Showing 99001 words to 102000 words out of 108906 words
Chapter 34 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt
hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar tarewa idan yayi mgn da Amatu.
Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar.
Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa
Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan wayar Yana wani gurin..
Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya.
Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace"
Thank you and you look great.
Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan juyowa ya kalleta Yakuma cewa''
Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news.
Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake taredashi tana iya hango damuwa ataredashi.
Numfashi takuma saukewa akaro na biyu kafin ta Kai hannunta ta Dora Kan nasa ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasukai laushi sbd rashin isashen bacci ta bude baki ahankali tace"
I'm really sorry MD sbd tun farko daban Bari ta tahoba da duk haka bai faruba,
Laifina ne na yarda Kuma Inshallah idan munhadu Zan fahimtar da ita hakan but for now idan akwai ta inda Zan taimakawa alamarin let me know please..
Shiru yayi idanuwansa a rufe na mintuna kafin ya budesu ahankali ya juyo ya kalleta na mintuna Yana NAZARIN yanayinta ya bude baki yace"
She respects you fiyeda komai sbd tanajin nauyinki fiyeda komai because of the old relationship that you two shared Wanda deep down haryanxu tana Miki kallon yayarta.
Kallonsa take da dukkanin girman idanuwanta bugun zuciyarta na sauyawa sbd Fara tammahar inda zancensa keson dosa muryarta na rawa tace"
To ta Yaya hakan zai.....
Ki tayani fahimtar da ita Abinda nakeson tagane please.
Saura qiris zuciyarta ta buga daga cikin qirjinta ta da Abinda ya fada din,
Wani dishi dishi take neman Fara gani sbd bugawar da zuciyarta keyi da sauri,
Wani irin zafi yafara taso Mata tun daga cikin qasan zuciyarta Yana mamaye zuciyar Tata take taji tsanarsa nason darsuwa a zuciyarta akaro na farko a rayuwarta Amma ta yakice hakan tareda kallonsa cikin Ido ta bude baki Kai tsaye tace"
For the first time yau MAHMOUD ZABEERA ka farkar Dani daga wani babban kuskuren danake ciki,
Miqewa tsaye tayi ta kallesa cikin muryar dake bayyanarda jarumtarta tace"
Zuciya ce a kirqina ba dutse ba dan haka inaga ko dan Abinda yake cikina na cancanci wata karramawar Amma duk da hakan tunda ka buqata Zanyi mgn da ita Amma bisaga sharadin idan Bata dawoba Nima nagama zaman gadin gangar jikinka sbd inason ayau kasan sonka zuciyata ya Kama bawai zuciyar ya cinye ba.
Zaiyi mgn tabar gurin batareda ta tsaya sauraronsa ba ta nufi dakinta ta shige tareda rufowa ta Isa bakin gado ta zauna tana son fashewa da kuka Amma Abinda takeji yafi qarfin kukan sai kawai ta miqe ta zari doguwar hijab da keys din motarta ta fice tanajin idan Bata bar gidanba komai zai iya faruwa.
##mamuh#
6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 48_*
*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*
Ina maâabotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na alâadance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nauâukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nauâuka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....
Ba Mu tsaya anan baââ?
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l
Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.
*******
*********
Suna Isa zabeera Kai tsaye motar data daukota sashen Andi aka nufa dasu sbd har Modibbo da umme na can dashi kansa MAHMOUD din Wanda ranar yakoma MD ZABEERA dinsa sak miskilanci da izzarsa sun motsa ko wayoyinsa duk akashe ma suke Abu daya kawai yakeji atare dashi shine nutsuwar zuciya data ruhi harma data gangar jikinsa Wanda yagama tabbarwa da kansa cewa tabbas Amatu tarigada tazama wani babban bangare an zuciya,jiki da rayuwarsa tunda haryakejin wannan nutsuwar me sanyin Dadi tattare da dawowarta garesa.
Suna shigowa akansa idonta yafara sauka ta dauke Kai Yana sunkuyarwa ta zauna daga qasa gefen umme dake kallonta fuskarta na bayyanarda farin ciki da murmushi.
Da MAHMOUD din Andi yafara nasiha akan haqqoqan Mata dake Kan mijinta dakuma ire iren halayen .ata da Dole namiji saiyayi hkr dasu sbd rauninta dakuma rashin zurfin tunani da Rashi haquri irin na wasu matan kafin yadawo Kan Amatu da nasihar zama da miji da girman haqqoqinsa akanta da girmansa dayafi na kowa akanta yanzu yaqara da nasihar adalci tsakanin mataye biyu dakuma haqurin zama da abokin zama Dana rayuwa kafin daganan Andi yayiwa Amatun kyautar aure ta sabuwar mota fil sak irinta zarah datake hawa banbancin kalane kawai dayace Tata Ash ce ta zarah farace.
Godiya sosai sukayi suka fito umme na riqeda hannun ta saka Mata wani acikin hannun dayake rufe cikin qaramar kwalbar roba suna shiga mota tace"
Shanye kiban roba.
Kallon ummen tayi tana sake kallon abun ta Dan 6ata fuska zatai mgn tace"
Bansan Jin komai hanzarta kishanye kiban.
Marairaice fuska tayi tana kallon abun.
Anty salamatu dake sit din gaba ta juyo ta kwace kwalbar ta bude tareda Dora Mata abaki tana cewa''
Dallah shanye da abin dadine da yanzu kinfara maganar qari to wannan dadinsa saikin fi kowa.....
Rufe Mata baki Amatun tayi da sauri tana zaro Ido kunyar umme kamar ta nitse ta saci kallonta tace"
Haba anty salamatu nidai karki fara zancenki Dan Allah.
Itama anty salamatu kunya taji sbd mantawa tayi da umme da iyami dasuke taredasu sbd sun Saba zantukansu na banza dasu maman junior shiyasa.
Shanyewa tayi ta miqawa umme kwalbar daidai isowarsu qofar part dinta motar har qofar palonta ta faka suka fito umme na riqeda hannunta tana fada maganganu qasa qasa na rikita miji wainda sukafi qarfin duk rawar Kan Amatun kunya kamar ta qwace hannunta ta zura da gudu Amma ummen ba ruwanta fada Mata takeyi har suka shiga suka zauna palon tana sake zayyano Mata zantuka masu qarfi wainda wasune suka samu damar shiga kanta wasu kuwa nauyinsu yasa suna kasa shigewa Kan nata.
Turaruka ummen ta fitar cikin jakar hannunta ta fesawa Amatun ko Ina jikin masu wani irin sanyin qamshi dagaji tasan bazasu wuce ouds ba masu tsananin tsada take qamshinta ya qaru tana fitarda wani qamshi me ni'imtaccen sanyin dadi suka Fara qoqarin tafiya anty salamatu tace"
Zarah ko lafiya Naga banganta ba na dauka ma zamu sameta anan gashi har zamu tafi.
Umme tace'
Eh Kam gashi dai Nima duk yau banganta ba Nima nai zatan zamu sameta anan din tana jiran isowarmu.
Iyami data miqe tsaye tana gyara zaman mayafinta yace"
Mezaisa zarah tazo ta zauna anan tana jiranmu karku manta bafa kamar da bane yanzu ana Magana akan Amatu tazama matar mijintane Dole wani abun zata Kama kanta ba kamar da ba da Amatun take matsayin qanwarta yanzu kishiyarta ce Dole akwai radadi ko yayane aranta.
Tsit Amatu tayi tana saurarensu sbd duk lokacinda akai Mata tunin kishiya saitaji kamar hankalinta nason tashi saidai girma da nauyin anty zarah da haryanxu take gani da ji atareda ita yana danne kishin datakeji shiyasa take sauke zafin kishinta agun MAHMOUD sbd bazata iya kallon fuskar anty zarah tayi fitinar kishi da ita ba duk zafin kishinsa kuwa sbd Abu daya data fahimta takuma lurarwa kanta MAHMOUD da kansa zai iya kiranta butulu akan zarah idan bata nutsu ta iya zama acikinsu ba yanzu Kam akwai aiki agabansu su dukan na iya zama da juna.
Bayan tafiyarsu iyami kasa tashi tayi daga Inda take zaune tashiga tunani daban daban akan rayuwarta da Kuma ranar farko da aka Fara kawota cikin part dinnan amatsayin matar KHALIL DAHEER ZABEERA yanzu Kuma gashi ankuma kawota amatsayin matar Dan uwansa MAHMOUD DAHEER ZABEERA,
Duk da ansauya sashen gabaki daya Babu inda zaka iya gane shine wancan din Amma dai memories diinsa suna cikin zuciyarta.
Hawayene suka ciko idanuwanta suna qoqarin gangarowa taji bude qofa
Bata dagoba Amma qamshin daya shiga cikin hancinta da motsinsa da baya qarfi yasa ta fahimci waye yashigo ta rufe idanuwanta ta bude ahankali batareda ta dago ta kallesa ba saima sake lumshe idanuwanta datai.
Qarasowa yayi cikin nutsuwarsa da kamalarsa ya zauna kusada ita sosai qamshinta ya Shiga hancinsa yanl dago fararen idanuwansa dasuka Gama gabalaituwa a sonta ya zuba Mata tareda riqo hannuwanta ya sarqe da nasa ya sauke ajiyar zuciya wadda itama ta sauke tata a boye cikin cikinta.
Kasa Magana yayi sbd bayajin yin maganar ya kwantarda kansa Kan kafadarta Yana sake sarqe hannuwansu ya lumshe idanuwansa sukai shiru ahakan sai numfashi da qamshin juna dasuke shaqa nutsuwa na shigarsu duk da Babu Wanda yafito yagfada Amma numfashinsu dake fita ya bayyanarda hakan.
Sun jima ahakan Babu wani motsi Saida yagama samun dukkanin nutsuwar daya rasa kafin ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli fuskarta suka hada idanu ta sauke nata tana qoqarin rufesu ya Kai hannu ya juyo da fuskar tata Yana kallon halittar da ita kadai ke iya rikita MD ZABEERA baisan lokacinda ya saki wani irin murmushi ba yana kallon bakinta daya iya fidda Magana ta arziki data tsiya.
Fuskarsa yakai dab da tata Yana kallon cikin idonta yabawa bakinta light kiss Yana sake sakin murmushi cikin taushin muryar data sanyata dago idanuwanta cikin rashin yadda ta zuba Masa yace"
I can't live without you Mrs MD ZABEERA so kada ki sake tunanin barina sbd komai zakiyi bazaki iya barin rayuwa Dani ba.
Miqewa yayi tsaye hannunta cikin nasa har lokacin ya miqar da ita Yana cewa''
Let's have dinner zarah is waiting.
Ba musu tabiyosa suka fito hannunsa na riqe da nata itama saiyi takeyi tana kallonsa duk da tasan so yake azauna lfy Amma dai mamakinsa bai daina kamata ba sbd ganin yanda ya sauya din dama ita batada niyar zama da miji Babu shaquwa Babu Wasa da dariya Babu hayaniya Babu muguwan wasan gudu gudu idan ma takama to Ina dadin rayuwar auren take tanason morewa sauran kuruciyarta a tareda mijin aurenta Dan haka Babu wani daga mulki sai oda a Shirin zamanta dashi.
Suna shiga anty zarah na fitowa daga bedroom dinta cikin adon riga da skirt na lace maroon tayi Yar simple makeup ga qaramin cikinta daya Dan fito tayi kyau itama sai qamshi take saidai suna qarasa shigowa qamshin dake fita cikin Amatun saita ji ta daina Jin natan ta qurawa Amatun idanuwanta dake son raunana da irin dacewa da kyan dasukai tareda juna ta kalli hannuwansu dake sarqe tafara Kiran sunayen Allah tana kore shedan daga zuciyarta ta saki murmushi tana kallonsu tace"
Sannu da zuwa Amatu.
Murmushi Amatun ta saki tana kallonsa da shima ita yake kallo tace"
Thank you anty.
Kallon MD din zarah tayi tana dauke idonta daga Kan hannunsa dake riqe Dana Amatu tace"
Dinner is ready fa.
Dining suka nufa su dukkansu suka zauna zarah ce ke zaune kusada MAHMOUD din sukaci abinci itadai Amatu drink kawai Tasha sai spoon biyu datai ta miqe tace ta qoshi.
Shima ba wata yunwa yakeji ba Amma ya zauna yaci abincin sosai tareda zarah haryana yaba abincin sosai sbd Fara sanin halin Mata dayayi ya fahimci sunfi son ko yaushe ka nuna musu yabawa da kulawa.
Aikuwa hakan ya faranta ran zarah musamman daya nuna Jin dadin abincin a fili saitaji damuwarta ta ragu sosai suka baro dining din itama Yana riqeda hannunta suka iso ya zaunar da ita Kan kujera ya zauna gefenta Yana kallon Amatu data matsu tawuce yafara musu bayani da nasiha tareda roqon Dan Allah a zauna lfy plus respecting juna duk da yasan suna ganin qimar junansu sosai kafin ya sanar dasu 2days ne kwanan daga haka aka tashi Amatu tafara wucewarta shikuma zarah yabi Dan sake lallasarta Abinda Baya faruwa a zamansu mamakinsa da Jin dadin hakan ya sanyaya zuciyarta sosai harta cemasa yatafi gurin Amatu tana jiransa.
Bedroom dinsa ya nufa yashiga wanka Yana fitowa Saida ya tsaya wata waya kafin ya fice.
Bedroom 'dinda ta tabbatarda shine nata tashiga data dawo daga sashen na zarah ta ajiye wayarta ka bedside drawer ta warware lafayarta ta nade takai wardrobe
tana budewa ta tsaya kallo cikin mamakin ganin Kaya a shaqe maqil da hadda wainda aka dinka da wainda ba'a dinkq ba ga qananun Kaya da jallabiyas ire iren wainda yasan tana sanyawa.
Murmushi ne yaso subuce Mata data Kai hannunta Kan tarin qananun kayan dake jere Wanda taga bumshorts ne sukafi yawa abin data lura yafiso kenen wato shigarta zata fiddo cinyoyinta duka a waje.
Rungumeta taji anyi tayi saurin juyowa sbd bataji motsin shigowarsa ba,
Kallon fuskarsatayi cikin basarwa ta zame daga jikin nasa ta jefa lafayar ta rufe wardrobe din ta bar gurin ta nufi toilet ta jima ciki Babu Abinda zatayi tana saqa da warwara kafin dai ta wanke hannuwanta tayi alwala kawai ta fito tana goge fuskarta da qaramin towel sai ganin lafayarta tayi ya miqo mata Yana cewa''
Ki mayar inason nizan cire miki inason sake ganinki cikinta you look innocent acikinta.
Batareda ta kallesaba ta karba ta nufi gaban mirror tana nadawa ya zauna Kan sofa Yana kallonta hannuwansa nade da qirjinsa.
Tana gamawa ta juyo ta kallesata ta gefen Ido ya taso Yana murmushi ya Kama hannunta suka nufi bedroom dinsa suna shiga wani sanyin qamshi ya doki hancinta sbd kalar turarukansa ba Arabians bane nasa designers Eglh perfumes yake amfani dasu,
As she expected komai na dakin fari ne da milk sbd sune colours dinsa.
Daddumar sallah ya Ciro itama milk color ce ya shimfada Yana kallonta yace"
Kinyi alwala right?
Saida ta dauke Kai kafin tabude Baki daqyar tace"
Yes.
Yanda taketa daure Masa din Yana sake burgesane Bata saniba sbd shi fushin ma nata Yana Masa kallon wani sabon feeling.
Sallah sukayi ta nafila rakaa biyu kafin ya juyo ya riqo hannuwanta duka biyun Yana kallon fuskarta ahankali ya furta"
Sorry.
Qin juyowa tayi ta kallesa ta zame hannuwanta zata miqe ya matse hannun Kai tsaye yace"
I love you..
Cak ta tsaya daga qwace hannun dazatayi zuciyarta ta Fara tsananta bugu takasa motsawa hakama takasa juyowa ta kallesa.
Ya lumshe idanuwansa yasake budewa ya Dora akan hannuwanta dayake riqe dasu cikin murya me taushi yasake cewa''
I love you AMATULLAH K SALEH and I am saying sorry so please wannan fushin yakamata ya sauka please.
Juyowa tayi tana kallon fuskarsa zuciyarta na qarasa bugawa da qarfi ta kasa yadda da Abinda taji idan MAHMOUD ZABEERA dinda tasani ne yake furtasu saidai zumudin zuciya dakeson kamata gudun bada kanta yasa ta miqe ahankali tana zare hannuwanta ya dawo da ita jikinsa ta hanyar fixgota ta Fado qirjinsa ya Bata kyakkyawar runguma Yana fada Mata Magana cikin kunnenta data sanyata saurin zaro Ido waje tana kallonsa takaici da muguwar kunya suka dabaibayeta batasan lokacinda ta Fara mintsinansa ba ta bude baki Dole tana cewa''
Wlh ni sharri ne wannan kakemin, Allah bazan yaddaba....
Dariya yakeyi Mara sauti da hayaniya wadda yaune karonta ba farko ganin dariyarsa ba murmushi ba.
Ganin ta kunnu sosai da Abinda ya fada din yasashi miqewa Yana Sosa inda ta mintsinesa Yana cewa''
Zaki fasamin fatane da wannan mintsinin naki..
Biyosa tayi tana sake kunnuwa har lokacin kunyar zancen bai saketa ba ta nufesa tana cewa''
Saika janye wannan sharrin dakamin bazan yadda ba..
Tana isowa gurinsa ya riqe hannuwan tareda shigar da ita jikinsa ya Kai fuskarsa Kai tsaye ya hade da Tata ya hade bakinsa da nata yana Bata wani ni'imtaccen kiss daya kashe jikinta harya warware Mata lifayar jikinta Bata saniba Saida ya cirata gabaki daya zuwa Kan qaton gadonsa Yana rage musu hasken dakin ta makunnin gefen gadonsa.
##Mamuh#
*_Thank you 4 d prayers_*ğ¥°ğ
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na bankiğğ
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)ğğ
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKUğğ
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYARğ¥
6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 47_*
_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÃMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_Â _NA ZINNEE SMARTÂ WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU
TA WANNAN NUMBERN_
ğğğ
08080840567
*******
.
Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo.
Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana kallonta tace"
Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda cikin baida qwari.
Tashi zaune tayi