Showing 42001 words to 45000 words out of 108906 words
Chapter 15 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt
saiga kiransa yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira da numbernsa tacan tayi saving.
Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba sbd gaban anty zarah ne tace"
Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai.
Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a natse yace"
Baga zarah Nan ba.
Shiru tayi kafin ahankali tace"
A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin tsaro da kulawa idan har bakanan,
Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa.
Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun nutsuwa yace Mata"
Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda zanbari yasameki sai qaddara.
Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita baqar wahala idan zatayi period,
Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima ana Yan dubaru har tagama period din tukuna.
Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data daina cin zaqi.
Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya takeba.
Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah.
Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa ya kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa.
Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku,
Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri.
Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan azaba.
A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace"
Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata takira Mata Dr Fatima.
Umme Kuma"""
Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta.
Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu.
Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri.
Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci.
Umme zarah ce
Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai.
Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa''
Uban Dr Fatima zankira muku,
Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki wlh.
Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a jikin dogon wandon Amatu din.
Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace"
Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace.....
Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin rudewa tana kasa Magana.
Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be
Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya sauko zarah din na bayansa.
Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu
Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin dake jikinta
Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito Yana cewa''
Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe.
##mamuh#
ZAFAFA BIYARğğğ
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 22_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğğ¾ââï¸ğğ½ââï¸?
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*ğ¯ğ½ââï¸ğ¯ğ½ââï¸?
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾
************
Cikin kulawa yake tambayarta ya jikin nata itama cikin kulawar take amsawa tanason fada Masa komai na Abinda yafaru tun zuwansu asibiti tanajin nauyin anty zarah
Ganin hakan yasa anty zarah miqewa tayi toilet Dan taimakawa ta hada Mata ruwan wanka tana hamdalar cikin dayake lafiya kalau Babu Abinda ya samesa.
Tun tanayin wayar a zaune harta Dan jingina da Kan gadon tana rufe idanuwanta tana sauraran abubuwan da Dr ke fada Mata tana murmushi sbd sbd girmqn mahimmancinta a rayuwarsa yake fada Mata Yana Mata fadan ta rage ciye ciyen kayan shiririta.
Ganin ba gamawa zasuyiba yasa anty zarah karbe wayar tareda kashewa Tana cewa''
Tashi kije kiyo wanka yanda jikinki zai qara warwarewa,
Miqewa tayi tana murmushi har lokacin ta cire kayanta tareda daura towel ta fada toilet din.
Ahankali take wanka tana tunanin Rabin ran Anty zarah ta yanda zai iya wanke jinin daba na matarsa ba,
A yanda yakeda tsafta da Shan qamshin Nan Bata tunanin zai iya taba rigar bare ya wanke da kansa,
Duk yanda za'ayi ita zata karbo rigar ta wanke da kanta tunda jinin natane koba komai abin kunya ne gareta wani ya taba jinin al'adarta Wanda ba mijintaba.
Kodata fito wanka anty zarah na dakin tana sauke abincin da hafsatu tashigo dashi Wanda akayi domin Amatun kawai.
Tasamu qarfin jiki matuqa sosai datayi wankan shiyasa cikin walwala ta shirya bayan tafara shafa Mai kadan ta sanya doguwar riga me Fadi sbd ganin anty zarah nata kallon cikinta cikin kulawa itadai lafiyar cikin ce a gabanta.
Zama tayi suka hau breakfast tareda anty zarah din suna 'dan taba firar Dr daya damu da haryana cewa zai dawo yau daqyar ta hanasa.
Suna gamawa ta hau gadonta ta mimmiqe Anty zarah takira hafsatu tana Mata tausa ahankali ahankali har bacci ya dauketa sai alokacin Anty zarah tasaki ajiyar zuciya tareda miqewa tabar dakin.
Dakinta tafara zuwa ta sauya kayan jikinta tareda qara shafawa jikinta body mist ta fito tana gyara zaman qaramin qyalen dake daure akanta Wanda yaqarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta nufi dakin mijinta.
So daya tayi knocking tareda bude qofar bedroom dinsa tashiga bakinta daukeda sallama Mai sanyi.
Tsaye yake gaban mirror daureda brown towel iya qugunsa Yana shafawa jikinsa spray din Hugo boss fuskarsa a fuske kamar dai koyaushe.
Kallon budadden bayansa tayi dayake fari tas Babu tambon sai qyalli yakeyi kamar na mace har zuwa wuyansa da faffadan qirjinsa datake gani ta jikin mudubi Wanda tuni yaji ajikinsa shi take kallo saiya juyo ahankali yayi Mata kallo daya yaga yanda take kallonsa cikeda so da qaunarsa saiyaji zuciyarsa ta danyi sanyi sbd yasan zarah mace ce me tsananin hakuri da juriya Wanda yasa yake matuqar respecting dinta akan hakan,.
Gabanta ya qaraso ahankali ya tsaya Yana kallon fuskarta itama shi take kallo tana jin sabuwar soyayyarsa na shigarta ahankali ta matsa ta shige jikinsa tareda zura hannuwanta bayansa ta rungumesa ahankali tana kwantarda kanta akan qirjinsa tareda lumshe ido tana sauke boyayyar ajiya zuciya.
Sai daya jima shiru Yana sauraran bugun zuciyarta dake dukan qirjinsa kafin ya daga hannuwansa ya rungumeta ahankali tareda lumshe ido ya sauke numfashi,
Sun dauki kusan mintuna biyar ahaka shiru Babu me motsi kafin ahankali ya dagota daga jikinsa ya dauketa gaba dayanta ya nufi gadonsa da ita Yana kallon fuskarta data soke cikin qirjinsa,
Yana kwantar da ita Kan gadon yayi Mata rumfa da fadadden qirjinsa Yana Kai hannu Kan zib din gaban jallabiyarta.
Bayan wasu lokuta haryayi sabon wanka ya fito ita alokacin take qoqarin saukowa daga gadon tayi saurin daukar fadawa toilet din nasa duk da shi mutum ne dabai cikason wani na amfani da toilet dinsaba Amma kasancewar yanzu Basu kadai bane Dole bazata iya fita ahakaba kamar da wani zai iya ganinta.
Wanka tayo tafito lokacin harya shirya cikin farin filtex transparent da hular qube coffee brown Yana fesawa jikinsa turarensa na IMPERIAL MAJESTY.
Kayanta ta maida bayan tagama goge jikinta ta shafa oil kadan tareda turarensa.
Sai alokacin ta tunoda Abinda yakawota ta kallesa Yana qoqarin daukar wayarsa dake Kan bedside cikin taushin murya tace"
Am...amm dama rigar dazu ta jikinka nace ko zaka kawo na bayar a wanke sbd Naga ta samu lalacewa....
Cak ya tsaya daga Abinda yayi niyar Yi hakanan yaji maganar Tata kamar ta ciza ransa,
Idan tunaninsa na aiki daidai yasan me wankin zarah din namiji ne Wanda kusan duka familyn shike yiwa wasu da yawa daga ciki wanki,
Tana nufin shi gardin zata bawa jinin dayake sirrin Amatune ga wani gardin ya wanke???
sake 'dan tamke fuska yayi tareda juyowa ahankali kamar zai kalleta saiya fasa ya juya ya dauka wayarsa batareda yabata amsaba yafara qoqarin barin dakin.
Saurin biyosa tayi tana cewa''
Nace bakajiba rigarka ta yau da safe nakeso kabani zanbawa wa....
Kallon daya dago yayi Mata yasata matsawa baya kadan tana sauke Kai zuciyarta na bugawa da sauri.
Kamar zai wuce baiyi Magana ba saikuma ya tsaya batareda ya juyo ya kalletaba cikin sautinsa me daukan hankali yace"
Karki sake kawo maganan riga da Abinda yasamu riga agabana ok????
Kallonsa tayi tana son sake maganar Amma ganin yanayinsa na Babu Wasa ko sakin fuskarsa yasa ta 'daga Masa Kai tana cewa''
Adawo lfy.
Can qasan maqoshinsa yace"
Thank you"tareda wucewa ya sauko qasa tareda ficewa zuwa office.
##Mamuh#
Gashinan please yauma kuyi manage gobe Inshallah zamu koma pages dinmu masu tsawo yauma uzurine ya riqeni kuyi hkr da wannan dinğğğ
ZAFAFA BIYARğğğ
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
SARAN BOYE
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 23_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğğ¾ââï¸ğğ½ââï¸?
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*ğ¯ğ½ââï¸ğ¯ğ½ââï¸?
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾ğ¤ğ¾
**********
Yinin ranar cikin farin ciki dukkaninsu sukayisa sbd musamman Andi da Modibbo suka aiko akaje da Amatu gurinsu suka duba lafiyarta qarima Dr Fatima Dr khalil yaturo ita taduba musu lafiyarta taqara Basu tabbacin komai lafiya daga ita har cikin,
Musamman Andi yayowa Amatu kyauta ta musamman Wanda tasake qara Mata baqin jini da qiyayya gurinsu umme da Haj maryam wadda taga Salman dinta na wani rawar Kai akan Amatun tun agabansu Modibbo ta buga tsalle tace"
Wlh Salman karka kuskura kace zakamin kwashe kwashen bacin Rai Dan ni ba dauka zanyi ba.
Ganin basusan akan me take Magana ba yasa kowa tayi watsi da ita saishi uban gayyar datake Magana akansa yafahimci Abinda take nufi sai anty zarah da Amatun dake aika musu da kallon hadarin kaji sbd yanxu daidai takeda kowa kaf cikin zabeera sbd Andi daya tsaya Mata.
Koda suka fito a hanyarsu ta komawa suka hadu da Nuratu tana ganinsu tahau yada maganganu in marasa Dadi Har Amatu zata tankata anty zarah tayi saurin riqo hannunta tajata sukabar gurin sunaji tana cewa zarah din munafuka Amma Basu kulataba suka wucewarsu.
Da yamma Salman da kansa yazo ya maidata asibiti tasake ganin Dr Fatima suna baro asibitin kamar a mafarki sai kawai tagansu qofar gidansu yayi parking mota
Da sauri ta juyo ta kallesa bakinta da fuskarta daukeda tsananin mamaki da farin cikin dayasa takasa mgn sai kawai ta bude motar ta fito da gudu tayi ciki.
Da iyami tafara cin karo a tsaye tana kwashe shanya cikin tsananin farin cikin ganinta ta rungumeta tana cewa''
Iyami wlh bansan haka nayi kewarkuba sai yau Dana ganni a qofar gida Ina kawu da usi???
Kawu dake fitowa daga daki Yana jinta dama ya fito Yana ganin yanda Amatunsa ta koma take ya washe baki Yana cewa''
Maza kuzo mu shige daki kada Ido da baki suyi Miki yawa kinsan gidan harda qarin 'yan bani na iya aka samu.
Dariya tayi tana sakin iyami tace"
Yanzu nasan Ina gaban kawuna.
Kallonta iyami takeyi itama cikin Jin Dadi da farin cikin ganin yanda ta sauya tayi kyau kamar 'yar masu kudi har wani qyallin haske fatarta keyi ga suturar alfarma ajikinta sai annushuwa takeyi.
Dakin suka nufa suka zazzauna Nan aka nude sabuwar fira saiga shima usi dake shirye shiryen tafiya jibi yashigo Nan aka Dora firar ga fankasu da iyami tayi aranar dayaji miyar Naman rago da Ganda Nan aka kawo musu suka hau ci suna Santi musamman Salman dan shima yamasa Dadi matuqa.
Suna Nan saiga Kiran Dr khalil yashigo wayar kawu dauka yayi suka gaisa ckin sakewa kamar 'dansa na cikinsa yakejin khalil sbd shiga ransu da yayi iyami ce madai takejin nauyinsa na sirikantaka sbd tuntuni sunsan Amatu yakeso Dan Yama fada musu Kuma sunyi na'am da hakan jira kawai suke tadawo asa ranar aure,
Sabuwar Hira suka Dora da Dr din a waya su Amatu na fada Masa Abinda suke ci Yana cewa''
Umma iyami idan nadawo Nima shi zakibani wandama yafi nasu Dadi.
Murmushi iyamin tayi cikin Jin nauyinsa tace"
Khalilu duk Abinda kakeso idan kadawo Inshallah duk sainamaka su.
Yawwa nagode umma.
Kawu ke tambayarsa ya aikin dayaje yi dafatar akwai nasara??
Eh yace Masa Yana qarawa da alhmdlh Inshallah muna gamawa zan juyoma.
To Allah yakawo ku lfy.
Amin
Basu bar gidanba sai kusan yamma sosai Wanda anty zarah tayi musu Kira yafi a qirga
Itama Saida iyami ta hado Mata fankasu suka je Mata dashi.
Kamar kada su tafi hakanan ta fito suka tafi tana sake dagawa Yan gidan hannu kowa nasakejin kamar kadata koma.
Saida suka biya sahad yayi Mata soyayya sosai har abin na Bata mamaki Amma ganin yanda ya dauketa kamar 'yar uwarsa ya nuna bayason godiyarta da mamakinta itama saita daukesa kamar usi Nan suka sake shiriricewa sai magriba suka kamo hanyar gida.
Suna tafe suna fira harda qyaqyata dariyarsu sukeyi Yana tuqi da gudu gudunsa aikuwa Basu ankaraba wata mota tayo Aron hannu a guje itama me motar yake tahowa,
Cikin wani razanannen firgici yaso kaucewa Amma ganin akwai express dayan gefen sai kawai yayi dayan gefen sukai Kan wata bishiya suka daketa Amatu da tuni ta saki ihun sadaqarwa kanta ya daki qofar motar tsananin tsoro da firgici yasata somewa agurin.
Cikin sauri ya juyo Yana qoqarin dagota Yana Kiran sunanta da qarfi cikin damuwa sbd yasan suman tsoroce kawai tayi gashi Babu wani abindama yafaru din sbd bai daki bishiyarba sosai.
Ruwan dayasha ya rage kafin alamarin ya dauka ya shafa Mata saigata tasaki nannauyan ajiyar zuciya a rude tana cewa''
Wlh banason na mutu yanzu saina cikawa Dr khalil burinsa na aurena.
Dariya maganarta ta basa duk da ta daki zuciyarsa Kuma.
Cikin kulawa yace"
Nima banason ki mutu sainaga rabon wace ke a qarshe.
Kallonsa ta juyo tayi cikin rashin fahimta tana qoqarin sake dawowa nutsuwarta.
Murmushi yayi tareda tayarda motar yayi ribas sukabar gurin Yana cewa''
AMATULLAH ki dinga tuna sauran bayin Allah yayin yiwa mijinki na baa dauraba addua.
Sake rudata yayi tasake juyowa gabaki daya tana kallonsa saidai ganin kamar reaction dinta nasake basa damar yadda da hasashensa koma dai yardarsa sai kawai ta basar da zancen tana dariyar tsoron dataji da sumanta tana cewa''
Dan Allah Dr Salman kada anty zarah tasani
Tana sani zata Fara daga hankali ta fadawa Dr banaso ta daga Masa hankali.
Sai alokacin ya Dan juyo ya kalleta zuciyarsa na wani sarawa Yana maida hankalinsa Kan titi cikin sautin nutsuwa yace"
Idan zuciyarki na tsananin kulawa da qaunar Khalil haka
Meyesa zata so MD ZABEERA???
Cak ta tsaya gabanta yayi mummunan faduwa Amma sbd Bata fahimci zancen nasaba saita saki wani yaqen dolen Dole tana kasa juyowa ta kallesa tace"
Meye hadina da Rabin ran Anty zarah kuma?
Ko gaisuwa Bata hadani dashi bama ya cikin mutanen danake qauna gaba daya sbd halayensa na wulaqanta antyna.....
Baya cikin wainda kike qauna sbd shi sonsa kikeyi Amatu.,
Amatu bansan meyasa shedan yake yawo atsakaninmu ba dayake haifar Mana da wani tunanin dabai kamataba bayan sanin cewa ke amatsayin matar khalil kike,
Amatu nafada Miki hakane Dan kije kiyi tunani kada ki auri Wanda farin ciki ya cancanta a rayuwarsa ba dakon son maso wani ba,
Dr Khalil zabeera shine duk duniya cikin maza ayanzu yafi cancanta daya asameki gaba dayanki daga zuciya har ruhi da ganganr jiki
Dan haka kada ki azabtar da rayauwarsa ta basa gangar jiki da qauna kawai
Yana buqatar dukkanki gaba daya har soyayyarki da zuciyarki sbd koba komai shi din Asthmatic patient Wanda yakeda alaqa da zuciya
Dan haka AMATULLAH kije ki zauna ki nutsu kiyi tunani ki Fara koyawa zuciyarki soyayyar khalil ba qaunarsa ba soyayyarki yake buqata.
Kallonsa takeyi sosai kanta na neman bugawa da maganganunsa ta girgiza Kai Yana rintse ido cikin rudewa take cewa''
Mezaisa naso Rabin ran Anty zarah ni Dr nakeso, shikadai nake qauna, shikadai nake tunani shikadai nake gani, shikadai nake.......
Mafarki fa???
Tsit tayi tareda kasa qwaqqwaran motsi sbd Jin tambayarsa,
Idan har ba qarya zatayi Masa ba to tabbas 'daidaikun ranakune Bata kwantawa batayi mafarkin Rabin ran antynta ba.
Cikin firgici ta dago idanuwanta na cikowa da hawaye zatayi Magana yayi parking Yana cewa''
Mun iso gida.
Da sauri ta juya ta kalla waje tagansu qofar part dinsu anty zarah din
Ta sake juyowa gurinsa zatayi Magana cikin rawar murya da sarkewar tunani
Ya katseta da sakar Mata murmushi me sanyi sbd jikinsa da zuciyarsa dasukai sanyi idanuwansa na Dan sauyawa sbd yanayinta ya Gama tabbatar Masa da hasashensa katseta yayi cikin sanyi da cewa''
Kije ki zauna kiyi tunanin Abinda yakamata.
Shiru tayi