Showing 39001 words to 39319 words out of 39319 words

Chapter 14 - AKWAI BAMBANCI Book Complete BY (MRS BB).txt

Mrs BB   

15 Dec 2024

2632

kad'an........haka kuwa akai.
Sun had'e kansu Bakajin kansu duk randa Mubee keda aiki to jaan zata d'auke Baby sukwana tare,
Har sai mamanta ta gama kwananta sannan,
Sosai Suke kulawa da mijinsu don kan wani lokaci yazama babban Mutun,kowa mamakin irin kibar dayayi yake,
Saidai yace ai shi d'an gatan matanshine,jidashi Suke sosai........ Mubee da Jaan saikace kawayen juna Idan wannan keda girki zata taya ta dawasu abubuwan, don yace gasudai bazaici abincin kuku ba,
Basuga laipinsa ba don dama hakan shine daidai.


*BAYAN SHEKARA GOMA*


Alhaji Adam yazama babban mutun da ake alfahari dashi ciki garin Lego's
Don yayi fice ta ko Ina GA addua da yake samu wajen iyayensa da matansa,
Zuwa yanzu yaransa biyar cif
Jaan haihuwar farko y'an biyu ta haifa, mace da namiji,
namijin sunan baban Mubee tace Adam yasaka,
Suna ce masa bassam wannan Abu yayiwa Mubee dad'i har kuka Tayi tana godewa masu da wannan kara......
Macen kuma maman jaan taci suna ce Mata basma.
Bayan nan Mubee tasake haihuwa ta samu bilal mai sunan baban Adam,
Sai baba Alhaji da Jaan ta sake haihuwa.
Alhamdulilkah komi yayi farko zaiyi karshe wannan family suna cikin farinciki, da annashuwa,
Nafee Kuma yaransa biyu shuhuda da shahid maman jabeer da babansa....


Kuma d'aya bayan d'aya saida Adam yakai kowa hajji,
Yakuma je yasaki uwayen kud'i aka saki maman Mubee,
Wannan lamarin yayiwa kowa dad'i don Mubee tama rasa da wane irin kalamin zata godewa mijinsu.... Don Hakika Sunyi dacen miji saidai muce Allah yabasu zaman lafiya, yakuma albarkaci zuria rasu Ameen


Alhamdulillahi Tammat


Allah Nagode maka daka bani ikon kawo k'arshen wannan littafi,ina godiya gareka kabani lafiya da tsawon Kwanan cigaba da kawo darussa acikin littafina,
Ina rokon Allah kabawa iyayena lafiya kakaramasu Nisan kwana, da bud'i na alkhairi.........
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Muhadu daku cikin sabon book d'ina mai suna ADUNIYAR MU Amman na kud'ine free page goma zanyi daga nan duk mai so zata tuntubeni.
TAKUCE MAMAN MUHSEN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login