Showing 12001 words to 15000 words out of 30605 words

Chapter 5 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

hankali yau fah Aliyu saboda yarinyar nan har tsawa yayi min kuma ya ɗaga hannu ya mareni har yana yimin kashedi akan nace zan kasheta"






Salati Amina tayi tace naga ta kaina Ni Inno ubanwa yace ki nuna masa haukanki bayan kinsan zaki iya nemawa kanki mafita to kiyi gaggawar saita kalaminki kada kija abinda zaiƙi yarda dake ke bakiga abinda ya faru ba lkcn da akayi min kishiya banyi hauka ba amma kwananta nawa?
Numfashi Salma ta sauke tace “Abin da ciwo Amy ƴar aikina fah...." Dakatar da ita tayi da cewa “in kuwa kinaso kici riba kiyi musu kisan mummuƙe to sai kin koyi riƙe kishinki kin jata a jikinki kin nuna mata so da hakane zaki cimma burinki"
Shiru tayi tana nazarin maganganun Yayar tata to ta Ina zata fara bayan ta riga ta bata rawar ta da tsalle bayan hakanma da wacce zuciyar zata iya danne kishin Aliyu harma ta ɗauki Anam matsayin da Amy takeso ta ɗauke ta?








Miƙewa tayi tana zagaya falon zuciyarta na ayyana mata abubuwa da dama ranar taci kuka kamar ranta zai fita hakanan tasa aka ɗebe kayan da tayi watsi dasu aka mayar dasu ɗakin Anam ta zauna ta zabga uban tagumi lkc Zuwa lkc tana duba agogo shaiɗan yana raya mata yanzu saboda Anam Aliyu ya manta da ita ko gdan yaƙi dawowa gashi har yamma tayi.
Ranar tayi dogon yini ita ɗaya damma Amee na kiranta tana sake bata logar yanda zata ɓullowa lamarin da dabarun danne kishi har shawara tabata kan karta bari ya raba musu gda akwai matsala inda ita kuma ta tubure kan cewa itafa batason ma takai ga ya haɗasun, daqyar dai ta samu ta shawo kanta ta yarda da abinda take ɗorata akai sukayi sallama tana shirin komawa sama ya buɗe ƙofar ya shigo ta tsaya suna kallon juna Lumshe idanunsa yayi ya raɓa ta gefenta zai wucce tace “Don Allah kayi hƙr...." Juyowa yayi da sauri ta rusuna a ƙasa idanunta na tsiyayar da hawaye tace “Bayan na dawo gda na kira Hajiya nake sanar da ita abinda yake faruwa shine tayimin nasiha tare da yimin furucin daya kashemin jiki Aliyu ba laifina bane abinda na aikata ɗazu kishin kane da ciwon abinda ka aikatamin amma insha Allahu hakan bazai ƙara faruwa ba nayi maka alƙawarin zanyi iyakar ƙoƙarina na tsare mutuncinka zan....."








Ɗaga mata hannu yayi ya wucce ɗakinsa yabarta shanye da baki ta miƙe ta nuna ɗakin tare da yin ƙwafa tace “akalar raƙumi me sauƙin juyawa zakayi bayani ne tunda ka shigo gonata" shigewa tayi ɗakinta ta kwanta tanata tunanin abinda ya dace ta fara yi.
Aliyu kam koda ya shiga ɗakinsa duniyar ce tayi masa zafi rikici sukayi sosai da Granny akan dawowar Anam gdansa ya kafe saita koma gdansa ita kuma ta kafe saidai su tafi da ita badon ransa yanaso ba haka ya hƙr ya bar su suka tafi da ita fam house nasu saboda Dad yace bazaa nakasa marainiyar Allah ba tunda ya baro asibitin yake ƙuncin zuciya.
Tunaninsa yana ga Anam yanaji kamar yaje ya taho da ita wannan tasa ya kasa saurarar Salma saboda itace taja masa komai.








Wannan dare kwana yayi yana juyi yanajin Salma ta gama bugun ƙofarta ta gaji ta tafi ta qyale shi. Da safe da wuri ya tashi yayi wanka ya fice a gdan ko haɗuwa basuyi da Salma ba ya nufi gdansu a ɗakin Granny ya ishe Anam tana kwance a gadonta tanata bacci kanta daure da bandeji ya tsaya a gaban gadon ya zuba mata idanu tana sanyi da jar rigar bacci iya cinya, ƙirjinta ya zubawa idanu yanajin wani shauƙinta batare daya shirya ba ya durƙushe a gabanta yakai hannunsa ya shafa fuskarta dake cike da suma sajenta ya kwanta luf kan smile face nata yankan manyan idanunta sunfi komai ɗaukar hankalinsa musamman ɗan ƙaramin bakinta,
Irin kallon ƙurullar da yakeyi mata shine yasata motsawa tayi miƙa tare da buɗe ido ta miƙe da sauri tana bin jikinta da kallo tare da jan bargo ta rufe jikin nata miƙewa yayi yana shafa sumarsa yace “Ya jikin naki?" Cikin sakaliyar muryarta tace “Da sauƙi ya kwanan su Farooq" numfashi ya sauke yace “basu dawo ba daga gdansu Salma zasu wucce makaranta idan an tashesu zanje na ɗaukosu zan kawosu su duba mamansu"








Sunkuyar dakai tayi ya sunkuyo daidai wuyanta yace “Granny tanason jamin layi dake Kharimatu na buƙaci ƙara aure ne don ina buƙatarsa Da gaske ina buƙatar kulawarki Please ki saki jiki da mijinki Aliyunki kinji"
Ƙasa tayi da kanta cikin tsoro da jin nauyin kalamansa tace “Nidai inajin tsoron Aunty Salma Daddyn Farooq nafika abin faɗa akanta domin nice nake yini da ita tun kafin ta fara aiki Allah inajin tsoron kada naje ta....."
Rufe mata baki yayi yana mata murmushi yace “babu wani abu da zai faru fa hasali ma tayi nadamar abinda tayi miki jiya har hƙr tazo ta bani"








_Tabbas zuciya tanajin takaici a lkcn da akayi banza da ita kuyi hƙr na jina shiru da kukayi nima ba haka naso ba duk da komai bai kammala ba yanda nakeso zanyi ƙoƙari idan nayi wannan yau gobe nayi wancan har zuwa lkcn da abubuwa zasu daidaitarmin insha Allahu kuyi hqr ku fahimceni musamman yan VIP section daya kamata na rinƙa yi muku post kullum😓_


[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *_MYJ 23-24 Oum Hairan_*




~Paid book~






_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_


_____________________________









Da sauri ta girgiza masa kai tace “Aa Daddyn Farooq nidai hƙrn zakayi shine yafi zame mana alkhairi wlh idan ka matsa saina koma gdannan zan gudu ne...." Kawar da kansa yayi a kanta yayi murmushi yace “dama dai baki kasance me taurin kai ba Kharimatu nine nayi miki alƙawarin babu abinda zai ƙara faruwa makamancin haka zan baki mamaki zan nuna miki na isa da gdana kuma nine me ikon zartarwa a gdana....."
Bai gama rufe bakinsa ba Granny ta shigo tana cewa “Anji kakaki Sarkin zartarwa kazo ka cikata da ɗebabben surutunka tana fama da kanta waini Aliyu yaushe ka koyi naci ne?" Kwantar da kansa yayi a katifar gadon yace “ba naci bane Granny kulawa ce Allah da gaske bansan zan ƙara son wata mace ba a duniya sai bayan da Kharimatu ta zama mallakina Please Granny kinfi kowa ikon zartarwa idan kikace eh dole kowa eh zaice ki taimaka ki amince Kharimatu ta zauna a gdana wlh naji bana sha'awar rabansu muhalli..."








Daƙuwa Granny ta watsa masa tace “Ashe dama yaudarar mu ka shirya zakayi lallai ma ɗannan yaushe ma aka haifeka da zakayimin wayo? Ni Sa'adatu na goyi ubanka amma ace yau ɗan Ma'aru ne zai gwadamin zamani, to ka kiyayeni bana ciki da iskanci Kharimatu ce bani baka har sai kayi mata gdanta domin Ni ba shashasha bace da zan ɗauki marainiyar Allah na baka ka kaiwa mahaukaciyar matarka ta illatata a banza sullutu babu abinda zaka iya sai ban baki"
Sanin cewa tunda tayi wannan furucin babu mai canza mata ra'ayi yasa ya saduda ya dafa cikinsa yace “to shikenan rigimammiyar tsohuwa ku sammin breakfast na karya" harara ta galla masa tace “ina matarka da zakazo ka cinye mana abinci?" Shafa kansa yayi yana kallon Anam yace “gata kin ɗauke min ita ai dama itace me bani abinci kuma kin ƙwacemin ita kinga kuwa hakanan zaki hƙr ki bani na safe na rana dana dare tsohuwa me fashin mata kawai"








Jan maganar yake nema shiyasa Granny ta fice ta rabu dashi ya juya ga Anam da kanta ke ƙasa tunda suka fara mgnr da Granny ya tashi ya koma kusa da ita ya riƙo hannunta ta janye ya sake kamowa ta kuma janyewa kawai saiya janyota gabadaya ya haɗata da jikinsa yace “Idan ya kasance mata zatake gudun mijinta to meye ribar auren Kharimatu?"
Bata bashi amsa ba saima ƙoƙarin janyewa da takeyi ya ɗora hannunsa saman kanta data ɗaure dogon gashinta da baƙin band ya buɗa gurin da akayi mata ɗinkin ya shafa ta rintse idonta yace “sannu kinga Salma tajamin asara an yankemin gashin nan me tsada" yana mgnr yana sunsunar wuyanta daidai lokacin Granny ta turo ƙofar ta shigo Kharimatu ta janye a jikinsa shima ya saketa cike da kunya








Ƙwafa Granny tayi ta aje masa kayan abincin ta kamo hannun Anam tace “muje kisha maganinki" murmushi yayi kasancewar yasan saboda shine ta janyeta shi abinma dariya yake bashi shida matarsa a rinƙa kangeta daga gareshi tsohuwar akwai rikici karyawa yayi sannan ya tafi gurin sabon ginin da yakeyi inda daganan ya wucce gurin aikinsa.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya Anam na samun sauƙi inda surukanta suke kula da ita sosai Hajiya Muniba ba ma'abociyar son taga ɗan nata namiji tilo cikin damuwa bace wannan tasa dole ta tursasa zuciyarta son duk abinda yakeso musamman Anam da ta kasance kusan tarbiyyar su tunda da ita da mahaifiyarta duka a ƙarƙashin kulawar su suka rayu tsayin shekaru,.
Babban abinda yasa suka mayar da hankalinsu ga Kharimatun shine tun auren Aliyu da Salma basu taɓa jituwa da mahaifiyarsa ba Salma batada mutunci bata ganin kowa da gashi Indai akan Aliyu ne har Hajiyansa kishi takeyi da ita.








Satin Mama Yabi biyu a Guru ta dawo lkcn ginin Aliyu yayi nisa sosai dake da masu gidan rana aikin kawai akeyi ma'aikata har kwana sukeyi a wannan aiki nandanan kuwa saiga gda ya kusa haɗuwa inda ya kafa ƙahon zuƙa akan daya gama ginin za'ayi biki abashi matarsa inda Granny it's kuma ta kafe kan saita ƙara murmurewa hakan tasa ya tsiro da wani sabon salon wulaƙanci baya tashi zuwa gdan sai dare idan yazo baya shiga sashin Granny sai ya daidai ci tara ta gota daidai lkcn yasan duk inda Granny take ta soma gyagyaɗi anan yake samu yaje ya takurawa Anam da taɓe² itakuma tayi ta tureshi bataso ko kuma ta sanya masa kuka.
Yauma tun Magrib yazo gdan Granny ce ta shigo ta ishe ta a zaune tana karatun hisnul Muslim ta zauna kusa da ita tace “Wannan ɗan neman ne yazo yake cemin zakuje a gwadaki ɗinkunan lefenki" da sauri ta ɗago tare da zaro ido tana tuno irin rabuwar da sukayi jiya daya matseta a mota yanayi mata magiyar tabashi yaci kaɗan" narkar da kai tayi tace “Don Allah Granny kice masa aa wlh tsoro nakeji" taɓe baki tayi tace “Ni Sa'adatu rufamin asiri da wannan soyayyen ɗan da akayi cikinsa da rana wlh nagaji da fitsarar Gadanga kije mijinki ne ban isa na hanashi iko dake ba kuma ma yau ta sama ya biyo uwarki yaje ya haɗani da ita itane take faɗamin"








Sunkuyar dakai Anam tayi tanaci gaba da gyara ƙumbarta Adama me aikin Granny ta shigo ta rusuna tace “Anam kije inji maigida Aliyu yana jiranki a mota" kallon Granny tayi gabanta na faɗuwa Granny ta kawar dakai tace “tashi kuyi kuje ku dawo kada dare ya ƙara nisa" sunkuyar da kanta tayi tanajin kamar tace bazata ba saidai babu dama.
Ganin batada niyyar tashi yasa Granny ɗauko mata mayafinta tace “bancika son gardama ba batayi miki kyau dake ba ɗabi'arki bace ki tashi yana jiranki" a sanyaye ta miƙe ta sanya mayafin da takalmi ta fito gabanta na faɗuwa. Tunda ta fito ya kafeta da ido ta cikin hasken daya haske harabar gdan zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yana ƙarfafar ƙudurinsa daidai lkcn da take isa ga motar ya budewa Yaran yace “oya ku koma gurin Hajiya idan na dawo saimu tafi gda" da gudu suka shige ciki shikuma ya buɗe mata ƙofar yana ƙarfafar zuciyarsa ta rakuɓa ta zauna a kunyace da irin kallon ƙurullar da yakeyi mata tace “ina yini" ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi yaja motar ya fice daga gdan suka nufi Tarauni anan yabada ɗinkunan nata basu wani daɗe ba telan ganinta kawai yayi yace suna iya tafiya.
Ta sauke ajiyar zuciyar da saida ya kalleta tayi ƙasa da kanta yaja motar suka tafi inda ta ɗago a firgice ganin ya canza hanya maimakon ya nufi Danladi Na Sidi sai taga ya nufi Airport road ta dubeshi da sauri tace “Daddyn Farooq...." Hannu ya ɗora a bakinsa alamun tayi masa shiru hakanan dole taja bakin ta tsuke tafiyar na ƙara tsayi tsoronta yana ƙara bayyana tana gani ya shigar dasu wani babban guri me yalwar haske yayi parking a parking space na gurin suka bashi pass ya buɗe ya fita bai jima ba ya dawo ya buɗe mata yace “fito muje"








Fitowar ce ta bata ikon ƙarewa gurin kallo a fili tace “Hotel Daddyn Farooq me zanyi a hotel?" Bai bata amsa ba ya riƙo hannunta yanajin wutar sha'awar da yake fama da ita kusan wata guda don tunda aka ɗaura aurensa da Anam Salma bata sauraronshi shekaran jiya ma ta tafi Niger yayarta Amee ta haihu janyota yayi ta faɗa jikinsa baya ko jin kunyar mutane a haka suka haura saman ya buɗe ɗakin suka shiga ya mayar ya rufe tare da ɗago kanta ga mamakinsa yaga ashe tuni ta ɓalle da kuka.
Janta yayi ya haɗata da bango ya ɗago fuskarta yasa hannunsa ɗaya yana share mata hawayen yace “Allah yana farin ciki da matar da take sanya mijinta cikin farin ciki Kharimatu don Allah kada ki hanani samun nutsuwa sake Allah feeling ɗina na kwanakin nan dabanne bazan iya control ɗin kaina a yau ba shiyasa na yanke shawarar ɗaukoki ki samamin nutsuwa.............




*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *_MYJ 25-26 Oum Hairan_*




~Paid book~






_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_






_Ina yan kasuwar mu ta online masu so a tallata musu hajojinku to albishirinku Oum Hairan tayi muku tsari me sauƙi domin tallata muku hajojinku cikin farashi me sauƙi su bazu a duniya ku samu customers ɗaga sassa daban² na ƙasar nan dama maƙotan ƙasashe kudai kuyi maza ku garzayo domin jin ƙarin bayani,_
_MORE IMFO CALL 09031307566 OR CHAT ME FOR WHATTSAP NUMBER 09013718241._
_TABBAS ME TALLA SHIKE DA RIBA SAI MUNJIKU_🤗


_____________________________




Janyewa tayi a jikinsa ta koma gefe tana girgiza masa kai yayi murmushi ya cire key na ƙofar ya nufi bayi yayo fitsari ya ɗauro alwala har yanzu tana tsaye inda ya barta yana gyara kwalar rigarsa yace "kinyi sallar Isha?" Ɗaga masa kai tayi ya shimfiɗa sallaya ya tayar da sallar bayan ya idar ya dubeta tare da nuna mata bathroom yace “kije kiyi alwala kizo muyi sallah"
Bathroom ɗin ta shiga ta ɗauro alwalar gabaɗaya a tsorace take dashi kallon da yake mata yafi komai tayar mata da hankali hakanan idan ta tuna haduwarsu kwanaki sai taji tsoronta ya ƙaru, sunyi raka'a huɗu ya dafa kanta yayi mata addu'a ya riƙo hannunta yasa yatsansa a tsakiya yana shafawa a hankali tanajin wani yar a jikinta yayi ajiyar zuciya ya janyo ledar daya shigo da ita ya buɗe sai ƙamshi takeyi tana tururi tsire ne da yaji kayan lambu ya ɗauka yakai mata bakinta ta kawar dakai ya ɗaure fuska yace “banason gardama kinsanni"
Hakanan ta karba sukaci suka sha yasata tayi brush ya fita bai jima ba ya dawo ya miƙa mata rigar bacci ta karɓa tana juyata yace “kisa ki kwanta" ɗagowa tayi idanunta sun cika da bacci da hawaye tace “ka taimakeni Daddy Farooq ka mayar dani gda Allah tsoro nakeji" lumshe idanunsa yayi ya buɗe kawai ya koma jikin window yana kallon ɗaiɗaikun mutanen dake wuccewa ganin bashi da niyyar yi mata abinda take biɗa ne yasata ta janyo duvet na gadon ta shimfiɗa a ƙasa ta janyo pillow ranta a tafashe tayi wurgi da rigar ta kwanta a ƙasan yana can yana kalle²nsa baisan abinda take ba saida ya juyo.








Ganinta a ƙasa ya bashi dariya ya fara rage kayan jikinsa idanunsa na kanta ta dunƙule guri ɗaya sai juyi takeyi, saida ya rage dagashi sai boxes yaje yayi brush ya ɗauki wani body spay ya fesa ya kashe hasken ɗakin ya haye gadon ya kwanta yana me karanto addu'ar kwanciya bacci.
Bawai baccin yake ba don ya ƙwallafa ransa akan abinda yasa ya ɗaukota yau shiyasa baccin ma ya gagareshi, yanajin numfashinta ya sauya ya miƙe ya sauko ya ɗagata cak ya azata a gadon ta miƙe zumbur yayi saurin mayar da ita ya kwantar ya kwanta a gefenta yana ɗaukar wayarsa dake ring ganin number Granny yasashi kashe wayar gabaɗaya.
Ya janyota jikinsa ta janye tare da kai masa duka abin ya bashi dariya sosai yace “Waike meye yake damunki ne?" Batayi masa mgn ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya matseta a jikinsa ta yanda bazata iya motsawa ba taja yaja dole ta sakar masa tanajinsa yana sarrafata yanda yaga dama bata da mafitar data wucce kuka haka ta rinƙa rera kukan duk da yanaci masa rai
Hakanan yaci gaba da tafiyar da ita har ya cimma inda yakeso yaje ta sauke rirriƙeshi tana kuka me ban tausayi tanayi masa magiya da yaruka kala² turanci Hausa barbanci duka shikam baima jinta bare ya fahimceta saida ya ƙarar da mgnrta sannan ya fara samun kansa cikin mintinan da basu wucce 40 ba gabaɗaya ya canza mata halitta ya massheta cikakkiyar mace da wuya da azaba yasata suma








Saida nutsuwarsa ta dawo jikinsa sannan ya fahimci halin da take ciki ya miƙe da sauri ya nufi bathroom ya jiƙo towel ya dawo ya rinƙa mammatsa mata
Jikinta ta sauke ajiyar zuciya tana tsiyayar da hawaye a idanunta ya sauke numfashi ya ɗagota ya haɗata da jikinsa yana shafa bayanta ya kasa yi mata mgn wani tausayinta yana zaga jikinsa daqyar da rarrashi ba furuci ya samu tayi shiru ya taimaka mata tayi wanka ta dawo ya bata paracetamol tasha ta kwanta ya rufeta baccin wahala ya ɗauketa.
Shima kwanciya yayi ya zubanta idanu yana kallon yanda take sauke numfashi a wahalce yana shafa gashin dake kwance saman goshinta da haka bacci ya ɗaukeshi sukayi bacci cikin nutsuwa da asuba ya tashi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login