Showing 21001 words to 24000 words out of 108906 words

Chapter 8 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt

08 Jan 2025

7716

Khalil da amatu sbd jin a hannunsa yarinyar zatayi rainon cikinda bai gama yadda da akwaisaba sbd aduniya shine yafi kowa sanin wannan ba halin Khalil din bane ya kalli inda Andi yakira sunansa ya taso cikin nutsuwarsa dake qarawa Andi ganin kwarjininsa ya qaraso ya tsaya gaban andin tareda sauke kansa cikin girmamawa yace"


Allah yaqarawa Andi tsawon Rai.


Matar 'dan uwanka zata zauna a hannun matarka har tsawon lokacinda zata haihu,
Cinta da Shanta duk na hannunka,
Ciwonta da maganinta na damqasu hannunka Dana matarka,
Na damqa maka tsaron lafiyarta Dana Abindake cikinta sbd aishatu ta tabbatar Mana da AMATULLAH da abundake cikinta na cikin hadari a hannunsu Dan haka Kaine kawai Wanda na yarda dashi nabaka amanarsu a hannunka.


Shiru yayi bai motsaba sbd Abinda andin yafada yaxo da wani al'amarine da kansa yake kasa dauka,
6arauniya a gidansa?ta Yaya zai iya Bari wannan yarinyar ta zauna acikin inda yake rayuwa
Khalil dinma haryanxu yakasa yarda da shidin ne uban cikin wannan yarinyar
ahankali yadan dago ya kalli gefen datake tsaye riqeda rigar Khalil sbd zuwa lokacin tafara firgita da abindake faruwa Jin hukuncin da aka yankewa Khalil daga farko taji bazata iya Bari tazama sanadin batawarsa da rabuwa da iyayensaba saiga zuwan wannan Andin Wanda ganinsa kawai yasa taji tsoro da firgici ya kamata gashi ana maganar riqeta ta haihu
Ta Ina dakuma ta Yaya zata haihu
Kasa riqeta qafafunta sukayi tsabar rawa shiyasa ta boye bayan Khalil din.


Taro ya tashi kowa ya watse nagama magana abubukar a aika mahaifiyarsa gida tareda kayan abinci da jarin sana'a me kyau sbd itace kakar Zabeera na shida Inshallah.


Modibbo a qarqashinka zaa kula sosai matuqa da AMATULLAH Ina fatar Nanda watanni kadan za'a bani zabeera na shida a hannuna.


Kallon amatu yayi akaro na farko data saki fuska dukkaninsu Saida suka bude Ido sbd ganin murmushi akan fuskar tasa yace"


AMATULLAH ni Andi nine gatanki keda Abinda yake cikinki acikin zabeera nayi Miki alqawarin baki kyakkyawar rayuwa keda Abindake cikinki sbd zalincin da khalil yayi miki da Wanda mahaifiyarsa ke shirin Yi na cutatar dake da Abinda ke cikinki Dan haka na Miki alqawarin idan har Ina Raye Kika haihu indai namiji sai yayi mulkin zabeera wannan shine babban adalcin dazan baki,
Kece mace ta farko Kuma mutum ta farko data shigo zuriar zabeera a tarihi ki riqe wannan a ranki Dan haka karki Bari har abada Nasameki da illa ko laifin dazai sakani takaicin hukuncina sbd cin Amana,yaudara da qarya ba abubuwan da Andi ke yagewa bane.


Kai Kuma Khalil hukuncinka na ranardazan daura maka aure da ita.


Kowa yatafi nagama mgn.


Hannu umme take Shirin dorawa akai tasaki kukan baqin cikin wannan alamarin Modibbo ya aiko Mata da mugun kallo Haj maryam ma dake Shirin fasa ihu Andi ya nuna musu qofa sunaji suna gani suka hadiye cikinsu bame iya Jan wani suka fito Babu me ganin gabanta tsabar tashin hankali.


MAHMOUD ma ficewa yayi batareda yaqara ko second dayaba.
Baba Jamila da Sha Taranta ta arziki aka kaita gidanta inda suka tsara komai Koda anxo bincike.


ZARAH aka kirawo ita tazo aka damqa amatu hannunta wadda atake alokacin amatun tashiga ranta ta kalli amatun dake qara damqe rigar Khalil sbd hankalinta daya tashi gaba daya da alamarin sbd ita yanzu Tama rasa Ina aikin data zoyi yaje Sam sun rikita 'yar qaramar qwaqwalwarta.


Kallon Khalil tayi tana sake matsesa tana girgiza Kai tace"


Dr gida zani nafasa bana......


Hannu ya Dora a bakinta tareda girgiza Mata Kai Ya bude bakinsa daya gama nauyi muryarsa na nauyi a karye yace"


Kije kibi ZARAH komai zai daidaita bazan Bari komai ya sameki ba na Miki alqawari,
Kuma zansamu kawu nayi mgn dashi zan Masa bayani yanda zai fahimta Inshallah.


Qura Masa Ido sosai take kallonsa sbd yadda dashi datayi dari bisa dari kafin ta daga Masa Kai tasakesa ahankali tareda kallon zarah dake Mata murmushi suka wuce.


Bayan fitarsu Kai tsaye motar zarah din suka nufa suka shiga ta jazu sukabi ta bayan gefens Modibbo zuwa part dinsu dakeda nisa cikin zabeera din sbd kusan sune na qarshe.




Umme nashiga palonta ta zube qasa tareda Dora hannu akai zata saki ihu juwairiyya tayi saurin rungumeta tana Kiran sunanta itama muryarta na karyewa dason yin kuka.


Haj maryam ma kuka takeyi wiwiwi itada nuratu dake wani irin kuka tana kwantawa jikin momyn Tata sukam yau wace irin baqar ranace agaresu.
##mamuh#






______________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


    Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________


#MIN QALB❤️
Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma


MIN QALB
mamuhgee


YANKAN BAYA
billyn Abdul


KIBIYAR AJALI
Miss xoxo


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano


Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 13_*
_mamuhgee_




ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!!


JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku,
Turarensu qarshene,
Qamshinsu na daban,
Kayansu tabbataccine,
Aikinsu ingantacce ne
shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa?
To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar.




ANNUR PERFUMES donjindadin customers munkawo muku dadadan turaruka na musamman masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari ina kano gaida layin massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.


ANNUR PERFUMES


TURAREN WUTA
KHUMRAH.
KULACCAM
MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)
DECORATIONS ..
KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)


TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!






Koda zarah tayi parking bakin flat dinsu motat MD na gurin tabbacin Yana ciki,
Fitowa tayi tareda zagayowa ta budewa amatu qofa tana murmushi tace"


Muje ko amatu.


Kallon flat din takeyi tana zaro Ido sbd tsarinsa da kyansa tun daga wajen,
Fitowa tayi motar tana zare idanuwanta Kan kusan motaci biyar dake gurin a jere kowacce sai daukar Ido takeyi ta nufesu zata shafa zarah ta riqota tana cewa'"


Muje ciki ki huta kina buqatan hutawa sbd hayaniyar da akayi gashi kinta kuka zai iya taba lafiyan babyn kinji Dan haka please ki kula.


Kallon zarah din tayi tareda shafa cikinta tana cewa''


Wannan cikin zaki kula Dani ne har qarshen rayuwarki idan kina Kiran na haifesa Dan Babu uban komai aciki sai wainar iyami ta safiyar yau danaci.


Magana kike?"zarah ta tambaya tana juyowa daga tura qofar babban palonsu.


Qaqalo murmushi tayi taba cewa"


Cewa nayi harna Fara kewar babata.


Riqo hannunta zarah tayi suka shigo cikin palon tana cewa"


Karki damu Inshallah zakiga jimawa sosai zakiga kin haihu lfy saiki koma gurin babah kafin daga baya saimu sake daukoki kidawo Nan shikenan kinzama ta Dr khalil dinmu.


Dan sunkuyar dakai tayi tana qaqalo kunyar Dole tana Dan murmusawa saidai suna shigowa cikin palon ta fiddo idanuwanta gaba daya tareda Fara jujjuyawa tana sakin baki tace"


Wayyo USI Zo kaga aljannar duniya a gidan Nan.


Kallonta zarah tayi tareda sakin murmushi tana qarasawa ta ajiye gyalenta da keys din motarta tana nufar kicin da kanta ta dauko ruwa Mara sanyi tadawo ta dube robar ruwan ta zuba a cup ta jawo amatun data zage tana taba duk Abinda ya burgeta tana fiddo idanuwa tana Kiran sunan usi.


Zaunar da ita zarah tayi tana miqa Mata ruwan tace"


Sha ruwa amatu Kuma ki zauna kada ki Fadi da wannan zagayen da kikeyi idan kin huta zakiga komai ahankali tunda anan zaki zauna kibari ki huta tukuna.


Kwankwade ruwan tayi ta miqawa Zara cup din idanuwanta nakan dining dataga me aikin zarah din na jere wasu irin manyan kulolin abinci masu daukar Ido da fresh fruits daga fridge sai hayaqin sanyi suke ta hadiye yawu tana satar kallon zarah dake sake zubo Mata ruwan fuskarta na bayyanarda annashuwar datake ciki ta Basu amatun da akayi.


Ganin yanda take kallon gefen dining yasa zarah juyawa ta kalli dining din saita fahimci kamar yunwa amatun keji ta juyo tasaki murmushi tana cewa'


Muje nakaiki kifara watsa ruwa zakifi Jin dadin cin abinci.


Bedroom 'din dake kusa da nata takaita da kanta tasake gyara Mata shi ta sauya Mata zanin gado tareda kunna AC ta sauyo Mata room fresheners tana cewa'
Duk Wanda kikaji bakyason qamshinsa kifadamin sai a cire Miki shi kada ya sameki.


Toilet ta 'dan wanke Mata sama sama Dan baida dattin komai sbd babuma Wanda yataba amfani dashi dandai ita dana bedroom dinta take amfani batama shigowa Nan dakin gaba daya bare MD dako nata bedroom din baitaba shigaba bare yashigo wannan.


Towel tabata sabo fil tareda kawo Mata shower gel din jaggins da sabbin undies da wata doguwar jallabiya Mara nauyi me dogon hannu ta fice tana cewa' idan kingama zankawo Miki abincinki har daki kibi ahankali a toilet karki Fadi Dan Allah.


Gaba daya hankalinta nakan dakin da ake nufin ciki zata zauna batamaji me zarah din ke fada ba ta fada Kan gadon da qarfi Yana jujjuyawa tace"


Wayyo amatu ko daga Nan aka tsaya qaramin burinki yacika kinshiga cikin Masa kudi.


Sai data gama juye juyenta akan gadon AC na shigarta tareda qamshi masu sanyin Dadi kafin ta miqe ta cire kayanta ta shiga toilet din Wanda tuni Shima ta rude da haduwarsa Wanda badan tayi aiki agureren masu girma ba kamar irinsu blue fox da bazata San ya ake amfani da irin wannan toilet din ba.


A toilet din tsayawa tayi gaban tangamemen madubin tana duba kanta tana shafa cikinta sai alokacin ta dawo hayyacinta gameda abinda yake faruwa ta lumshe ido tana tunano Khalil da halin dayake ciki,


Ita Sam Abinda Bata ganeba shine
Haj Mama data aikosu wannan aikin kukan datakeyi na qarya ne kokuwa?
Idan har kamar yanda tace MAHMOUD da KHALIL yayantane to meye banbanci Dan ance Khalil ne ba MAHMOUD ba?
Shin wannan abindaya faru yau din menene ainihin Abinda yake nufi sbd saitake ganin kamar yanda aka tsaro abin kamar ya sauya taku me matuqar hadarin gaske,


Ta Yaya zata haihu bayan batada ciki,
Ta Yaya zata auri Khalil bayan ba ranar haihuwa tunda ba ciki,
Shogowarta fa anan kamar tashigo wani mugun keji ne ta rufe kanta sbd tunda Babu ciki Babu ranar haihuwa,
Babu ranar haihuwa Babu ranar tafiyarta..


Shiru tayi tana jinjina Kai tace"


Ina buqatan ganin Haj Mama naji ni meye matsayina a yanxu.


Wankan tayi tana shaqar gel din me qamshin Dadi tafito ba wani shiririta ta shirya cikin kayanda zarah din takawo Mata tana cikin saka hula akanta zarah din tashigo daukeda tray din kayan fruits hafsatu me aikinta na bayansa daukeda tray din abinci.


Washe baki tayi tana zama qasa Kan qaramar carpet din dake gefen gado tana cewa"


Anty sannu da aiki kinata fama tunda nazo.


Aje tray din zarah tayi tana murmushi tace"


Amatu tunda aka banike nasan hidimarkice yanzu nafara harsai kin haifarmana me kama da Dr dinmu kokuma gwara dai ki haifar Mana me kama da MD dinmu dagani har Dr din saimunfi sonsa sbd MD shine 'dan uwanda Dr yafiso acikin familynsa gaba daya,
As for me nikuma MD shine rayuwata.


Apple amatu tayiwa babbar gutsura tana ci tace"


Anty Dr Yana ina yanzu?


Yar dariya zarah tayi tana zuba Mata Salad Kan dafaffen dankalin da aka dafa matashi da zallar Naman kaza da cabbage tace"


Dr Yana bangarensa Amma nasan tunda matarsa da babynsa na Nan bazamu Kai dare batareda yazoba Dan haka ki kwantarda hankalinki Dr nanan zuwa idanma baizoba zankirasa yazo.


To kawai tace tana cika bakinta da dankali da nama sbd 'dadin da abincin take Mata tace"


Anty idan nagama cin abinci mezanyi Kuma??


Bacci zakiyi ki huta amatu kafin zuwa gobe zanfadawa MD saimu kirawo Dr dina yazo afara dubaki da lafiyar baby.


Sarqewa tayi da qarfi tasaki tari Jin Abinda zaran tace.


Da sauri Zara ta dauki ruwa tana miqa Mata tana Mata sannu tace"


Amatu kodai abincin be Miki bane??


Girgiza Kai tayi da sauri har lokacin tana tari tace"


Ba Dr ne zai ringa dubani ba tunda shine Mijina??


Aje cup zarah tayi tana cewa''


Aa Dr bashi zai ringa dubaki ba munada Dr dinda zai ringa dubaki wato gynecologist Dr likitan Mata Wanda Nima shi nake gani sbd matsalar rashin haihuwarta.


Shiru amatu tayi tana tura abincin kawai sbd tasan ba jimawa asirinta zai tonu duk aka kawo wani likita yadubata zaisan batada ciki
Andi sakawa zaiyi a harbeta da kibiya sbd da gaskia ta fito.


Tana gamawa zarah tasata kwanciya bayan tayi sallah ta rage Mata sanyin AC ta fice bayan tasa hafsatu ta gyara gurin suka ja Mata qofa.


Shiru tayi tsawon mintuna tana tunanin goben idan likita yazo
Miqewa zaune tayi tana cewa''


Dole Naga Dr khalil yau nafada Masa kafin goben Amma dai yanzu inason Fara magana dasu usi.


Jakarta da aka saka cikin wardrobe ta bude ta dauko matacciyar wayarta ta lalulo numbrn USI ta Danna Masa Kira.
##mamuh##




______________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


    Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________


#MIN QALB❤️
Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma


MIN QALB
mamuhgee


YANKAN BAYA
billyn Abdul


KIBIYAR AJALI
Miss xoxo


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano


Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:02 AM - ': _*MIN QALB 11*_
_mamuhgee_






Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins hudu golden and red sbd girmansa ga kalar dasuka qara qawata palon,
Shine palon da dukkanin familyn ZABEERA ke meeting acikinsa qarshen kowane wata to wannan watan ma hakan ce tafaru dukkanin daukacin zabeeras dake jahar suna cikin palon kusan su sama da arbain kowanne yasamu guri ya zauna ana tsimayin fitowar me kankat wato Modibbo Wanda fitowarsa tayi daidai da tsit da gurin ya dauka sai gaisuwa kawai dake tashi Yana amsawa ta hanyar 'daga Kai batareda ya bude baki ba.


Zama yayi Yana bin kowa da kallon jinjinawa na riqe wannan al'adar dasukayi har idanuwansa suka sauka akan MD ZABEERA wanda ke zaune can bayani iyayensu dukkanin hankalinsa gabaki daya Yana Kan waya dayake karanta email din saqo daya shigosa,


Kallon zamansa Modibbo yayi har zuwa fuskarsa dake daukeda wani irin kwarjini da haiba ya jinjina Kai Yana cewa'


Tabbas Babu wani zabi daya wuce akan mulkin zabeera ayau taron naka ne.


ZARAH kuwa duk da ta shige cikin 'yan uwa da qawayenta 'yan uwanta Amma hankalinta na kansa akai akai take satar kallon gefen dayake sbd ganin yauma dai kamar ko yaushe arayuwarsa ya kebe ne daban duk da yanzu duk Wanda yashigo cikin qanne da tsaransa ma harma da wainda suka girmesa zuwa sukeyi suna gaidashi Wanda Shima yawanci daga Kai ne kawai bai cika bude bakinba Yana amsawa musamman sbd rashin sabo da Yan uwan duk wasu da dama baisansuba.


Khalil ne abokin zamansa akowane meeting tun quruciya Amma yau Khalil din baishigo da wuri ba Abinda baitabayiba ranar meeting wato latti.


Khalil kuwa yanacan ne hanyar gidansu amatu data Hana rayuwarsa da zuciyarsa sukuni,
Tsawon kwanakin Nan bayan haduwarsu da ita bincike yayi me kyau akanta sbd shigo da ita a rayuwarsa Dan sauya musu ingantacciyar rayuwa dakuma tunaninta daya kasa fita ransa da kansa,
Tabbas yasan babban laifine a zabeera neman aure a waje wanda bama ataba yiba asai yanzu dazai Fara shigo da tsarin karya dokar manya sbd bayajin zai iya hkr da maganar amatun a shirye yake daya tallefi yarinyarda zuciyarsa ta riqe a gani na farko Koda hakan na nufin barin zabeera ne barema yasan zai shawo kansu da taimakon MD.


Babban rashin sa'ar dayaci shine bayan isarsa kawu yayi Masa bayanin aiki tasamu ta tafi training Amma dai yabasa numbernta Dana usi din duk da shi Usin Rakata kawai yayi dawowa zaiyi.


Koda ya karba lambar agogo ya duba yaga yayi lattin meeting ga umme Bata gansa ba sai kiransa takeyi
sai bai tsaya Kiran numbrn ba yayi saving tareda dawowa zabeera cikin sauri sbd yasan zuwa yanzu anfara meeting din.


Yana qoqarin shiga gate din zabeera yaga motar 'yan jarida na tsayawa ta gate suna qoqarin gyara cameras dinsu ya Dan tsaya Yana kallonsu cikin mamakin meya kawosu musamman ma da zabeera basa muamala da duk Abinda zai hadasu da 'yan jarida sbd tsira da mutuncinsu da sunans ahalin,
Ganin yayi latti sauri yakeyi yasa bai tsayaba yashigowarsa,
Yanayin parking harabar gidan Kiran nuratu nashigowa wayarsa ya saki siririn tasaki Yana dafe kansa dake Masa ciwo sbd rashin bacci kwana biyun yayi rejecting kiran ko Ina bai tsayaba Kai tsaye ya nufi palonsu na meeting dasuke Kira da zabeera hall.


Yana shiga yaga har anyi nisa yayi saurin yin gefenda ya hango md zaune Ya lumshe fararen idanuwansa ya kwantarda kansa ta baya jikin kujerar dayake Yana sauraron Abinda ake fada cikin nutsuwa.


Qoqarin miqewa alhaji qarami yakeyi zaiyi mgn suka Fara jiyo hayaniya me 'dan qarfi tana tashi daga wajen qofa,
Sharewa sukayi alhaji qaramin yafara bayani Amma sai gaba hayaniyar keyi
Alhaji qarami ya kalli yakub babban 'dan alhaji qaramin yace"


Yakub dubo meke faruwa ne.


Miqewa yayi ya fita Dan dubowar sukuma suka cigaba da meeting din.


Mintuna biyu da fitar yakub sai gashi yadawo da sauri yazo gefen babansa yayi qasa da murya yafada Masa abin dake faruwa da sauri ya kallesa Yana cewa'"


Mene?


Kowa najin haka yayi tsit suna jiran jin abindake faruwa.


Je kashigo dasu""alhaji qarami yace Yana qoqarin cigaba da bayanin dayakeyi.




Sallama sukayi wadda tasa kowa juyawa hadda Shima dazaiyi maganar duk suka kalli qofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login