Showing 18001 words to 21000 words out of 108906 words
Chapter 7 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt
tayi daidai kwanar gidansu amatun Wanda yasata juyowa ta kalleta ta yanda tasan gidansu zatayi magana hajiya aishan ta katseta Kai tsaye da cewa"
Zan baki naira miliyan uku tareda makaranta me tsada wa 'dan uwanki harya gama sai gidan zama me kyau ga kawunki da jarin sana'a me kyau ga matar kawunki idan har zakimin Abinda nakeso.
Suman zaune amatu tayi tareda sakin baki gaba daya ta daga hannu tana lissafa abubuwan da hajiyar tace har lissafinta ya 6ata tayi saurin girgiza Kai tana 'dan dukan kanta tace"
Amatu amatu amatu dawo kanki... Dawo kanki.....
Hajiya mama duka abubuwan Nan dakika fada saidai naji kokuwa kunnuwanane????
Qaramin tsoki umme tasaki tareda bude wata 'yar jaka dake daukeda kudi dubu 'dari uku ta miqa Mata tana cewa"
Kije kibawa su kawunki wannan idan kingama aikin zanbaki dukannin Abinda nace
Qaninki kuwa zanbaki takardun makarantarsa ki riqe a hannunki.
Da sauri ta karba kudin ta shafa cikin zaquwa take cewa"
Wannan yanxu duk nawane halak malak??
Hajiya mama na amince zanmiki aikinki koma wane iri ne na shekara biyarma zanmiki bana wata biyar ba.
Kallon takaici umme tai Mata tana mamakinta saidai duba da 'yar tashace Kuma 'yar bola hakan ba wane abin mamaki bane Dan duka tarihinsu tasamu agurin binciken datasa akai Mata akansu Wanda alhaji mande ne yabada bayajin
Shiyasa tasan tsaf amatun zatayi wannan aikin ba gashi indai akan kudi ne.
Zanje dake gidana zaki gabatarda kanki a matsayin wadda akayiwa fyade harda ciki ajikinki,
Ba shaidu,
Duk wasu manyan shaidu na tanadar Miki su tun daga Kan likitoci harzuwa Abinda zai biyo baya,
Aikinki na kammala na tanadar muku gida da sanaar yi a wani guri can nesa da Nan bazaku sake dawowa Nan ba shikenan kunyi bankwana da talauci da damuwa zaku samu damar Fara sabuwar rayuwa.
Duk iya yanda ta rude da Jin abubuwan dazata samu Bata taba kawo hajiyar batada isashiyar lafiya ba sai yanxu datai wannan maganar Amma Kuma bataga alamar hauka atareda ita ba,
Itadai yanxu matsalar dayace ko haj nada lafiya ko batada bazata mayar Mata da kudin nanba.
Yanda amatun ke kallonta yasa ta fahimci tunaninta ta 'dan qaqalo sakin fuska tace"
'dana ne nice na haifesa
Nasa kimin hakan ne sbd banason abawa 'yayana mulkinda zasu cutu Kuma Allah ya tambayesu ranar qiyama,
Mulkin zabeera akwai hadari,
Za'a iya hallakarmin da 'yaya sbd kwadayin mulki shiyasa nakeson kije amatsayin hakan Dan kada abawa 'yayana mulkin da zarar an nada wanda yakamata a nada zan kaiku inda zakuyi rayuwa cikin farin ciki da walwala.
Shiru amatu tayi tareda gyada Kai sbd soyayyarta da kudi yasa Kai tsaye tayi na'am da hakan Kai tsaye tunda daima ceton Rai ne zatayi koba komai Babu ruwansu da wani abin kunya tunda dai bayi tayiba tasan dai kawu ne bazai yadda da wannan tsarin ba bare iyami.
Kallon kudin tayi ta kalla hajiya aishan tace"
Kinada tsarin fadawa kawuna ya amince???
Dan nidai nariga na amince.
Murmushi umme tasaki tareda tayarda mota suka qarasa shiga layin gidansu amatun tace"
Kawunki bazaisan gskia ba sbd gudun samun matsala agaba,
Kidai saka aranki aikin kudine zakiyi domin samun ingantacciyar rayuwarsu kawai zan aiko a sanar dashi kinsamu aiki a zabeera tareda albashi me kyau zaki ringa zuwa duk sati kina ganinsu har tsawon wata biyar.
Kawu bazai yadda ba"tafada tana tunanin mafita.
Karki damu zai yadda idan wadda zanturo tazo saiki qara da dubarunki ta yadda zai yarda.
Kallonta amatu tayi kafin ta kalli kudin tsawon daqiqu tana nazari zuciyarta na son yin rawa a alamarin Amma burinta na hana hakan.
Rintse idanuwa tayi tareda sauke ajiyar zuciya me qarfi ta furta na amince saitazo nikuma Ina fatan wannan alqawarin yacika.
Gyada Kai kawai hajiya aishan tayi tareda nuna Mata qofa.
Fita tayi tareda kudin tabi motar hajiya aishan da kallo harta bace mata ta sauke ajiyar zuciya tana cewa'
Amatu wannan sa'a ce ko rashin sa'a???
Tana shiga gida Kai tsaye gurinsu kawu taje Allah yasa duk suna dakinsu kawun harda USI dayashigo yanashan magani kawu Kuma na gefe yanashan waqar 'dan indo,ta qaraso ciki tana sallama tareda qarasawa ta zauna gefen iyami dake ballowa usi magani ta ajiye Daurin kudaden tareda sauke boyayyan numfashin zancen dazata qirqiro.
Idon kawu na sauka kan kudin yatashi zaune da sauri daga kishingiden dayake Yana qarar radionsa Dan kada aji Abinda zai fada yace""kudi" Yana sake bude idonsa akansu.
Iyami ma dakatawa tayi daga bude maganin ta kalli amatu da sauri,
USI ma kallon amatun yakeyi zaiyi magana ta rigasu da cewa"
Duk nasan tunani kukeyi dabam dabam
Iyami wlh tallahi ba kudin wasu bane na dauko,
Kawu aiki aka koreni sbd nayi kwanaki banje ba to, to ,to shine dama inawa wata babbar hajiya mama aiki a saloon dinmu shine tace ita zata daukeni aiki zata budemin gurin aiki irin fire fox me sassa dabam dabam wanda nice zanzama managan gurin Amma....
Amma me????iyami ta tambaya da sauri zuciyarta naqin gasgatuwa da zancen..
Amma Wai sai nashiga training dinda zaayiwa manyan ma'aikatansu a can inda aka kebe na tsawon wata biyar zuwa shida.
Tsit sukayi a dakin duka kowa na qoqarin fahimtar zancen saidai ta Yaya??
Kallonta USI yayi dakyau yaga itama shi take kallo yace"
Amah idan har cigabanki ne me kikeso yanxu to.
Kallon kawu da iyami tayi Shima kawun kallonta yake yace"
To wannan kudin fa???
Kai tsaye tace kudin albashinane aka bani na watannin Dan daukar nauyin Kai kafin mu fito training din.
Iyami ta kalla tace"
Wlh iyami aiki zanje Yi ba qarya nakeyiba na rantse Miki...
Duk shiru sukayi kafin kawu yace"
Naji kuje zanyi tunani akai.
Miqewa tayi ta fito usi ya biyo bayanta suna fitowa yafara watso Mata tambayoyi tajasa zuwa dakinta da sauri Dan kar kawu yajisu suka zauna tafara yimasa bayani komai Kai tsaye yace wlh bai amince ba.
Hayaniya suka Fara tayi saurin rufe qofa tana cewa"
Idan baka gaji da yawon cell ba ana maka dukan wulaqanci to ni nagaji da ganin hakan,
Rayuwa me kyau nakeson muyi kamar kowa Usman,
Idan har kanason farin cikina danasu kawu wannan maganar mungamata,
Banyi Dan Jin dadinaba sai Dan wainnan bayin Allan dasuka sadaukar da komai saboda mu,
Babu uqubar dabasu shigaba amma suka riqemu da Amana,
Kaima inason ganin kasamu ingantacciyar rayuwar sbd ka tallafesu a gaba Dan ni nasan rayuwata acikiku taqaitacciyace kobanaso nasan Dole wata Rana kawu saiyamin aure..
Usman mubar maganar Nan kawai qwarin gwiwarka nake nema.
Kallonta yayi idanuwansa na cikowa da hawaye yanajin inama ya mutu ya rage Mata 'dawaimiyar datake ganin itace akai,
Maimakon yazama jagora Amma yazama wani irin koma baya itace jagorar.
Ficewa yayi Yana share hawayen fuskarsa dasuka saka jikinta yayi sanyi matuqa Amma batajin zata fasa sbd tariga takai qarshe zasu bar Nan din sbd karatun Usman din.
Kwana biyu ana rigima sosai a tsakaninsu kafin iyami da Usin suka amince akan aikin nata bayan dattijuwar da aka aiko tayi zuwa kusan hudu tukuna.,
Kwana uku masu zuwa zata tafi Amma duk sai jikinsu su hudun hakanan ya mutu sosai suka shiga damuwar tafiyarta duk da dai Basu fadaba sai hakan yataba 'yan gidan Suma sbd su kawun dadu amah sune hayaniyar gidan dake qara Raya gidan shiyasa Suma duk sai sukaji ba Dadi,
Amatun ma hakanan takejin kamar zata rabu dasu kawun ne rabuwar har abada Wanda usi ne ma tadawo Yana qoqarin cire Mata damuwa,
Iyami da kantace ta hada mata duk wani abin buqata a 'yar Jakarta ta goyawa ranarda akazo tafiya da ita iyami duk hakurinta saidatayi hawayen rabuwa da amatun sbd zuciyarta takasa samun nutsuwa da tafiyar,
Kawuma kasa rakiyarta waje yayi saidai Usman ne aka tafi dashi Dan yaje yaga inda take.
Su maman junior hadda rungumeta sukayi sunajin kewarta tun Bata tafiba.
****
Wayarta data gamayi ta kalla tareda kallon haj Maryam dasuke zaune a palon tace"
Su amah ne gasunan a hanya isowa zasukai mintuna ashirin kafin su iso zuwa lokacin an halarta gurin meeting din familyn ZABEERA daza'ayi yau
Yau komai zai qarewa MD ZABEERA.
Murmushi haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye tace"
'yan jaridar Dana gayyatoma suna daga baya suna jiran kirana suzo ya sakarwa duniya wannan labarin da dumi duminsa.
Dariyar farin ciki suka saki atare daidai lokacinda nuratu tashiga cikin kyakkyawar adonta na wata Kuwait jallabiya datayiwa fatarta kyau sai qamshi takeyi tace"
Momy kusan kowa fa ya halarto dan gasu anty bahijja nacan sun iso taredasu anty juwairiyya dasu baba qarami.
MD ZABEERA ma Naga shigowarsa yanxu tareda ZARAH.
Kallon juna sukayi tareda cewa"
Shikenan muje.
***
_40 min later_
A bakin babban qaton gate din ZABEERA motarsu ta Parker Wanda akayi juyensu da ita zuwa wata matacciyar golf baqa.,
Akaro na farko ta 'dago hoton MAHMOUD ZABEERA da aka Bata bayan anmusu bayani wasu abubuwa akansa ta kalli hoton zuciyarta tayi wata irin bugawa akaro na farko...
Rintse ido tayi zuciyarta na wani irin tsalle tayi saurin rufe hoton tana dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi tace"
Ya Salam..
Meyasa zuciyarta ke bugawa da ganinsa a hoto???
Kallon Babar dasuka Zo tare tayi tana qoqarin Hana zuciyarta bugawa Amma sai qara bugawa tayi tayi saurin miqa Mata hoton tana cewa'"
Ki riqe a hannunki nariga Naga hotonsa zan ganesa da kaina.
Kallonta baba Jamila tayi tana cewa'"
Ki nutsu fa.
Gyada Kai tayi tana yiwa qatoton gate din zabeeran kallon kwadayi da qauyanci.
Shima usi kalle kallen yakeyi baki abude sbd tsananin girma da kyan gate din kafin suka nufo gate din Babu dogon musu sbd babban security in charge yasan da zuwansu yasa aka Bari suka shigo suna kalle kallen baki asake
Amatu tace"
Usi kana ganin Abinda nake gani kuwa????
Kasa magana yayi yafarabin manyan motacindake harabar gidan da kallo Yana cewa'"
Wlh amatu wannan gidan aljannar duniya ce muka shigo.
Itama motacin tahau shafawa tana cewa'"
Aikuwa sa'a takawoni Nan ni amatu.
##mamuh##
______________
KUNA BUÆATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ÆIN BOOKS ÆIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samuğğ»ğğ».
    Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziÆan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saÆo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buÆatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuÉar waÉan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks Éin kana buÆata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buÆata koda Éaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauÆin gaskeğ¤.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauÆiğ»ğ»ğğ¤.
______________________
#MIN QALBâ¤ï¸
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 12_*
_Mamuhgee_
Kasa riqe hawayenta umme tayi suka gangaro Kan fuskarta ta shafa cikin firgici ta dago hannunta ta kalla taga tabbas hawayene,
Yau ni Aisha mezan gani ne??
Wace masiface wannan yarinyar na gayyatowa kaina ranar farko data sako kafarta gidana hawayenda na manta ya akeyinsu tun quruciya yau sune a fuskata,
Wlh shirina bazai lalace ba Koda kowama zai rasa saidai kowa ya rasa...
Juyawa tayi Kan khalil cikin tashin hankali da rudewa tace"
Khalil karkayiwa kanka haka ka 6ata rayuwarka kafada gaskia wannan yarinyar bakada alaqar komai da ita,
Rintse ido yayi Yana danne tsananin 'dacin da zuciyarsa ke Masa
Ummin ta girgizasa da qarfi tana sake Marin fuskarsa tace"
Kafada gaskia Khalil wlh bazan yadda a maqala maka cikin qaryaba wannan yarinyar 6arauni.....
Katseta Modibbo yayi da cewa"
Aishatu ki nutsu kisan a inda kike,
Shiru yayi Yana nazari cikin tsananin baqin cikin da takaicin Abinda ke faruwa ya dago ya kalli khalil
Khalil din yayi saurin sauke kansa
Yace"
Khalilu Abinda kayi a tunaninka meye shi??
Modibbo a musulunce shi aure idan har an daurashi Akan yanda sharuddan aure sukace to banyi laifi ba,
A tsakanina daku iyayena Kuma laifi ne sbd na boye Muku nayi bada izininku ba saidai nayine sbd girmamaku Dan inajin tsoron kawo muku zancen sbd tsoron bazaku Bari,
Dan haka na aikata laifi babba Kuma Ina neman yafiyarku dakuma amincewarku da amatun kodan Abindake cikinta baida laifin komai kada a hukuntasa ko mahaifiyarsa nine me laifin Kuma na dauka a shirye nake da dukkanin wani hukunci saidai Allah ya huci ran Modibbo ina fatan itama amatu abata adalcin datazo nema duk yanda akayi hukuncin zamu dauka.
Tsit sukayi suna kallon bakin Khalil din cikin girgizuwa da kalamansa,
Dukkanin Abinda yafada jin sukayi kalmomin na son tabasu,
Shi cikin babu ruwansa to meye mafita ga wannan alamarin?
Kallon mahaifiyar amatun Modibbo yayi yace"
Ina mahaifin yarinyar??
Ya rasu tun tana yarinya qarama.
Ina danginsa?
Daga maiduguri mukayo Nan munrasa kowa bamuda kowa nanma amatsayin 'yan gudun hijira muke har mahaifinta yasamu aikin sanaar Saida kayan Miya harya rasu daga Nan ne muka hadu da......sai tayi shiru tana satar kallon hajiya aisha sbd Abinda zata fada itama ba yanda ta iya Dole tabi tsarin yanda al'amarin ya juya kodan fita da ranta tace"
Daga Nan ne muka haduda likita shine yake taimaka Mana harya sanyata makaranta shine yakawo maganar son aurenta nikuma na amince saidai bai fada Mana cewar iyayensa Basu aminceba yakawo Mana wani amatsayin mahaifinsa aka daura auren yanzu shekara daya kenan,
Mu Kuma kusan wata biyu kenan bamu sake ganinsa ba munyita zuwa asibiti bama samun ganinsa saigashi ciki ya bayyana atareda ita
mutane harsun Fara binmu da gori da maganganu marasa Dadi shiyasa mukazo...
Faduwa ummi tayi Kan kujera tayi zaman 'yan bori tana kallon baba Jamila tayi wani kukan kura tayi kanta tana cewa''
Qarya takeyi Modibbo wlh taron maqaryata ne....
Saurin riqeta hajiya Maryam tayi cikin tashin hankali take itama tace"
Modibbo Sam wannan matar qarya takeyi wlh daga gani sharri ne zuke qullawa sbd kudi......kallonda Modibbo yayi Mata yasata yin shiru baqin cikin future din 'yarta dake Shirin lalacewa na cinta kamar ta rufe amatu da bugun mutuwa.
Khalilu duk Abinda tafada gskia ne kokuwa?
Gyada Kai yayi kansa na qasa Dan duk duniya bai ta6a Jin tsanar wani lokaci 'daya ba kamar baba Jamila.
Bsyan dogon nazari da tunanin irin rashin 'da'a da wulaqanta zabeera da Khalil din yayi take yafita ran Modibbo da kusan kowama a gurin kai tsaye cikin nuna qyamarsa ga khalil din da halayyarsa Modibbo yace"
Ban karbi wannan auren naka ba likita haka Kuma kaima na cireka daga iyalina ka dauki matarka kuje kibar Nan karka sake Kiran kanka da zabeera har abada,
Kuma kuje ga adalcin dakuke nema Nan anbaku,
Anbarwa 'yarki mijinta har abada duk ranarda qafarku ta tako zabeera aranar ne zakusan asalin hukunci da zafin Zabeera.........
Kuka ne qarfi umme ta fashe dashi tareda riqe Khalil din da idanuwansa suka qarasa rinewa jajir Yana Mata kallon kece Kika jawo..
Girgizasa tahauyi tana kuka Mai qarfi tace"
Dan Allah Khalil kafada musu gskia bakai bane
Wlh bazan yardaba nizan fada gskia..
Girgiza Mata Kai yayi tareda zamewa daga hannuwanta yayi qasa da murya cikin qunci Yana cewa'"
Ummi kema kisani idan har kina Sona da 'dan sauran farin cikin daya ragemin bazaki taba fadar gskia ba sbd zata saki keda amatu cikin hadari Wanda bazan iya daukaba,
Umme kece rayuwata gabaki 'daya amatu kuwa itace zuciyata
Meyasa zakiyi haka ummi....??
Mutuwar tsaye tayi tana kallonsa cikin tsananin tsoro da tashin hankalin Abinda yafada,
Me Khalil ke nufi?
Amatu zuciyarsa,
Dama sunsan juna da gske kokuwa ita yakeson rainawa hankali,
Amatu dama tasan 'danta shine ta karbi aikinta kenan ita take rainawa hankali tabbas zatasan tayi Wasa da wuta.
Gangarowa wasu sabbin hawayenta sukayi ta girgiza Kai tana cewa'"
Khalil wlh bazan iya gani na rabu dakaiba,
Ka saketa saki uku,
Cikin ma a zubar kabawa Modibbo hkr Amma Dan Allah Khalil kada katafi yaqarasa cikin kuka tana sake riqesa.....
Cikin tsawa wannan karon Modibbo yakira sunanta Yana kallon Khalil yace"
Ko bayan kabar Nan duk ranardaka saketa daga ranar zakasan ainihin fushin mahifinka,
Haka cikin dake jikinta.
Zubewa qasa umme tayi da sauri Yana cewa'"
Na roki Modibbo daya taimaka ya sassautawa Khalil wannan hukuncin.
Miqewa Modibbon yayi Yana cewa'"
Taro yaqare kowa ya tafi.
Kamar daga sama sukaji security din bakin qofar shigowa na bada sanarwar isowar Andi Wanda yasa kowa miqewa cikin tsananin firgici sbd Abinda andin yafi shekaru ashirin beyiba wato zuwa meeting palon.
Hajiya Maryam data yiwa amatu text din takira andin tafada Masa halinda ake ciki ta saki ajiyar zuciya tana riqo umme data miqe da sauri itama ganin Andi yau da kansa take ta shiga taitayinta tana shanye kukanta saidai hawayenta dasukaqi tsayawa ta kalli hajiya Maryam tace"
Kin kyautamin Maryam sbd Andi ne kawai zai iya ceton Khalil Dina yanxu.
Modibbo da kansa ya miqe yabawa mahaifinsa dake tattareda wata irin izzar mulki da cika Ido tareda razanarda mutane da kallo 'daya idan yayi maka Wanda kaf cikin zuriar zabeera mutum biyu ne suka 'daukosa sak alqasim zabeera mijin haj Maryam daya rasu sai MAHMOUD ZABEERA wanda beyi mulki ba Amma Yama wucesa a mugun miskilancin da kwarjini me ban tsoro.
Shigowar Andi tasake saka kowa cikin tsoro da firgici Saida yayi zaman minti biyar tsit bayan gama amsa gaisuwar kowa kafin ya bude muryarsa me amsa amo yace"
Khalilu da kanka zakayi bayanin abindake faruwa daga farko.
Ba inda inda Khalil yasake koro Masa bayanin komai tareda hukuncinda Modibbo ya yanke Masa ya 'dora da fadin"
Na aikata babban kuskure Kuma na amsa laifina nakuma karbi hukuncina Andi,
Zanyi nesa da Nan Kuma bazan taba Bari maganar ta fitaba bare sunan zabeera ya baci,
Nayi alqawarin daga lokacinda zan fita Nan zan aje sunan zabeera Dan kada gaba nayi Abinda zan kawo batanci gareku ba da......
Cikin firgici ummi tayi saurin zubewa qasa tana cewa'"
Allah ya taimaki Andi Dan Allah Andi ya tausaya a sauqaqawa Khalil tsaurin hukuncinsa kada arabasa da sunansa da zuriarsa indai akan laifin wannan yarinyar ne Andi abasa dama yayi Mata saki uku bayan ancire cikin.......
Maganar ummin yasa Andi dagowa ya kalli Modibbo
Modibbon yayi saurin qasa da Kai Yana cewa'"
Ayi Mata afuwa Andi uwa ce dake cikin firgicin rabuwa da 'danta.
Kallonsa andin yasake hakan yasashi yin shiru Yana cewa"
Allah ya huci zuciyar Andi da Abinda aishatu tafada.
Kallonta Andi yayi tareda kallon baba Jamila yace"
Aishatu matsayinki na mahaifiya kikeson a cutatarda 'yar wata sbd naki 'dan wannan ba adalcin Andi bane.
Kallon baba Jamila yayi cikin sautin dayasata rudewa qafafunta suka hau rawa yace"
Kinxo neman adalci anbaki adalci
Kin aminta da auren 'yarki Dan haka 'yarki zatayi zaman sure bayan munyi bincike akan auren,
Zaki bar 'yarki anan Kuma zata zauna cikin gata da aminci
Zata raini cikinta a hannun matar 'dan uwansa MAHMOUD ZABEERA bayan haihuwarta anbawa mahaifiyarsa halak malak saimu sake daura musu aure,
Aishatu kinason kashe abindake cikin tun baizo duniyaba to kece zaki rainesa har girmansa bayan zuwansa duniya an mallaka Miki shi halak malak.
MUHAMMAD""fada sunan Yana 'daga sautinsa.
Sai alokacin MAHMOUD ya dauke idanuwansa daga Kan