Showing 27001 words to 30000 words out of 39319 words

Chapter 10 - AKWAI BAMBANCI Book Complete BY (MRS BB).txt

Mrs BB   

15 Dec 2024

2638

komi don baisan yazai cewa baban bah,
Don yariga yahakura da ita tunda har maganar wani tashigo kuma har an anshi kud'insa,sannan koba komi d'an uwanta ne bazai haddasa fitina bah yahakura Allah ya bashi hakurin hakan.


"Kai nake saurare,karkadamu dakomi sanar dani Abunda yake damunka."


Ajiyar zuciya yayi yace"Baba tun bayan kammala zaman kotun da akai nakejin wani bak'on lamari akan jannat Wanda hakan yaja jinkirin daidai tawata da mubee, nazauna tunanin yadda zanb'ullowa Abun nakasa samun mafita, nasanarwa jabeer shine ya bani shawarar hakuri da ita nikuma sainaji bagamsu da hakanba,don banajin rabuwa da ita,lokacin dana yanke shawarar sanar da ita sai nasamu har An anshi kud'in aurenta,mafarin shigata damuwa kenan Baba."


Numfashi baban yasauke yana nazari tsawon minty biyu baice komiba,
Kafin yamuskuta yace"Adam banji dad'in sanar dani dakai awannan lokacin bah,meyasa tun dakafara jin haka bakazo kasaman da maganar bah,wallahi ni maibaka jannat ne nakuma biyama ka sadakin ta,
Banji dadi bah sosai wallahi gashi kuma Usman d'ane wajen yayan labuda yayi mata komai narayuwa,yatai makemu lokacin da muka gaza, kaga kuwa bazamu iya Hana d'ansa y'armu bah."


"Kayi hakuri Adam dama ba rabonka bace haka Allah yaso daman."


"Bakomai Baba wallahi ni na hakura kawai ina kokowa da abunne shiyasa kuke ganin Kamar ina cikin damuwa Amman insha Allahu dana tafi komai zai wuce".


"Shekanan Allah yayi maka Albarka,yakuma sanya alheri acikin abunda zakatafi nema,"
"Ameen Baba"


"Yanzu idan kuntafi sai yaushe sai yaushe kuma."


"Eh to gaskiya idan ba biki yatashi bah banajin zamuzo nan kusa."


"To Allah yakamu tashi kaje daman maganar da zanmaka kenan"
Tashi yayi yafita baban yanajin babu dad'i don wannan damar ce kad'ai zata k'ara kusantashi da k'anensa don yanzu wata soyayyar baban Adam d'in take shigarsa yana sake nadamar Abunda yayi mashi baya.


Maman jannat tashigo tasameshi,
Tace"Alhaji me yaron nan yake fad'a ne"
Ajiyar zuciya yayi yazayyane Mata komi.
Kallonsa tayi tace"haba malam ai anabarin halak don kunya, yanzu Kai koda babu Usman saika bari haka tafaru, yanada Mata fah kuma d'iyar wanka ce ita y'an uwan junane AI sai araba kan zuminci wallahi, agara ma daya b'oye don bazan yarda dahaka bah,bawai don inakyamar Adam ba aa saidan ita wannan yarinyar AI yanzu abun tausayi ce wallahi."
Har tagama maganarta baice komiba don tadai riga tafaru balle ai tunanin wani sauyin.




Sorry wlh nagaji.


MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻


Kuma


Magajiyar kainuwaπŸ˜‰πŸ‘ŒπŸ»
[2/19, 5:18 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALK'ALAMIN*
πŸ‘‡

*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
πŸ‘‡πŸ»


*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻


```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


*42.*


Labarin tafiyarsu yagame gidan kowa saiyakejin bayajin dad'i akan tafiyar saboda irin yadda suka Saba.


Baidawo gidan bah sai bayan isha,i duk Ana d'akin mama Ana kallo arewa don lahadice Ana kallon kwana casa,in.
Sallama yayi yashiga jannat nacan kan gado tana more wayarta da Usman, dayake yau yakoma.


Bayason ko kallonta saboda mikin dake tasomai,
Kauda kanshi yayi suna gaisawa da Mamar,tana jajanta tafiyar kamar karsutafi.


Shikuwa tafiyar tafiye mashi zaman don idan har yazauna akai bikin to bamakawa zuciyarsa zata iya bugawa shikad'ai yasan irin zafin dayakeji akan kirjinsa.


Nafee tace"Allah yasa dai zakudawo biki"


"Ai nafesa inajin dak'er idan ba lokacin mubee ta haihu bah ko."


yafad'a yana kallon mubee dake zaune nafee na matsa Mata k'afafunta.


Hararar Sa tayi tad'auke Kai saboda kunyar mama datakeji Amman yayi Mata wannan tambayar gabanta,
Tace"bansani bah nima"
Murmushi mamar tayi batace komiba don talura mubee d'in kunyarta takeji.


Jannat tuni tagama wayar tacigaba da kallonta tanajin su bata saka masu bakiba don har yanzu mugun haushinsa takeji har yanzu,yaji Mata ciwo Amman sannu bata tab'a had'asu bah tunda abun yafaru.
Harara tabanka Mai sadda ya mike zaifita saiyayi kamar baigani bah yace ma mamar,


"Don Allah asa wani yakawo man Abinci ina d'aki don naga wannan bazata iya motsawa bah tayi nauyi, wallahi kirage wannan jibgewar kisamu sauki."


Yacewa mubee hararar Sa tayi tace"Duk motsa jikin danakeyi bai isaba ko, to bazan kashe kaina bah wallahi."


Mama tace "rabu dashi kinji Neman magana ne kawai."


Mik'ewa yayi yace "to kidai shirya karfe shidda zamubar garin Nan Allah yasa ki iya tashi don nasanki da nauyin bacci kamar kasa.
Fita yayi yana dariya tare da sauke wata wahalallar ajiyar zuciya yawuce d'akinsa.


Mama tace "jannat sauko kije kikaiwa Adam abinci tunda kingama wayar."


Wata bugawa kirjinsu yayi itada mubee,
Har basu san sadda idanunsu sukahad'u bah kowa da irin Abunda taji, ita mubee kishine yarugo yadanne Mata kirji jitake kamar tace abarshi takai mashi dakanta, batasan haka zaifaruba duk tunaninta nafee mamar zata tada.


Jannat kuwa hakanan taji batason had'uwarsu har yatafi don batasan meyasa idan takasance dashiba take jin wani sauyi,
Takasa banbance tsanarsa ce takeyi ko menene......"wai badake nakeba kikatsaya kina kallona"
Cewar mama.


Yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tace"wayyo mama don Allah kibarni nahuta wallahi jikina ciwo yake "


"To wakikeson natada bakiganin aikin da nafee keyi, ita wannan baki tausayinta idan lafiya lafiya ai itace Mai hidima dashi ko! Amman tunda bazakiba nibari naje nakai mashi...... AI bata k'arasa fad'aba tawuntsulo tafice nafee da kabir nayi Mata dariya itama mamar har tadara.


Takai minty biyu tsaye takasa shiga,
Yana kwance wayarsa yake ta danna wa yunwa yakeji sosai, kuma yaji shiru yasaka yatashi don zuwa yazuba dakanshi.


Yad'aga labulen sukai wani irin karo da juna kanta yabugi kirjinsa dakarfi, Wanda har saida yace washh.


Kad'an yarage tire d'in dake hannunta yazube saida yayi saurin tarewa,Wanda hannuwansu suka had'e gam da juna wani mahaukacin shock yakamasu duka Wanda yaja babushiri tiren yafad'i saman kafarta.
Miyar wainar maizafi tazubar mata....... Wata irin k'ara zata fasa har tace wayyoooo.......yayi saurin rufe Mata baki da hannunsa.


Jawota yayi cikin d'akin da sauri yabud'e toilet yazaunar da ita,
Ya zubama k'afar ruwan sanyi tana rik'e da ita tana zubar kwallah.


Riko ta yayi suka fito yazaunar da ita kan kujera yahau gyaran wajen,
Yagoge sannan yazo yazauna wani magani yad'auko cikin drower yakamo k'afar zai shafa mata, tafizzge tana kuka k'asa k'asa.


K'ara mik'a hannu yayi zaikamo cikin fushi da masifa tace"karka tab'ani! Nalura makasata kawai kake nema, to ta Allah bataka bah,duk bak'in cikinka kwanaki na basu k'areba baka isa kakasheni ba waccen ranar daga taimako ka so karyamun k'ashin baya,Allah yakiyaye Abun yatsaya iyakar targad'e shine yanzu kakeson idasani k........hannu yasaka yarufe mata bakin ya tsura Mata idanunsa masu masifar ladaftar da kowace gab'a tajikinta,kasa cigaba da kallonsa tayi idonta yana fitar da kwallah masu zafi ita kanta bazata ce ga dalilin zubarsu bah,idan don toyewar datayi ne bawata Mai zafi bace saboda miyar ba Mai zafin nan sosai bace.


Sauke hannunsa yayi ahankali yana kamo k'afar yashiga shafa Mata maganin,
Kallon hannayensa takeyi da yalwatacce gashi ya yawaita ajikin Han nun, y'an yatsunsa takalla aranta tace masha Allah,saboda yadda taga sunmata kyau.


Fuskarsa tasauke idon ga sajensa bak'ik'k'irin yakwanta luf ga fuskarsa sai matashin gemunsa shima sai salk'i yake hasken farin kwan nefa yahaske shi.
Jitai zuciyarta tana bugawa dak'arfi sadda yagama yamaida maganin bai Juyoba yace,


"Kiyi hakuri duk Abunda nayi maki da wancan da wannan bawai ina sane bane, idan kuma kina ganin nayi don b'ata maki rai to kina iyayiman duk Abuda kikasan idan kinyi zaki huce, gobe zantafi zanso murabu dakowa lafiya, musanman ma ke! Yafada cikin karyewar zuciya."


Alokacin idonsa yayi jawur saboda irin yadda zuciyarsa take masa zafi,
Idan yatuna jannat ta haramta agareshi danne mikin dake taso mashi yayi yacigaba dacewa,


"saboda nasan nayi maki badaidai bah awancen lokacin kina gidan baba Muhd (watau baban mubee kenan) tabbas nasan nayi abunda zaki k'ullaceni awancen lokacin Amman yanzu inayin komi ne don ganin nawanke wancan laifin awajenki."
Juyowa yayi idonsa kamar jangauta saboda rinewa dayayi.


Gabanta yak'araso yarage tsayinsa ya na saka idonsa cikin nata kamar yadda itama take kallonsa, jikinta babu inda baiyi sanyiba.
Yariko duka hannayenta yana Mai zuba masu ido,
Kafin yad'ago yakalleta yace"kiyafeman laifin danayi maki Abaya, narok'eki daki manta kicigaba da kallona matsayin d'an uwanki kuma yayanki, yadda kike d'auka *jann* bahaka bane zanso murabu lafiya saboda balallai kisake ganina nan kusaba,
*plzzzzz jann forgive me* runtse idonta tayi wasu Alburusai suna harbin zuciyarta,yayinda idonta yakeson cikowa da kwallah, hannayenta daya rik'e sunyi matuk'ar yin sanyi kamar yasasu frige, ga wata irin kerma dajikinta yake.


Cikin k'arfin halin da dauriya akan yanayin datakeji tace cikin rawar murya kamar meson fashewa da kuka,
"Nayafeka nima kayafe man."


Abunda ta iya fad'a kenan ta Mike daga inda take zata fita don kukane yakeson kucce mata,
Jitai yariko hannunta cakk ta tsaya bai motsa daga inda yake bah itama bata juyo bah tsayin y'an secons,
Yatashi yasaka hannu cikin aljihunsa yafiddo kyakkyawan zoben azurfah,Mai dutsen dake jikinsa pink color ne ajiya yasiyeshi dubu biyar cass, batare dayace komiba yasaka Mata shi ga y'atsanta kamar kuwa don d'anyatsan akai zoben yace,


"Bansan mezan baki gundun mawar aurenki bah naga ya dace nabaki wannan, Allah yasaka alkairi aciki yazaunar daku lafiya sunbatar yatsunta yayi tare da sakin ta."


Aguje tafice tana shashshekar kuka Mai tab'a zuciya.


Abincin dabaici bah kenan don wata irin soyayyar ta ce tataso mashi,
Jiyake daidai da fitar numfashinsa da zallar kaunarta yake fita,
Haka yakwanta cikin tsananin bege da tarin shauki.


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
Tunda kowa yayi sallar asuba babu Wanda yakoma,
Saboda tafiyar su Adam mama sai lallab'a mubee take jitake kamar karta tafi, saboda tana tausayin ta da tsohon ciki zatatafi wata duniya batada kowa wajen,
Sai gaya Mata yadda zata kula dakanta take, Wanda yasaka mubeen fashewa da kuka don saitaji itama batason yin nisa da mamar, saboda irin yadda take kulawa da ita.


Lallashi tashiga yi tana bata baki,
Shidda da rabi jabeer ya iso shine zaikaisu Abuja subi jirgi zuwa Lego's din.
Duk kowa yafito don ganin tafiyarsu Amman jannat tana d'aki tana gurzar kuka Wanda tunjiya take yinsa ab'oye don karwani yajita.

yanzu ma ganin duk sunfita yasaka takeyin Abunta afili,
Duk yadda taso tayiwa mubee sallamar kirki Abun yafaskara tadai ce Mata Allah yatsare yakuma kaisu lafiya.


Adam ganin bata wajen yasaka yashige mota don dama sungama sallamar, mubee ce aketa lallashi tana kuka.


Daker tayi shiru baba ayabud'e Mata tashiga haka sukai bankwana dasu suka bar k'ofar gidan duk saisukaji babu dad'i,
Kowa kagani sukuku.


don Allah kuyi hkr wlh naso ace typing din yafi haka wlh daker nayi wannan kuyi hkr jikin ne babu dad'i.


TAKUCE MAMAN MUHSEEN✍🏻✍🏻


Kuma


Magajiyar kainuwaπŸ˜‰πŸ‘ŒπŸ»
[2/21, 3:52 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


43.


Tafiya tayi ribah karfe takwas suka isa cikin garin Abuja,
Saida suka biya gidan wannan Alhajin suka gaidashi, yakuma ji dadi sosai sannan tare dashi akarakasu filin jirgin saida sukaga tashinsu sannan suka tafi.


Jabeer duk saiyaji kewar Abokin nashi taka mashi,
Koda yaushe suna tare bacci kerabasu gashi yanzu yatafi wata duniyar da ganin sama wahala zaimashi.


Acikin jirgin kuwa mubee kuka take Mai tab'a zuciya bakomi ne yasata kuka bah face mamanta data tuna.
Dole ya danne abunda ke taso mashi yaja matarsa ajikinsa yana lallashinta har yasamu tayi shiru saidai ajiyar zuciya datake ta saukewa.


Runtse idonsa yayi yana tuna nano moment d'insu da *Jaan* ajiya, wata suka yakeji ga kirjinsa kansa har saida yasara,yanajin kewarta har cikin ruhinsa kamar yakoma yakeji,Amman inaa bakin alk'alami yabushe tunda awanni hudu masu zuwa sun sauka, kuma tafiyar itace mafi aala awajensa saboda bazai iya zama yaga wannan aurenba,baya fatan ace ma ya sake sakata ga idonsa zaiyyi k'ok'arin ganin yagujewa ganinta.


Ganin zuciyarsa tafara bugawa dak'arfi yasa yayi jarumtar tsayar da tunanin ta don ba abunda zai k'areshi dashi face azabtar da lafiyarsa,Mubee bacci take sosai don dama bata samu isashshen bacci bah.
Cikin ikon Allah jirginsu yasauka lafiya karfe shidda na yammaci, sunsamu motocin tarbarsu sai lokacin nasan bafa k'aramin muk'ami Adam d'in yasamu bah,
Don motocine sukai shidda dasukazo d'aukarsa basusha wata wahala bah akad'auki kayansu suka shiga akawuce dasu masauki.


Duk da anriga da anturo mashi hoton gidan,
Bai zaci ganinsa hakaba yayi mashi kyau bamashi bah har Mubee saida tayi santinsa,
Gidane hawa daya Mai bene Amman yahad'u iyakar had'uwa,
Babuce kawai babu acikin gidan,yasha kayan alatu nazamani ga ma,akaita nan tako ina kowane da aikinsa tun saura sati suzo aaka d'auki ma,akatan don sufara aikinsu, gidan fah sai sambarka,
Ga bedroom nan sai Wanda kakeson zama falo uku ne mai d'auke da wasu arnan kujeru masha Allah.


Cikin kwanaki k'alilan Adam yawaye da aikinsa,
A company yana d'aya daga cikin wad'anda akeji dasu don shine nabiyu daga director sai shi.
Mubee kuwa bata komi sai d'an abunda ba,arasaba Amman wani gyaran gida, wata sanwa, wani wanki,wata shara,duk and'auke Mata su don duk akwai masuyi iyakarta tagyara jikinta tagyara turakar maigidan tah.


Tasamu mak'ociya Mai kirki shiyasa kewar tata dasauki,
Gakuma Mai aikinta maijidda wadda duk cikin y'an aikin sunfi shak'uwa da su.
Babbace akan Mubee shiyasa take nusar da ita akan wasu kurakuran datakeyi tsakaninta da mijinta.


Hakan kuwa yayi Mata dad'i sosai.


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*WAI INA LABARIN JAAN*


tunda su Adam sukatafi Jannat bata da wani kuzari komai zatayi, zatayi shi cikin kasalanci takoma so silent duk yadda zaka jata da surutu saidai kagaji kayi shiru don bazata tanka kaba.


Abunda duk yatada hankalin kowa nagidan kenan,
Bama kamar mama don tafi kowa damuwa Jannat d'in da akasani da kazar_kazar,Bata zama waje ita d'aya Amma yanzu saita wuni cikin d'aki ita d'aya idan ba wani babban abune yafito da itab,
Don dama mama tahana su yin sanwa tunda bikin yarage saura sati uku.


Usman kuwa duk yabi yadamu saboda gimbiyar tashi yakasa shawo kanta,
Batada wata magana idan yakira sai eh KO aa kokuma girgiza Kai kawai.


Hakan yasaka yabar duk abunda yake yataho KO zaisamu wani canji, tunda dafari yad'auka laifi yayi Mata saida yazo yaga kowa mah haka take mar.


Kakar jabeer data haifi babanshi itace tace damuwar Aurece dama dayawan y'an Mata suna shiga irin wannan yanayin,
Mama tace"to meyasa ita Nafee batayi."


Tace Mata"aidama bakowa bah, kowace da tata kalar damuwar don lokacin muna y'an Mata mu bama sanin ma wazamu Aura sai anyi, saboda damuwa har kwanciya muke ciwo."


Wannan maganar ta kaka itace tasaka kowa samun natsuwa dakuma yarda da hakan ne.


Jannat kuwa jinsu kawai take ita d'aya tasan irin uk'ubar da takeciki,don saitayi dagaske take iya had'iye Abincin bakinta idan tasaka,saboda k'uncin da zuciyarta take ciki.


Bata da wani tunani sai nashi, duk dare batada mafarkin daya wuce kasancewa dashi,idan tarufe idonta tabud'e gizo yake mata idota har ya k'ek'ashe da zubar kwallah saidai kukan zuci datake.


Aduk sanda ta tuna da yatafi yabarta,kum ya na can ya kasancewa da matarsa,wani kullutu ne yake tsaya Mata ga mak'oshi batajin yawuce saitayini tana kuka daga safe zuwa yamma.
(Nikau nace aiki yasameki jannat,don KO idonki zaifito aikin gama yagama)


Ita kanta mamakin kanta take,
Wannan damuwar tata duk don shi takeyi, shin saida yatafi tafara jin wannan yanayin koko dama tanaji yanzu ne yabayyana?
Amsar data kasa bawa kanta kenan.


Yau Mubee tatashi da ciwon nak'uda,
Kasancewar Maijidda nanan ita tataimaka sukatai asibiti, komi yazo da sauki tahaihu lafiya tasamu kyakkyawar budurwa son kowa k'in Wanda yarasa.
Nanfa Aka ranbad'ama Adam kira cewar matarsa ta sauka,ai babu shiri yarugo asibitin cike da tsananin murna da farinciki,har kwallah yayi don bak'aramin farinciki yake cikibah,har saida yayiwa Maijidda babbar kyauta ta Albishir d'in datayi ma shi.


Nan take yabuga waya gida yasanar wa da baba,
Shikuma yagaya ma sauran gida yad'auka cike da farinciki,mama taji dad'in jin babu wata matsala.
Jannat tayi murna itama sosai saitaji inama zataga hoton yarinyar,tace wa Nafee"ki masa magana ta what's app yaturo hoton babyn."


Tace"yanzu kuwa Yaya wallahi nima zanso naganta,tad'auki wayarta don mashi magana"


Sosai Adam yake cikin murna duk Wanda yake tare dashi yasan yana cikin farinciki.
Mubee har mamaki take yadda taga yazage yana basu kulawa fiye da lokacin kafin tahaihu.


Zaune yake yana ba jaririyar ruwa sai wasa yake Mata Wanda batasan yana yibah,tunda jaririn kwana uku meyafara Sani ma lokacin.
Kallonsu take tanajin dad'i tabbas ko iyahaka tasamu ya isheta, yanzu bata da wani buri daya wuce tacigaba da kulawa da mijinta da yarta, takuma rok'ama mahaifiyarta yafiyar ubangiji,wasu kwallah suka zubo Mata tunawa da tayi sunso zubar da cikin Allah baibasu damaba.


Share kwallar tayi tace"Abban baby ni har yanzu banji kace ga sunan babyn bah tunda aka haifeta."


Murmushi yayi yakalleta yad'auke Kai yana goge Mata bakinta yace,
"Ai nad'auka bazaki tambaya ba."


"Abunda yasa nayi shiru nad'auka zaka gayaman ne saikuma naji shiru."


"sunan ta *MURJANERTUU*."


wata irin bugawa k'irjinta yayi idonta yad'an cicciko da kwallah tana kallonshi,
Ajiye ta yayi yad'ago yana kallonta yace,
"Bakiji dad'i bah KO?"


Bata iya bashi ansa bah sai kauda Kai datayi tana kallon wani wajen daban,
Tabbas taji haushi takumaji kishi shiyasa yakasa gaya Mata cewar ga sunan da yasaka Mata........


"Ki waigo kiyi kukanki bazan hanaki bah,ai band'auka donkinji nasaka wannan sunan ki damuba!ta citoni daga cikin wata rayuwa wacce nafidda ran cewar zansake wata rayuwa Mai y'anci,saigata tasadaukar da ranta,lokacinta,dakuma lafiyarta duk dan tawa rayuwar."


"Kigaya man tawace hanya zanbi nasaka Mata?"


Kallonsa take idonta nafidda kwallah tace,
" *KA AURETA*"


Murmushi yayi maikyau tare da gyara zamanshi,
Yana kallonta kafin yace,
"Mubeenatu kenan."
Sunan da koda yafara zuwa zance gidansu baiya fad'a Mata shi sai yau.


"Tabbas hakan naso nayi Maman baby,saidai Abari yahuce shike kawo rabon wani, bara bona bace shiyasa kinga da basai kinfurta bah."


Kwallah ta share tace cikin kishi da haushi,
"Ai nagano abunda kake dannewa tun acan gida aida sakace ba kayar daba, idan ba itaba sai rijiya Mai kwalabe"


Tafad'a tana mik'ewa don barmashi falon...... Dariya yakeyi yajawota jikinsa yana cigaba da dariyarsa tuttureshi takeyi tana kukan shagwaba,
Matseta yayi gam yana shinshina wuyanta, tare da bata zazzafam kiss.


Ba arziki ta bar zille zillen,
Suka zauna suka fahimci juna bai b'oye Mata komai akan son dayake wa jannat bah.
Tare da gaya Mata cewar shi yariga yayafeta tunda har maganar wani tashigo,cikin k'ank'anen lokaci suka daidai ta dajuna suka kuma fahimci juna,


Anan yake gaya Mata cewar jibi jabeer zaizo suwuce gida acan za,ai suna tazauna har tayi Arba,in idan yasamu lokaci zairinga shigowa,
Batayi musuba don itama tayi kewar mama dasu Nafee.




Fatan bakuyi fushiba jiya,
Wlh jikin ne sai aslow😊


TAKUCE MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻


Kuma
πŸ‘‡πŸ»
Magajiyar kainuwaπŸ˜‰πŸ‘ŒπŸ»
[2/22, 4:42 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login