Showing 18001 words to 21000 words out of 30605 words
Chapter 7 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt
Aliyu ya karɓa ya tusa Kharimatu a gaba yana bata da farko ƙinci tayi saida ya rinƙa amfani da hikimomi sannan ta karɓa tana haɗiyarsa kamar magani yanata lallaɓata abinda ya ƙara tunzura zuciyar Salma ta cije leɓe a ranta tana kissima da aikinta yayi yanda sukaso da tuni ba zancen Kharimatu akeyi ba babban baƙin cikinta da akace mata wai Kharimatu har ɓarin cikin Aliyu tayi to waima yaushe har Aliyun ya zaga har yayi mata cikin? Lallai namiji ɗan babansa ita lissafin ta ma bata yake tun kafin auren yayi mata cikin.
Yini tayi a asibitin tana ƙuncin rai tana haɗiyar takaici tana ganin yanda mijin da yakeyiwa kishi irin na a mutu ko ayi rai yanata lallaɓa wata macen a gabanta bata ƙara ƙuluwa ba sai lkcn da ɗakin ya rage sai su uku can ƙasa taji muryarsa yana cewa da Anam “Meyesa kika ɓoyemin kinada cikina a jikinki har saida ya fita nasan dashi?" Itadai batace komai ba yaja dogon gashinta yace “koda yake kema ba lallai kinsan dashi ba Khary nayi baƙin cikin zubewar cikin nan amma babu komai Insha Allahu da wuri zan sake baki wani ai kinaso ko?"
Idanunta ta sauke kan Salma data sunkuyar da kanta tana danna waya shima ta kalleshi yayi mata murmushi yace “yeah so nake ki ƙarajin sauƙi komai zaiyi saiti" Bazata iya jurewa kalamansa ba hakan yasata miƙewa ta saɓi jakarta tace “ƴaƴana sun kusa dawowa daga school mal zan wucce" miƙewa yayi yana kissing hannun Kharimatu yace “Zan shigo anjima ki kulamin da kanki"
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ31-32 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566
Wani Mugun kallo da Salma ta watsawa Kharimatu saida hanjin cikinta ya kaɗa tayi saurin sunkuyar da kanta inda ita kuma ta fice daga ɗakin ya lura kowanensu da saƙo a zuciyarsa so bayason ɓatawa kansa lkc akan abinda bashi da muhimmanci hakan yasa ya rufawa Salma baya tana tsaye jikin motar sai girgizar bala'i takeyi ya kalleta ya watsar ya shiga yayima motar key ganin alamun zai iya tafiya yabarta yasata shiga ta rufo ƙofar da ƙarfi ya kalleta ya watsar ya ja motar ya bar harabar asibitin.
Sunyi nisa sosai taji bazata iya haɗiye abinda kecin zuciyarta ba tace “Me yasa kakeson zubar da ƙimarka da darajarka gurin yarinyar nan ne Aliyu kai ko kunya bakaji jibi yanda kake wani zaƙewa tana jisgaka....."
Kallonta yayi da gefen ido yace “kunya? Zubar da ƙima?" Kuma a matata ta sunnah waɗannan kalaman suka samu gurbi? Hmmm!" Daga haka yaja bakinsa yayi shiru itama ta tsuke nata bakin badon ta rasa abin cewa ba sai don batason kalamanta suyi yawan da zai fahimci tuban muzuru tayi masa.
Har suka isa gida babu wanda ya sakewa kowa mgn sun jima a wannan yanayin shiyasa abin bai wani dsmunsa ya haye sama ya fara ayyukan dake gabansa bayan ya kammala ya fito ɗaure da towel tana zaune a parlourn ta rafsa tagumi ya matsa gabanta ya sanya hannu ya cire mata tagumin tayi firgigit kamar wacce ta tashi a bacci ta dubeshi yayi mata murmushinsa me sanyata ƙara jin kishinsa yace “Meye yaja kike sanya kanki cikin damuwa ne akan abinda ubangiji ya hukunta Salma kinsan ita ƙaddara tana zuwarwa mutum ne batare da ya shirya mata ba abin buƙatar kawai ka zama mumini na ƙwarai wajen karɓar ta a duk yanayin data faɗo maka mi kyau ko akasinta, bare a aurena da Kharimatu banga abinda zaisa ki damu ba kinsanta kinsan wacece ita batada matsala kusan kece kika raineta so meye damuwarki?"
Ajiye zuciya tayi ta janye kuncinta daga hannunsa ta miƙe ta nufi kitchen yabi bayanta da kallo ya rasa wanne irin mugun kishi ke addabar zuciyar Salma da har yake neman taɓa muhibbar aurenta"
Taɓe baki yayi ya miƙe ya koma ɗakinsa ya dauki doguwar riga yasa ya
fito da key na mota a hannunsa tana tsaye jikin window taji bude ƙofar tasa ta juya ta zubansa ido wani tuƙuki nayi mata zillo a zuciya tunda ta tsaya tunanin ta inda zata ɓullowá wannan baƙon lamari daya faɗo rayuwarta takeyi. batare data shiryawa furuci ba ya kufce mata tace “Aliyu...." Tsayawa yayi yana gyara kwalar rigarsa tace “Ina zaka?" Cikin dakiya ya juyo ya dubeta ya ɗan saki mata fuska yace “zanje nagano jikin Kharimatu ne" ganin yanda yanayin fuskarta ya sauya yasan mgnr ta daketa batare da yayi zaton cewarta ba yaji tace “Ina buƙatar lkcnka inason muyi wata mgn dakai idan ka dawo ka gaisheta kace nace inayi mata sannu" ta faɗa a ƙarshen furucin nata tana aro murmushin yake tanayi masa. Bin ta yakeyi da kallon mamaki da sallamawa yace “Ok ba daɗewa zanyi ba"
Yana faɗin haka yasakai ya fice ta taune leɓe cike da ƙunar zuciya ta zauna daɓar bisa kujerar tana lalubar number Ameey ta ɗaga tana cewa “sarkin ƙorafi yau da wanne akazo?"
Tattara numfashinta tayi ta ajiyeshi waje guda tace “Idan naci gaba da bin shawararki zuciyata bugawa zatayi Yaya Amina mijina ya wucce tunaninki akan yarinyar nan nifa na fara zargin basubar ƙasa haka ba sunbi ta ƙarƙashinta wajen siye zuciyarsa yau da bakiga yanda ya rinƙa yi mata a gabana ba ko kunyar ganin idona baiji halan Malamin nan bai fara aikin bane har yanzu?"
Murmushi Ameey tayi tace “Kin cika gajen hƙr ke yanzu zakice baki fara ganin tasirin aikinmu ba kina gani fah Mal cewa yayi muddin uwar Kishiyarki na raye duk wani sihiri da za'ayi mata bazai yi tasiri ba nice na koma nace masa a kawar da uwar gashi har anyi an gama yanzu kuma nasa akeyin aiki akan ya haɗeku guri guda ta yanda zamufi samun damar aiwatar da abubuwa" Girgiza kai tayi tace “Nifa bangano alkhairi a zamana gda ɗaya da wannan yarinyar ba zuciyata bazata ɗauka ba" “Aikuwa dole ki ɗauka muddin kinason kiyi nasara" cewar Ameey taci gaba da cewa “idan kika lallaɓashi tare da nuna masa amaryarsa tana buƙatar kulawa da tattali duba da rashin Mahaifiya da tayi da kuma lalurar dake tattare da ita kisan dai yanda zakiyi da salo da hikima ya amince ya haɗaku idan ya amince da hadekun ki sanar dani zan sanar da Mal ka iya zai turo baƙaƙen aljanu suyi biso a ɗakin nata muddin wannan abun yana ɗakinta ita da zama lfy har abada zasuyita bata kashi har sai ta gudu da ƙafafunta idan kuwa bata gudu ba to tabbas zasu kasheta kamar yanda suka yiwa Zuhrah Kishiyar Janah ƙawata kedai ki zuba ido kiyi kallo kuma ki koyi kirsar ɓoye kishinki ga mijinki gareta domin muddin kika ɓata takun aiki zai lalace"
Daɗi matuƙa Salma taji da mugun tanadin da Yayar tata take shiryawa kishiyar Tata hakan yasata wani tsallen murna tace “Shiyasa nake matuƙar ƙaunarki My sis ki daɗe kiyi ƙarko Indai dake bamayin kukan baƙin ciki amma fah dole mu iya taku kinsan Hajiya kullum wai wata nasiha takemin wai naji tsoron Allah koda tsoronta nakeji" dariya suka sheƙe da ita Ameey tace “Manta da tsohuwar nan ita kullum bata ganewa aini nuna mata nake nafi Shaikh Sudais tsoron Allah"
Dariya suka kumayi tare da sallama ta aje wayar ta miƙe ta nufi kitchen ya ɗauko juice da cake ta dawo ta zauna tanaci tana latsa wayar zuciyace ta raya mata ta fara aikinta tun yanzu hakan ya bata ƙwarin gwiwar kiran wayar Aliyu ya daga tace “Baby ya jikin Sis?" Kallon Anam yayi yace “Tanajin sauƙi kinganta tanata shagwaɓa bacci ma takeji"
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ33-34 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566
Haɗiye abinda ke damun zuciyarta tayi ta harari gefe tace “Uhm madalla ka gaisheta aje wayar tayi shima ya aje suna kallon juna yace “ki daina zama da yunwa banason zama da yunwa Khary" lumshe idonta tayi ta buɗe yace “Ok bazaki daina ɗinba kenan" ƙasa tayi da kanta tana wasa da hannunta ya riƙo zara²n yatsunta da sukasha lalle ya lumshe idonsa yace “lallai nan yayimin kyau" ɗagowa sukayi tare ya zuba idanunsa cikin nata yace “likita yace gobe zai sallameki kinji sauƙi am idan an sallameki gdanki zan kaiki" da sauri ta dubeshi ya ɗaga mata gira yace “hakan ya kamata zaman nan naki a gda bazai yiwu ba gara kije gdanki kema ki samu ladan aure kamar kowacce mace"
Girgiza masa kai tayi ya sanya hannu ya ɗago fuskarta yace “idan kika koma gdanki zakifi samun nutsuwa" bata iya jayayya ba hakan yasata yi masa shiru yayi murmushi yace “shiyasa nakesonki" ya ɓata lkc a asibitin kafin sukayi sallama da Granny ya tafi tunda yaje gda Salma ta kawo masa abinci ta zauna kusa dashi tana wasa da yatsunsa yana cin abincin suna hirarsu tana dariyar yaƙe saida taja hankalinsa sosai sannan ta ɗago ta dubeshi tace “My Haidar!" Dubanta yayi tare da tattara hankalinsa waje guda yace “yadai My Salmah
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tace “Da zakayimin wannan alfarmar da zanji daɗi sosai Aliyu nayi alƙawarin duk wani abu da kake tsoro bazai faru ba don Allah ka amince dani" aje cokalin yayi ya zubanta ido tare da cewa “Wanne Alfarma kenan?" Sosa kanta tayi tace “Kada ka raba mana gda da Kharimatu saboda yarannan kaga Ni ina zuwa aiki kuma ina yawan tafiye² idan tana gdan zasu zauna tare tunda dama sun saba rainonta ne kuma kaga nan yafi kusa da makarantarsu fiye da can inda kake gini bayan haka kaima sauƙin ka ne komai katashi siye ɗaya zaka siya na amfanin gda memakon idan ka rabamu da komai saika nemi biyu sannan inason mu samu kusanci kamar yanda Hajiyata da Hajiya ƙarama suke inason mu zama abu ɗaya ta yanda zakayi alfahari damu, Amma fah kada ka canza min fassara iyakar gskyta kenan"
Tana mgnr tana cigaba da wasa da yatsunsa.
Zubanta idanu yayi a hankali yakai hannu ya ɗago fuskarta ta lumshe idanunta tare da shigewa jikinsa shikuma ya matseta cike da so yace “Meye ya canzamin ke kikayi laushi haka ne My Salmah naga a farko kin ɗauki abin da zafi yanzun kuma kin sauka da wuri" murmushin bakada wayo tayi masa tace “tausayin Kharimatu ne ya fara canzamin tunani sai kuma nasihar Hajiyata Aliyu na gane abinda kake nufi kaine ka cancanci riƙe maraicin Kharimatu shiyasa naji a raina zan taimaka maka na tayaka riƙon amanar nan musamman da akace Mahaifiyarta kafin ta rasu ta damƙa maka ita amana"
Sosai Aliyu yaji daɗin kalaman matarsa nan take yayi mata alƙawarin haɗa su gda ɗaya da Kharimatu suka tashi sukaje suka kwanta washegari tun safe yasa aka gyara masa daya bangaren na gdan dake dama gdan nasa yanada girma akwai ɓangare ɗaki biyu manya da parlour da toilet a kowanne ɗaki sai kitchen ƙarami batare da ya sanar da kowa abinda suka shirya ba yasa aka ɗebo kayanta da aka shirya a sabon gdan aka dawo dasu nan masu shirya gidaje suka baje fasahar su wajen tsara mata sashin duk da cewar kayan sun yima ɓangaren yawa haka aka shiryasu aka zuba mata wasu a store da yake Alh Ma'aru ya narka mata kuɗi sosai a wancan gdan.
Kwana uku ta ƙara aka sallameta a asibiti da farko sunso tafiya da ita gda suci gaba da kula da ita saidai basu samu wannan damar daga mijinta ba yayi kicin²n ya matse lamba kan saidai abashi matarsa shi ya gaji da wannan galantoyin hakanan da Granny ta fusata tace “ga matarka nan idan ka tafi da ita kasa mata mai da yaji ka cinye ƙarewar so sakarai kawai"
Baiji haushi ba ta fice driver ya ɗauketa shima ya haɗa musu kayansu sai gda tunda suka taho take hawaye har sukazo ƙofar get na gdan yayi horn ta ɗago gabanta yayi muguwar faɗuwa ganin gdan da ya kawota ta dubeshi cikin kaɗuwa tace “Daddyn Farooq gdan Aunty Salma ka kawoni fah" shafa sumarsa yayi ya ɗaga mata gira yace “Gdan Aliyu dai ko Kharimatu tunda Salma batazo dashi a gara ba" numfashi ta sauke yana matsowa jikinta tace “Amma ai ba anan zan zauna ba kace dasu Granny" murmushi ya sake yi mata ya tallafi kuncinta ya ɗora bakinsa saman nata ya lashi lips ɗin ta da harshensa ya ɗago yace “Zanfi samun nutsuwa idan kuna a guri ɗaya kada ki tashi hankalinki bazaki samu matsala da Salma ba ta sauko sosai kinji My Khary"
Ƙasa tayi da kanta cikin zullumi zuciyarta na bugawa da ƙarfi taji ya buɗe motar ya fito ya buɗe mata ta zuro ƙafafunta cikin fargaba yayi gaba tana binsa a baya kamar mara gaskiya ya buɗe falon suka shiga da sallamarsa Salma dake zaune ta miƙe Kharimatu tayi saurin raɓewa a jikinsa domin mugun tsoron Salma takeji abinda yaja sukayi dariya su biyun Aliyu ya shafa bayan Kharimatu yace “My Salma kin tsoratamin mata da yawa" dariya tayi tace “Double sorry Ƙanwata ki daina jin tsorona babu abinda zanyi miki kinji" hannu tasa ta janyeta a jikinsa ta kama hannunta tana mata murmushi suka haura saman.
Ta buɗe mata ƙofar shiga sashin ta yana biye dasu a baya saida ta shigar da ita har cikin bedroom ɗinta ta zaunar da ita a gefen gado tace “amarya kike sak yau gaki a angonki ina fatan hannun bazai hana ku sakewa ba?" A mugun kunyace da al'ajabin canjin na Salma tayi ƙasa da kanta Aliyu dake tsaye yana mamakin yanda matar tasa ta sauko cikin ƙanƙanin lkc yace “sai abishi a hankali ai kinsanni da tausayi" juyowa tayi ta sakar masa murmushi tace nasan wannan yanzu meye zakuci a sama muku?"
Agogo ya duba takwas da minti biyar na dare ya ɗago yace “na hutassheki kema kije ki kwanta ki kulamin da kanki zan fita na samo abinda zamu tari baƙuwar tamu" lumshe idonta tayi tace “Idan kayi hakan zanji daɗi kaje ka dawo zan tayata hira har ka dawo" jinjina kai yayi ya juya ya fice ta zauna kusa da Anam tana kallonta tana saƙa abubuwa da yawa a ranta tana murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa haka suka zauna jefi² tana yima Anam hira itadai saidai tayi ajiyar zuciya domin kuwa zuciyar Tata a karye take kukan ne kawai batason tabashi damar zuwa.
Sun jima a zaune Kharimatu har ta farajin bacci sukaji shigowarsa ya buɗe ƙofar ya shigo da sallamarsa ya aje ledojin ya fara ƙoƙarin cire rigarsa yace “Am My Salmah ki ɗauki leda biyu ki tafi dashi na gde da kulawa Allah yabarni daku a haka" miƙewa tayi ta ɗauka tayi musu sallama daƙyar ta haɗiye abinda yake cakar zuciyarta ta shiga ɗakinta ta kulle tayi jifa da ledar hannun nata ta zube a jikin ƙofar ta ɗora hannunta akanta zata kurma ihu tayi saurin toshe bakinta taja ɗuwawu ta isa jikin gadon ta haɗe kanta da gadon ta saki kuka.
Zama yayi kusa da Kharimatu ya kamo hannunta da hannunsa yakai bakinsa yayi kissing nata yaja fasali yace “ya kikeji a zuciyarki game da wannan sauyin da aka samu a gurin Auntynki?" Ɗago manyan idanunta tayi ta saukesu akansa baisan meye yasa ba baya jure su haɗa ido da yarinyar mugun kwarjinin takeyi masa hakan yasa ya sauke idonsa yace “kiyi mgn" ajiyar zuciya tayi ta yunƙura zata miƙe ya janyota ta faɗo jikinsa yakai hannu ya riƙe hannunta me ciwon ya saita fuskarsa a tata tare da haɗe bakinsu guri ɗaya suka lumshe ido a tare duk da a mugun tsorace take dashi haka ya rinƙa sarrafata bai ƙyaleta ba saida ya samu nutsuwa da ita sosai ya shafa saman goshinta yace “kina da baiwa My Kharry Allah yayi miki albarka" itadai kunyarsa takeji sosai duk da ba wannan ne karo na farko da hakan take faruwa tsakaninsu ba inda sabo ma kusan ta saba dashi a cikin watannin auren nasu baya bata da sauƙi.
Bayan komai ya nutsa ne sunyi wanka ya buɗe musu abinda ya siyo sukaci dakansa ya rinƙa bata a baki sukaci sukayi hani'an sannan sukayi brush Suka sake kwanciya, saime cikin dare kamar wacce aka tsikarawa allura ta zabura ta miƙe cikin wani irin tashin hankali tana furta “A'uzubillahi minasshaiɗanur rajim Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un" shima tashi yayi a firgice ya riƙeta da ƙarfi yana kiran sunanta ta ƙanƙameshi jikinta yana wata muguwar tsuma ƙirjinta sai bugawa yakeyi da ƙarfi.
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ35-36 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566
Kiran sunanta yayi da ƙarfi yana cewa “Me... Meye ya firgitaki haka meye damuwarki" sake shigewa tayi jikinsa tanajan ajiyar zuciya ganin yanda ta fice a hayyaci lkc guda yasashi fara tofa mata ayatul kursiyyu a tsakiyar kanta da addu'o'in neman tsari a hankali yaji zufa yana keto mata zuwa anjima kuma yaji taja fasali ya nitsa hannunsa cikin sumarta yace “Meye ya tsorataki haka My Khary?" Numfashi ta sauke ta ɗago ƙwayar idanunta da suke cike da bacci ta sauke akan fuskarsa ta sake jan fasali ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tace “Wasu irin halittu ne masu kama da gizo² suka biyoni suka ɗafemin jikina suna cizona kuma duk inda suka cijeni rami yakeyi shine inata neman taimakonka kawai kayi tafiyarka ka ƙyaleni a tsakiyarsu inata kiranka kaƙi juyowa"
Shafa bayanta yayi yace sharrin mafarki ne kawai shine kika tashi kina ihu salon ki tashi mutanen gidan oya koma mu kwanta saida safe" komawa sukayi suka kwanta ta sake sabuwar addu'a bacci ya ɗauke ta tana maƙale a ƙirjinsa shikam hakanan yaji zuciyarsa taƙi kwanciya da labarin mafarkinta data bashi koda yaga tayi bacci saida ya sake tofeta da addu'a sannan shima yayi baccin.
Da