Showing 30001 words to 30605 words out of 30605 words
Chapter 11 - ME YA JAMIN NEW BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN.txt
nasa a lalata miki mahaifa kiyita zubar da jini idan kin samu ciki kiyita ɓarinsa ashe kaina zata juyo shekara biyu kenan bantaɓa hutawa da zubar jini ba kullum cikin ƙaramin jini ake.
Gashi waɗannan ƙurajen dana sa a turo miki sun dawo jikina kullum cikin ɗoyi nake da zubar da mugunya gashi duk me maganin da naje gurinsa cemin yake kin samu kariya daga Ubangiji babu kuma wanda zai bani maganin ciwon nan nawa sai Babanki Mal Wada Na'ibi jiya mukaje gurinsa yace sharaɗin shine nazo na sanar dake nice nayi miki komai idan kika yafemin zai bani magani idan baki yafeba kuma saidai na zauna da ciwo na don Allah na roƙeki ki yafemin Kharimatu ina cikin mawuyacin hali....."
Ta karashe mgnr da wani kuka me gunji Tsaki Aliyu yayi ya miƙe yace da Kharimatu ta tashi tabar gurin kallonsa tayi da idanunta da itama suketa zubar da ruwa tace “Duk da inajin ciwon kasancewarta silar gushewar rayuwar Mahaifiyata bangona Yaya Aliyu bazan kasa yafe mata ba kodon arziƙin su Farooq da Muwaddat da Jannat kije Allah ya baki lfy Ni na yafe miki haƙƙin rai kuma banida ikon yafeshi tsakaninki da ubangijinki ne" miƙewa tayi tabar gurin da sauri don Allah ya sani batason ganin Salma.
Duk da halin da Salma take ciki miƙewa tayi tana ƙwafa a ranta tana cewa zakuyi bayani ne kudai jira naje na samu wancan tsohon banzan ya bani magani na warke wanda zanyi muku gaba ma sai yafi wannan saikin haukace kin fita tsirara mota ta takeki tunda kika zamo silar rabuwata da mijina sannan kika rabani da ƴaƴana"
Daƙyar Aliyu ya rarrashi Kharimatu ta manta da komai sati biyu tsakani suka samu kira daga gun Mom take sanar dasu sunji lbrn mutuwar Salma kuwa sosai Kharimatu ta shiga cikin tashin hankali tace wlh batasani ba nan Mom tace mata ai sunje Guru sun dawo ambata magani taji sauƙi suka ɗauki hanyar Maiduguri gurin wani sabon bokansu so kafin sujene sukayi hatsari mutum biyu ne suka fita ciki harda ƙawar Salma wacce tayi mata jagora zuwa gurin bokan"
Mutuwar ta bugesu sosai Kharimatu taji tausayin su Farooq ƙaunarsu ta ƙara shiga ranta duk da Aliyu yaso hanata zuwa ta'aziyyar tace masa yayi hƙr yabarta suje da yaran hakanan ya ƙyalesu suka tafi harshi sukayi ta'aziyyar suka dawo, Kharimatu ta sake ɗaukar ɗambar riƙe yaran sukaci gaba da rayuwarsu kai zaka zacima duka ita ta haifa cikin ikon Allah bata yaye twins ba ta kuma haihuwar ƴa mace taci sunan Mahaifiyarta Ruƙayyatu sukece mata Amnah bayan shekara biyu ta ƙara haihuwar namiji shikenan haihuwar ta tsaya dake ita dama ahlinsu ba masu haihuwar da yawa bane.
Ta gama karatunta a fannin Business and Administration dake Allah yayita da son ƙamshi hakanan takeyin turaruka matan lay-out ɗin nasu suna siya ganin hakan batare data sani ba Aliyu ya siya mata wani babban shago ya zuba mata kayan kwalliya tare da kayan gyaran gashi da kuma ɓangaren boutique da turaruka humra kulacca turarukan wuta da kuma turaruka ƴan waje cikin lkc ƙanƙani Ubangiji ya sawa Kharry Boutique and cosmetic albarka ya haɓaka ko ina zancen sa akeyi a yankin arear tasu haka ta kuma buɗe wani shima ya samu karɓuwa ga ƴaƴanta biyar dana mijinta uku yaransu takwas ta haɗa ta riƙe rayuwa tayi daɗi tayi riba albarka ta sauka ta wanzu a wannan zuri'a
_Tammat bi hamdullah_
_Alhmdllh gdy ta tabbata ga Ubangijin talikai daya bani ikon kammala wannan littafi a yau ɗin nan ina roƙon Allah daidanmu ya karɓa akasinta ya share ubangiji yasa ya amfanar_
Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!
Insha Allahu sabon littafi na me suna BAƘIN RUHI zai fara zuwar muku 20/11/2021
*Oum Hairan*