Showing 63001 words to 66000 words out of 108906 words
Chapter 22 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt
saura kadan ta fado qasan gadon iyami da maman junior da idanuwansu sukai jajir musamman iyami da har lokacin hawaye Basu dauke daga idanuwanta ba sukayi saurin tarota ta kallesu da manyan idanuwanta dasuka firfito sun bushe sai wani irin ja dasukayi tafara qoqarin miqewa qafafunta da hannunwanta tareda muryarta dasuke wata irin rawa tana cewa''
Ina...ina..Ina khalillll????
Sunkuyar dakai sukayi Banda iyami datayo kanta tana neman rungumeta tayi saurin qwacewa tana nufar qofar dakin asibitin USI dake kuka sosai yayi saurin tarota Yana kuka yace"
Amatu Ina zakije antafi dashi gida muke jira ki farko muma muke gidan.......
Zamewa tayi ta zube qasa tareda sakin wani irin gigitaccen kuka me qarfi dayasa asibitin suka qara daukar shiru kowa na sake rafka tagumin rashin Khalil din dakuma kuka da tashin hankali dazata shiga idan ta farka Wanda suka shirywa Sha dama.
Tsayawa sukayi kowannensu na nasa kukan me tsananin cikin tausayinta da Kuma zafin rashinsa Suma daya bugesu Babu Wanda yayi yunqurin hanata sbd kuka Kam yariga ya sameta abarta tayisa ko zataji sassucin radadin ZUCIYA.
Irin kukan datakeyi ne yasaka hankalin duk Wanda ke asibitin tashi sbd kukan nata taba zuciyoyinsu yakeyi Yana sake tuno musu da Dr khalil sbd rashinsa ne kawai yasa take wannan kukan Dan kuwa da Yana Raye Amatunsa bazatayi irin wannan kukan ba matuqar ba al'amari yafi qarfinsa bane.
MAHMOUD ne da kansa Modibbo yasashi yadawo asibiti yadaukosu Amatun tunda yashigo asibitin yaji tsit Yana Kama hanyar dakin datake yafara jiyo kukanta dayasashi tsayawa cak qafafunsa da zuciyarsa na qara daukar nauyin rashin Dan uwa mafi soyuwa garesa.
Jin kukan na kakkaryasa yasa yayi jarumtar qarasawa dakin ya tura ahankali yaci karo da ita zube bakin qofar tana kukan idanuwanta kamar zasu zazzago qasa.
Saurin juyawa yayi yacewa su iyami su kamota sutafi gida.
Daqyar suka tattarota suka saka mota suka nufi zabeera inda take cike tundaga farkon layin anguwar talakawane tako Ina bulbulowa sukeyi dukkaninsu yawanci mutanensa ne da taimako ya hadasu.
Ko a anguwarsu kawu jama'ar dasuka halarto dan jana'izarsa basa qirguwa
Hakama ko anguwar gidan Ibrahim daya zauna Saida yayi mutane sbd ko acikin rashin Saida ya taimaki mutane da dama.
Sashen Modibbo akayi da ita inda gawarsa take shimfide an lullubeta su Modibbo da Andi taredasu alhaji qarami da kawu dake gefe zaune Yana tsiayayar hawayen dasuka kasa tsaya masa,wallahi ayau ki yakeyi tamkar 'dan daya fito daga tsotsonsa ne ya rasa sbd Khalil yarone daya shiga ransa Wanda yakejin inama ace haddashi ya tsinta lokacinda ya tsinto su Amatu da Usman.
Kukan umme ne dake zaune gaban gawar ta daga qafafunsa tana addua tana kukan da bayama fita sbd disashewa da muryarta tayi hakama ko gani batayi sosai ayanzu sbd kumburin da idanuwanta da fuskarta sukayi.
Tun kafin ta iso gaban gawar tasa qafafunta suka kasa daukarta ta zube tana sake sabon kukan dake taba dukkanin mutanen dake palon tafara rarrafowa tanajan jikinta ta matso gaban gawar tana kallon fuskarsa dake bude tayi fari fes Yana sheqi kamar zaiyi murmushi.
Qoqarin daukewa numfashinta yafarayi Salman da USI sukayi kanta suna Kiran sunanta anty juwairiyya dake palon itama tayi saurin tarota tana shafa Mata fuskarta zuwa bayanta numfashin na Dan daidaituwa.
Cewa akayi su fita za'a yiwa Khalil din wanka sbd lokacin jana'izar yayi sabon kuka Amatu tafashe dashi tana kallonsa tana Kiran sunansa ganin zata karya musu zuciya yasa Andi yace juwairiyya tayi cikin gida dasu itada umme wadda sai anriqeta sbd sosai Bata gani komai sai dishi dishi.
MAHMOUD ne yabiyo bayansu bayan sun fito Yana rintse idon damuwar tambayar dasu Andi suka turosa yayiwa Amatun ya tsaya bayansu kadan yayi Dan gyaran murya kadan yakira juwairiyya ta tsaya tareda juyowa tana kallonsa da jajayen idanuwanta
Ya Dan kalli Amatu da umme dake hawaye Babu me lakkar qwaqqwaran motsi acikinsu a taqaicema baya tunanin zasu fahimci Abinda zai fada ya Dan dauke Kai cikin qaqalo nutsuwa yace"
Zaki tambayetane ko da akwai janaba atare dashi.
Dummm taji itama juwairiyyar tareda sauke Kai ta gyada Kai tareda matsawa gurin Amatun dake tafiya tanajan qafa jiki a sake ta riqota tana kallon fuskarta datai ja ahankali tace"
Amatu wanka za'a yi Masa anason sanin idan da akwai janaba ataredashi¿
Cak Amatu ta tsaya tareda juyowa ta kalli anty juwairiyya da jajayen idanuwanta dasuka Fara bushewa taji sabon kuka na zuwar Mata sbd tun yanzu taqara tabbatarda mutuwa tonon asiri ce, Amma tunda tariga ta rasashi meya rage Mata tun yanzu tafara ganin tonon asiri ahankali ta juyar dakai tana qoqarin wucewa ta 'dagawa anty juwairiyya din Kai Wanda yasa MAHMOUD ZABEERA dayaga amsar data bayar juyawa ya koma Yana qoqarin Hana mutuwar jikinsa bayyana, cikin sanyin jiki ya sanardasu Andi Nan aka Fara yimasa wanka,
Suna gamawa aka shiryasa cikin farin likafaninsa aka shimfidesa tsaf aka sake aikawa matarsa da mahaifiyarsa sukazo sukai masa adduar data Kuma Kai Amatu ga Suma akai ciki da ita aka dauki gawarsa aka fito da ita inda dubban mutane ke jira Wanda yasa iyayensa da Yan uwansa mamakin lokacinda yayi wainnan jama'ar a waje wanda yawancinsu talakawane da marasa lafiyarsa Wanda yasa Andi Jin kunyar kansa alokacin dasuke zaune suna zuba mulki da oda alokacin 'yayansu nacan suna taimakawa talakawa da marasa qarfi,
Ya tabbata koshi ya mutu yanzu bazaiyi jama'ar Khalil ba Wanda sukewa fatan ya dace tun anan.
Anyi jana'izar Dr khalil zabeera ankaisa kwancinsa na qarshe andawo anci gaba da karban gaisuwar da aketa ganin mutane kala kala a zabeera Wanda yaketa saka iyayensa da Yan uwansa alfahari da Jin sasssaucin zafin rashinsa sbd ganin Inshallah ya dace tunda kowa yazo da alkhairin dayake fada akansa.
Acan cikin gida kuwa a sashen umme ake karban gaisuwar
Umme ko Magana Bata iyawa idan anmata gaisuwa saidai daga Kai kawai Dan ko mutanen Bata ganewa sosai,
Amatu kuwa zazzabine me qarfi ya rufeta bayan anty juwairiyya da anty zarah sun taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tareda sallar asuba aka kwantar da ita a quryar bedroom din umme anty zarah ta zauna tareda ita tana shafa kanta sbd irin ajiyar zuciyar datakeyi Babu qaqqautawa kuka tuni idanuwanta suka bushe ko zuwa bayayi sai ajiyar zuciya da idanuwan datake zarewa.
Nuratu kuwa hajiya Maryam tafi kowa shiga tashin hankali bayan iyayen Khalil din da matarsa sbd Nuratu da abin ya buga sosai sai zabura takeyi tana somewa qarshe dai ankira likita yace saisun tafi da ita asibiti fatarsu alamarin bai taba qwaqwalwartaba.
Da daddare Amatu sashenta aka maidata tareda iyami da da anty salamatun gidansu da zasu zauna da ita kafin agama zaman gaisuwar asan abin yi.
Bedroom dinsa tashiga ahankali ta kunna wutar dakin tana juyowa ahankali da jikinta da Babu qarfi ko kadan idanuwanta suka tsaya akan shimfidar dasuka kwana a Daren jiyan ta qurawa jinin dayake Kan shimfidar ido tafara takawa ahankali ta Isa bakin gadon ta zube qasa tareda jawo zanin gadon ta qanqame tana sake kuka ahankali tana tuno Daren na jiya wanda yayisa a cikin yanayi na ciwo da rashin qarfin jiki sosai kamar Wanda rabo ke cizo Kuma kaman yasan rabuwa zasuyi, gwara da Bata hanasa kantaba Ashe datafi kukan datakeyi ayanzun.
Cukuikuye zanin gadon tayi cikin jikinta tana shaqar qamshin jikinsa dake jikin zanin cikin kuka tace"
Jiya kana taredani Dr meyasa zaka tafi??????
Kuka take fitarwa me qaramin sauti a bakin gadon har wahalallen bacci ya dauketa zaune a qasan.
Sai asuba ta bude idanuwanta dasukai nauyi sbd kumburi ta tashi tana gyara zamanta kafin ta miqe ahankali tana kallon zanin gadon dake jikinta ta sake kallonsa kafin ta nannadesa ta nufi cikin wardrobe din dakin tayi Masa kyakkyawan boyo ta fito dakin takoma dakinta inda su iyami suke sanyin AC yasa wani irin dogon bacci ya daukesu,
ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa iyami na farkawa ganin alamar alwala atareda ita dakuma Jin ana sallah a masallacin cikin zabeera yasa tasan asuba ce ta tashi zaune tana qoqarin saukowa gadon ta nufi bayin itama.
Sallah Amatun ta tayar kanta na tsananin ciwo kamar zai tsage qarshe dai a zaune tayi sallar.
Guraren qarfe Tara na safiya aka kawo abincin safe aka jere musu a dining tareda sabuwar me aikin da aka iko ma Amatun.
Anty zarah ma tunda safe ta iso sashen ta gaidasu iyami dake zaune Palo jigum sbd Amatun ta rufe kanta a dakin Khalil din tanata kuka ita kadai taqi fitowa.
Duk yanda anty zarah tayi qin fitowa Amatun tayi salman da USI ma sunxo sunyi sunyi taqi bude dakin Saida akaje aka sanarwa umme.
Ummen na zuwa qofar bedroom din nasa kasa Magana tayi itama sai kawai ta fashe da sabon kukan daya daga musu hankali
Amatu dataji kukan ummen hankalinta yaqara tashi ta rarrafo ta bude qofar tareda fadawa jikin ummen tanajin kukan ummen har cikin ranta kamar yanda idan Dr na Nan tasan zaiji kukan ummensa.
Daqyar juwairiyya dasu anty zarah suka sallashesu aka fadowa su Modibbo saiga Andi dakansa ya zauna yayi musu nasihu masu karya zuciya da saka tawakkali Nan suka dauki qaddara suka dangana.
Anty zarah ce da iyami suka Bata abinci Dan Dole Tasha tea kawai sai guntun slicebread anty zarah takaita ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga da hijab suka dawo Palo ta zauna cikin mutane.
Dukkanin kulawa da cinta da yanayinta anty zarah ce takeyi sai su iyami dasuke kwana yimata addua suna tofa Mata sbd yanda take firgita cikin bacci idan ya dauketa.
Anyi adduar uku anyi ta bakwai an watse kowa yakoma inda yafito sai anty salamatu da sabuwar me aikinta da aka bar Mata tayi zaman takaba Wanda taso takoma gidansu tayi umme ta ringa roqonta kada ta tafi tabarta Dole akace ta zauna anan tayi takaba tukuna.
****
Rayuwa me sauyawa kamar yanda mutuwa take Dole hakama dangana daci gaba da rayuwa yake Dole.,
Kusan sati hudu kenan yanzu da rasuwar Dr khalil zabeera Wanda tuni wasu suka manta suka koma harkokinsu Banda Amatu da mahaifiyarsa da har abada mutuwarsa bazata taba sakinsuba,
USI yakoma makaranta daqyar sbd kasa tafiya yayi yabar Yar uwarsa alokacin datafi buqatarsa Amma itace da kanta ta tuna Masa cewa burin Dr khalil ne yayi karatu me zurfi Dan ya tsayu da kansa ya tsaya musu wataran kamar irin yanzu da basuda Khalil din tabbas sunyi Rashi Dan yanzu zasu koma Matsin rayuwarsu ne na dah.
Sosai anty zarah da anty salamatu ke kula da ita hakama kullum umme saitazo da kanta ta dubata musamman saka mutuwar arai datayi arai sosai sai lafiya take neman gagararta sbd kullum cikin zafin jiki da zazzabin dare take,
Modibbo da kansa kullum yake Kira yaji lafiyarta da kansa ba saqo ba shikuwa Andi kullum saiyayi musu aikin idan da Abinda Amatun ke buqata saidai Kuma MD ZABEERA baibar ko wace irin qofa dazasu buqaci wani abinba koyaushe buqatarsu cikakkiyace daga garesa duk da baitaba zuwa inda takeba rabon daya kalli ko inda sashen yake tun ranarda ta dawo.
Rasuwar 'dan uwansa ta dakesa sosai harsaida hakan ya taba himmarsa da jajircewarsa a aiki shiyasa take dukkanin iya qoqarinsa gurin cire tunanin wanzuwarta a zabeera yariga ya damqawa zarah komai na buqatar Amatun harta fita takaba Dan haka yagama komai baida sauran tunani akanta saima busy daya qara saka kansa zama Dan yanzu tafiye tafiyensa sundawo dama sbd Khalil ne dake takura Masa yasa yarage tafiye tafiyensa Amma yanzu Kam sai ya qarawa kansa yawan tafiye tafiyen.
##Mamuh#
*_'yan uwa inaga anan zamu tsaya sbd duba da azumi daya riga yazo inshallah saimu Bari idan Allah yabamu yawancin ran kaiwa bayan sallah saimu qarasa Inshallah._*
_NAGODE_
6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 32_*
Gyara zama anty zarah tayi tana sake qurawa fuskar Amatun datayi haske sosai Ido tana maida kallonta zuwa hannuwanta dasukai haske sosai har wani yellow yellow sukayi taji hankalinta nason tashi gabanta na faduwa ta maida kallonta Kan fuskarta tanabinta da kallo ko Ina har zuwa qasanta ta ajiye cup din furar da Amatun tasa aka kawo Mata tana cewa''
Amatu yanayinki na bani tsoro da rashin nutsuwa sbd yanayinki na nuna kamar bakida jini,
Ruwa idanuwanta ke qoqarin kawowa tana kallon fuskarta Amatun dake zaune ka kwantarda kanta jikin sofa idanuwanta a lumshe Wanda yanzu hakan yazama tamkar dabia gareta sbd aduk lokacinda ta zauna tayi shiru idanuwanta take lumshewa sbd tunanin rayuwarta data juya Mata kamar upside down Dan kuwa sai yanzu take sake tabbatarda rashin Dr khalil zabeera arayuwarta babbar gibi ce ga rayuwarta sbd shine farin cikinta, walwalarta,gatanta,burinta,alfaharinta, nutsuwarta gatanta dama asalinta gaba daya...
Hawayen datake riqewane suka gangaro daga cikin rufaffun idanuwanta Wanda yasa hankalin Anty zarah sake tashi tunanin qilan eh da gasken Amatun batada jinin tunaninta ya zama gaskia ta dafe goshi tana rintse ido cikin tsananin damuwa da firgici tace"
Amatu Dan Allah ki bude Ido kiyi magana wannan kukan naki na zuci Yana wahalardamu masu qaunarki,
A zabeera kaf gaba daya yanzu Babu Wanda akeji dashi ake tsananin qaunarsa fiyeda kowa kamarki sbd kece Abinda duniya gaba daya ta shaida Dr khalil zabeera naso fiyeda komai har rayuwarsa,
Damuwarki damuwar kowa ce,
Kukanki baqin cikin mune,
Amatu Dan Allah kiyi hkr ki dauki dangana tareda daukar qaddarar rashin Dr Khalil sbd ganinki ahaka na karya dukkanin qwarin gwiwar ummen khalil,
Yanzu Amatu bansan yazanyiba gaki da rashin lafiya ajikinki ta zazzabin dare kullum Amma kinki ko karban magani gashi yanzu Ina sakaran ko jini na neman gagararki Amatu meyasa,meyasa......hawaye ne suka katse Mata takasa qarasa maganar ta miqe da sauri zata bar gurin Amatu ta riqo hannunta ahankali tana bude idanuwanta dasukai jajir ta zubawa fuskar anty zarah din dake hawaye tanajin qaunarta tako Ina tana shigarta tareda tausayinsu su duka.
Jawota tayi ta maidata zaune tana kallon fuskarta ta tashi zaune ahankali tareda sake hannun anty zarah din tana dauke idanuwanta daga kallonta ahankali ta bude baki cikin yanayi na karyewar zuciya tace"
Anty zarah meyasa kike qaunata har haka?
Meyasa keda Dr kuke min irin wannan son haka?
Anty zarah kinsan arayuwata bantaba samun soyayya irinta Dr khalil zabeera ba,
Shine ya koyamin sonsa alokacinda zuciyata batasan wata soyayya ba saita kudi,
Shine yabani sunan mutunci da martabar mace,
Dr khalil zabeera yazabi soyayyata fiyeda komai da kowa,
Yasa zuciyata takamu da zazzafar soyayyarsa me wuyar Bari bare mantawa Amma yatafi ya barni a daidai lokacin da zuciyata batasan komai da kowaba bayanshi,
Meyasa yatafi yabarni anty zarah Ina tsananin buqatarsa.......
Rufe Mata baki anty zarah tayi tana girgiza Mata Kai hawayenta itama suna gudu tace"
Amatu kada kiyi sa6o ki dauki dangana shima da ana bada zabin mutuwa da bazai taba zabin barinki ba sbd bazaiso ganinki cikin irin wannan halin dakike cikiba yanzu..
Kiyi hkr ki rungumi hukuncin ubangiji akanku hakan da yayi shine daidai kizama me godewa ubangiji aduk halinda Kika tsintsi kanki.
Sauke Kai Amatun tayi hawayenta suka Gama gangarowa ta dago tana sharewa ta kalli anty zarah datake kallonta cikin tsananin damuwa ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda lumshe ido ta bude ta miqawa anty zarah din hannu tana kallon cup din furar data kawo Mata.
Da sauri anty zarah din ta dauki cup din ta Bata tana bayyanarda Jin Dadinta na sassautowa da Amatun tayi cikin guntun zumudi tace"
Thank you AMATULLAH.
Da sauri Amatun ta kalleta tana fasa Kai cup din bakinta sbd duk duniya Dr khalil dinta ne kawai ke Kiranta da cikakken sunanta AMATULLAH.
Fuskewa anty zarah tayi tana qaqalo murmushi ganin tana neman dawo da gaba baya tace"
Banma iya fadar sunan yayi Dadi ba kaman yanda ake fada.
Ganin tashiga kame kamen fadar sunan datayi yasa Amatu sake sauke ajiyar zuciya tana Kai cup din bakinta tana kurba ahankali ta lumshe ido tana gyara jinginawarta sbd dadi dakuma karbuwa dataji bakinta da cikinta sunayi da furar saita saki jiki tanasha ahankali furan na sake sanyata lumshe ido.
Anty zarah ganin yanda furan tasamu karbuwa sosai agun Amatun yasata miqewa da sauri ta nufi fridge ta dauko gaba daya jug din furan ta dawo dashi ta ajiye gaban Amatun tana cewa''
Kawo cup din aqara zubawa Kisha
Dama nasan zakiji Dadinta sbd har sabuwar Madara na zuba Miki aciki.
Qara Mata tayi takuma shanyewa Saida ta shanye kusan cup uku kafin tace ta Isa abarta haka.
Cikin Jin Dadi anty zarah tagyara zama tana Mata fira ahankali tana matsa Mata qafafunta dasuka Dan kumbura sbd zama guri daya
Ahaka har bacci ya dauketa cikin nutsuwa Wanda rabonta da irinsa tun kafin rasuwar mijinta sai yau.
Gyara Mata kwanciya zarah tayi kafin ta zame ta fice daga part din gaba daya takoma nasu Nan ma wani aikin tahau sbd MAHMOUD datake saka ran dawowarsa ayau din duk da gaba daya yinin ranar basuyi wayaba dama itace tafi Kira to itakuma yau ganin yanayin sauyin jikin Amatu yasa hankalinta yadan dauku ko yanzu tana ganin kamar hasashenta gaskia ne Amatu na buqatar ganin likita jikinta bai nuna tana lafiyaba
Dole zata fadawa umme kokuma MD idan yadawo yau asan nayi kada wani ciwo ya kamata basuda masaniya.
Aikin gyare gyare da girki suka hau Yi itada hafsatu sbd tuntuni ta zauna tayi nazari zata dauki shawarar Amatu ta kawo gyara arayuwar aurenta da tsakaninta da mijinta,
Zata cire shakku da tsoron mijinta ta fuskanci reality rayuwar aure sukeyi ba zaman darasiba Dan haka zata sauya kanta ta sauya zamantakewarta da MAHMOUD ZABEERA kada tayi sake lokaci ya qure Mata.
Sai yamma suka Gama komai tayi wanka ta sanya doguwar riga ta atampa tareda yafa qaramin qyale akanta ta hada abincin data dibarwa amatu ta jera a tray hafsatu ta dauka suka nufi can.
Koda suka shiga futowarta wanka kenan itama ta sanyo riga da skirt na atampa ta sanya.,
Abin mamaki maimakon taji kayan sun Mata yawa sbd Rama saitaji kamar skirt din ya kamata hakama rigar.
Kallon anty zarah dake kallonta cikin yanayi na tunanin dabasanma na menene ba haka kawai idan tana kallon Amatu wani lokacin saita Shiga tunanin yanzu saime Kuma zaizo gaba a rayuwar Amatun.
Anty zarah kina ganin na qara jiki ne kokuwa nece naji hakan?
Numfashi anty zarah din ta sauke tana matsowa gaban Amatun ta Dan ja rigarta daga gefe gefe taji ba wani space tasaki murmushi tana cewa''
Gskia baki wani qara ba inaga sbd dai kin Dade baki sakasu bane shiyasa gashi bakida wasu tsofin kayan bare kisaka Amma kiyi hkr kiyi manage tunda ba abin ado bane Kuma ba fita zakiyi ba bare kice Zaki takura.
Gyada kanta tayi tana sanyawa kanta hula Mara nauyi ta Dan saki fuska ta qaqalo murmushin yaqe sbd faranta ran Anty ZARAn