsayawa bare yasaran zata waiwayo ganin haka yasashi binta da sauri dake itan ba sauri takeyi ba baisha wuyar cimmata ba yasha gabanta saura ƙiris ta shige jikinsa tayi baya da sauri yaja numfashi yace “Wai meye ke faruwa ne Kharimatu na zaci idan kowa ya juyamin baya ke zaki kalleni ta gaba" ɗagowa tayi ta kafesa da manyan idanunta ya janye nasa daga cikin nata sosai idanunta keyi masa kwarjini baya jurewa kallon ƙwayar idonta baki ta buɗe cikin sanyin muryarta tace
“Matsa zan wucce" baice mata komai ba kuma bai matsa ba ta canza hanya ya riƙota yace








“Ki fahimceni Kharimatu wlh ba laifina bane bansan matsalar da haɗaku gda ɗaya da Salma zata haifar kenan ba da wlh bazan haɗaku ba kinaji ba kinsani Baba Na'ibi ne yazo bama na ƙasar nan lkcn aka buɗe masa gdana ya shiga suka ƙwaƙule binne binnen da akayi a ɗakinki da ƙofar shiga gdan ko shekaran jiya munyi waya dashi ina faɗa masa matsalata inasonki inason dawo dake cikin rayuwata amma na kasa takawa naje inda kike idan na kiraki baki ɗagawa cemin yayi na jirashi minti biyar babu jimawa ya kirani yace naje ɗakina cikin wardrope ɗina ta tsakiya cikin kayana na birkita sosai akwai wata laya nayi bismilla na ɗauketa na warware na zuba mata fitsari ko ruwan kwata na ƙona ta wannan itane abinda ya raba tsakanina dake. Kharimatu
nayi yanda yace ɗin kuma tun ranar na samu relief ya kasance kullum cikin tunaninki nake Kharimatu ki tambayi Mama Saude cikin kwanaki ukun zuwana Guru biyu tana cemin bakyanan na tambayeta inda kike taƙi faɗa min na dawo na tambayi Granny ta ci mutuncina Dad har marina yayi akanki Mom ce kawai take tausayina cikin lamarinki"








Murmushi tayi me ciwo tace “Naji bani hanya na wucce" yanda tayi mgnr yasashi kallonta yace “Baki yarda ba ko Kharimatu?" Ɗagowa tayi ta kalleshi tayi masa murmushin daya sanyashi sakin baki yana kallonta tace “Ina tunanin saboda ɗanka daka banzatar ka watsar da rayuwarsa ya kasance da mutuwarsa da rayuwarsa duk basa cikin abinda ya dameka kake bibiyata ko? Ok Indai saboda Jawad ne gashinan ka riƙe abinka don Allah ka rabu da rayuwata Aliyu inason Jawad amma na hƙr nabar maka abinka nasani tunda Allah ya azurtani da cikin haihuwa idan Ya nufeni da sake aure zan haifi madadinsa....."
Wata tsawa ya buga mata yana huci jikinsa na rawa yace “Ni kike faɗawa zakiyi aure ki haifi wasu yaran kuma da igiyoyin aurena uku akanki saboda bakida mutumci" bata tsaya sauraronsa ba ta juya tayi tafiyarta tanaji yana kiranta bata juyo ba saima sauri data ƙara ta shige sashin Granny ta datso ƙofar ya iso da sauri ganin yanda Jawad ya ƙara rushewa da kuka.








Granny ce ta fito saboda kukan da ta jiyo Jawad yanayi turus taja ta tsaya ganin Kharimatun zaune a falon tana share hawaye, matsawa tayi gareta ta dafa kafaɗarta tace “Ina kika baro Jawad ɗin nake jiyo kukansa?" Ƙasa tayi da idanunta tace “Ya....yana gurin Babansa" bata kuma ce mata komai ba ta nufi ƙofar ta buɗe ta ishe Aliyu sai rarrashin yaron yakeyi yaƙiyin shiru.
Yana ganinta ya fara miƙa mata hannu ta dubi Aliyu da duk ya ruɗe duk da darene hasken dake gurin ya bata damar ganin yanda idanunsa ya kaɗa yayi jawur tayi juyawarta zatayi tafiyarta ya riƙota yace “kiyiwa Allah kada ku hukuntani da haka kuka yakeyi Granny kuma nono yakesha idan ita batada hankali ta tafi ta barni dashi aike babbace kinsan daidai" fusge hannunta tayi tace “Irin hankalinmu ɗaya Aliyu itama tana buƙatar hutu tunda ba ita kaɗai tayi cikin ba hasali ma kafita ƙarfi lkcn da za'a samu cikinsa domin gashinan ya bayyana kansa duk wanda yagansa yaganka yasan jininka ne kaje ka haɗashi da ƴan'uwansa"
Zuba mata ido yayi kukan yaron yana masa kuɗa a kunne ya juya zuciyarsa na zafi idanunsa sai raɗaɗi sukeyi ya isa motarsa ya buɗe ya shiga har lkcn Jawad kuka yakeyi ɗagashi yayi ya rungumeshi a ƙirjinsa yaron ya ƙanƙameshi yayi luf a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya, so ƙauna da tausayin ɗan nasa yaji yana ratsa jinin jikinsa yanda yaron yayi luf a ƙirjinsa yasa hawaye zubo masa wato shima yana buƙatar duminsa, meye yasa ya nesanta kansa dashi?"








*Oum Hairan*
[11/14, 8:41 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ45-46 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566








Kasa tashin motar yayi yaci gaba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login