Showing 21001 words to 24000 words out of 30605 words

Chapter 8 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

asuba ita ta tasheshi yajasu sallah suka sake kwanciya ya maƙaleta batason yanda yake nuna mata nacinsa saidai bazata iya hanashi haƙƙinsa ba haka suka bawa juna aikin safe suka sake sabon bacci sai goma sukaji ana taɓa ƙofar ta miƙe da sauri ta faɗa bathroom shine ya tashi ya buɗe ƙofar yana miƙa Salma ta leƙo ɗakin tans cewa “Ina sister na kaida baka gajiya da bacci ka makarar da ita koda yake yau Sartuday ku huta abinku"
Lumshe idanunsa yayi yace “Tana bayi yanzun zata fito" yana mata bayani idanunta nakan gadon da suka turmushe da kuma bra ɗin da take ƙasa wani mashi ya caki ƙirjinta ta haɗiye wani yawu me ɗaci ta dubeshi tace “ok idan kun shirya ga breakfast can a dinning" jinjina kai yayi ta juya ta fice ya koma ya ɗebe kayan daidai lkcn data fito a wankan tana goge sumarta ya zagaya ya rungumeta ta baya yayi kissing wuyanta yace “Morning My Chocolate" murmushi Kalmar tasata.








Ta janye a jikinsa tace “kayi wanka tukunnan" nufar bathroom ɗin yayi yana cewa “kamata yayi kiyimin wankan nan ba kibani umarnin yin wankan ba" shiru tayi masa ta buɗe wardrobe ta ɗauki kayanta wasu sabbin riga da zani na atamfa tasa ta ɗaura ɗankwalin tana sanya ɗan kunne ya fito ya karɓa ya saka mata ya miƙa mata mai ya kashe mata idanu tare da nuna mata jikinsa inda sabo ta fara sabawa da sangartarsa ko lkcn da yake ɗaukar ta yakaita hotel idan yayi wanka miƙe mata yake yace ta shafa masa hakan yasa ta saba ta shafesa tsaf ta ɗauko masa kayansa data gani a gurin ta taimaka masa yasa ya kamo hannunta suka fito.








Salma na zaune ta zuba uban tagumi a parlourn taji saukowarsu tayi saurin kawar da damuwarta tana mamakin yanda taga Kharimatun lfy ƙlau nandanan taji wani baƙin ciki ya cushe mata zuciya wannan wacce irin yarinya ce duk abinda aka shirya mata yake neman watsawa a banza, ƙwafa tayi a zuciyarta tace “in kinsan wata ai bakisan wata ba zanyi maganinki bari muga kamun ludayin wannan da akace nasa miki a abincin tukunna" zama sukayi a dinning ɗin ta gaisheta cikin ladabi ta amsa da murmushin da baikai zuci ba da kanta ta haɗawa kowa break ɗin Kharimatu ta ɗauki nata a kunyace tayi bismilla takai bakinta nandanan annurin fuskar Salma ya ɗauke jin tayi bismilla abincin da bata iya ci ba kenan komanta ya rushe duk kuɗin data kashe sun tashi a banza wannan shegiyar yarinyar dole a canza taku ƙaramin asiri bazai kaita ƙasa ba saidai tsafi.
Daƙyar Salma ta rinƙa tura abincin bayan sun gama ta tashi ta kwashe kayan Kharimatu ta miƙe domin ta tayata tace “aa yi zamanki ki huta amarya bata wahala kedai ki kula mana da mijinmu shine kawai aikinki" kunya ce tasa Kharimatu ƙasa da kanta ya riƙo hannunta yace “kinji abinda akace miki ko ki kula dani" yanda yayi mgnr yabasu dariya sukayi dariya ya miƙe yace “Zanje na gaida su Hajiya ku kulamin da kanku" fatan alkhairi sukayi masa Kharimatu ta miƙe ta sake gyara parlourn suka zauna suna hirarsu sama sama Salma ke janta da hirar nandanan ta saki jikinta sukayita harkokinsu tare ranar har girki tare sukayi abinsu can yamma aka dawo musu da yaran gdan da suka tafi hutu gdan kakanninsu yaran suna ganinta suka fara murna ta jasu jikinta sukayita shirmensu a haka Aliyu ya dawo ya tarar dasu yaransa sai nishaɗi sukeyi da ganin Uwar goyonsu shima sai yajishi cikin farin ciki ya zauna a cikinsu yana tayasu Salma sai tsiya takeyi masa wai yamai da kansa yaro.








Basu suka bar parlourn ba sai goma saura na dare Muwaddat tace “Aunty yau ɗakinki zan kwana" Farooq ma yace “nima acan zan kwana" Aliyu dake zaune ya miƙe yace “Nima Aunty yau a ɗakinki zan kwana" dariya sukayi Salma tace “aikuwa saidai kai ka hƙr kabarwa yara Auntynsu" murmushi yayi yace “dake don yara aka halicce ta ba to aikuwa saidai su su hƙr subarmin so nake na samo musu ƙani da wuri" haɗiye takaicinta tayi ta nufi saman tana cewa Allah ya taimaka zanyi murna da hakan mukam munyi adabo da haihuwa" ɗaukar Jannat tayi tace “muje mu kwanta saida safe ko" miƙewa dukansu sukayi suka bita suna murna yau zasu kwana da Auntynsu. Muryar Aliyu taji a bayanta yace “My Kharry!" Tsayawa tayi ya tako ya dafata yace “ina jiranki a ɗakina" saida ƙirjinta ya buga tayi ƙarfin halin cewa ok bari na kwantar dasu"








Jinjina mata kai yayi ta nufi saman yana biye da ita ta buɗe ɗakin yaran ta kwantar dasu tare dayi musu addu'a bayan tasa musu kayan baccinsu kwanciya tayi a gefen su sunata yi mata surutu har bacci ya ɗauke su Dukansu.
Shirun Aliyu yaji tayi yawa ya miƙe ya buɗe ƙofar ya nufi ɗakin yaran ya isheta tana bacci rungume da Jannat ya zubanta ido shauƙin ƙaunarta da sha'awarta suna ɗibansa ya matsa ya zare Jannat ɗin ya kwantar da ita ya ɗagota gabadayanta ya nufi ɗakinsa da ita ya kwantarta kamar wata baby yana ƙare mata kallo yaja numfashi ya ɗora bakinsa saman lips ɗinta ta buɗe idanunta akansa shima ita yake kallo tace “ina yaran?" Dariya tambayar tabashi ya janye yace “da kina tunanin kinci bulus ne zaki tafi gurin yara kibarni shanye kamar mayafi" miƙa tayi ta tashi zanne ya zauna a gefenta yace “meye na miƙewar?" Murza idanunta tayi tace “kayan nan zan cire" janyota jikinsa yayi yace “ki kwanta abinki zan cire miki" hannu yakai bayanta ya zuge zip ɗin ya zuge na sikelt ɗin ya zare mata ya ɗora bakinsa saman wuyanta yana lasa ta lumshe idonta tanajin wata muguwar faɗuwar gaba da batasan meye ya sabbabata ba cikin lkc ƙanƙani kanta yayi wata muguwar sarawa ta sanya hannunta biyu ta riƙe kanta ta saki wata razannanniyar ƙara data sanya kowa na gdan fitowa...........








Oum Hairan
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ37-38 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566








Ƙoƙarin riƙeta Aliyu yakeyi saidai tafi ƙarfinsa watsoshi tayi ƙasa itama ta zube tana wani irin abu daya tashi hankalinsa ya matsa ya riƙe ta daidai lkcn da Salmah ta turo ƙofar ta shigo tayi kansu da sauri tana faɗin subhanallah meye ya sameta?" Kallonta kawai Aliyu yayi yaci gaba da yima Kharimatu addu'a amma kamar Bama yi yakeyi ba ganin abin bana wasa bane ya tashi ya fita yana kiran wayar Alh Ma'aru dake dare baiyi nisa ba ya sameshi nan yake faɗa masa abinda yake faruwa hankalinsa ya tashi matuƙa da kansa ya fita ya ɗauko limamin unguwarsu suka nufo gdan nasu bayan ya ɗauki Granny yanayin da suka tarar da ita ya basu tsoro liman ɗin ne ya soma yi mata addu'a ta rinƙa miƙewa tana son ƙwacewa daƙyar Suka samu ta fara mgn cikin wata irin murya data tsorata kowa dake gurin sukaji ta fashe da kuka tana cewa “mu ku ƙyalemu bamu muka kawo kanmu ba ita ta taɓomu mu haukatata ko mu sanya mata ciwo mun kasa yin ko ɗaya sharaɗin zuwanmu bazamu barta ta samu ciki ba amma abin takaicin saida ciki ya shigeta" wata dariya ta ƙara fashewa da ita data sanya Salma matsawa taci gaba da soki burutsun surutunta liman nata kwarara mata karatu.








Basu suka samu ta jirge ba sai wajen asuba sannan ta kama bacci liman ya sharce gumi ya dubi Aliyu yace “ka biyoni gda ka karɓo mata rubutu gdy yayi suka fita suka barta kwance tanata baccinta suna fita Salma ta sheƙe da dariya ta matsa kusa da gadon tace “yaro man kaza kin tabka kuskure da kika bari kika shigo gonata zaki gane kurenki mijina gdana sunfi ƙarfinki sai na mayar dake abar tausayi kuma abar kwatance a duniyar maciya amana" tsaki taja ta juya ta fice daga ɗakin bai jima sosai ba ya dawo kamar yanda Mal Kabir ya faɗa masa.
Haka ya rinƙa shafa mata rubutun a ƙasan mararta zuwa ƙirjinta ta rinƙa sakin ajiyar zuciya bai jima da gama shafa mata ba ta buɗe idonta ta saukeshi a saman agogo takwas da rabi ta yunƙura zata miƙe ya ɗagata taja numfashi tare da sauke idanunta akansa yayi mata murmushi yace “Ya jikin" lumshe idonta tayi kanta har yanzu sarawa yakeyi ta buɗe idonta akansa tace “Meyesa baka tasheni da asuba ba?" Kawar dakai yayi yace “bakida lfy ne shiyasa" da wannan ta miƙe ta shiga bathroom tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallah ta shirya cikin wasu riga da sikert na jeans tayi kyau sosai sauka yayi ƙasa ya ɗauko mata break ya dawo.








Zama sukayi da kansa ya rinƙa bata abincin a baki tun daga wannan rana ya zame mata al'ada duk dare basa bacci kwana yakeyi akanta sai safiya tayi suke samun nutsuwa tsayin wata guda sai kuma laulayi ya sawo kai kullum tana kwance kamar ruwa tun ga amai da take fama dashi babban abinda ya fara bata mamaki da tsoratata a yanayin zaman gdan nasu idan yana gda Salma zata nuna mata tafi kowa kulawa da ita idan bayanan kuwa ko leƙota batayi haka suke rayuwa sannu a hankali lkc ya rinƙa tafiya cikin yanada watanni hudu cikin wani dare da bata mantawa dashi ranar ba ita keda girki ba Salma ce tun yamma takejin yanayin zazzaɓi ajikinta haka ta gama abinda takeyi a daddafe ta kwanta bacci ya ɗauketa cikin baccin taji wani mugun huci yana tunkarota ta buɗe idonta da sauri tare da dirowa a gadon daidai lkcn da wata doguwar halitta ta ƙaraso gabanta batayi aune ba taji an feso mata wani abu me azabar raɗaɗi a jikinta azabar data ratsa ta itace tasata sakin wata gigitacciyar ƙara ta zube a gurin kasancewar dakin a kulle yake Tsakanin ɗakinta dana Aliyu akwai tazara baijita ba amma Salma taji ta basar hakanan tayita juyi tana murƙususun azaba ta daɗe sannan ta samu raɗaɗin ya ragu tana addu'a sannan ta buɗe idanunta taga wannan mutumin ya ɓace taja ajiyar zuciya tanabin jikinta da kallo.








Me zata gani wasu irin ƙananun ƙuraje ne gabaɗaya jikinta sai zubar da ruwa sukeyi aikuwa ta mike a razani tana ƙara bin jikin da kallo tana faɗin “Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un" tsoro ya sake kamata ta tsigar jikinta tana tashi wasu zafafan hawaye suka zubo mata cikin tashin hankalin da bata taɓa shigaba tace “Na shiga uku Ni Kharimatu wannan wacce irin masifa ce?" Ashe wasa farin girki ne cikin lkc ƙanƙani taji kanta da jijiyoyin jikinta sun ɗaure ɗam ta kasa ko matsa komanta kafin kace meye wannan ta yanke jiki ta faɗi.
Bata farka ba sai a gadon asibiti tana buɗe idonta jikinta ta fara kallo ta rintse idonta cikin ƙyanƙyami da tashin hankali ta rushe da wani kuka me gunji tace Innanillahi Granny meye wannan a jikina" Granny da Mom da suke zaune a gefe suka nufota da sauri cikin tsananin tausayi Granny tace “Sannu Kharimatu ke kuma taki ƙaddarar kenan daga wannan sai wannan Ni waɗannan ƙuraje don dai sun dage akan ayi maganin asibiti ne nikam nafi tunanin sihiri ne" Mom ce ta cafe da cewa ashe muna ɗaya dake lamarin yarinyar nan akwai alamun bincike Hajiya iyakar zamanmu da ita batada jinnu kina gani fah dagayin aurennnan abu yaƙi daɗi kullum ita kenan ta yanke jiki ta faɗi yanzu kuma ga wata sabuwar masifar ta sako kai kiga fa jikinta yanda ƙurajen nan suka girma fata me kyau ta zama kamar bayan bishiya sai daddarewa takeyi"








Jinjina kai Granny tayi tace “Ma'aruf ne yake biyewa yaron nan Ni dama Muniba tun farko banso zaman Kharimatu da Salma guri ɗaya ba nasan sai an cutar da yarinyar nan" karɓa Mom tayi da cewa “ai gashinan sun fara gani Hajiya dole idan yarinyar nan ta samu sauƙi ya raba musu gda ko kuma ya sawwaƙe mata tunda zamansu taren ba dole bane" akan wannan shawarar suka tsaya.
Tun ranar data farka a asibitin take sanya idon ganin Aliyu shiru babu shi babu labarinsa har yau gashi kwana uku da farkawarta abinda yake bata mamaki ko a waya bataji yana kiran Granny ba yau tun safe ta tashi jikinta sai ruwan mugunya yake zubarwa abinda ya tashi hankalin kowa babu shiri Granny ta Kira Aliyu ta sanar dashi abin mamaki sai cewa yayi da ita shifa ayi duk abinda ya dace Bama ya gari yana Lagos zai turo musu da kuɗi" jinjina kai Granny tayi tace “Anya Aliyu yau yarinyar nan watanta guda a asibitin nan tun washegarin ranar da aka kawota baka ƙara dawowa ba matarka ma batazo ba meye yake faruwa ne haka?"








A kausashe yace “Itama batanan muna tare anan yaran suna gdansu Salma daganan Dubai ma zamu wucce Salma keda ciki zataje ta huta acan maybe sai yakai 6 months zamu dawo" murmushi Granny tayi tace “Lallai ne Gadanga kabar yarinya marainiyar Allah cikin lalura ka ɗauki matarka kunbar gari kuma har kana sanar da cewa zaku wucce Dubai to ita ame kabarta da nata cikin?"
Tsaki yayi yace “Ke wlh Granny da son takurawa kike naga gashinan kuna kula da ita" bazata iya jure lamarin ba wannan tasa ta kashe wayarta takai dubanta ga Kharimatu da takejin duk abinda yake faruwa tace “Inason ganinsa Granny kice yazo don Allah" hawayen tausayinta Granny ta share tace “zaizo Kharimatu wani aikine na gaggawa ya taso masa ya tafi Lagos amma kina ransa kiyi hƙr kinji kiyi fatan Allah ya baki lfyrki kawai"
Komawa tayi ta kwanta tana share hawaye kewar mahaifiyarta tana sake bijirowa zuciyarta sosai tayi kuka Granny nata aikin rarrashinta cikin kukan tace “Ba damuwata yazo ba Granny damuwata shine son sanin yanda ya karɓi amanar da Mahaifiyata ta bar masa, meyesa ta amince na zauna da Aliyu tun kafin na amince dashi? Meyesa ta zaɓamin shi tace naje na zauna dashi harma take bani wasiyyar na zauna dashi iyakar wuya bayan shi tun yanzu ya fara juyamin baya Granny tunda na farka kwana uku kenan banga Daddyn Farooq ba kuma yanzu naji kina faɗa cewar tunda aka kawoni asibitin nan washegari bai ƙara zuwa ba"








Sharce gumi Granny tayi ta kamo hannun Kharimatu da taketa zubar da hawaye tace “kinga Kharimatu inason ki cire komai a ranki don Allah ki manta da komai kinga cikinki ya tsufa watanni bakwai bakya buƙatar hayaniya ga kuma lalurar nan da take damunki don Allah ki daina sa Aliyu a ranki Kharimatu ba haka akabar Aliyu ba kinsani wannan lamari yana buƙatar addu'a me tsanani"
Jan zuciya tayi tace “Yanzu a haka zanta zama kenan?" Murmushi Granny tayi tace “Aa bazakiyita zama a haka ba yanzu abinma dake akwai zaki koma gabanmu ne aci aci gaba da magani har Allah ya baki lfyrki"
Zuciyarta na suya haka ta hƙr tabar mgnr ta koma ta kwanta kwana takwas ta ƙara a asibitin suka sallameta domin suma sun fahimci ciwon nata bana asibiti bane dole tasa aka nemi maganin Hausa tare da yin waya Guru aka sanar dasu halin da ake ciki Baba Na'ibi wane a gurin babanta shine ya niƙo gari ya taho Kano ya kawo mata magani cikin ikon Allah Suna fara amfani da maganin sauƙi yayita samuwa sati guda bata rufa ba wannan ƙanzo²n da fatarta tayi duk ya ɓare asalin fatarta ta dawo Baba Na'ibi yana kallonta yayi murmushi yace “komai zai wucce da yardar Allah"








*Oum Hairan*
[11/10, 8:59 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ39-40 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566








Kwanaki har watanni sukayita wuccewa babu Aliyu babu Salma Kharimatu tanata rainon cikinta har ya isa haihuwa ranar wata asabar da yamma ta shiga bayi tana tsugunnawa taga wani jini me yauƙi ya zubo mata ta miƙe da sauri ta fita ta kira Granny dake a sashinta take zaune. Tana gani ta gane meye ke faruwa tayi murmushi tace “Abin yazo Kharimatu haihuwa ce" gabanta ya faɗi tace “Granny tun jiya marata take ciwo fah" kama hannunta tayi tace “kije ki zauna bari nayiwa Mal Hassan mgn yayi miki rubutu idan haihuwar ce ciwon zai tashi ayi a wucce gurin idan ba ita bace kuma zaiyi sauƙi"
Zaunar da ita tayi ta shiga ɗaki bata jima ba ta fito ta tarar da ita ta riƙe ciki ta cije leɓe tana ƙoƙarin zamewa daga kujerar kamota tayi ta saukar da ita ƙasa tanayi mata sannu itadai kallonta kawai takeyi tana karɓar azaba babu jimawa Mal Hassan ya aiko da rubutun Granny ta bata tasha tace ta kwanta, kwanciya tayi bacci ya ɗauketa cikin baccin taji azabar ciwon ta ƙaru ta zabura ta miƙe da sauri tana faɗin Innanillahi wa Innah Ilaihirraji'un Granny bayana marata ƙirjina wayyoh wayyoh Granny shikenan na mutu na ƙare...." Rufe mata baki tayi tace “ke ar sakarya ki rinƙa salati" fita Granny tayi tayima driven gdan mgn tazo ta ɗauko mata hijjab ɗinta tasa mata daidai lkcn Mom ta fito itama suka nufi asibiti suna zuwa aka shiga da ita labour room.








Bata wani ɓata lkc ba Ubangiji ya yassare mata ta haifo sankacecen ɗanta namiji kyakkyawa kamannin sa na mahaifinsa ne sak sumarsa da bakinsa sune kawai nata, ana gyara yaron aka sallamesu suka tafi gda sunata murna kamar ba'a taɓayi musu haihuwa ba.
Waya sukayi Guru ƙanwar Mama Yabi tazo ita da Granny suka rinƙa kula da ita abinda ya dami zuciyarta tun ranar data haihu take kiran wayar Aliyu bata shiga shikuma bai kirata ba zuciyarta na faɗa mata to ko baisan ta haihu bane?" Wannan abu sosai ya damu ranta ranar da ɗanta ya kwana biyar suna zaune take tambayar Granny Daddyn Farooq kuwa yasan ta haihu?"


Shiru Granny tayi tsayin lkc fuskarta ta sauya daga fara'a zuwa damuwa hakan ya tashi hankalin Kharimatu idanunta ya kawo ruwa tace “kiyi hƙr Granny bansan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login