Showing 84001 words to 87000 words out of 108906 words

Chapter 29 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt

08 Jan 2025

7712

ZABEERA..


Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga Abinda tafada din.


Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace"


Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi.


Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri ba.


Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa''


Bari nashiga ko sallah banyiba wlh.


Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan juya yabi bayanta da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje.
Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba suka fice.


Tunda tagama sallah tayi wanka ta fito taci abinci take zaune Palo tayi waya dasu iyami,tayi da kawu,tayi da umme,tayi da Dr salman zabeera tayi da USI Wanda sukafi awa suna Magana duk Dan tasamu sauqin Abinda takeji aranta Amma takasa samun salama sai kawai ta kunna TV tafara kallo tana dariyar qarfin hali kamar wata wawuya.


Kallon agogo tayi taga qarfe goma harda minti arba'in ta miqe taje kicin ta hado tea tadawo ta zauna tana durawa cikinta idanuwanta akan kallo.
Goma da Sha daya da minti Tara taji bude qofarsu ta Dan kalli agogo taga lokaci taci gaba da kallonta tana Shan tea suka shigo ta Dan dago ta kalli anty zarah ta saki murmushi tace"


Lah anty Ashe fita kukayi banma Ankara ba wlh na dauka kina ciki kina bacci.


Kallonta yayi da mamaki saidai ko inda yake batada niyyar kalla ta tashi tana cewa''


Anty kawo kayan na riqe Miki.
Ta karbi kayan hannun anty zarah din yakai Mata har dakinta ta fito tana cewa''


Bari naje na kwanta gobema inada zuwa makaranta da safe.


Shigewa tayi ta rufo qofa ta Isa bakin gado ta zauna tareda sauke ajiyar da numfashi me qarfi idanuwanta na cikowa da hawaye batasan lokacinda ta kifeba Tana sakin kukan kewar Dr khalil dinta.


Washe gari ko abincin breakfast qin Yi tayi ta wucewarta makaranta taga keys dinta na mota ya ajiye Mata a palon taqi dauka ta tafiyarta.
Bata dawoba sai yamma tayi shigewarta bayan tashiga har dakin anty zarah sungaisa.
Washe gari ma haka takuma ficewarta ba Wanda yaganta sai abin yazama kamar tana wasan buya dasune Dan tasawa kanta zama very busy kullum Babu me ganinta take fita har gwara idan tadawo sukan gaisa da antyn tata ogan gidan kuwa Sam taqi Bari suga juna tuni kewar su Anty salamatu da Muhammad suka sanyota gaba gashi meenat batanan bare taje gidanta,
Wata Rana idan tafita shopping kawai take zuwa idan ba makarantar sbd kawai ta Hana kanta zama gidan.
Kusan kwana takwas kenan tana wannan wasan buyan dasu duk da itama ta matuqar gajiya da wannan yawon hutu take buqata Amma bazata iya zama gidan ba matuqar ba tafiya sukaiba sbd har yau fama take da ciwon zuciyar Abinda idanuwanta sukai Mata gani shiyasa ta zabi raba kanta da zaman gida.


Yau sai magriba tadawo gidan amatuqar gajiye take Bata tararda kowa agidan ba da alama sun fita basa Nan Dan har dakin anty zarah tashiga Bata nan sai kawai tayi wankanta tayi sallah ta sanya wata qaramar riga Mara hannu red da bumshort baqi wanda ko cinyarta bai saukaba sosai tafito ko dankwali Babu akanta taje ta sanyawa qofar shigowa key tana sakin numfashi Dan rabonta data sakata acikin gidan tun ranar dasuka Zo tasaba Bata cika son Kaya masu nauyiba yanzu kullum kayanta gajeru ne dasuna sukadai Amma tunda sukazo take a takure.


Kicin ta nufa ta hada celeals din Muhammad Tasha acan kicin din Tasha ruwa tadawo Palo zata zauna sai ganin mutum tayi zaune Yana waya a natse cikin tsananin firgici da tsoro ta bude baki Yana lurada Abinda zatayi ya janyota ta Fado kansa ya sanya hannu daya ya rufe Mata bakin Yana kallon cikin tsakiyar idanuwanta dake kallonsa ahankali yace"


Shihhh wayana me mahimmanci ne don't make a sound..


Tsit tayi tana kallon bakinsa dake Magana da Wanda yake wayar cikin burgewa da rashin garaje.
Maida kallonta tayi Kan qofar shigowa taga tananan rufenta to kenan Yana dakinsa Koda tayi tunanin basa gidan.,
Qofar dakinsa ta kalla batasan lokacinda tace"


Ina anty zarah??


Wani kallo ya juyo yayi Mata na tsawon mintuna kafin ya datse wayar dayakeyi ganin yafara rasa gane Abinda suke tattaunawa ya ajiye wayar Yana kallon fuskarta da ba annuri ya sake matseta cikin jikinsa yace"


Mezaki Bata da kike tambayarta?


Qin kallon fuskarsa tayi tafara qoqarin qwacewa tana cewa''


Sakeni kada ta fito ta......


Menene koyaushe kike cewa kada ta fahimta?


Kallonsa tayi a gundure tana sake qoqarin qwace jikinta tace"


Matarka ce Dan haka bazataji dadin ganinka da wata ba..


Bakinta ya kalla cikin taushin muryar son qureta yace"


Hakan kikeji shiyasa kike ganin kaman itama hakan takeji.
Da sauri ta kallesa tace"


Menene?
Ni banma San me kake cewaba.


Matsota yayi ta qarasa mannewa jikinsa ya kalli fuskarta zuwa bakinta dazaiyi kissing saikuma ya fasa ya miqe da ita a jikinsa ya nufi hanyar dakinsa sbd dukkaninsu idan ya fahimci matsalarsu ta baifi kowacce data Ganshi da 'yar uwarta ba Amma na Amatun yanason tabbatarwa ne idan yashiga zuciyarta kamar yanda yake tunani sbd zafin kishi me tsananin daya hango a idanuwanta.


A tsakiyar gadonsa ya kwantar da ita tareda sakar Mata dukkanin nauyinsa ta rintse Ido sbd idanuwansa dake son karya kuzarinta tadan juyarda fuskarta ta bude baki daqyar sbd mutuwar jiki tace"


Anty zarah zata.....


Rufe Mata baki yayi Ahankali da nasa Yana Dora hannunsa Kan wuyanta zuwa kirjinta dake harbawa da sauri har batasan lokacinda ta qanqamesa ba tana bude idanuwanta akan nasa idanun dake kallonta cikin wani irin yanayin daya qarasa kashe jikinta
Ya saka hannu yafara zare qaramar rigar jikinta ahankali tayi saurin rufe Ido sbd rigarce kawai ajikinta batada ko bra...


Qarar doorbell ne yasata bude idanuwanta ahankali ta Dora akan nasa idanun dasuka sauya kala ta janye jikinta ahankali tareda mirginawa gefe tana Jan duvet ta rufe qurjinta ya saki wani qaramin numfashi tareda tashi zaune yafara daidaita kansa ya miqe ya fita dakin.


Kobaa fada ba yasan zarah ce tadawo daga gidan qawarta dataje Dan haka Kai tsaye ya bude qofar fuskarta daukeda murmushi ta shigo zatai Masa Magana yanayinsa yasa gabanta mummunan faduwa ta kalli fuskarsa da sauri zatayi idanuwanta na cikowa da hawaye ganin hakan yasashi Dan dafe goshi Yana cewa''


Wat a hell""zama da Mata fiyeda daya.


Kallonta yayi Kai tsaye sbd bai iya kame kame ba yace"


Zan kwanta and kada ki nema AMATULLAH zata Kwana adakina after 2 days Zaki kwana so please don't make it too difficult for me kije ki kwanta I know you're tired.


Kadan ya rage anty zarah ta Dora hannu akai ta zunduma ihu
Tafi kowa sanin MAHMOUD din Dan Kai tsaye ne bai iya kwana kwana ba Amma Bata dauka rashin kwana kwanarsa yakai hakaba da zai iya haikatata wata ran.
##mamuh#
6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 40_*






Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana tunanin inda rayuwa ta daukota tun kuriciya da inda zata kaita kokuma inda yakawota yanxu,


Auren mijin wata Sam baya cikin mafarkinta ko tunaninta sbd itama tafison ta bugi gaba da mijinta natane bawai na wata tazo ta aura ba Wanda koma dai yayane mijin wata ta aura za'a ce,
Babbar damuwarta yanxu shine rashin sanin makomarta a wannan auren yanxu,
Tarigada tasani tabbas yaudarar kanta take da tunanin rabuwa da Rabin ran Anty zarah sbd a zabeera Kam ba Maganar saki sai bisaga girmammiyar qadda ko mutuwa,
To ita ga mutuwar ma ta raba Amma Basu barta ta tafiyarta ba an daureta da auren Wanda takewa kallon ya haramta gareta sbd Yana mijin Zarah....


Motsin bude qofa taji Wanda yasata sake rintse idanuwanta tana sake yin tsit sbd sanin shine yadawo
Bata tunanin iya kallonsa sbd dai ba tantama a daki daya zasu kwana dan haka gwara ta lafe gari ya waye su Dan inda dare yamusu.


Kallonta yayi yaga yanda take lullube har Kai sai bai damuba ya nufi closet ya tube yafada toilet yayo wanka Yana fitowa shima kayan baccin ya dauka ya sanya tareda fesa mist ya nufi gadon ya hayewarsa ya kwanta tareda Dan Jan lullubin ya shige a gajiye yake shiyasa Yana kwantawar bacci ya daukesa ba Bata lokaci.


Mamakinsa takeyi ta yanda ba wani tunani ya hau gadon ya kwanta bayan yaganta akai kwance,Abinda Bata saniba shi Sam baima San wani Wai ka kwanta qasa ko Kan kujera ko wani dakin Kan kowane dalili ba Abu daya yasani baya sauya gurin kwanciyarsa akan komai,
Ko agida zarah ce ma idan ta fahimci Yana tattareda gajiya wani lokacin take komawa dakinta ta kwana tabarsa ya huta shikuma tunda raayaintane wannan baitaba hanata tafiyar ba saima sakewa dayafi Yi da hakan wani lokacin
Tana cikin tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.


Da asuba saidata Gama sallah ya tadata ta tashi tayo alwala da jallabiyarta tayi sallar tana gamawa ta cire Takoma tayi kwanciyarta Takoma bacci abinta sbd itamadai bazata iya takura kanta sbd shi ba musamman ma data lura idan ta takura kanta din ko ajikinsa.


Shima tana jinsa yagama wayoyinsa yazo ya kwanta kusan atare bacci Yakuma daukesu Basu farkaba sai guraren 10 na safen.
Itace tafara bude idanuwanta ta sauke akan fuskarsa dake fuskantar tata tafara kallonsa ahankali tana tuno haduwarsu ta farko data biyu data uku duk agun sata ne take taji kunyar abin nadawo Mata har batamasan tana rufe fuskarta ba tana girgiza Kai saijin tayi cikin muryar bacci yace"


Kadama kifara wani banzan tunani akaina I can smell your blushing..


Zaro Ido tayi da sauri cikin wata sabuwar kunya Amma saidatace"


Wane tunani zanyi akanka dazaisani Abinda kace kanaji?ni bana tunanin komai....da sauri ta yunqura ta tashi zaune zata sauka ya riqo hannunta Wanda yasata saurin juyowa ta kallesa zuciyarta na Fara bugawa da qarfi shima ahankali ya bude idanuwansa dake rufen bacci baigama dakinsu ba ya sauke akan fuskarta tayi sauri dauke Ido zuciyarta na tsananta bugu har kirjinta na sama da qasa
Ya gangaro da idanuwan nasa Kan kirjinta dake sama da qasa da sauri alamar zuciyarta ce ke harbawa da sauri batareda yayi Magana ba sai ya saketa ta dira da sauri ta shige toilet batareda tasan abinyi ba sai kawai ta bude sabbin brushes din data gani ta dauki daya tafara brush tana kasa kallon fuskarta ko a madubi sbd Jin wani iri kamar kunya kamar fargaba da tsoro.


Murtsike kunyarta tayi ta fito tana daure fuska ta tarardashi zaune Kan sofa Yana kunna wayarsa daya kashe da asuba ta nufi fridge ta bude ta aduko lemun carrot da lemon ta zauna a wata kujerar ta bude tafara Sha ahankali batareda ta kalli inda yake ba.


Yana cikin toilet aka kawo musu breakfast din dayayi oda da kayan sawa ta karba tareda ajiyewa tana qoqarin duba kayan sbd jeans ne da riguna take gani Abinda takeda burin yiwa Dr khalil zabeera kwalliyarsa har saiya manta da kowace mace duniya Bayan mahaifiyarsa Amma Ashe basuda wannan rabon.


Astaghfirllah" tace tana ajiye kayan daidai fitowarsa
Taso Fara cin abincin Amma gabaki daya Babu Abinda ta taba gani aciki bare tasan ya akecinsu shiyasa ta haqura harya Gama Jan ajinsa da ja Mata Rai yazo ya zauna Kai tsaye tace"


Nifa yunwa nakeji bansan wanne ne naciba wanne ba'a ci Yi sauri ka nunamin....


Baisan lokacinda ya juyo gaba daya Yana kallonta ba wato yamayi sauri...


Irin yanda take kallon abincin yasashi sakin wani boyayyan murmushi akaro na farko
Jin shiru tafara hasala tace"


Nifa yunwa nakeji nace fa.


Baisan lokacinda bakinsa yace"


Ok" ba


Fara zuba Mata tea yayi ya miqa Mata kafin yafara zuba Mata egg source cikin boiled veggies sbs taji dadin ci Amma Ina tana shanye tea din taci spoon daya na abincin taji zuciyarta na neman tashi ta ajiye tana kallonsa tana girgiza Kai alamar bazata iya ciba.


Tea din yasake zuba Mata kafin yasanya spoon yacire komai na cikin tsakiyar burger dinsu ya miqa Mata yana nuna Mata Tasha da tea din.


Kaf tea din ita tashanye shi sbd shikadaine Abinda zata iya sawa cikinta shikuma tana kallo yanacin abincin cikin kwanciyar hankali ganin abin zai tayar Mata da zuciya yasa ta miqe ta shige toilet wanka.


Bata San yanzu akeyintaba Saida tagama wanka ta daura towel takasa fitowa ta zauna ciki ta shafa Neutrogena oil din data gani aciki tazo jikin qofar ahankali tace ya miqo Mata kayanta...harta juya ta tsaya cak sbd tuno hadda bra zai miqo kenan saiya taba Mata gidan nono da sauri ta fito tana cewa''


Barshi barshi nafito Zan dauka da kaina,. tsayawa tayi tana Masa kallon mamaki ganinsa zaune ko alamar ma zai miqo Mata kayan beyiba kamar yanda ta zata kenan da barinta zaiyi a toilet din tayita zaman jira.


Takaici yasanyata daukar kayan da qarfi tana daure fuska zuciyarta na zugata akan tabi takan qafarsa ta take Amma ta share ta nufi wardrobe ta bude ta dauko undies dinta tana juyowa taga bayanan kenan yashige toilet a fili taja guntun tsaki tana cewa''


Anty zarah kinada qoqari gskia.


Turarensa ta fesa kafin ta shirya cikin kayan ta tsaya tana kallon kanta tanajin wani iri sbd irin pencil jeans dinnan ne yakama Yan dogayen siraran cinyoyinta har gwara rigar is loose me Fadi ce sosai Amma ba wani tsayi gyalen jallabiyarta ta daura akai bayan tagyara Daurin talwataccen gashinta daya dan yamutse gurin bacci.
Zaunawa tayi abinta tana lallatsa wayarta sbd dama can ita Allah beyita da nuku nuku ba Kuma burintane samun wayayyar rayuwar Jin Dadi da sakewa, Bata samu daga Wanda taketa mafarki da buri ba wato Dr khalil dinta yanzun dinma bawai tana maida burinta akan MD bane kawai dai zata sakewarta ne bazata takura kanta ba shiyasama batai wata doguwar damuwar akan kayan ba.


Dagowa tayi Jin motsinsa idanuwanta suka sauka Kan budadden jikinsa dake tsiyayar ruwan wanka qugunsa Kuma daureda towel brown da sauri ta dauke kanta tana Dan Sosa kanta daya dau qaiqayin bazata.


Ganin da gaske shiryawa zaiyi gata a zaune yasata saurin miqewa Takoma gaban TV ta qurawa Mata idanuwa ko qyaftawa batayi tana jinjina ko inkularsa lallai wannan mutumin dasuke gani a zabeera Basu sanshi ba.




Tsaf ya shirya cikin qananan kayan wainda suke kalar nata sky blue jeans da farar transparent shirt ko zama beyiba ya kalli Inda take yace ta tashi suje.


Da sauri ta miqe zata dauko jallabiyarta yace no need for that
Aiko tabiyosa suka fice.


Wata kyakkyawar mota ya karba daga hotel din tareda driver suka fita.


Gurin abokanan aikinsa suka Fara zuwa wani hotel dake kusada wani ruwa acan suka kwasa sukai bakin ruwan taredasu da abokin nasa mr folaye da matarsa me sabon qaramin ciki daya 'dan fito kadan.


Sakewa tayi da meenat matar folaye sbd yanda tayita janta ajiki take suka Fara sabo anan ne ma taci abinci sbd na Nan yanada dama sosai akan na hotel dinsu sbd akwai chips da noodles akwai pasta duk tasamu taxi daga Nan suka kwasa zuwa wani farm house inda Nan ma sunyi ciye Amatu tasamu abokiyar ciye Nan tasake suka ringa cin duk Abinda bakinsu zai iya daukar dandanonsa Dan itama meenat zuwansu na farko ne Nan da mijinta yayi da ita.


Basu Fara Shirin komawa ba sai dare sosai inda taji tafison masaukinsu meenat yafi Dadi ba kunya ta roqesa su koma can ga mamakinta kuwa baice komaiba Amma saigashi anyi musu folaye yasa anmusu reserving suite sukai kwanciyarsu anan.


Washe gari sukaso komawa Amma suka shiririce itada meenat wani gurin shopping da aka kaisu gashi yau dinma qananun kayan ne ajikinsu na yau sunfi daukar kalar fatarsu da yimusu kyau sbd black ne gashi ba laifi dukkaninsu sunada hasken fata matuqa


Suna zaune a wani snacks and coffee restaurant dake bakin ruwa saiga Kira yashigo wayarsa Yana dagowa yaga video call zarah na Masa.


Sam baisan meyasa zarah yanzu take Masa video call ba Bayan shi tunda sukai aure bai tana cewa sunyi video call.


Dauka yayi a natse saigata ta bayyana kyakkyawar fuskarta dataji simple makeup na Masa murmushi
Ahankali ya sauke numfashi Yana amsa gaisuwarta da dorawa da cewa''


You look great.


Wani irin Dadi ne yakusa kasheta sbd baitaba yaba kwalliyarta ba sai yau din ta washe baki tana kallon kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani sirrin kwarjini da kyau tace"


Thank you,ya kake?ya Athens?


Dan kallon wuyanta dake bayyane sbd fadin wuyan rigar jikinta yayi ba laifi yanayin shigar ya burgesa baisan yaushe zarah tafara koyan saka irin kayan Nan ba ya bude baki a hankali yace"


Alhmdlh..


Amatu dake hotuna da meenat tunda yafara wayar hankalinta ya Dan koma kansa tafara qoqarin sharewa gano da anty zarah yake wayar meenat ta kalleta tana cewa''


Da waye MD ke video call and he seems to be relaxed and cool da yanayin wayar?


Numfashi Amatu ta sauke tana murmushi tace"


Da matarshi yake waya antyna.


Kallonta meenat tayi dakyau tana sake duban MD dako inda suke baya kallo sai kawai tura Amatun kansa da qarfi tana cewa''


Oh I'm so sorry I lost my y balance.


Kyakkyawar faduwa tayo ajikinsa sbd Saida gaba daya qirjinta ya hadu ya manne da nasa dayake shima a bazata yajita jikinsa saiya riqeta sbd karsu Fadi qasa daka Kan kujerar dayake.


Anty zarah maganar da zatayi bace Mata tayi sbd ganin Amatun jikin MD ba qaramin raunana ganinta da zuciyarta yayi ba ta maida kallonta Kan kayan jikin Amatun saitaga komai iri dayane Dana MD din banbanci nata na Mata nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da wani irin kuka Mai ciwo.


Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba.


Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login