Showing 81001 words to 84000 words out of 108906 words

Chapter 28 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt

08 Jan 2025

7709

Amma kin zauna kin qoshi abinki.


Anty salamatu kenan
Wane miji Kuma?
Ina umme ko bacci takeyi?


Dining anty salamatu ta nufa da abincin tana cewa''


Umme ta tafi gidan yarta tace da Dan nisa daga Nan acan zata zauna sai ankwana biyu zata Zo.


Kallon tsoro takebin anty salamatun tana cewa''


Meyasa zata tafi to?
Da Ina Nan wlh can zanbita nayi zamana acan Nima.


Abincin anty salamatu ta jere Masa a dining din bayan ta diba ta wuce daki batareda tacewa Amatun komaiba sbd takaicin zancenta na cewar zatabi ummen.


Itama miqewa tayi jiki a sanyaye ta nufi dakin saita tararda anty salamatu ta maida Mata kayanta dayan dakin da umme tabari sbd yafi girma ta jere Mata kayanta tsaf a wardrobe ta sake gyare dakin.


Tubewa tayi tayo wanka tazo tayi sallah Tasha maganin ciwon Kai ta kwanta take bacci yayi gaba da ita.


Wanka yayi shima ya fito Bayan yayi sallah ya zauna dining ya dauki box din chips daya yaci da Burger yasha energy drink ya dawo Palo ya zauna ya kunna news Yana kallo sama sama Yan amsa wayayo har tsawon lokaci kafin yakoma bedroom dinsa.


Washe gari Babu Wanda yagansa acikinsu sbd bai fitoba kwata kwata sai yamma lis yafito ya fice bayan fitarsa ya aiko da mota aka kaisu asibiti Basu jimaba aka dawo dasu.


Washe garima hakan ne yafaru ankaisu asibiti Kuma Basu sakashi a Ido ba,
Kwanaki suka Fara tafiya Amma Babu wani sabon alamari a rayuwar zaman gidan,gabaki daya Basu cika ganinsa ba sai jefi jefi sbd baya zama idan Kuma Yana Nan bai cika fitowaba,
Kullum ana kawo musu abinci so uku a yini har Anty salamatu tagaji dacin na wajen tafara Dan yimusu dubarun abinci dayake ta iya girki sai suka koma cin nata ganin sunfi son na gidan sai yasa akazo aka dauki anty salamatun aka kaita shopping din komai na abincin dazata iya girkawa.


Yanayin zaman yafara gundurar anty salamatu sbd Sam ko gaisuwa Bata Shiga tsakanin Amatun da MAHMOUD din saitaji duk ta tsargu da zaman gidan ta sanarda Amatu tafiyarta zatayi yabi umme inda take idan har Bata sauya ba ta ringa gaida MAHMOUD din har dakinsa Koda bai fitoba.


Da farko share zancen antyn tayi Amma dataga alamar da gaske antyn tafiya zatayi Dan harta Kira umme saita Fara zaman Palo tana kallo ko wayoyi idan yadawo kokuma idan yafito zai fita takan gaishesa batareda ta kallesa.
Ta bangaren Muhammad kuwa suna ganin cigaba sosai sbd sauki yafara samuwa Dan yanzu Yana kuka sosai kamar sauran babies wani lokacin idan taje asibitin sukan batashi tabasa nono da kanta basai ta tatsa Masa a roba kamar yanda ake Masa ada Kuma Yana 'dan kamawa yanzu ba laifi.


Yau zaune take a Palo ita kadai tana kallon wayarta data gama waya da USI tanason Kiran anty zarah Amma kamar koyaushe tanajin kunya da nauyinta takasa Kira sbd batasan ta inda zata Fara yiwa anty zarah din bayani ba.


Bude qofa taji ahankali cikin nutsuwa sbd baya komai cikin hayaniya yasa tagane shine yafito daga dakinsa
batai niyar juyawa Amma ta daure ta 'dan juyo a sace ta 'dan kalli qofar.


Sanye yake cikin qananun kayan Shan iska sky blue me haske sosai sai slippers farare dake qafarsa da keys din mota da waya a hannunsa da alamu gurin Shan iska zaije.


Anty salamatu ce ta fito sanye da riga da skirt na atampa ganinsa da yanayin shigarsa yasa tadanji kunya tana dauke Kai tareda yaba kyau da kwarjini irin na MAHMOUD,
Har zata koma daki cikin Jin nauyi data Zo ta darshe tsakanin amare Kuma qanne saita Dan tsaya batareda tajuyo gaba daya ba tace"


Inason zuwa gurin umme nai Mata kwana biyu shine nace ko za'a kaini?


Zulum Amatu ta miqe tana kallon anty salamatun cikin mamaki da firgici tace"


Nima zanje Bari nashiryo.


Ko kallonta Babu Wanda yayi acikinsu ya nufi qofar ficewa Yana cewa''


Muje na ajeki da kaina.


Ko Kaya anty salamatu Bata tsaya daukowaba sbd kada Amatu tafito Basu tafiyarsu ba tabu bayansa da sauri.


Aikuwa kodata fito cikin Shiri tana gyara zaman gyalen jallabiyar dake jikinta taga ba kowa a palon ta nufi qofa da sauri ta fito ta hau lift zuwa qasa tana Isa suna barin harabar building din ta tsaya tana bin hanyar gate din futa da Ido tanajin wani Abu aranta na baqin ciki Amma hakanan ta hkr ta juya Takoma ko daki Bata shigaba a Palo ta zauna baqin ciki da damuwa na cinta ta Yaya zasu tafi su barta ita kadai a gidan daga ita sai shi.


Har kusan qarfe goma sha biyun dare baidawoba tana daki duk da kwance take hankalinta na qofa taji shigowarsa sbd Sam takasa samun sukuni ita kadai cikin gidan aqalla dai taji motsin mutum cikin gidan zai rage tsoronta.


Sai qarfe daya saura taji shigowarsa ta sauke ajiyar zuciya daga kwancen tareda juyawa ta gyara kwanciyarta tana rufe Ido.


Washe ma haka ta wuni ita kadai gidan bataga dawowarsa ba sai cikin dare ahaka sukai kwana uku take hankalinta yafara tashi sbd tun tashinta Bata Saba rayuwa gurinda Babu hayaniyar jamaa ba Sam Bata taba ma zama ita kadaiba sai abin yake Bata tsoro shiyasa ranar kwana ta biyar tana kwance cikin damuwa tunda safe taji fitowarsa ba Shiri ta wuntsulo daga Kan gadon ta fito ko wula da suturar arziki Babu ajikinta tana futowa shikuma Yana zama Kan Kan dining da cup din ruwan tea a hannunsa sai jinta yayi kwasam akansa ya dago idanuwansa ahankali ya zuba mata ganin suturar dake jikinta take ruwan tea din dake cikin bakinsa suka Dan sarqesa ya dauke Kai Yana Dan tari ahankali batareda ya juyo yakuma kallontaba ya miqe zai bar gurin takuma saurin Shan gabansa tana cewa''


Bazan iya zama anan ba inason zuwa gurinsu umme.


Tsayawa yayi cak tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasukai 'dan ja sbd tarin da yayi Yana kallon fuskarta yace"


Su umme nada damar barin Nan ke Kuma akan dalilin me Zaki bar Nan?


Sakin baki tayi tana kallonsa Kai tsaye tace"


Akan dalilin ni kadai nake rayuwa kamar Mara galihu,
Inason zama tareda mutanen dasukan darajata sukasan su......


Idon daya watsa Mata yasa maganarta yankewa tana Dan sauke Kai daga kallon idanuwansa qasa qasa tace"


Nagaji.


Ringing din wayarsa yasashi dauke idanuwansa akanta ya dauka Yana cewa''


I will be there in 10min and the ticket make it 2.


Wuceta yayi Yana cewa''


Kije ki shirya.


Juyawa tayi ta koma daki tana cewa''


Dadai yafi sbd nagaji da wannan zaman rashin yancin gwara ka kaini gurinsu Kona farfado rayuwata.


Tsayawa tayi gaban madubi zata tube tayi saurin kallon jikinta tana Dan fiddo idanuwa sbd ganin kayan jikinta tana furta taslimah...


Rigar bacci ce ajikinta gajera sosai wadda ko cinya Bata Gama hawaba Kuma irin me gidan nonuwan nan ce agabana yadin me sulbi sosai gashi rigar baqace saita fiddo kyan farar fatarta.


Dafe goshi tayi tana sakejin damuwar abin tareda kunya me tsanani kafin dai ta tuben ta nufi toilet.


Wanka tayo ta Dan shafa man jaggins kadan sai spray da body mist data shafa ya sanya doguwar Turkish gown royal blue tayi rolling gyalen tafito da handbag dinta qarama sai wayarta.


Qoqarin zama takeyi saigashi yafito sanye cikin qananan Kaya blue black shima sai qamshinsa ya doke nata ko kallonta baiyiba ya nufi kofa Yana duba agogon hannunsa.


Mr Jeremy ne yazo daukarsu atunaninta gidansu ummen zasu Amma taga sunzo asibiti suka Gama Abinda zasuyi kafin suka nufi gurin shiga train Wanda yasata bude idanu tana kallon tsarin gurin suka shige first-class tun kafin su zauna aka Fara gabatar musu da jaridar karatu da abin sha,


Wayarsa ce tayi ringing Yana dubawa yaga video call ne zarah ke kiransa Abinda Bata taba ba
Da farko yaso qin dauka Amma ya dauka daidai lokacinda Amatu ta juyo zatai Masa Magana saigashi idanunsu sun gane musu juna itada anty zarah baro baro jikin waya take kowaccensu gabanta yayi mummunan faduwa sbd ganin Yar uwarta musamman ganin irin adon dake jikin kowaccensu
Amatu ce tayi saurin sauke Kai zuciyarta na harbawa da qarfi adon anty zarah din na cika Mata Ido sbd kwalliya ta musamman anty zarah tayi cikin wasu qananun Kaya ba komai akanta sai gashinta data zubo sbd kawai ta burge mijinta.


Itama Kuma anty zarah idanuwanta Basu sauka akan komaiba sai akan fuskar Amatun data canza sosai tayi fresh kamar tana cikin kwanciyar hankali da amarci.


Shikuwa ganin yanayin shigar zarah din tun kafin tayi Magana ya datse Kiran Yana kashe wayarsa gabaki daya sbd kada aganar Masa iyali.


Take Amatu taji tafiyar tafita ranta jikinta yayi matuqar sanyi batasan lokacinda ta juyo ta quresa da kallo ba tanason karantar yanayin dayake ciki da Abinda yafaru yanzu din ba.


Jin idanuwanta akansa yasashi Dan kallonta yaga batada niyar barin kallonsa
ahankali cikin cool muryarsa me taushi yayi gyaran murya
Ta dauke kanta ahankali har lokacin zuciyarta Bata daina bugawa da qarfi ba.


Tafiyar awa daya da rabi sukayi saigasu awani gari dayake da tarin sanyi da qarancin mutane Wanda daga gani garin shaqatawar Yan honey moon ne sbd yanayin tsare tsarensa.


Wani boyayyan hotel suka sauka Wanda ya tsarinsa yasa take tunanin shine babba agarin sbd komai nasa farine.


Aiki yakawosa shiyasa suna shiga suite dinsu ko zama baiyiba ya fice yabarta bayan yayi odar abinci dakomai yasa akawo Mata.


Itakuma zama tayi bakin gado jikin asanyaye sbd har lokacin Bata daina ganin anty zarah da kallon datake Mata a idonta take tasakejin matsuwar gobe tayi sukoma kodan Takoma gurin Muhammad dinta da akace za'a iya Basu sallama kwanakin
Gabaki daya Jin haushin komai taji tanasake yi
Daqyar tagama Abinda zatayi ta kwanta Bayan ta sanya riga da wandon bacci masu Dan nauyi da aka kawo musu set na mace Dana namiji ta rintse idanuwanta tana son bacci ya dauketa.
##Mamuh#
6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 41_*


*_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_*


Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi Amatun dauke wuta tana cewa''


Anty zarah sannu da zuwan bazata.


Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema ta rasa sai kawai ta 'dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace"


Amatu sannu da gida mun sameku lfy?


Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki tana cewa''
Alhamdulillah anty.


Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba'a iya ganewa sai kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana 'dan satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye tray din gabansu tace"


Dady sannu da zuwa.


Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty ko ruwan yayi sanyi ne da yawa.


Batareda ya kalletaba yace"


Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita urgent.


Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace"


Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner.


Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa''


Ina zuwa anty idan akwai Abinda za'a yi Miki ki kirani.


Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah.


Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi tana cewa''


Ya Salam.


Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.


Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage source me kidney aciki.


Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren 7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta 'dan gaji.


Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci.


Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai tsaye ya nufi dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa.


Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda tray
Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta shiyasa ya bude matan.


Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye abincin tana cewa''


Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce?


No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha magani.


Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace"


Zansha magani Ina buqatan ruwa.


Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa.


Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa ya miqe yafito hannunsa daukeda magani


Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani
Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace"


Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka..


Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana kallon tsoron dake bayyane fili akan fuskarta da bakinta dake Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta ankare da inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa tace"


Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam.......


Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe tace"


Dan Allah anty zarah nake gudun ta.....


Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi.


Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama.


Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta durqusa tahau kwashe plates din tana cewa''


Anty zarah Yi hkr wallahi.....


Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da danne kukan dake zuwar Mata tace"


Saida safe zanje na kwanta.


Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake Shirin kufce Mata.


Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA.
Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar.


Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school.
Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be tashiba tunda bataji motsinsa ba.


Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi.


Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta ma anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace"


Good morning.


Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa ta dubo Amatu.


Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita to
Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce makaranta.
Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi ahankali.


Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa noodles da kwai itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd yafi Mata dadi.
Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa sukuma suna tafiya.


Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta..
Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace"


I love you so very much MAHMOUD

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login