Showing 21001 words to 24000 words out of 39319 words

Chapter 8 - AKWAI BAMBANCI Book Complete BY (MRS BB).txt

Mrs BB   

15 Dec 2024

2640

isassun kud'i atare dani,
Abdul K'ara so muwuce dare nayi yayiwa Abokinsa magana dayaketa zuba waya da cikarsa.


Kowa yashiga yazauna jannat tayi tsaye tana waige waige,
Jabeer yafito yace"lafiya kuwa"
"Ina fah lafiya kuna shirin tafiya banga mubee bah"
Kallon compound din wajen yayi yace"may be tayi wani wajen"
"Bana tunanin hakan gaskiya, ina zargin tana ciki don tunda akafito banganta bah"


"OK zo muje mugani"


Shiga sukai Neman ta sak'o dalungu Amman basu same ta bah,
Duk hankalinsu yatashi sosai maigadin suka tambaya,
Yace"kuzaga baya naga wata d'azu tabi tawajen tunanina zata kewaya ne"


Har suna tuntub'e suka bi wajen,
Zaune take tasaka kanta cikin guiwarta tana wani irin kuka Mai ban tausayi, don da alama tajima tanayin Sa don gashi nan muryar bata fita sosai.


Cikin tausaya wa jannat ta durkusa k'usa da ita tace"haba mubeenat taya zakizo ki zauna nan kedaya maimakon kitaho cikin mu, saikace ba yan uwanki ba kinga dare yanayi tashi muje."


Cikin muryarta data dishe tace"jannat kubarni nan inajin kunyar ki nakasa yafewa kaina inajin tsanar Kai na akan abunda nayiwa mijina da ke, ta sake rushewa da kuka."


Kama ta tayi ta mik'ar da ita tace,
"Muje banason wani dogon bayani saikije kiyita tsanar kankin tunda nidai nace maki nayafe,to kuma tada maganar tamiye shikuma Adam wannan tsakanin kune, idan angama zaman k'ara kwa dai daita."


Bude baya tayi wajen nafee tazaunar da ita,
Takoma gaba tashiga yatada sukabar kotun,
Babu Mai cewa komi har suka karasa wani k'ayataccen hotel cikin k'an kanen lokaci yabiya kud'in dakuna uku,
D'aya shida baba, d'aya maman jannat da maman jabeer sai kakarshi d'in, sai d'ayan mubee da jannat sai nafee.


Order abinci yayo yakawo masu ishashen Abinci kuwa Wanda sukaci suka k'oshi,
Saida jannat tayi Jan ido ga mubee sannan tasamu taci Abunka ga Mai juna biyu saigashi taci dayawa, dama kuma ga yunwa tanaji.


Sukai sallolinsu kowa yasauke kafad'ar Sa saman katifa,


*JANNAT,MUBEE,NAFEE,ASUBA TAGARI*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*RANAR WANKA BA,AB'OYON CIBI*


Kotun tayi wata irin cika taban mamaki,
Don jiya anwatsa jaridar zaman da akai manyan mutane dadama sunkaranta,wasu saboda zalk'i da k'agara suji yadda za akaya sukataho don ganewa idonsu,
Don yau wasu saidai atsaye suke, wasu jingine da bango,
Adam ne akashigo dashi y'ansanda biyu ke tsaron bayansa har yatsaya mada katarsa.
Zuwan can akashigo dasu mama sukazauna,daka kallesu zakasan basu samu ishashen bacci bah,idonsu ya yakunbura.


Jannat tana sanye da kayan ta na lawyer tayi kyau har tagaji,
Satar kallon ta yake itama haka akai Sa,a yasake jefa idonsa cikin nata batasan sadda sassanyan murmushi yakucce Mata bah,


Alk'ali yashigo aka Mike don girmamawa saida yazauna sannan kowa yazauna,
Rubuce rubucensa yake yad'auki lokaci yanayi kafin daga bisani yayi gyaran murya tare da sallama yafara dacewa,


"Don tabbatar da cewar labarin da Adam yabayar gaskiyane, kuma duk abunda yafaru aciki hakan yake, ko barrister murjanatu tanada kwararan hujjojin dazasu tabbatar ma da wannan kotun cewa gaskiyane duk abunda yagudana,muna saurarenki."


Cikin girmamawa ta mike tayi gaisuwa sannan tace"yamai girma Mai shaira idan babu damuwa zanso kotu tabani damar gabatar da shaidata mafi k'aranta acikin shaiduna"


"Kotu tabaki dama"


Wani d'ansanda dasuka taho dashi daga gida Wanda yana d'aya daga cikin wad'an da suka kama mutanen dasuka biyo su jannat da jabeer ranar dazasu zo hunkuy.
"Tace inspecter jamil kashigo da mutanen nan damukazo dasu"


Babu b'ata lokaci yaje inda akarufesu yafiddosu duk sunyi ligif,
Saboda wuyar da akabasu cikinsu kuwa hada Bala.


Wajen tsayar da Mai laipi aka kaisu,
Qur ani akaba su don yin rantsuwa zasu fadi gaskiya, kuma duk sukai don KO idonsu basa iya budewa sosai.


Wajensu ta isa tayiwa nafarkon magana,"kozaka gayawa kotu sunan ka"


Idonsa d'aya saboda kumburi yarufe bakinsa yafashe jinin har yabushe saboda wuya, daker ya iyace wa"sunana hasanu"


"Meye alakarka da Adam"


"Oganmu ne alokacin baya damukai aiki dashi"


"Kozaka gaya ma kotu gaskiyar Abunda kasani akan wannan k'arar"


"Bazan iya b'oye abunda na saniba, oganmu barau shine yahad'a mashi wannan kullin saboda yafita daga cikinmu,Wanda dokace idan kashigo bazaka taba fitaba, kasancewar shine jarumin cikinmu oganmu yanaji dashi,shiyasa fitarshi cikinmu tayiwa oganmu zafi sosai, duk hanyar dazai ga yamaidoshi yabi Amman abanza,
Wataran muna zaune bala yashigo cikin d'okin sanar da oganmu cewar ai Adam zaiyi aure kuma diyar mutumen dayake farauta ce zai Aura, wannan wata damace da yakamata muyi anfani da ita wajen daukar fansa"


"Oganmu yace shikenan yasan mezaiyi,Bayan wani lokaci kawai yakiramu nida abokin aikin mu yace mushirya yau Adam zai tai abuja shida matarsa, bayason d'ayansu yarayu dagashi har matar tashi, haka mukabisu mukaringa harbe harbe ahanya har yayi nasarar tsere mana,
Mukadawo babu nasara
Amman oganmu bai hakura bah yasake turamu sadda sukazo kano zasu koma abuja,
Nan mukai nasarar turasu wani rami da tunanin sun mutu bansan ina oganmu yake samun labarin suba,
Yace basu mutuba angaya Mai,
Don haka lokaci yayi dazasu aiwatar da abunda suka shirya, bansan mesuka shirya bah kawai dai tsakar dare yakiramu zamu fita operation saigamu cikin gidan sirikin Adam,
Waya oganmu yad'auka yayiwa Adam text bansan meyace mashi bah,
Bayan yayi mashi text d'in ya sake yin wani kiran naji yana cewa hajiya muna iya shigowa yanzu,
Tace mashi Aa sukara d'an jinkir tawa, bansan dawa yayi wayar bah,Amman gaduk alamu bala yasani.
Mundauki awa guda darabi awaje kafin wacce yakira tasake kiransa, tace muna iyashigowa tak'ofar sama mukabi bayan mundaure maigadi gidan,


D'akin maigidan muka shiga yana kwance bacci yake don da alamar bai dad'e dafara shiba,
Wani bugu oga barau yakai mashi ga wuyansa,
Ahaukace yatashi yana kallonmu cikin tashin hankali,
Dariya oga yayi yace"barka da zuwan ranar mutuwarka,"


Sosai wannan mutumen yarud'e yana cewa mezan baku duk abunda kakeso zanbaka karkarabani da rayuwata,
Dariya ogan yayi yace"AI aikin gama yagama yau saika bak'unci lahira,Amman kafin nan bari naje nahuta da iyalinka don daman itace taturoni nakasheka,nakuma kwashi dukiyarka,sannan Adam nabisa hanyar zuwa cetonka,sadda zaizo kadad'e da tafiya barzahu dayazo kuma zaitaka sahun b'arawo, hukuma ce zata Kama shi akan shine yayi ajalinka,wata dariya yakwashe da ita, wanna bawan Allah yana kuka yana rokonsa Amman oganmu yabuge mai baki har hak'oransa suka fita,
Yafice yana kwance belt din wandonsa,
Yace mana mudaure shi muje mukwashi duk Iyakar kudi'n damukeso kafin yadawo, karkuma mubarshi yayi yunkurin guduwa,
Bayan oganmu yafita bala shima yafita don duba sauran d'akunan,
Ganin duk sunfita "nace mashi bawan Allah mezan taimakeka dashi kafin yadawo"


Yana kuka yace"kakunceni inason zanrubuta wasiyya ga y'ata kwanceshi nayi yadauko takadda da biro yafara rubutawa,
Yagama sannan yabud'e durowar Sa yaciro wani mukulli ya ajiye saman takaddar,
Yadawo yace na daureshi inajin tausayinsa dole nayi don idan nayi kuskure oganmu bayajin komi wajen kashe rai.


Haka yadawo daga aikata zinarsa,
Gabana yasakar mashi bullet ga kirji yakuma Sakar mashi wani ga ciki har guda biyu,
Mukafice mukabarshi yana halbe halben mutuwa,
Ficewa mukai daga unguwar, naga sadda motar Adam tawucemu,
Dariya oganmu yayi yace" shege Dan iska zaka gane kurenka,iyakar Abunda nasani kenan akan wannan case din
Sai kuma ranar da muka biyoku daya turomu akan karmu barku darai"


Shiru kotun tayi kowa najinjina irin rashin imanin da mutane kedashi,


"Mungode malam hasanu"


Tajuya ga bala tace"malam bala kozaka iya gayama kotu gaskiyar Abunda kasani akan wannan k'arar"


Shima dai muryar bata fita sosai yace"duk Abunda hasanu yafad'a gaskiyane, kuma K'arin wani Abun oganmu yasan matar marigayi don tsohuwar karuwar sace tun tana budurwa kan tayi Aure,
Sadda nakai mashi wannan labarin na auren Adam da diyarta,cewa yayi takwan gidan sauki bayan bikin ne yashirya yaje gidan nine narakashi,
Yazo amatsayin bako koda taganshi hankalinta yatashi,take cewa meyazo yi gidan Aurenta shine yace ta kwantar da hankalinta shi maslaha yazo sunema shida ita,
Yace kinsan Wanda kikabari yarki ta aura kuwa nan yake gaya Mata irin abunda ke tsakanin mijinta da Adam,
Yace tadalilin yaga y'arki yafita daga cikin harkarmu don haka ni tayani d'aukar fansa zakiyi kekuma nasan mekikewa,
Bai wuce kikashe mijinki bah kukwashe dukiyar data tsole maki ido keda shegun yaranki ko bahaka bah"
"Tace hakane kullum ranar duniya da wannan burin nake kwana nake tashi, saboda inahar nabari Alhaji yamutu bani nakashe shiba kaf dukiyarsa ta waccen shegiyar yar tashi ce dayake sonta fiye da kowa, ni Nahaifeta Amman jinake Zan iya hadasu du kana kashe shegu, yanzu mekake ganin zaai."


"Zamu Fara gamawa da Adam da d'iyarki daga baya maji dashi Mijin naki"


Tace "Yawwa haka za,ai yanzu jibi zasu wuce Abuja zanso daga lokacin sunbar duniyar"
"Yace angama saman number ki"


Haka kuwa akai Amman bamuyi nasara bah kamar yadda hasanu yafad'a
Haka nan rana tabiyu dazamu bisu itace tagaya mana tafiyarsu,
Wanda muka jefasu wani rami da tunani munyi nasara Ashe Bahaka bah,
Karshe suka yanke shawarar kawai sukashe alhajin sai adorawa Adam laipin,
Wanda za,ayanke Mai hukincin kisa batare da tsaurara bincikeba,iyakar Abunda nasani Kenan Amma Adam bashine yakashe Alhaji bah matarsa tabada kwangilar Kisan"


Jannat tajuyo tace"ya Mai sharia, wannan ma kad'ai ya isa yawanke Adam daga wannan zargin, Amman don kara tabbatar ma da kotu da mutanen ta gawata shaidar........




*MUHADU NEXT PAGE DONJIN WACE SHAIDAR CE KUMA ZAMUKARA JI*


TAKUCE HAR KULLUM MAMAN MUHSEEN✍🏻✍🏻
*KUMA*
πŸ‘‡πŸ»
_MAGAJIYAR KAINUWA_πŸ‘ŒπŸ»πŸ˜‰[2/11, 1:39 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


35&36.


Wannan akwatin tad'auko ta sanya makulli tashiga bud'ewa,duk inda hankalin mama yake yakai k'ololuwa wajen tashi, tabbas akwai matsala sunshiga uku inji mamar don tuni jikinta yafara b'ari.


Babu komai cikin akwatin face takaddu,takadda tafarko ta shaidar rabon gadoce tana magana akan cewar gadon su baban adam anrabashi,gashaidar anba babana nan sannan gashaidar anba baban mubee, sannan ga shaidar anba baban Adam da maman jabeer.


"Yamai sharia gashi kagani"


Tamika mashi sannan tacigaba dakaranta wata takaddar,
"Yamai sharia anan annuna cewar anaba mahaifin Adam gadon Sa Amman wannan wasikar da marigayi yayi ta bayyan cewa anba kowa kasonsa Amman banda mahaifin Adam."


"Ga abunda marigayi yake fada"


_"HAKIKA DUK WANDA BAIDACE MATA TAGARI BAH YANA CIKIN GARARIN RAYUWA,NAYI DANA SANIN DUK ABUBUWAN DASUKA FARU,HAKIKA MATATA CE KANGABA WAJEN GANIN NA HANDAME GADON Y'AN UWANA BANSAN MEYASA IDAN TASAKANI ABU NAKE KASAYIN MUSU AKAI,DUK ABUNDA TACE DANI TO NAKE CEWA KUMA INYI ABUN WALA MAIKYAU NE KOMARAR KYAU,ALOKACIN DANA SANAR MATA HALIN DA GADON MU YAKECIKI,ITACE TAZAUNAR DANI TAGAYA MAN YADDA ZANYI DUKIYAR TADAWO WAJENA,BANYI MUSUBA HAKA NAJE NA SATO KANENA MAIKAUNA TA NADINGA GANA MASHI AZABA,AKAN SAIYA GAYA MAN WAJEN DA YABOYE KUD'IN HALIN DAYAKE CIKI YASAKA YASANAR DANI,CAN KAUYEN NAJE HAR INDA YAGAYA MAN YA BINNE TA NAJE NATONO,NADAWO DA ITA MAMUDA DA MARIYA SUKA BUGA KAI GA BANGO SAI ANRABA ANBA KOWA KASAN SA,SUN SAKONI GABA DA TASHIN HANKALI,BANSANAR DA ITABA NAKIRA WANI LIMAN YARABA MANA AKAI KOMI ARUBUCE,DANA SANAR DA ITA CEWAR GA HALIN DA KUDI SUKE,NAN TAKE TACE TO WALLAHI KARNA SAKE NABA WANCEN BAREN,BANYI MUSUBA NACE MATA TO NASAKA KUDIN CIKIN JARINA NACIGABA DA JUYAWA,HAKAN BAISAKA NASAKI MUDASSIR BAH,DON GANI NAKE IDAN NASAKAI ZAI IYA KAIMU K'ARA,HAKA TARINGA BANI KWARIN GUIWAR GANA MASHI WUYA KALA KALA,HANKALINA BAIGAMA TASHIBA SAIDA NAGANO MANUFAR ABUNDA TAKEYI,ASHE BADAN ALLAH TA AURENI BAH TANA DA BURIN MALLAKAR DUK WATA DUKIYAR DANA TARA,BOKAN DAKE MATA AIKI SHINE YATONA MATA ASIRI SABODA TAKI BIYANSA KUDINSA,ASHE DUK YARAN DATA HAIFA MUBEENAT CE KADAI TAWA,SANNAN DUK ABUNDA TACE NAYI BANA MUSU ASHE SUNANA TAKAI WAJEN BOKA,SANNAN TAZIGANI AKAN DUKIYAR YAN UWANA SABODA TASAMU TAHADA MALLAKE. DAGA SADDA NASAN WANNAN NADAINA CUTAR DAD'AN UWANA NAKUMA CIGABA DAYIN TAKA TSAN TSAN DA ITA,SADDA SAGIR YANA BINCIKE AKAINA BANSANI BAH SAI RANAR DA TASAKA AKA KASHESHI WANI YARONA YAKE GAYAMAN,BANSAN CEWAR YARON MUDASSIR NE YA AURI MUBEE BAH SAIDA GA BAYA AKAYOMAN WASIKA AKABAN BANSAN KOWAYE BAH,DA ALAMA MATATA TASAN HAKAN,NAYI WA MUBEE KURARI NE AGABANTA DON KARTA ZARGI WANI ABU,SABODA INASON DAGA BAYA NAJE CAN ABUJAR,MUYI MAGANA DASU INDA HALIMA HAR NAYI MASU VISA SUBAR KASAR HARDA SHI MUDASSIR DIN,SABODA MUGUWACE TABUGAWA AJARIDA."_


_"BANSAN SHIRIN DATAKE SHIRYA WABA AMMAN TABBAS DUK NASAN TANAYIN WANI ABU MARAR KYAU,RANAR DANACE ZANJE ABUJA TABBAS BATA YARDA DANIBA SHIYASA TAYI DUK YADDA TAYI BANJEBA,KARSHE DAGANAN JIKINA YAMUTU NAKASA YIN KOMI,DON HAKA KOMI YABIYO BAYA MATATA CE TAK'ULLASHI KAR AZARGI KOWA SANNAN MUDASSIR YANA NAN CIKIN KOSHIN LAFIYA YANA GIDAN AMININA ALHAJI KAMILU MATAWALLE ACIKIN GARIN ABUJA SANNAN KASHI BIYU DARABIN DUKIYAR DANA BARI TA MUDASSIR CE KASHI GUDA SHINE NAWA SANNNA ACIKIN ZAINAB DA SAMA,ILA DA MUBEENAT TAU MUBEE ITADAYA CE DIYATA TA SUNNA SAURAN DUK YAN DANDI NE."_


Bayan tagama karantawa tamika mashi wasikar, tacigaba da cewa.


"yamai sharia kaji Abunda marigayi yafada,don haka ina rokon wannan kotu Mai adalci tawanke Adam daga zargin da ake mashi Sannan amallaka mashi hakkin mahaifinsa,akuma biyasu hakkin su da akadauka anzalincesu ancuta masu....... Hawaye take sharewa kuka nason kucce Mata,daker adakatar dashi,


Yamai sharia dauki kwak,kwaran mataki akansu, akuma hukunta masu ruwa da tsakin wannan case."


"Sannan har walau gawasu takaddu nan yamai sharia,nasamesu ne adakin hajiya deluwa da gani kasan masu muhimmancine anmasu wani irin boyo na musanman"


Tafiddosu tana dubawa,
"Yamai sharia wanann takadar mallakar gidan man shine,wannan kuma takardar mallakar gidajen Sa guda uku ne dake nan garin, wannan kuma ta filayensa ne guda biyu dake kano, wanna kuma takrdar gidan dasuke cikene akano."


"Yamai sharia sun sacesu ne sun yi sing don idan anzo nan suce shine ya mallaka masu,
Bacin karya suke macuta kawai, ina rokon wannan kotu da ta hukuntasu hukumci daidai da laipinsu,sanna inason abiya magabatan marigayi sagir diyyan ransa...... Kuka yakucce Mata Mai cike da tsananin kunci da kewar masoyin nata, taya zata iya mancewa da sagir Wanda yayi Mata wata kalar soyayya wacce bata tunanin hat tagama rayuwarta zatasamu Mai yimata.


Komawa tayi tazauna tana shashshekar kukanta.




*KUYI HKR DA WANNAN, MUHADU GOBE DONJIN IRIN HUKUNCIN DA ALK'ALI ZAI YANKEWA WAD'AN NAN MUTANEN.*


TAKUCE MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻


Kuma
πŸ‘‡πŸ»


Magajiyar kainuwaπŸ˜‰πŸ‘ŒπŸ»
[2/13, 8:08 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.




37&38.


Alk'ali yagama rubuce_rubucen Sa yad'ago yafara dacewa,


"Wannan kotu Mai Adalci tawanke Adam mudassir daga wannan zargin da akemai,sannan y'ansanda sukamo Barau sugurfanar dashi agabanta."


"Dukiyar marigayi kuwa kotu nabukatar lauyansa tare da duk wata kadara dayabari,domin fidda hakkin malam mudassir,sannan hajiya deluwa kotu tayanke Mata zaman gidan kaso watau daurin rai darai agidan yari tare da aiki Mai wahala,yaranta kuma zasuyi zaman shekara guda batare da cutar waba don yazama izna gakowa bama sukadai bah."


"Bala da sauran abokansu zasu kasance zaman din din din agidan yari tare da aiki tukuru,Barau kuma kotu ta yanke mashi hukuncin kisa ta hanyar rataya.......akawo Barau gobe y'ansanda sukeda alhakin wannan..... *KOTU TA SALLAMI WANNAN KARAR*.......


Hayaniya kotun keyi sosai bayan da Alk'ali yasallami kowa,


Kuka mama keyi itada su Zainab kamar zasu mutu yayinda y'ansanda suka sakamasu unka, bawanda yaji tausayinsu kokad'an mubee kau ko kallonsu batayi bah,don fatan ta awuce dasu ko zata daina ganinsu wata irin tsanarsu takeji acikin zuciyarta,idan tatuna dadynta dakuma irin yadda suka dorawa mijinta laifin da bashida hakkinsa,suka kuma zugata tayi mashi Shari akotu, wani irin zafi kirjinta yake Mata taji kwata_kwata tatsani kanta kuka tafashe dashi Mai rikita zuciya da ban tausayi sunagani aka tusa k'eyarsu cikin motar yan sanda.


Daya wan mutane murna da farinciki suke zuwa yiwa Adam shikuwa bakinsa yakasa rufuwa,don tsananin farinciki marar misaltuwa Mata da maza gaisawa kawai sukedashi Amman duk dahaka hankalinsa yakasu kashi biyu hangen ta inda zaiga jannat yake,
Daker yasamu mutanen suka ragu jabeer yabud'ema shi gaba yazauna.


Mubee tana jikin maman jabeer kuka take kamar ranta zaifita, don tayi nadamar kasancewar mamace mahaifiyarta jitake inama itace akayanke wa hukuncin kisan, lallashinta kawai suke cike da tausaya wa haka suka karasa wajen motar Abokin jabeer Abdul.


Alhaji malam yatunkari jabeer cike da kunyar Adam,don bayason suhada ido baisan da wane idon zai kallai bah.


"Jabeeru inajin baikamata mutafi gida bamuje mun ga mudassir bah kokuwa."


Huci yafurzar yana kallon gefe don bama Adam bah,harshi yanzu saiyaji haushin Alhaji malam din yake,Amman saiya danne yace.


"Aa baba kuje gida kawai danida Adam da jannat zamuje, duk dare insha Allah yau hunk'uy zamu kwana."


Bazai iyayin jayayya dashiba don sosai yakejin kunyarsu,
Yace,


"To shimenan aidashi zaku dawo ko"


"Sai yadda tayuwu dai don idan muntaho dashi bamuda gidan dazamu saukeshi."


Shiru yayi don baiji dadin maganar bah sai yace,


"Haba jabeeru gidana aigidan mudassir ne karkace haka, wallahi sharrin zuciya ne kodacan abunda yafaru,don Allah kitaho dashi naganshi nakuma roki yafiyarsa."


"Shikenan baba jeka insha Allah zamu taho dashi karkadamu."


Haka yajuya wajen motar yashiga,
Abdul din yaja motar suka nufi garin Kaduna konace hunk'uy d'in.


Duk abunda jabeer da Alhaji malam suka tattauna Adam yana jinsu,
Baice masu komiba saida jabeer din yashigo motar sannan yace mashi"meyasa kayi mashi Alk'awarin dabazaka cikaba."


"Kamar yakenan"


"Kace zaka taho dashi har gida bacin ni banada wannan ra,ayin zansamar mana mazauni nidashi wani wajen Mucigaba da rayuwar mu kamar lokacin baya."


"Karkace haka Adam, komi yariga yawuce karkace zakadauki gaba dakowa yanzu kowa yadauki darasi, sungane kurensu kuma kodan jannat kayafewa Alhaji malam."


Shiru yayi kafin yace"nemota muwuce yunwa nakeji,ga gajiya jikina ciwo yake salloli najirana."


Fita yayi yashiga nemanta daker yagano ta,
Taci kuka tagodewa Allah duk tanbayar dayayi mata takasa bashi Ansa haka tabude baya tashiga bata ma Lura da Adam dake gaba bah.


Cikin garin suka nufah kowa yayi jigum yana sak'e sak'e
Jannat ganin babu motarsu baba yasaka tace,


"yah jabeer ina su baba ne."


Yace"suntafi gida tundazu."


"To mu ina zamuje."


yace"zamuje mutaho da baban Adam ne."


Bata sake cewa komiba duk da sai yanzu ta Lura da Adam d'in.


Gaba d'aya tarasa meke cin zuciyarta kwata_kwata sai takejin haushin kowa takeji,
Sai take ganin bai rasa nasaba da tada Mata tsumin soyayyar sahibinta da akai ne shiyasa.


Basu sha wata wuyaba suka gano gidan mutumen,saboda sananne ne cikin garin babban mutun ne kuma d'an siyasa,
Anyi masu tarbar mutunci sosai angabatar masu da kayan cinye_cinye Amman babu Wanda yasamu damar saka komi cikin cikinsa,
Burinsu suga baban kawai karma Adam yaji labari.


Jannat dai tashiga ciki tayi salla harma tadan ci Julluf din cus_cus da ferfesun kaji da aka kawo Mata sai lemu.


Acan falon Alhajin yashigo cikin Fara,a suka sake gaisawa cikin mutunci,
Yace"gashi kuma babu Wanda nagane cikinku y'an samari."


Cikin girma mamawa jabeer yace,
"Alhaji mu yaran malam mudassir ne munzo tafiya dashi ne"


Cikin mamaki da Fara,a ssosai fuskarsa yace"dagaske! Amman gaskiya naji dadi waye Adam acikin ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login