Showing 87001 words to 90000 words out of 108906 words
Chapter 30 - MIN-QALB Book Complete Document Hausa Novels By Mamuhagge .txt
waya zasu hade a asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota suka nufi asibitin.
Koda suka Isa sun tarardasu umme
Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd yanayin 'yar walwalarta daya Fara dawowa.
Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna agurin kowannensu ba'a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa sanyi na shigarsa sosai sukace sunji.
A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana sake kwana biyu umme ta tahowarta shima MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu.
Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma,
Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi gwanin sha'awa,
MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira.
Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar.
Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al'amarin ba.
Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima.
Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta.
Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama ta nesa ba.
Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu.
daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron yace"
Muhammad you're looking great and handsome.
Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa''
Sannu da zuwa.
Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing Muhammad da yayi a fuska Yana cewa''
Thank you.
Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa''
Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba.
Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani irin haske
Kodan ta Dade Bata gansabane.
Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine shigarta na farko
Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom.
Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau.
Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata.
Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo gida.
Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai dare sosai yake maidasa hannun mamansa.
Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum Muhammad na taredashi.
Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai,
USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar zai hadiyesa sbd so da qauna,
Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna.
Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu saina qaunarsu data zama kamar daya akan 'dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni.
Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba farin sani kayi mataba,
Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH zabeera,
Sam halayyarta da yanayinta sun sauya,
Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala,
Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta,
Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba
Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje wannan karon,
Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin zabeera.
Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking kamar sauran baqi.
Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa.
##Mamuh#
6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 42_*
Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da idanuwanta ke 'dan gani hakama kaf kuzuri da qarfin qafafunta sun Gama sarewa tun kafin ta Isa bakin gado ta zame ta zauna tareda sakin wani wahalallen kukan dakeson fito Mata tun lokacinda MAHMOUD yabude baki yafara Mata mgn.
Shikuma fridge ya biya ya dauko freshmilk me sanyi da ruwa ya nufi bedroom dinsa yanajin wani irin walwala da nutsuwa na qadatuwarsa.
Har lokacin kwance take cikin lullubin data rufe jikinta da Babu riga tayi zuciyarta na qoqarin zuqar numfashin dake neman gagararta,
Tasan tabbas anty zarah ce tadawo shiyasa ya, yafi kowa@' try da kansa and xa
zuwa ga bude Mata qofa batareda yasamu ko damar ce Mata Yana zuwa ba,
7 ya tube yashiga bai wani jima ba yafito ya sanya kayan bacci kamar koyaushe farare tas dasu yazo ya zauna Yana duba saqonni ta laptop da aketa kiransa akai yanashan freshmilk data rage sanyi yanayi Yana kallonta cikin kulawa tunaninsa tayi bacci.
Rufe aikin yayi ya miqe tareda qarawa AC din dake aiki qarfi sbd lullubin dazaiyi shima ya nufi gadon yahau tareda shigewa duvet din inda fatar bayanta da Babu komai ta hadu da fatar qirjinsa dake bayyane sbd rufe botiran rigar baccinsa da bayayi a qaida.
Rufe idanuwa da qarfi tayi zafin zuciyarta na tunzuro Mata da fitar da yayi dazun ta yunqura zata matsa daga jikinsa saiga wayarsa na qarar data sanyasu tsayawa su dukan musamman ita data gama sanyawa ranta Anty zarah ce sbd idan ba ita matarsa ba waye zai kirasa cikin dare daidai wannan lokacin.
Shi Sam baida niyar ko kallon wayar sbd Koda Rana ma daukar wayarsa ganin dama ne bare yanzu da dare,
Katsewa Kiran yayi yakai hannu ya dauko wayar da niyar kashewa saiga shigowar massage daga umman zarah ne ya tashi zaune Yana duba Kiran daya katse yaga ita 'dince takira saiya koma ya bude massage dinta,
"_Mahmoud Dan Allah kaje kayi mgn da zarah ka fahimtar da ita qarin aurenka ba Wai qarshen rayuwarta bane tanata kuka hankalina yatashi nakasa samun nutsuwa nasake kira Bata dagaba morethan 8times. _"
Yana Gama karanta saqon ya 'dan dafe goshi Yana Jin tun yanzu kamar kansa na neman qullewa,
Ta Yaya zarah zata damu kanta da kuka Bayan bawai yanxu ne akai aurenba,
Auren da shekara uku yanxu Amma tanason saka Masa ciwon Kai ga Amatun ma yaga alamar ita buga kansa zatayi ma da rigimarta.
Bai sake kallon Amatun dake kwanceba har lokacin taqi motsawa ya sauko Kan gadon ya zura slippers tareda aje wayarsa ya fice dakin.
Yana fita ta rintse ido sai alokacin hawayen dasuka bushe Mata suka Fara gangarowa ba qaqqautawa
Zuciyarta wani irin radadi da bugu takeyi kamar zata fasa qirjinta,
Wannan wace irin qaddarace tahadata auren Dame Mata,
Wace irin masiface wannan takejin kanta ciki sbd tiririn dake fita daga qirjinta Jin takeyi gwara ta mutu tabi Dr khalil dinta ba aure da wannan masifa,
Uban me yasa zai ajiyeta Dan ya ringa barinta Yana tafiyarsa saikace wata Mara sanin ciwon Kai.
Ta sauko daga gadon tabar dakin ma takasa sbd Sam ko qafafuwanta bataji ajikinta sbd rufewar zuciya,
Hawayentane ke tsananta gudu suna jiqa pillon da kanta yake kai.
Tashi zaune tayi ta kalla agogo idan tana qirgen mintuna daidai to yafi mintuna talatin da barin dakin.
Tana Nan zaune idanuwanta na sake rinewa har tsawon awa daya da mintuna ta miqe tsaye ta janyo towel ta daura ta nufi qofa ta fice bayan ta share idanuwanta dasukai jajir ta nufi dakinta.
Tana Murda qofar dakinta Yana fitowa dakin anty zarah din ko kallon inda yake bataiba ta shige kafin ta rufe saigashi a bayanta Yana kallon idanuwanta dasuka bayyanar Masa da halinda take ciki ya riqo hannunta ta janye batareda ta dago ta kallesaba ta nuna Masa qofa tace"
Bacci zanyi can you leave please.
Kallon fuskarta yasakeyi yanason ta kallosa su hada Ido Amma taqi saima gado data nufa ta haye zata kwanta cikin qosawa da fitinarsu yace"
Akan zarah ne??
Tsayawa tayi tareda dagowa tayi Masa wani irin kallo sai alokacin shedan ya lurar da ita kamar rigarsa jikinsa tayi squeezing ta maido kallonta Kan fuskarsa tace"
Meya kawo sunan anty zarah anan?
And akan wani dalili zaisa naji haushin kebantuwarka da matarka bayan nafo kowa sanin kanada iko zuwa inda take aduk lokacin dakaga dama Koda kuwa waye agabanka ko atare dakai.
Idan kinsan hakan then wats all this drama da kukan nan.???
Wani mugun takaici ne ya ciyota ta sauko Kan gadon tazo gabansa ta tsaya tace"
Idan har kana tunanin nayi kuka kokuma kukan danayi akan kaje gurin matarkane then u're dreaming sbd hakan baya gabana and idan kana buqatan kebewa da ita meyasa ka zabi zuwa Nan da ita akwai guraren dazakuje da basai ka tsaya yiwa wani bayanin Abinda yakaika dakin matarka,
Matark,Matarka,Matarka,Matarka please spare my life nagaji da Jin wanna hayaniyar infact inaga I will have to give you guys a break ta yanda zaka......
Will you just keep quiet" yafada a Dan hasale shima sbd tashin hankali da fitinar daya samu kansa ciki kaf rayuwarsa wannna shine karo na farko da wani ya tsaye yake fada Masa magana mace ma kuma bama namiji ba shi baima taba sa'insa da wani ba.
Kukane ya balle Mata tace"
Nazamar muku lalura da zamana atsakaninku Nima kun Hana zuciyata nutsuwa da shigowarku cikin rayuwata ta bangaren aure..
So yayi yai Magana Amma yafasa sbd juyawar da kansa keyi tuni idanuwansa suka sauya ya juya yafice daga dakin.
Bakin gado ta koma ta kwanta tareda sakin wani sabon kuka tana Kiran sunan Dr khalil daya tafi yabarta har haka ta sameta.
Washe gari gidan kaf cikinsu Babu Wanda yayi bacci musamman shi da sautin kukan daya baro tanayi ya hanashi ko rintse idanuwansa Wanda ya haifar Masa da ciwon Kai me tsanani Dan haka Koda gari ya waye ya yanke shawarar zaiyi tafiya kozai samu samu nutsuwar zuciya data cikin kansa.
Tun kafin su tashi Amatu tariga kowa tashi ta wucewarta makaranta bayan ta barwa anty zarah note din ta tafi school bakin qofar dakinta Dan batai niyar Shiga dakinba sbd kada antyn ta fahimci halinda take ciki,
Itama zarah din daga ciki ta rufe qofar yau batada niyar budewa Amatun sbd kada ta fahimci halinda take ciki sbd nemawa kanta sauqi ma cikin Daren tayiwa kanta booking ganin likita a _Santorini_ ta Dan samu tabar gidan na kwana biyu ko zata samu nutsuwa Dan haka tanajin ficewar Amatu itama ta tashi ta shiga wanka tana fitowa ta shirya ta dauki duk abin buqata ta dauki waya takira numbern MD cikin sa'a kira 'daya tana daf da katsewa ya dauka tafara gaidashi cikin sanyi da nutsuwa
Ya amsa Mata kamar ko yaushe kafin tayi Masa bayanin tafiyarta ganin likita yayi shiru da farko saikuma yadan gyara murya kadan yace ta fito idan tashirya su tafi tare sbd shima Dana Santorini din yayi niyar zuwa.
Jin hakan ta fito cikin farin ciki harta hada musu tea saidai itakadai Tasha yace shi Yana azumi.
Wayar Amatu yakira so daya Bata dauka ba sai kawai yayi texting dinta kafin suka wuce
itadai Anty zarah mamaki da ikon Allah kawai take kallo MAHMOUD dinda wani lokacin saiya Isa inda zaije yake fada Mata yayi tafiya wani lokacinma sai idan taga baidawoba takira yace Mata sorry ya aiki yadauki hankalinsa bai fada Mata yayi tafiya ba bayanan Amma gashi agabanta yake Kiran Amatu zai sanar da ita zaiyi tafiya 'yar ikon Kuma taqi dauka qarshe ya qare da rubuta text.
Jin tayi tafiyar tafita ranta Amma Kuma sbd lafiyartane Dole zataje kodan Allah yabata haihuwar Nan dai itama ko ALLAH zaisa hankalin MD din ya tsaya akanta itadake son abinta.
Lokacinda Text din ya shigo wayarta tana zaune cikin wani restaurant tareda annah sunacin abincinda Sam batamada appetite cin kawai takeyi tana karanta massage din tagama tabbatarda MAHMOUD ZABEERA qarshenta yakeson gani wato ta mutu ya huta,
To baza'a yi hakaba zaisan dawa yakeyi.
Gida Takoma ko makarantar Bata komaba tana zuwa tahau hada kayanta tana qoqarin danne hawayenta daga saukowa.
Saidata hada kayanta acikin akwati biyu kafin takira annah tace ta tayata ayi Mata arranging room a hostel zata dawo Nan.
Ba musu suka shigarda application din accommodation akace sai Nanda 7 to 8 days zata samu.
Dole ta hakura har zuwa lokaci tanata fatar asamu kafin dawowarsu din.
Daina fitama tayi Sam tana tsumayin jiran akairata akan angama Mata arranging komai na zaman hostel din wani gefen Kuma har yanzu zuciyarta batada nutsuwa bare sukuni gashi tun Yana Kira Bata dauka harya tattarata ya share dama baiwani Saba da duk irin wainnan abubuwan ba.
Kwanansu biyar suka dawo da anty zarah kawai ta gaisa ta shigewarta Bata sake fitowaba sai dare data fito cin abinci tagansu a dining ta wucewarta kicin ta dafa noodles taci tafito ta wuce daki
Anty zarah data fahimci da akwai matsala wato a tsakaninsu taso yin Magana saikuma tafasa tana cewa''
Kama kanki zara'u kafin abin ya juyo kanki Dan abin juyi juyi ne kowa da ranar baqin cikinsa indai zaman kishi ne.
Data lurada shima ko kallon inda Amatun tabi baiyiba saita sake Kama kanta da shishigin shiga tsakani karta jawowa kanta fitinar da gwara tasu musamman da yanzu magungunan da likita ya dorata akai yace ba'a son tana saka damuwa ko kadan shine zasufi aiki da yardar Allah zata samu ciki Dan haka saurin dauke kanta tayi akansu ta maida himma taci abincinta ta qoshi Tasha ruwa Tasha magani tana satar kallonsa sbd kobai Bari angani ba a fuskarsa tana iya hango tension ataredashi.
Kwana biyu gidan ana zabga rayuwar ba ruwan wani da wani tsakaninta dasu anty zarah ce kawai take zuwa har daki ta gaidata musamman dataga tana Shan magunguna ta tambayeta batada lafiyane ta sanarda ita na neman haihuwar tane take ta Kama kanta saima taji son komawa hostel dinta yaqara qarfi.
Duk wata hanyar haduwarta dashi ta toshe duk da dai yanzu futowarta take Palo tayi abindake gabanta sai hakan yaso ya daga hankalin anty zarah Kuma yanayin shegun kayanda Amatun ke sawa kamar wata baby ko ita dake mace idan taganta dasu dauke Ido takeyi bare ace namijine yaganta ahaka.
Ranar daya dawo idanuwansa suka sauka akanta da wata riga guntuwa Mara hannu tana kicin tana dafa taliya saura kadan yafadawa anty dake Masa sannu da zuwa ta kallesa tana mamakin irin yanda idanuwansa suka kasa daukewa daga Kan Amatun sai kawai ta juyawarta tabarshi tsaye Yana nufar hanyar kicin din
Amatu hangosa tafe ta sauke abincin ta fitowarta tana dauke kanta daga kallon inda yake harta gotashi taji yadawo da ita gaba dayanta ya matse cikin jikinsa Yana kallon idanuwanta datake dojewa kallon cikin idanuwansa tana qoqarin janye jikinta ya matseta dakyau cikin jikinsa gudun zarah ta fito tagansu wani aikin yasamesa yasashi dagata gabaki daya ya nufi dakinsa da ita bai sauketa ko inaba sai Kan gadonsa yaqi sauketa daga Kan jikinsa Kai tsaye yace"
Ankirani daga hostel na makarantarku cewan ur accommodation is ready,
Abinda banganeba anan waye zaikoma hostel din?
Sai alokacin ta dago da idanuwanta ta kalli cikin idanuwansa tace"
Nice zankoma hostel.
Wani wadataccen murmushin da Bata taba ganin yayiba yasaki Yana sake tungumarta yace"
Keep dreaming.
Daure fuska tayi tana qoqarin qwacewa daga jikinsa tace"
Nagaji da zama anan zantafi I need a break.
Serious yayi da fuskarsa Yana sakinta yace"
You are not going anywhere ki cire ran zama koina.
Masifa takeson suyi Dan haka Kai tsaye tace"
Bazan zauna anan ba nafi son zama can din.
Kallon fuskarta ya Dan Yi zuwa lokacin ransa ya Dan Fara baci ya sauko Kan gadon Yana cire agogon dake hannunsa tareda links din rigarsa yacire takalmin qafarsa ya nufi toilet Yana cewa''
Zangani idan kina zaman kanki ne coz I can see hankali bai isheki ba ita wadda kike kishin tafiki iya son mijin sbd tana kiyaye bacin ransa.
Kadan ya rage ta Dora hannu akai ta kurma ihun Abinda yafada idanuwanta sukai jajir ta sauko gadon ta nufi qofa ko gani batayi sosai sbd masifa ta fice tana cewa''
Yau wallahi bazan kwana a gidan Nan ba tunda dai kafito fili kafada Banda amfani.
Tana shiga dakinta ta janyo jallabiya baqa ta sanya tareda janyo akwatinta dasuke dama a shirye ta adauki Jakarta tafara Jan akwatin tana fitowa dasu ta nufi qofa idanuwanta