Showing 15001 words to 18000 words out of 30605 words

Chapter 6 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt

tasheta jikinta zafi zau haka sukayi sallar ta sake kwanciya tanajin yanda jikinta yayi tsami duk da gasa jikinta data ƙarayi.








Shima da yayi sallar kwanciya yayi basu tashi ba sai 10:00am ya fita ya samo mata abinda zataci suka karya ya dubeta da kulawa yace “Zan kaiki gda ko zaki zauna anan sai zuwa anjima kin ƙarajin ƙarfin jikinki?"
Sunkuyar dakai tayi yayi murmushi yace “Kuma kunyar ta meye?" Batayi masa furuci ba sai miƙewa da tayi tasa mayafinta ta nufi ƙofa ya miƙe yana kallon tafiyarta yana dariya ƙasan zuciyarsa da taimakonsa suka fita ta shiga motar yaja suka tafi, suna zuwa kafin ya gama parking ta buɗe motar ta fice tayi dururu ta faɗa gurin Granny bazata iya shiga cikin gdan ba kunya takeji batasan aikin banza tayi ba Mama Yabi tana ganinsu.
Tana shiga Granny ta miƙe tace “Naga ta kaina Ni Sa'ade wannan gantalallen yaron yakai ɗan kuka wato bazai iya bari ki tare ba shine saida ya fafake ki to yadai shiga hankalinsa ya kwanta ɗan banza zaizo ya sameni, koda yake algunguma kema so kike shiyasa kika badakai"








Itadai bata da lkcn cakaki da Granny ta shige ɗakin ta kwanta
tanajin yanayin baƙo a jikinta da haka bacci ya ƙara ɗauketa batasan sanda ya shigo ya fita ba sai azahar Granny ta tasheta tare dayi mata sannu yanda take lallaɓa jikinta ba ƙaramin tausayi ta bawa Granny ba hakanan tayi mata ƴan jiƙe²nsu na tsoffi ta bata tasha sannan ta ɗan samu ƙarfi ta shiga gdan suka gaisa da Momy tana bin surukar Tata da kallon tuhuma yanayinta kaɗai ya isa ya nuna wani abu ya faru da ita.
Bata zafafa ba tana kallonta ta shige ɗakin gyatumarta ta ishe mama saman sallaya ta zauna a kaikaice suka gaisa tace “yau zukuɗun najiki shiru koda yake Granny tace bakida lfy ne meye yake damunki?" Sunkuyar da kanta tayi ƙasa cike da kunya tayi shiru, sarai Mama tasan dama bazata iya faɗi mata ba shiyasa itama bata zafafa da tambayar ba taci gaba da lazuminta bayan ta gama ta miƙe tace “ki ɗauki wancan rubutun kisha maganin sammu ne ɗazu Hassan ya kawo shi wai Granny ce tasashi ya rinƙa yi miki"








Batayi gardama ba ta karɓa ta sha da bismilla ta ƙara bin katifar Mama haka ta yini a kwance kamar ruwa abinci ma ta kasa ci sai ruwan zafi kawai da takesha sallah kawai ke tashinta har Magrib ta tashi daƙyar ta shiga wanka ta fito ɗaure da towel a ƙirjinta.
Ja tayi da baya da sauri daidai lkcn da Mama ke fita daga ɗakin taja ƙofar Aliyu ya miƙe ya nufota ta janye da sauri yakai hannu ya riƙota jikinta ya fara rawa ta buɗe baki zatayi mgn ya haɗe bakinsu yana sakar mata wani zazzafan kiss ta rintse idonta tanajin yanda yake tsotsar bakinta kamar ya samu sweet a sanyaye ya saketa yana mayar da numfashi yace “kinajin tsoron karna ƙara ne?"
Saurin ɗaga masa kai tayi yaja numfashi yace “idan kika tare a gdana ma haka zakike jin tsorona?" Ƙasa bashi amsa tayi yayi murmushi ya sanya hannu ya zare mata towel ɗin tare da matsawa jikin ƙofar ya murɗa mata key.
Itadai Kharime tana tsaye jikinta sai ɓari yakeyi zuciyarta bugawa takeyi da ƙarfi yace “kinga nifa ba wancan abin zanyi miki ba ko a gidana kike zan ɗaga miki ƙafa ki warke kafin na ƙara shiga kawai Breast zaki bani nayi wasa dasu kaɗan na ɗan rage zafi" kafin tace komai ya kamota ya haɗata da jikinsa ya fara shafa mararta zuwa ƙirjinta da salonsa me tsayawa a rai.








Sun jima kafin yaja wata ajiyar zuciya ya saketa yana kallonta cike da ƙauna yace “gsky bazan jureba Kharimatu zanyiwa Dad mgn su bani ke kafin na ɗauke ki" itadai batada bakin cewa dashi ƙala ya tashi yace idan kin gama azumin mgnr mayi mgn a waya" zaro kwalin waya yayi sabuwa dal ya miƙa mata ya sake miƙa mata wata leda yace “Granny tace yau gabaɗaya bakici abinci ba zan kira na tambayeta idan kinƙi ci zan dawo zan ciyar dake da kaina sannan kema zaki ciyar dani"
Karɓa yayi sai lkcn ta magantu tace masa “na gde Allah ya ƙara arziƙi" jin addu'ar tata yayi har cikin ruhinsa yace “na gde ya juya ya buɗe ƙofar ya fita ta aje wayar da ledar ta dauki rigar baccinta ta sanya ta zura hijjab tayi sallar Isha sannan ta buɗe ledar nama ne gasasshe sai fura damammiya sai ice cream da tarkacen chocolate cake da sauran kayan ciye²


[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ27-28 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 0931307566








Neman guri tayi ta zauna ta zubawa kayan idanu a haka Mama ta shigo ta ishe ta a zaune ta rafsa uban tagumi tayi murmushi ta zauna tare da dafata ta ɗago firgigit ganin Mama yasata jan numfashi ta cire hannun Mama tace “Banyi tunanin zaki samu kulawa daga Aliyu irin haka ba saboda yanayin izzarsa da kwarjininsa da kuma soyayyar da yakeyiwa matarsa Kharimatu shi namiji da kike ganinsa kamar yaro ƙarami haka yake duk inda yafi samun kulawa nan hankalinsa yafi karkata na fahimci akwai dalilin auren nan naki da Aliyu ya aureki ne domin wasu dalilansa koda yake dalilansa suna da ƙarfi matuƙar zai kwatanta adalci, nidai fatana Allah ya tsaremin ke"
Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannunta ta ɗauki wayar daya kawo mata tana dubawa waya ce me tsadar gaske ta girgiza kai tana ƙara bin wayar da kallo iyakar tunaninta bata taɓa kawo ranar da zata riƙe waya me tsadar wannan ba taci naman sosai ita dama masoyiyar kayan sanyi tasha ice cream ta kwanta itadai Mama binta kawai takeyi da kallo tana mamakin irin sanyin da ɗiyar tata tayi duk da dama ita ba ma'abociyar hayaniya bace.








Da dare ne wayar tayi ta ring ta janyota ganin sunansa akan sensor yasa gabanta faɗuwa haka dai tai ƙarfin halin ɗagawa baijata da doguwar mgn ba tambayarta kawai yayi taci abincin tace eh ya kashe, tun daga wannan ranar ya zamewa Aliyu farilla kullum sai yazo gdan ya ganta kafin ya fita aiki wataran idan ya dawo ko kuma yace abashi ita zasuje unguwa ran Mama bayaso saidai bazata iya ce masa a'a ba shida matarsa Granny cema me ƙoƙarin hanawa to itama dole tanada iyaka musamman da yaje yayi mata daɗin baki ya kasheta da kalamai shikenan tayi muƙus a gdan ma idan yazo sai ya kira Anam ɗin sashin Granny ya lallaɓeta da yaudararrun kalamansa ya samu nutsuwa da ita tun tanaƙi har ta saduda.
Satin Salma uku a Niger ta dawo 9ja a lkcn shirye²n bikin yayi nisa sosai don har kayan amarya ankai sabon gdan daya gina mata komai Abba ne yayi mata tarkacensu ne na barebari kawai sukayi kayansu duk akaje aka jere a gdan ana jiran sati yazo akai amarya ɗakin mijinta.








Cikin kwanakin da aketa shirye²n shagalin bikin ne kuma ɗif ya ɗauke ƙafarsa a gdan nasu babu wanda ya kawo wani abu kowa yabar abin a cewa hidima ce tayi masa yawa Anam ce kawai jikinta yayi sanyi ganin ko waya ya daina kiranta ana saura kwanaki biyu bikin har an fara shagalin biki ana saura kwana uku bikin suka ɗunguma ita da Mama suka koma Guru acan zaaje a ɗaukota ranar da zasu tafin ne ta kira shi a waya kira uku bai ɗaga ba sai a na huɗu ya ɗaga yace ta fito harabar gdan yana jiranta.
Ta zari mayafinta ta fito da zaƙuwa saboda sun kwana biyu basu haɗu ba tun daga nesa ya kafeta da idanunsa kallon kusan faɗuwa yasata daƙyar ta iso gareshi har zuwa lkcn ita yake kallo ta tsugunna tace “Ina yini" numfashi ya sauke ya cire hularsa ya shafa sumarsa yace “kina lfy kinjini shiru amma baki nemeni ba" ƙasa ta sakeyi da kanta cikin kunya tace “nayi tunanin hidima ce ta ɓoyeka" murmushi yayi yace “daba ita ce bafa?" Nuni yayi mata da ta miƙe ta tashi tsaye tana wasa da zara²n yatsunta ya kwantar da kansa jikin mota yace “Granny ce tayimin tsakani dake shiyasa na ƙaurace miki"






Da sauri ta kalleshi ya ɗaga hannunsa ya ɗora daidai goshinsa yace “amma kiyi hƙr nasan zuciyarki ta ayyana miki wasu abubuwan ko? Am kamar me dame ta ayyana miki nasan dai tace miki Aliyu ya gujeki ya daina kiranki ya daina zuwa inda kike, bayan haka sai me?" Dariya tayi da ta bayyana kyawawan Haƙoranta ya zubanta idanu yana murmushi yace “naso ayi komai anan a gama Abba yace a'a saidai ayi a garinku okey ki kasance cikin aminci kiyimin tanadin Pure honey da zaki shayar dani a daren angwancina" turo baki tayi tace “meye ma ya rage bayan komai ka kwashe....." Rufe mata baki yayi yace “Aa bari faɗa ban ɗauki komai ba kawai rage zafi nayi za dai ɗauka zanci na ƙoshi ranar da su Granny bazaa sanyamin idanu ba.








Juyawa tayi zatabar gurin yayi saurin riƙota ya haɗata da jikinsa yace “Da banida wani uzuri tare zamu tafi amma babu komai saura ƙiris" haka ya rinƙa yi mata kalami duk ya kashe mata jiki kafin yace “kinsan me" girgiza masa kai tayi ya matso kusa da ita sosai yace “ina sonki...." Kwasa tayi da gudu tana waiwayensa tana dariya shima yanayi mata dariya baibar gdan ba saida yaga tashin motarsu.
Suna ɗagawa juna hannu cike da shauƙin juna har sukayi nisa sannan ya hƙr tunda motarsu ta tashi yaji gabansa na faɗuwa jikinsa duk ya mutu hakanan ya tsinci kansa cikin kewarta daƙyar yaja motarsa ya nufi gdanta da yasa aketa shiryawa ya zauna a falon ya zubawa manyan hotunan su idanu tsayin lkc ya shagala da kallon hotunan daya sanya akayi musu manya ya kafesu a falon kyawunta sihirtacce ba kowa yake gane tana da kyau ba sai wanda yasan asalin sirrin kyau shi kansa a farko idan Nazeer yana yaba kyawunta musawa yakeyi sai yanzu ya gaskata itaɗin kyakkyawace ta kwatance musamman cikin watanni biyun nan daya gyarata da manya mayuka oily skin nata sai wani ɗaukar idanu sukeyi.








Wayarsa ce ta katse masa tunanin Second wife ya gani a rubuce saman sensor na wayar ya ɗauka da sauri tare da lumshe idanu ya kara a kunnensa kafin yayi mgn yaji hayaniya ta cika masa kunne ya miƙe da sauri tare da cewa “Khamilu ina Kharimatun...." A ɗaya ɓangaren akace “mal ka nutsu mun tsinci wannan wayar ne a cikin wata jaka Allah yasa babu security so muna dubawa sai mukaga wannan number ansa Zaujhnoor shiyasa muka kiraka....." Katseshi yayi da cewa naji malam ina matata kardai kacemin hatsari sukayi ida drivern ina Mama?" Wani ne ya karɓi wayar yace “bazamu tantance komai ba amma dai an ɗaukesu ankasu asibitin Dutse saboda yafi kusa da inda sukayi accident ɗin so ana buƙatar makusantans......"
Bai gama sauraron wayar ba ya fice da gudu ya shiga mota ya fice a gdan cikin tashin hankali shidai bazaice ga yanda akayi yaje Dutse ba sai ganinsa yayi a cikin asibitin yana zuwa ya tarar da Alh Ma'aru a asibitin lkcn suna emergency ana ƙoƙarin ceto rayuwarsu abu da ƙarar kwana an samu nasarar samun rayuwar kowa amma banda ta Mama Yabi Allah ya karɓi rayuwarta a wannan hatsari inda Khamilu ya samu karaya huɗu Ita kuwa Anam doguwar suma da Ɓarin cikin da babu wanda yasan dashi ta samu sai karaya ɗaya a ƙafa.








*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ29-30 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 09031307566








Tashin hankali da ɗimuwar da Aliyu ya kasance a ciki ba kaɗan bace daƙyar da rarrashi Abba yasashi ya nutsu tare da nuna masa hƙr shi ya kama da dauriya saboda Anam a gurinsa kawai ya rage zata samu nutsuwa idan shi bai nutsu ba taya ita zata nutsu?
Da wannan kalaman ya ɗan samu salamar zuci ya zubawa amaryar tasa ido da take cikin halin suma sosai yaji takaicin suɓcewar cikin nasa duk da kasancewar baisan sashi ba a ransa yake raya da yanzu yaransa sun kusa zama huɗu fah rashi biyu sukayi ga rashin surukarsa ga rashin cikinsa, a haka Su Mal Datti kakan Anam sukazo aka tafi da gawar Mama zuwa Kano don tafi kusa domin a sutura ta Aliyu baije ba haka ya wanzu a asibitin sai yammaci liss komai ya ɗan tsagaita sukayi transfer ɗin petiant ɗin zuwa asibitin Mal Aminu Kano aka ɗebe su a Embulance zuwa Kano Granny ke jinyan Anam cike da tausayi da jin ƙai tana tuna kalaman yarinyar a mafi yawan lokuta idan anyi zancen mutuwa takance mata.






Granny nidai fatan da nakeyi kada mutuwa ta ɗauke min Mama tabarni nikaɗai ina Gantali a duniya wlh duk ranar dana buɗi ido naga babu Mamana a gefena tabbas idan nima ajalina bai rigaya ba to kuwa sai an rinƙa haɗamin da addu'a domin tsaf zan iya zaucewa"
Hawaye ta ɗauke a idanunta yau ga ranar da take tsoron zuwa ta iso babu mama Yabi mutuniyar kirki da duniya bata ɗaɗsta da ƙasa ba gashi abin yazo mata a daidai lkcn da tafi buƙatarta fiye da komai, Granny ta Jima tana alhinin wannan rashi kafin ta tashi ta nemi makwanci ta kwanta haka suka wanzu a asibitin wajen kwana huɗu sannan Anam ta fara dawowa hayyacinta.








Ta fara buɗe idonta tana me ambaton sunan Allah a hankali ta fara sauke idanunta kan mutanen dake zagaye da ita ta jima idanunta akan Aliyu da shima ya kafeta da idonsa da suke cikin farin glass a nutse ta ɗaga hannunta ta miƙa masa ya kama hannun nata ta yunƙura alamu sun nuna masa tashi takeson yi ya ta rintse idanunta tanajin azaba da zugi a hannun nata daya karye ta saki wata yar siririyar ƙara data sanyashi kallonta ta buɗe idonta da hawaye ke ƙoƙarin gangarowa a hankali cikin muryar tausayi yace mata “Sannu" daga masa kai tayi tana kallon Granny da taketa matsar hawaye a kasalce tace “Granny meye ya kawo mu nan ina Mama...."








Ƙasa taga Granny tayi da kanta yayinda Aliyu ya fice daga ɗakin da sauri, dukkansu tabisu da kallon rashin fahimta tanabin hannunta da kallo ta zuro ƙafafunta ƙasa ta tashi tsaye tana layi ta nufi Granny ta Kama hannunta tace “Idan zan iya tuna wani abu kamar hatsari mukayi ko Granny please ki faɗa min ina Mama inje inganta ince dai ita bataji ciwo ba?" Rungumeta Granny tayi da Muryar kuka tace “kiyi hƙr Kharimatu duk abinda da Ubangiji ya zartas akan bawa shine daidai tabbas mutuwa batada daɗi musamman ta iyaye Kharimatu muna tayaki alhinin rashin salihar mahaifiyarki Ubangiji yasa lahirarta tafi duniyarta...."
Tun kafin Granny ta ida rufe bakinta sabuwar tashin hankali tayi wankan tsarki ta samu gurbi a ilahirin sassan jikin Anam ta rinƙa kallon Granny kanta na juyawa tana ganin abubuwa hurhuɗu kafin kace meye wannan ta sake zubewa a ƙasa luuuuuu.
Daidai lkcn da Aliyu da likitan suke shigowa suka nufota a guje Aliyu ya tallafota yana kiran sunanta amma ina babu alamun zatayi motsi, ɗagowa yayi ya dubi Granny yace “Fada mata kikayi ko?" Share hawayenta tayi tace “To Gadanga meye amfanin ɓoye mata abinda dole zata sani?" Shiru yayi cike da jin takaicin abinda Granny ta aikata ya ɗagata ya ɗorata a gadon ya kwantar da ita likitan yayi yan aikace²nsa ya fita daidai lkcn da Momy ta shigo asibitin suka gaisa da Granny ta tambayeta me jiki ta bata lbrn farkawar ta Hajiya Muniba ta jinjina kai tace “Insha Allahu zata tashi rashin Mahaifiya da ciwo saidai Allah ya bamu ikon yi musu addu'a"








A ranar Anam Bata sake farkawa ba sai kashegari ta tashi lkcn Aliyu bainan sai Granny kaɗai shassheƙar kukanta ne ya ankarar da Granny ta farka ta isa gareta tanayi mata sannu ta ɗago tace “Yanzu shikenan Mama ta tafi ta barni? Shikenan bazan ƙara ganinta ba bazan kuma jin kalamanta ba Granny ta tafi kenan?"
Kama hannunta Granny tayi tace “Haka Allah ya tsara sai hƙr da abinda baka isa ka canza ba Kharimatu kedai kiyita addu'a kuma kiyima mijinki biyayya likitan da ya karɓi Habiba kafin ta rasu yace second 2 kafin rasuwar ta sunanki da mijinki take ambato tana barin wasiccin kada a fasa kaiki gdan mijinki tare da faɗawa likitan ya faɗawa Aliyu ya riƙe ki amana ke har rubuta duk abinda ta faɗa likitan yayi sannan ya sanya mata kalmar shahada tayi ta cika"
Kwantar da kanta tayi jikin Granny tanata kukanta me ban tausayi a haka Abba da Aliyu suazo suka ishesu Abba yace “Assha Kharimatu meye na kukan hƙr ai ya zama dole agun duk wanda irin haka ta sameshi" zama Aliyu yayi kusa da ita ya kamota ta dawo jikinsa ya rinƙa shafa bayanta yana raɗa mata “Sorry Please!" Salma dake tsaye kamar gunki ta haɗiyi takaici iya takaici tayi kamar ta juya saidai kuma ta tuna kalaman Yaya Ameey dole ta haɗiye kishinta ta matsa tace da Kharimatu Sannu ya jiki" a hankali ta ɗago suka dubi juna ta janye a jikin Aliyu cike da kunya da tausayin kai tace “Da....da...sauƙi" taɓe baki Salma tayi ta harari gefen da surukarta take tace “Allah ya ƙaro afuwa ya jiƙan Mama" duk ɗakin saida suka amsa da Amin banda Granny da Hajiya Muniba da kusan itace Ummul aba'isin zuwan Salma dubiyar har gda taje ta sameta tayi mata tatas tare da nuna mawa Aliyu gangancin da yakeson yayi na rusa gdansa daga tushe wannan tasa yace “Indai batazo ta duba Kharimatu ba to karya dawo ya tarar da ita.










Tana gama dubiyar da batakai zuci ba ta juya zata fita Aliyu ya kirata ta tsaya yace “Ina zaki?" A gajarce tace “Gda" murmushin takaici yayi yace jirani mu tafi" batada zaɓi haka ta dawo ta zauna Hajiya Muniba ta haɗa abinci tabawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login