Showing 27001 words to 30000 words out of 30605 words
Chapter 10 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt
jijjiga yaron har saida yaji numfashinsa ya sauya ya saukeshi yaga ashe yayi bacci yaja fasali ya kwantar dashi a kujera yaja motar ya fice a gdan zuciyarsa a hassale ya nufi gdansa yayi parking ya fito ya ɗauki Jawad ya kulle motar ya nufi cikin gdan buɗe ƙofar yayi ya shiga dake shi ɗaya ne a gdan ya kwantar da yaron a gadonsa ya zauna ya haɗe kai da gwiwa yanajin zuciyarsa na tafashi lkc zuwa lkc yana furzar da iska me zafi bashi ya kwanta ba sai wajen 1:30am bawai bacci ya kwanta yayi ba tunanin mafitarsa kawai yakeyi.
Bayan tafiyarsa Granny ta koma ɗakin da Kharimatu take ta dubeta tace “meye yasa kika bari ya ɗauki yaron nan?" Ɗago idanunta da suka jima da jiƙewa da ruwan hawaye tayi tace “bansan ya ɗauke shi ba Granny Jawad ya fita wajen parlourn Mom yana wasa anan ya ɗaukeshi" jinjina kai tayi Hajiya Bushira tace “Yanzu ina Jawad ɗin?" Granny ce tace “cewa nayi ya tafi da abinsa itama ta huta...." Zaro ido Hajiya Bushira tayi tace “Ya tafi dashi kuma Hajiya amma kunyi ganganci yanzu idan matar nan da ba ƙaunar Kharimatu take ba ta huce haushinta akan Jawad fah" Murmushi Granny tayi tace “Nasan Halin Aliyu koda Salma nanan bazai taɓa yarda ta taɓa masa ɗa ba balle Bama tanan tana gdansu tana jinya tunda ta haihu ta haɗu da lalura Cancer mahaifa ce ta kamata sai kuma irin ƙurajen da kikayi da cikin Jawad sunanan sun feso mata sai mugunya take zubarwa sunje asibitin sunyi na gargajiyar ance dasu ƙaiƙayi koma kan masheƙiya akayi mata ita tayiwa kishiyarta shine Abin ya dawo kanta"
Zuciyar musulmi sai Kharimatu taji tausayin Salma ya ɗarsu a ranta tace Allah sarki Granny na tausaya mata ciwon nan akwai wahala ubangiji ya bata lfy" taɓe baki Granny tayi tace “karma ta samu lfyr mugun nufinta ne ya koma mata nifa dama bantaɓa ƙaunar yarinyar nan ba wlh bata kwanta min ba shima donta zame masa jaraba ne"
Itadai Kharimatu tunanin ɗanta kawai takeyi ta kwanta ta juya musu baya sai hawaye take sharewa tana tunanin yanda zai kwana babu ita daƙyar bacci ɓarawo ya saceta shima bana daɗi ba da safe ma data tashi duk wani sukuku ta tashi ga nononta ya cika sai damunta yakeyi basarwa kawai takeyi tana duba agogo lkc zuwa lkc kawai so take taji zuwan Aliyu amma shiru har la'asar.
Sai bayan Magrib ya shigo gdan yayi parking tana tsaye jikin window ta zuba masa ido tana ƙare masa kallo cikin hasken daya mamaye gurin sai yanzu take ganin ramar da akace yayi Granny ta Bata lbrn wata tunda suka dawo Salma ta tafi gdansu yaran nasa a gurinsa suke shine komansu Salman da kanta tace bazaa ɗorawa iyayenta wahala ba sosai taji tanajin tausayinsa duk aikin da akace ba naka bane idan aka Barka dashi an jarabci rayuwarka, ganin ya saɓa Jawad a kafaɗarshi taji kamar taje ta kwace ɗanta tana ganinsu suka shiga sashin Mom ta zari mayafinta tayi waje itama ta nufi sashin Mom ɗin tana kai kanta zata shiga shikuma yana fitowa ganintan da yayi yasashi cafkar hannunta da ƙarfin da bata isa ta ƙwace ba ya nufi motarsa da ita suka tsaya jikin motar ya ja numfashi ya ɗago idanunsa akanta yace “Wlh duk girman laifina gareki ban cancanci wannan horon ba Wlh Allah ɗaya Kharimatu da rana ɗaya bantaɓa rabuwa da tunaninki ba don Allah kiyi hƙr ki manta da duk abinda ya faru nayi miki alƙawarin bazai sake faruwa ba har abada insha Allahu"
Zame hannunta tayi ta juya tabar gurin yabita da kallo yana mamakin kafiyar yarinyar a fili yace “dama haka kike?" Tambayar kansa yayi bashida amsa haka ya shiga mota ya tafi ta shiga sashin Mom tana shiga Jawad ya taso da gudu har yana faɗuwa yana fasa baki amma bai fasa isowa gareta ba ta kalli Mom so take ta ɗaukeshi kunyar Mom ta hanata murmushi Mom tayi tace “ki ɗauki ɗanki Kharimatu banda shashancinki meye na barinsa ya tafar miki da ɗa" ajiyar zuciya tayi tasa hannu ta ɗaukesa ta rungumeshi ya ƙanƙameta shima hawaye ya zubo mata tayi saurin sharewa ta zauna suka gaisa da Mom suka taɓa hirarsu Mom tace mata “Kharimatu nafi yi miki sha'awar komawa gdan mijinki fiye da zaman nan da kikeyi Aliyu yana sonki Kharimatu wlh na tabbata bayin kansa bane abubuwan da suka faru da farko naji haushinsa sai daga baya na fahimci sharrin mace ne yasashi aikata duk abinda ya aikata kiyi hƙr badon Aliyu ba domin Allah ki komawa Aliyu kinji?"
Tunda Mom ta fara mgnr take matsar idanu harta gama ta zuba mata idanu tanason taji cewarta, ƙasa tayi da kanta tana wasa da ƙafar Jawad da yaketa ɓaɓɓaka dariyarsa mom ta sake magantuwa da cewa “bakice komai ba Kharimatu ko bakyason zamanku da Aliyun ne?" Hawayen ta share tace “Ba haka bane Mom kawai inajin tsoron kada tarihi ya maimaita kansa Mom banida uwa banida uba banida ɗan'uwa shakiƙi da zanyi magana dashi naji daɗi idan na rasa gatan miji to rayuwata batada wani amfani domin zanyita da ƙunci ƙuncin da zaike azabtar da ruhina Wlh Mom Inason mijina Amma inajin tsoron abinda ya faru ya kuma faruwa" murmushi Mom tayi tace “Indai kinason mijinki to kuwa zaki koma ɗakinki Kharimatu itafa wacce kike wannan abin akanta ma yanzu ba matarsa bace ita da kanta tace saiya saketa wai asiri kikeyi mata akansa mukuma bincikenmu ya nuna mana itace tayi abinta ya koma mata itama mahaifar tata data taɓu taketa zubar da jini ba ciwo ne na Allah da Annabi ba ke akaso ɗorawa abinta ya dawo kanta amma ta kwarzabi kanta shine fa yayarta ta kirashi Suka ƙare masa tanadi kinsanshi shikuma babu hƙr aikuwa a ranar ya raba kansa da ita ta rigashi dawowa ma daga tafiyar da sukayi ashe ita tafi wata biyu a ƙasar nan shine da yaran acan koda suka dawo ma bai sanar damu basa tare ba sai jiya daya kawomin yaran"
Cike da tsoro tace “Mom basa tare fah kikace" jinjina mata kai tayi alamun tabbatarwa tace “harma ta kusan gama idda zanyima Alh mgn yayima Granny magana tayi hƙr ta baku dama ku gina rayuwar ku kinji" Kharimatu dai shiru tayi tana tunano irin mulkin da Salma ta shimfiɗa a gdannan wai yau batanan lallai rayuwa babu tabbas dole kabita a sannu.
Wayarta ce taji tana ring ta zarota ganin sunansa yasata kifa wayar tare da sata a silent yayi kira yafi nawa taƙi ɗagawa shigowa yayi parlourn ya cika da mamaki ganinta zaune arziƙin ɗaga wayar tasa ne babu ya jinjina kai kawai ya fice, bata wani damu ba taci gaba da zamanta saida taji tashin motarsa sannan ta miƙe ta nufi sashin Granny bata gama zama ba Granny tace “Yanzu mijinki ya fita nikam ya sanyaya min jiki harma nayi karambanin cewa dashi yaje nanda sati biyu zaki koma gdanki amma da sharaɗin koda zai dawo da matarsa bazai haɗaku gda guda ba sannan zai barki kiyi karatunki kuma duk ya amince harma yace cikin satinnan zai siya miki mota".......
*Oum Hairan*
[11/17, 9:16 AM] Oum Hairan&Affan: *MYJ47-48 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566
Shiru tayi tana tariyo irin abubuwan da suka faru a baya zuciyarta na ayyana mata idan ta koma fah waɗanda suka fisu zasu iya faruwa ita kanta ta shaida tanason Aliyu saidai tana tsoron rayuwa da asiri komai addu'arka wataran saiya taɓaka tunda ya taɓa ma'aikin Allah hawaye taji ya zubo mata Hajiya Bushira ta sanya hannu ta share mata tace “Haba Kharimatu ai da canma sakaci akayi yanzu kuwa tunda komai ya bayyana ai kije ki rayu gidan mijinki da zuciya ɗaya ki ƙaddara fah komai ya wuce" jinjina kai Granny tayi tace to mema zai faru ai insha Allahu Salma tabar Aliyu kenan har abada"
Kasa furta komai tayi saidai kawai ajiyar zuciya da take
Shawarwari Hajiya Bushira ta jata ta rinƙa bata duk jikinta ya mutu da dare suka kwanta washegari da wuri suka shirya tafiya Patiskum ɗin suna tsaka da shiri ya shigo suka gaisa da su Granny Itako ko kallonsa batayi ba ta miƙe ta shige ɗaki ya jinjina kai ya juya ya fita batare da yace komai ba Granny ce ta shiga ɗakin ta sameta tace “Mijinki yace “Tare zakuje kukai Hajiya Bushira ku dawo da sauri ta ɗago idanunta tace “Mu dawo kuma Granny?" Jinjina kai tayi tace “Eh ki biyosa ku dawo" shiru tayi amma hukuncin yayi mata tsauri sosai batason takura a rayuwarta.
Fita akayi da kayan akasa a Motar suka fita suka shiga yaja suka tafi yanata jan Jawad da wasa itadai ta gimtse ko uhm bata cewa sai bin hanya kawai da takeyi da kallo lkc zuwa lkc tana share hawaye tunda suka taho ya lura da sharar hawayen da takeyi baidai ce mata komai ba zaman kurame akayi har sukaje Patiskum idan anyi mgn a motar to shida Hajiya Bushira ne ko kuma yana yima Jawad wasa suna zuwa ta fita a motar ta shiga gda ta shige ɗakinta sai yanzu ta samu damar yin kuka isasshe ganin rayuwarta takeyi matsayin ƙararrriya wahalar da tasha ta kasa goge mata Allah ya sani badon girma da mutumcin Iyayen Aliyu a gurinta ba da ko zata mutu saboda sonshi bazata sake yarda ta zauna zaman aure dashi ba saidai kash sunfi ƙarfin komai a gurinta dole haka zata zauna dashi tayi hƙr da ƙaddararta
Basu wani jima ba abinci kawai sukaci wajan la"asar yace su fito su tafi Hajiya Bushira dakanta ta rinƙa shirya mata kayanta tare da bata wasu tarkacen mata masu yawa ta rubuta mata yanda zatayi amfani da kowanne ya ɗaukesu suka tafi tunda suka taho lkc zuwa lkc yake kallonta Lkcn da suka shigo Kano ana sallar Isha ya dubeta ya kawar dakai tare da juya kan motarsa zuwa Nassarawa G.R.A ya nufi wani babban gurin saukar baƙi saida yayi parking ta fahimci inda ya kawosu gabanta ya faɗi ta ɗago da sauri tace “Ya haka?" Murmushi kawai yayi mata ya fita tana ƙoƙarin fita ya kulle motar ta zauna ita ɗaya don ya ɗauke ɗansa basu jima ba suka fito ya buɗe mata motar ta fito fuskarsa babu wasa yace mata "muje" babu musu tabisa suka shiga ya buɗe dakin daya kama musu ta maƙale a ƙofa ya shiga ya kwantar da Jawad dake bacci ya tako ya iso gabanta ya riƙo hannunta ya janyota ciki ya kulle ƙofar matsawa tayi daga kusa dashi ya shafa gemunsa yace “Ina mamakin yanda kike son azabtar dani da wata sabuwar ɗabi'a Kharimatu kiyi hƙr badon niba domin Allah babu abu ɗaya da nayi miki don raina yanaso Kharimatu anayin tafi haka ma kuma a dawo a zauna so don Allah ki manta da komai muyi rayuwa me inganci"
Ɗagowa tayi ta zubansa idanu can ta kautar dakai tace “Naji ka bani dama na tafi gda banason hotel ɗin nan daka kawoni idan ka matsa zan ƙara yarda a raina har yanzu banida yanci banida galihun da za'a saurari cewa ta sannan....." Rufe mata baki yayi yace “Ba haka bane Kharimatu taimakona zakiyi don Allah kada ki gaza nasan keɗin me tausayi ce" tubure masa tayi ta zauna ta sashi a gaba ta rinƙa kuka iyakar kalamansa saida suka ƙare gashi bazai iya jure kukanta ba hakan yashi miƙewa ya ɗauki Jawad yace “Shikenan muje Kharimatu" miƙewa tayi da sauri ya buɗe mata ɗakin ta fice suka shiga wamota yanata huci zuciyarsa nayi masa zafi ya rasa yaushe Kharimatu ta koyo kafiya da taurin kai.
Yanayin parking bai gama tsayawa ba ta fice daga motar yabita da kallo tare da murmushi ya fita yabi bayanta suka gaisa da Granny tayi musu Barka da dawowa sannan yayi musu sallama ya tafi.
Yana fita ta faɗa wanka ta haye gado ta kwanta sukaci gaba da hirarsu da Granny har bacci ya ɗauke su. Cikin kwanakin da suka rage mata na komawarta gdan mijinta tasha gyara ba kaɗan ba tare da karɓar mata magungunan tsarin jiki takanas Babanta Mal Wada Na'ibi yazo ya sake kawo mata magungunan tsarin jiki ta kuwa duƙufa yi takeyi sosai yanda ta bashi amanna ko magungunan matan bata basu haka ba,
Yanda Aliyu keta rawar ƙafa yana bata mamaki kuɗi yake kashe mata bana wasa ba duk abinda Granny ta kirashi tace kawo miƙawa yakeyi ranar juma'a ta kama zata tare itadai yinin ranar yinsa tayi jikinta duk babu ƙwari da magrib yazo gdan tana kwance a ɗaki Dad ya Kira wayarta ta ɗaga suka gaisa da ladabi yace taje yanason ganinta.
Tashi tayi ta yafa mayafinta ta fito ta nufi sashin Mom tana falon suka gaisa ta shiga ciki gabanta ya faɗi ganin Aliyun zaune a parlourn ta nemi guri ta zauna suka ƙara gaisawa da Dad yayi gyaran murya yayi musu nasiha me shiga jiki dukkansu saida jikinsu yayi sanyi yayi musu fatan alkhairi yace “idan ƙura ta lafa Aliyu nasa a canza mata admission daga Alƙalam zuwa B.U.K so amma samu angama registration da komai fara zuwa ne kawai nata am ga motar dana siya mata can a rufe d tampol a waje Kharimatu sai a mayar da hankali ayi karatu don Allah kada asa wasa"
Jinjina kai tayi tace “Insha Allahu Dad na gde ubangiji ya ƙara girma da Arziƙi Allah ya rabaka da Granny lfy" amsawa sukayi da Amin suka tashi suka tafi ya buɗe mata mota sai wani baje baki yakeyi yaja suka tafi saida sukaje gdan ta gane ashe sabon gdan daya gina zaisata farkon aurensu ne da ba'a bari yasata ba taja numfashi yayi parking suka shiga ciki suna shiga ya ajiye Jawad ya janyota jikinsa ya rungumeta ya sauke ajiyar zuciya yace “Allah shine mafi soyuwa daa godewa Allah na gde maka daka sake dawomin da Kharimatu na cikin rayuwa ta"
Yanda ya rinƙa lallabata ya tabbatar mata yau saidai ƙwacen Ubangiji ne zai fitar da ita aikuwa hakance ta faru bayan sunci sunsha komai ya lafa suka shiga domin kwanciya ta kwantar da Jawad ta cire kayanta tasa na bacci ta haye gado ta ja bargo tare da rungumeta ɗanta yana kallonta baice mata ƙala ba yaci gaba da danne²nsa a system ɗinsa bayan ya gama ne ya tashi ya shiga bayi yayi wanka ya ɗauro alwala ya dawo ya haura gadon ya janye Jawad yamai dashi gadonsa ya shige gurin daya ɗauke yaron ya fara shafa fuskarta zuwa ƙirjinta tana jinsa ta shareshi kamar bataji ya rinƙa sarrafata yana wasa da ita dole saida ya kamata a hannu wannan dare Aliyu ya kwashi gara itakuma taci wuya lkcn da zaiyi release yanda ya ƙanƙameta kamar zai tsaga jikinta ya shiga sun jima a haka sannan ya janye jikinsa ya koma gefe.
Dole ce tasa ta saki jikinta dashi suka ɗora rayuwarsu fiye ma data baya satinta uku da dawowa gdan ta kama zazzaɓi me zafin gaske duk dauriyarta saida suka dangana da asibiti aka bincikata sosai suka tabbatar musu shigar ciki ke gareta wata runguma da Aliyu yayi mata saida ya bata tsoro ta ƙanƙameshi yayi kissing nata yace “Wlh ranar da muka fara haɗuwa cikin nan ya shiga Kharimatu naji yanayina dama ya bani hakan zata iya faruwa ubangiji ya raya mana ya inganta"
*Oum Hairan*
[11/17, 10:33 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ49-50 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566
Lumshe idanunta tayi yajata ya zaunar da ita likitan ya rubuta mata magunguna ya fita ya siyo ya dawo suka tafi kwanaki kaɗan komanta na makaranta ya kammala da farko Aliyu so yayi ya hana wai sai ta haihu Dad yace kada ya soma yabarta tayi karatunta dole haka ya barta amma ya hanata jan mota saidai ya kaita idan lkcn tashinta yayi yaje ya ɗaukota cikin watannin koma ya saitu ta sanyashi ya ɗebo mata yaran duka ta haɗasu su huɗu a gabanta ta riƙe dama dake sun saba da ita basu wani samu matsala da ita ba sukaci gaba da rayuwarsu kamar baya.
Sannu² lkc yayita shuɗewa har ubangiji ya nufeta da haihuwar yaranta biyu duka maza aikam yaran sunga gata bayan suna da sati ɗaya da safe suna falon suna hirarsu dake ranar ta kama asabar ce Aliyu yana gda yaran ma dukkan sunan knowking na ƙofa akayi ta miƙe ta buɗe gabanta ya yanke ya faɗi cikin firgici tace “Aunty Salma!" Dukka har yaran suka ɗago suna kallon me shigowar ta ƙara so a duke kamar tsohuwa ta zube a tsakiyar falon.
Wani wari ya dumame gurin yaran suka tashi da sauri suka gudu Farooq yana cewa “Aunty mu mun gudu bamason ganin dodon nan Jawad zo mu gudu Aunty ki bani twins mu tafi sama dasu" hawaye Salma ta share cikin kuka tace “Me yajamin banda nadama nayi jayayya da hukuncin ubangiji Yaya Ameey ta ɗorani a muguwar hanya gashi nice na kwana ciki inason mijina tasani na rabu dashi na rabu da ƴaƴana Kharimatu duk akanki baƙin kishina yajamin na nayi muku asiri akan idan kun tafi hanyar zuwa Guru lkcn bikinku kuyi hatsari ku mu dake ƙaddararki bata mutuwa bace kika tsallake saidai haƙƙin ran mahaifiyarki daya rataya akaina babu wanda yasan wannan haka nayi amfani da damar na yaudari mijinki ya amince zai haɗamu gda ɗaya da nasa aka turo manyan shedanu da zasu illataki daƙyar suka samu damar shafsrki suka zuba miki firgici wannan bai isaba nasa aka turo miki lalura sannan nasa a kashe ɗan cikinki bansan ya akayi ba duk abubuwan dana ƙulla suka dawo kaina na juyar da hankalin mijinki na janyeshi munbar ƙasar a lkcn da bakida lfy ashe kaina nayiwa memakon ɗan cikinki ya mutu tawa ce ta mutu