Showing 9001 words to 12000 words out of 30605 words

Chapter 4 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

ranta take tambayar kanta wai dama haka auren yake ko kuwa ita natane yazo a haka? Ranta yana raya mata anya Bama daɗin bakinsu bane na maza yazo yayi mata domin ya samu biyan buƙata? Miƙewa tayi da sauri ta lalubo akwakun wayarta ta danna number Mama lkcn ɗaya ta wucce na dare har tayi ring ta gama ba'a ɗagaba hakan yasata yanke shawarar kiran Granny tasan ita zata iya samun ta tunda ma'abociyar tsaiwar dare ce yawanci a gurinta ta koyi abubuwa da suka shafi ibada duk da yake iyayen ɗakin Mama basuyi mata mugunta ba sunsata a makaranta ta samu ilimin addini daidai gwargwado.
Cikin saa kuwa tana kira ta shiga kafin ta katse aka ɗaga akace “Amaryar bazata dan ƙaniyarki ina kika baro angon kike kiran mutane a tsohon daren nan ince dai lfy" wani yawu ta haɗiya muƙut cikin sarƙewar murya tace “Wai....wai da gaske Daddyn Farooq yakeyi Granny meyesa kuka amince kuka haɗa wannan......"
Katseta Granny tayi da cewa “Ke banson sakarar magana inace da amincewarki yazo ya sanar aka ɗaura...." Rushewa tayi da kuka tace “Wlh tallahi bansan komai ba bansan haka yake nufi ba ni cemin yayi wani mutum Granny nashiga uku tayaya zan rayu da Daddyn Farooq matsayin miji ta yaya zan zauna da mijin Hajiya Salma wlh Granny bazan iya rayuwar aure a gdannan ba itama wannan rayuwar kawai don nasan lkc ne watarana zata wucce ne shiyasa Please Granny kiyi wani abu...."






Gwauron numfashi Granny taja tace “Eh lallai wannan ja'irin yaron ya shammacemu yayi mana bazata to hakanan zaki hƙr bamuda wani abin yi tunda wuƙa da nama na hannunsa" kukan take rerawa me ban tausayi daya sanya Granny kasa kashe wayar ta rinƙa bata baki da aikin rarrashi ganin batada niyyar hƙr da kukan yasata cewa “dadai kin hƙr kin daina wannan kukan duk abinda Allah yayi Annabi sai ceto Kharimatu banji a raina zakiyi nadamar wannan aure ba domin kuwa da so da ƙauna ni na jima da fahimtar akwai wani abu da ubangiji ya ɓoye tsakaninki da Aliyu saboda haka ki kwantar da hankali kibi komai a sannu na faɗa masa karnaji karna gani ya bari komai ya tafi yanda akeso tunda yace gini zai fara to yayi ginin idan ya gama sai ayi biki abashi ke"






Cikin Muryar kuka tace “To... to Granny don Allah kiyimin alfarmar na dawo nan gdan nikam bazan iya ci gaba da zama anan ba Mmn Farooq zata iya illatani babu wata alaƙa ma tsakanina da mijinta ta nemi sabauta ni idan ta fahimta kasheni zatayi"
Murmushi Granny tayi tace “yaro man kaza shikuma naku zaman da haka zaayisa ai shikenan da safe zan kirasa ki kwanta Allah bamu alkhairi" tana shirin mgn taji ta datse layin ta jefar da wayar ta faɗa katifarta taci gaba da kukan rashin mafita gyara kwanciyarta tayi saboda nononta da yakeyi mata zugi ya matsesu sosai ciwo sukeyi mata ga ƙasanta daya sossoka mata yatsansa shima sai zugi yakeyi, gara tabar gdan gabaɗaya Bama ya ganinta bare ya rinƙa lalubeta tsautsayi yasa Salmah ta ritsasu wataran ta baƙunci Lahira babu tsammani


*********
Washegari da safe kamar yanda ta saba ta riga kowa tashi tun kafin kowa ya fito ta fito tayi aikace²nta ta shiga kitchen ta ɗaura break saida ta gama ta gyara inda ta ɓata sannan ta koma ɗakinta tayi wanka ta shafa mai cikin mayukan daya siyo mata jiya ta fesa turare ta koma ta zauna tana lallatsa wayarta.
Ji tayi an buɗe ƙofar ta ɗago da sauri suka haɗa idanu fuskarsa a ɗaure hakan yasa gabanta faɗuwa ya kulle ƙofar ya nemi guri saman kujerar dake ɗakin ta sauko ƙasan cikin rawar murya ta tsoro tace "ina kwana" numfashi ya sauke yace “Yaushe kikayi waya da Granny??" Sunkuyar dakai tayi jikinta na ɗaukar rawa takaici ne yasashi buga mata tsawa yace “inayi miki mgn kina yimin rawar jiki banson sakarci"
Kukane ya ƙwace mata yaja zuciya ya miƙe yace “kince mata wani abu ya faru ne?" Girgiza kai tayi da sauri ya sauke ajiyar zuciya yace “ok to meye yasa tace na mayar dake can?" Cikin “in...ina tace “ni nace mata inason komawa don Allah ka barni na koma bazan iya zaman nan ba tsoro nakejin"






Zubanta ido yayi yace “idan kuma ban amince bafa?" Da sanyin jiki tasa kanta saman katifar ranta babu daɗi ya miƙe ya zari kuɗi a Aljihunsa ya ajiye mata saman katifar yace “zanje yau za'a saka foundation na ginin gdanki" itadai batace masa ƙala ba ya fita yana fita ta kulle ɗakin taci gaba da kukanta tana kiran wayar Mama amma taƙi ɗagawa ƙarshe ma tajita a kashe dole saita ƙanin Maman ta kira suka gaisa tace ya kaima Mama koda aka kai mata ta karɓa jin tanata kukane yasata cewa “Naji a jikina hakan zata faru shiyasa naƙi ɗaga wayarki tun daren jiya Kharimatu babu abinda mutanen nan zasu nema a gurina muddin inada iko akansa na kasa basushi abinda nakeso dake ki ninka hƙrnki sannan kiyi biyayya zakiga ribarta a gaba domin Allah ki riƙe maraicinki kuma ki dage da addu'a Insha Allahu komai zaizo muku da sauƙi"








Nasiha sosai Mama ta rinƙa yimata har saida taji ta daina kukan sannan sukayi sallama ta aje wayar daidai lkcn da taji Salma na ƙwala mata kira ta miƙe a saluɓe ta fito suna zaune a dinning table na gdan ita da Aliyu kansa yana kan cup ɗin dake gabansa yana jujjuya kunun gyaɗar dake ciki inda Salma ta kafe Anam da manyan idanunta masu firgitata mamakin yanda ta iya ratso parlourn batare da ta sanya hijjab kamar yanda ta sharɗanta mata ba takeyi gashi doguwar rigar blue tayi mugun yimata kyau ta fito da asalin surar ta hips ɗinta daya daɗe yana tsonewa Salma ido take baƙin ciki dashi da ɗuwaiwakan Anam sai rawa sukeyi ga uwa uba boobs ɗin ta masu ɗaukar hankali.
Batasan ta ƙara so ba saida taji dukan siririyar muryarta a kunnenta tana cewa “barka da safe Aunty fatan kin tashi lfy" wani Gwauron numfashi Salma ta sauke tace “wato kin fara rainani Anam saboda kina ganin makwanci na waima waye yabaki damar yawo a gidan nan babu hijjab...."
“Nine....." Taji ya faɗa idanunsa nakan Anam yar sarkin tsoro da jikinta yaketa rawa... Kujera ya nuna mata yace “zauna anan kiyi break...." Wani kallo Salma takeyi masa na tsananin mamakin yanda yake neman zubar mata da ƙimsrta gurin yar aikin nasu tace “meye hakane Aliyu kwana biyun nan na fahimci kana takurawa da yawa akan Anam a gdannan ko aiki nasata sai kace bazatayi ba wai so kake wannan yar talakawan baiwa da suka tsiru suka rayu a bauta ta raina......"








Wata muguwar tsawa ya daka mata ya miƙe a hassale da fushinsa na Aliyun gaske yace “meye bambancinki da ita Salamatuh bambamcemin abinda kika fita asali ko nasaba? Ƙaryane baki fita da ko ɗaya ba saboda haka karna ƙarajin kin ambaceta da wannan kalmomin Abun da yasa kuma na sanya kika kirata itama tanada haƙƙi akaina ne kamar yanda kikejin kinada shi nayi niyyar ninkeki a baibai har zuwa lkcn da komai zai fasu ne so na fahimci idan nayi haka zan cutar da sashi akan sashi Salamatuh ki sani ki shaida Kharimatu matar Aliyu Ma'aruf Gusau ce hakan na nufin matsayinku ɗaya daga yau na haramta mata duk wani aiki da takeyi a baya da yasa kike ganinta matsayin baiwa ta ƴantu sannan daga yau tabar wannan ɗakin na ƙasa zata koma sama itama taci ɗakin matar gda, tanada kwanaki bakwai da shari'a ta bata na budurci zata shigesu daga......."
Wani ihu yaji Kharimatu ta saki daya sanyashi katse mgnr da yakeyi yayi kansu a guje ganin yanda jini yake malala a saman kanta Salma ta kuma rarumar wuƙa bayan flat na glass data buga mata yayi kukan kura ya tareta aikuwa ta zuge masa hannu da wuƙar inda yayi nasarar csfketa.............










*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?




~Paid book~




Oum Hairan




Last Free Page19-20




_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafai ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_


_____________________________



Kokowa sukeyi sosai a burinta na ganin ta daɓawa Kharimatu wuƙar dake hannunta inda shikuma ya riƙe ta gam da hannunsa dake zubar jini Aliyu wata irin zuciya ke gareshi da idan ransa ya ɓaci baiji bai gani hakan tasa yayi watsi da Salma cikin rashin saa take kanta ya daki corner table nandanan jini ya wanke mata fuska itama.
Baiko bi takanta ba yayi kan Anam data rakuɓe bayan kujera jikinta sai tsuma yakeyi. Jin takun tafiyar ne yasata saurin miƙewa zata zura da gudu yayi saurin riƙota ya jin ɗumin hannunsa yasata rushewa da kuka ta rusuna tace “Ni.... Aliyu bansonka wlh banson aurenka ka taimakeni ka rabani da kanka kada ta kashe.....








Jan hannunta yayi ya wullata bayansa jifan da Salma ta kawo mata ya wucce yaje ya daki tv ta kumayin kukan kura ta kawo mata cafka ya tureta inda ita kuma Anam take ta kuka ta ƙanƙame Aliyun hakan ba ƙaramin tashin hankalin Salma yayi ba Aliyun zaiyi mgn ta dakatar dashi tace “wlh saina kashe yarinyar nan inyaso nima a kashe ni.... Cije leɓe yayi yace “kin rantse zaki kasheta nikuma na rantse kema zaki mutu labari zai canza za'a daina bada lbrn kishiya ta kashe kishiyarta tana jiran Shari'a zan barwa duniya tarihin matata ta kashemin amaryata nima na kasheta mu zuba Ni dake shege ka fasa kuma kiji ki sani banyi niyyar haɗaku gda ɗaya ba amma zan baki dama ki gwada abinda kike shiryawa Salma Kharimatu dai tariga ta ɗago matsayinku ɗaya da Aliyu kike taƙama itama shine bangonta"
Cikin tashin hankali tayo kansa tace “Shine me ka kashenin banida asara Indai na kashe wannan shegiyar yarinyar wlh dadai na zauna dakai wannan ƙazamar yarinyar tana matsayin matarka gara ace ka kasheni ɗin ko banza burina ya cika.








Wafta takaiwa Anam ta kwasa a mugun guje tayi waje inda suka dasa tsere a harabar gdan shi yana ƙoƙarin riƙeta ita kuma tana ƙoƙarin tsira daga Salma dake farautar rayuwarta inda Salma ta zage takecin uban gudu a burinta na kamo Anam ɗin.
Ubangiji ne ya dubeta ya bata saa ta isa get ɗin a guje megadi bayanan ta fice a speed tana cin uban gudu kamar zata tashi sama idanunta na tsiyayar da hawaye. ganin ta fita a gdanne yasa Salma zubewa ta rushe da mahaukacin kuka tana cewa Allah na shiga uku kishi da ƴar aikina meye nayi maka daka jarabceni da wannan masifa......
Bata gama surutun ba taji tashin motarsa ya fice a speed ta miƙe itama da sauri ta shiga gdan ta zari mayafinta tayo waje ta shiga tata motar ta kwasa a million saidai ko ƙurar Aliyu bata gani ba hakan yasata tunanin ina sukayi to?
Yana bin bayanta ya hangeta saicin uban gudu takeyi ya rinƙa danna mata horn ita kuma tana ninka gudunta kamar barewa daqyar yasha gabanta tana ganinsa ta juya zatayi baya ya cafki hannunta da sauri aikuwa ta rintse idonta ta saki wata mahaukaciyar ƙara abinda yaja hankalin mutane suka taru a gurin.








Bai lura da yawan mutanen ba yace “meye hakane Kharimatu nine fah mijinki Aliyunki ne fah....." Cikin firgici da ficewar hayyaci na wanda ya gama tsorata tace “Wlh bansonka ba mijina bane kai ni nabarwa Salma dama kaiɗin natane da ita ka dace......"
Ƙum sukaji an ƙuma mata wani ƙaton abu tuni tayi baya luuu yayi saurin tareta ta zube a hannunsa babu alamun motsi a tare da ita, hankali a tashe ya ɗago yaga Salma ce sai huci takeyi riƙe da wani ƙarfe a hannunta yace “Sal.... Salma kin kasheta na shiga uku mahaukaciya ce ke kin kashemin mata....." Sai yanzu mutanen dake gurin suka fahimci abinda yake faruwa nandanan suka fara hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakinsa inda Salma ta nuna Aliyu da yatsa tace “Munafuki Azzalumi saura kai kaima zaka tafi inda ta tafi badai Ni kaci amana ba Aliyu iya hakama ka cuceni karasa wacce zaka aurarmin matsayin kishiya sai ƴar aikina....zabura ta kumayi tayo kansa wani mutum yayi kukan kura ya riƙeta yana cewa “haba Hajiya wannan ba girmanki bane....." Ɗaukeshi tayi da mari tace “girman durun uwarka ne aci amanata kace ba girmana ban...."







Ƙura ce ta buɗesu tana juyawa taga Aliyu ya ɗauke Anam sunbar gurin da mugun gudu itama mota ta shiga tabi bayansu bata hangeshi ba gashi ta kasa gane hanyar da yabi zuciyarta ce ta raya mata tayi dama inda shikuma yayi hagu domin kai Anam ɗin ga likita yana shiga asibitin ya saɓeta kamar ƴar jaririya ya nufi ciki da ita likitocin sukayi mata cahhh tashin farko takardar ofishin yan sanda suka fara nema, kansa gabaɗaya ya kulle daƙyar dabarar kiran wayar Nazeer tazo masa ya sanar dashi abinda ke faruwa take yace masa gashinan.
Babu ɓata lkc sai gashinan da ɗan sanda guda ɗaya sannan suka shiga da ita suka fara treatment nata saida sukayi mata ɗinkin a gefen fuskarta inda Salma ta yanketa da glass sannan suka gutsire gashinta ta tsakiya inda nanma ta ƙwala mata ƙarfe suka wanke gurin suka ɗinke.








Har hawaye Aliyu yayi mata na tausayi sosai ya rinƙa jin haushin Salma da kuma kansa da ace ya amince da shawarar Granny ƙila duk da haka bata faru ba da yaji roƙon da Anam ɗin ta rinƙa yi masa da tuni hakan bata faru ba yanzun gashi saboda kafiyarsa ta tsiya yajama yar mutane wahala.
Dafashi Nazeer yayi yace “Ka zama namiji Zaki karka manta kirarinka kenan Alee gadanga ƙusar yaƙi kada wannan haukan ya firgitaka idan ka karaya burin wannan mahaukaciyar matar taka ya cika ta samu yanda takeso am Amma ni Ina ganin kawai ka mayar da yarinyar nan gdanku gurin mahaifiyarta idan ma kana buƙatar wani abune sai kayi ƙoƙari ka sama mata gurin zama ayi biki ta tare a gdanta ka zuba mata masu gadi har zuwa lkcn da waccen mahaukaciyar zata gaji ta gama haukan ta hƙr amma kai ya kake gani?"








Zuciya yaja yace “Haksne mgnrka saidai zuciyata tafi aminta da haɗesu guri ɗaya duk rigimar da za'ayi ayita inanan Nazeer Salmah cikakkiyar mahaukaciya ce akan kishi na yarda zata iyayin komai idan na rabasu dole zan tafi nabar Kharimatu duk ranar da bana gdanta za'a iya amfani da wannan damar a cutar da ita idan kuwa gda ɗaya muke rayuwa ina ganin komai zaizo da sauƙi.....
“Ba wani sauƙi” abinda Nazeer yace kenan ya tashi tsaye yace “Idan ka haɗasu guri ɗayan zaka rinƙa yini dasu ne?" Girgiza kai yayi Nazeer yace hakan ce tasa akafi maka sha'awar nesantasu kowacce zata manta da kowacce" murmushi yayi yace “hakanne banaso nikuma"










Shiru Nazeer yayi masa tunda ya riga yasan halinsa Indai ya kafe akan abu wuya batasa ya janye, Granny ce ta ido p asibitin tanata sababi ita da Hajiya Muniba na tujarar da Salma taje tayi musu Granny tace “Ɗannan waini matarka ta kalla tacewa munafuka tsofe² dani na haifi ubanta" shidai kasa mgn yayi nan Nazeer yake mayar da yanda akayi kamar yanda Aliyun ya sanar dashi aikuwa Granny tayi tsalle ta dire tace “Kajini da Tankaɗaɗɗiyar yarinya zata nakasa yar mutane dama Muniba ashe ita kaɗai kika haifawa Aliyun da take neman kisa akansa?"
Ƙasa Hajiya Muniba tayi da kanta tace halin kishi dai irin na wasu matan da basu da lissafi da control ɗin zuciya akansa in banda haka meye abin tashin hankali akan Kharimatu Ni ganin ma da nakeyi batakai kishiya ba yarinyar nan....."
“Eh aifa dama Dole kice haka mana tunda ba Abida aka ɗaukarwa ba idan batakai kishiya ba kisa gyatumin mijinki ya auro......"






Dafe kuncinta tayi da sauri saboda wasu faya fayen maruka da Aliyu ya sauke mata a kuncinta ta saki ƙara tare da matsawa baya ya nufota cikin muguwar Hassala yayi ball da ita ya rinƙa ƙoli da ita har wajen asibitin yace “Zan iya ƙyaleki akan duk wani rashin mutumcinki amma ki kiyayi abu biyu taɓamin iyaye da kuma ƙara gigin taɓa lfyr Kharimatu....." Miƙewa tayi tayi kansa tace “inkaga dama ka kasheni bazan fasa ƙudirina akanta ba wlh Indai baka saki yarinyar nan ba saina kasheta" murmushin takaici yayi yace “na roƙeki karki fasa kiyi duk abinda zakiyi abinda kike baƙin ciki akansa saita jishi a jikinta kuma itama saita haifamin kamar yanda kika haifa kekam na daɗe ina nadamar auren jahilar mace irin ki tabbas aurenki jalabi ne gareni ba alkhairi ba wawuya mara lissafi to waima ke a haukanki wannan ce zatasa nafasa abinda nayi niyya? To kuwa ki canza tunani domin na fahimci ko a makaranta ta ƙarshe kike ɗauka shiyasa kike tunanin barazana zata canzama Aliyu ra'ayi"..........


*_21-22Oum Hairan_*




~Paid book~






_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi ta hanyar biyan kuɗinku ₦300 ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_


_____________________________




Cije leɓe Salma tayi tana kallonsa ya juya ya shige cikin ward ɗin tare da faɗawa security na ƙofar kada su kuma barinta ta shigo cikin asibitin aikuwa duk bala'inta basu barta ta kuma shigar musu ba dole tasata juyawa ta fice a asibitin ta koma gdanta tuburan take hauka duk wani abu da yake mallakin Anam a gidan saida ta watsoshi waje sannan ta nemi guri ta zauna ta rushe da wani irin mugun kuka tana lalubar wayarta ta kira number yayarta Amina dake Niger tana aure ta rushe mata da kuka tace “meye yasa duk abinda na tsana yafi kusanta ta Amina meye yasa duk cikinku da muka fito ciki ɗaya babu wacce mijinta yayi gigin yi mata kishiya saini kuma ma don tozarci ya rasa dawa zai haɗani saida ƴar aikin gdana...."
Wata uwar ashar Amina ta saki tace “kiname kikayi wannan sakacin? Koda yake aike yar daɗi miji ce tausayinsa kikeji gashinan shi ya fara nuna miki kalar nasa tausayin....." Cikin kuka tace “wlh bantaɓa tunanin haka daga Aliyu ba Amina ki bani mafita ina cikin tashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login