Showing 18001 words to 21000 words out of 39319 words
ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```
29&30.
Kowa yafito don gabatar da sallar la,asar dayake akwai masallaci cikin compound din kotun na maza da mata,
Sai duk kowa yashiga yin alwallah don alkali dakanshi zaja jam,in.
Yayinda Mata sukuma zasuyi tasu sukadai,
Mubee tunda akafito take kuka kamar ranta zaifita don sai yanzu take datasanin abunda ta aikata wa mijinta Mai kaunarta,
Kuma sai yanzu takeji garanta tabbas bashine yayi wannan kisan ba,don tayi imanin Adam bazai taba kashe Mata mahaifiba saboda duba dayadda takeson dadyn,
Tunda yafara sonta yadaina bibiyarsa akan case din babanshi kuma daidai darana daya baitaba nunamata wata alama dazata gane akwai abunda yake tsakaninsu da dadynta,
Lallai soyayyar da Adam yake Mata bayar karama bace.......
Ganin jannat tafito daga masallaci yasaka tatsagaita da tunanin nata,
Wajen datake hangota tanufah idonta jawur kamar wuta.
Tana zuwa rungumeta tayi kawai tasaka kuka Mai taba zuciya,
"Jannat don Allah kiyafeman kiyiwa girman Allah karki rikeni aranki, wallahi nayi danasani har saudubu akan abunda yafaru nasan nayi maki badaidai bah kiyafeman.....jannat kiyafema....takasa karasawa saboda tsananin kukan datakeyi... Juyoda ita jannat tayi tarungumeta sosai ajikinta itama tana goge kwallah tace"wallahi mubee bantaba rikeki cikin rainaba daidai da kwayar zarrah,nasan sharrin zuciyane dakuma zigar dakike samu kiyi shiru komi yazo karshe niban yi niyyar taimakon Adam don komi ba nayine don Allah dakuma kare wa dady hakkin ransa don makasanshi suna tare dashi"....
Mamarsu tajawo jannat din tana lallashi,
Nafee tausayinta yakamata don kodama can ita sarkin tausayi ce.... Kuma duk halin mahaifiyarsu suka dauko.
Adam yayi addua sau babu iyaka,
Yakuma godewa Allah dayajefo mashi yan uwansa acikin wannan shariar don daba don Allah yana sonsa bah duk daba hakaba, jabeer yaketa karamai kwarin guiwar cewa"kasa ki jikin ka kazayyane komai Adam, wannan kotun Mai aadalci ce fiye dakowace acikin wannan Nigeria inamai tabbatar maka dacewar saika kubuta kuma da idonka zakaga munafukai dasuka so jefaka cikin wanann bala,in"
"Jabeer banida bakin dazan iya godemaka kaida jannat,hakika inajin kunyarta jabeer saboda irin abunda naringayi Mata duk sadda mukahadu agidan,Amman yau itace ta tsaya Kai da fata don ganin tacetoni daga cikin wannan halin, abunda ya dace ace mubee ce keyi Amman ita takasa anhada baki da ita don agabaya na.... Shin metare Mata itakuma... Yafada yana zubar da kwallah yana gogewa"
"Karkadamu insha Allah komi yazo karshe muk'arsa cikin, yansanda suke tsare dasu don tsaro, haka suka isa cikin kowa yasamu wajen yazauna,
Alkali shima yagyara zaman sa don yanason jin yadda akai wannna abun yafaru.
kallon Adam yayi yace"muna saurarenka"
Jannat dake gabansa takallai,
Duk yakoma kalar tausai Amman idan tatuno irin yadda yaringa cin mutuncinta sataji tama daina jin tausayinsa,cikin dakiya yacigaba dacewa.
"nayi matukar farinciki dajin labarin datake sanar dani saidai bangare guda inacikin kewar mahaifina, taya zankub'utar dashi daga hannunsa gashi yanzu inashirin zama sirikinsa,yazanyi da wannan al,amarin kuma.
Jin nayi shiru yasa tace"kodai baka murna ne"
Cikin yak'e nayi Mata murmushin dole nace zanzo yaushe yake gida"
Tace"anjima wajen karfe takwas zaka taddashi"
Nace"Mata insha Allah zanzo haka muka yi sallama jikina yayi sanyi kalau, sainakejin kamar naso kaina dayawa taya inacikin neman hanyar ganin naceto mahaifina kuma nake kokarin ganin nayi aure kuma da diyarsa, shin taya Zan iya kubutar da babana.
Haka nakasance cikin jullumin haduwarmu don ina tunanin kokarya ganeni duk da bai taba ganin zahirin fuskata bah,
Cankuma wajen su ogana nema na kawai suke kasa rik'a don alokacin ya hau sosai akan rashin binbayan kiran shi da kkume text dinshi gashi yanzu yana nemana baisamuba,sosai suka baza mutanen su nemana acikin garin,
Dadaddare nashirya don zuwa gidansu mubee banyi niyyar hawa motata bah,saboda tsaro kawai sai nahau tahaya dayake akwai yafiya maidan nisa daga gidan danake zuwa cikin gari,
Awa guda tasadani da unguwarsu ina wajen get nayi Mata waya gani na iso,
Taturo kanwarta tayi man iso
(Yasaci kallon jannat don yasan tatuna lokacin,don har sannan saida ya yabamata magana)
Gani ga mamanta ga dadynta cikin mutunci suka gaisa dani yake tambayata karatuna nagaya Mai yace KO ina aiki yanzu, nace masa aa bana aiki yabani ID card dinsa yace nakaimai takadduna gobe office dinsa zaisaka asamar mun aiki, wane gari nake sha,awar zama nace masa duk inda yasamu zanzauna,
Yajani da hira sosai nayi mamakinsa haka yake cikin iyalinsa Amman yanacan yana gana mawasu azaba saboda kudi hakadai nabaro wajenshi ina cike da tunane tunane,
Tayi man tayin zata rakani gida nace Mata aa tabarshi Amman takafe dole nace Mata Amman gaskiya saidai ta ajiyeni bakin hanya don ina gudun kar wani Abu yasameta tace taji,
Haka muka tafi cikin farinciki take mun fira inadaurewa inabata ansa hankalina baitashi bah saida naga mota nabin bayanmu,
Gashi sunkusa iskomu ansar tukin nayi nasaka Mata belt nima nasaka,
Mukahau tseran gudu dasu saman titi ganin suna gaf dasamunsu saboda harbin dasuke masu yasaka Nataka motar damugun gudu mukai masu nisan dasuka kasa isokomu,
Kuka take sosai akan wannan al,amarin wani waje suka fake daker nashawo kanta tayi shiru shine take tambayata suwaye,
Ban boyemata duk abunda yakefaruwa tsakanina dasuba tashiga tashin hankali Mai girma kuka tayi tayi ina lallashinta,
Karshe dai mubee banbarta takoma gida itadaya bah,
Saida dare yadan raba namaidata nikuma nakwana wajen maigadinsu dasafe nakoma gidana,
Bayan kwana biyu take ceman yakamata amatso da bikinmu kusa mubar garin don samun zaman lafiyata,
Banki ta tataba nace Mata to zanyi magana da magabata na,
Tace tasanar da mahaifinta asamar mani aikin abuja yadda zamuyi nisa dasu, nikaina naji dadin shawarar data yanke haka mukai sallama,
Nafara tunanin wazan tura matsayin dangina jabeer nanemo shiysaka iyayen Abokinsa suka ansarmun auren mubee,
Ranar kuma mahaifinta yaman albishir dacewar aikina yasamu yabani opper din andaura mana Aure da sati guda komai yakammala,
Har anje anyimata gyaran daki ansaka komai tarewa kawai zamuyi,
Har lokacin inacikin zullumin su ogana,
Ranar wata litinin mahaifinta yadankaman sabuwar mota yace gashinan dagani sai matata zamutai, daga baya zamuzo da yan gida gaba daya,haka mukai bankwana dasu cike dakewarsu mubee tarabu da yan gidansu.
Alokacin inaji ajikina akwai abunda zaifaru Amman rashin sanin menene yasaka nayita addua,
Tafiya muke muna hira har tayi bacci saboda tsaron laluri yasaka nafiddo bindigata na ajiye kusada ni gudu nakeyi sosai,
Kamar daga sama nahango motarsu gabana yafadi haka nad'age glass din tagogin,
Nasamata belt nima nasaka narike bindigar ga hannuna,
Nasaki male jin matar tsere mukashiga yi dasu Wanda hakan yatasheta daga bacci kuka taringayi bakamar dataji muna musayar harbi tsakanin mu,
Motar su tabangaje mu kadan yahana bamu sirmiya cikin wani kwakware ren rami,
Cikin ikon Allah nayi nasarar dawowa kan titi,
Saita tayar motarsu nayi nasakar Mata harbi nan take tafashe,
Inaganin haka nakara gudun motor mukai masu nisa sosai,
Saida taga dagaske babu su bayanmu sannan tayi shiru,
Tace"Amman Adam tayaya sukasan zamuje abuja,
Anya bawani yagaya masu bah kuwa,"
"Wallahi mubenat bansani ba Amman babu mamaki wani zai sanar dasu, ko ranar da sukabimu dole akwai yadda akai saboda banyi tunanin zasu San inda nakeba"
Haka mukaita jajanta wannan al,amarin har muka isa Abuja,
Gidan yayi kyau nakuma yaba da kokarin dadyn satinmu guda nafara zuwa aikina Wanda yayi man dadi hakika inajin dadin aikin nawa,
Awannan lokacin jabeer yazo man da labarin wani babban dan bincike, nace zanzo garin muhadu nayi mashi bayanin abunda nakeso,"
Tare da ita mukatai kanon nasamu ganawa da *SAGIR UMAR YAWALE*
Azabure jannat tajuyo tana kallonsa cike da tsananin mamaki,
Tace"kace sagir umar yawale,"
*TAUFAH MEYAKAWO SAGIR DIN JANNAT CIKIN WANNAN LABARIN,KUBIYONI DONJIN CIGABAN WANNAN SHARIA MAI MATUKAR DAUKAR HANKALI*
*INA ALFAHARI DAKU MASOYANA KUNA RAINA AKODA YAUSHE*
TAKUCE MAMAN MUHSEEN.βπ»βπ»
_MAGAJIYAR KAINUWA_ππ»π
[2/5, 4:01 PM] MAGAJIYAR KAINUWAπ: πππ
*AKWAI BAMBANCI*
ππππ
*DAGA ALK'ALAMIN*
*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*
*{MAGAJIYAR KAINUWA}*
*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
31&32.
Shima kallonta yayi yace"tabbas sagir umar yawale, shine mutumen danagana dashi ranar dansauke mubee gidansu nawuce inda mukai zamuhadu dashi,
Mungaisa sosai dashi bayan munsamu waje mun natsu yake ceman banine mijin mubenat Muhammad ba,
Nace masa kwarai nine yasanta ne, yace sosai makuwa don kanwarta budurwasa ce har ma anyi masu baiko,Amman me yake tsakanina da Mahaifinta har danake son binciken abunda yake aikatawa Aboye,
"Nagaya mashi gaskiyar abunda yafaru da babana yatausaya man sosai yace"insha Allah nikuma zantai makeka akanhaka zanyi maka duk binciken dakakeso idan ma nasamu nasara kila kaga nadawo maka kafata kafar babanka,
Nashiga farinciki Mai tsananin yawa nabashi kudi dubu hamsin yace bazai ansaba sai yagama aikinsa,
Mukai exchange din number waya mukarabu cikin mitunci,
Kwanan mu uku kano nace mubee tashirya muwuce tace man to,
Amman gaduk alamu akwai abunda yafaru agidan Wanda bansani bah,
Saboda irin kallon wulakancin da mahaifiyarta taringayi man lokacin yatsaya man garai,
Sannan yayanta munsaba gaisawar mutunci sosai Amman ranar KO kallona baiba,
Haka mukabaro kano munyi da sagir zamuringa waya akai akai,
Still wannan ranar ma saida oga yaturo yaransa subiyo mu,
Nayi mamaki da al,ajabin hakan shin wai waye yake sanar dasu halin dasuke ciki,
Wannan karon Allah ne yacece mu don kadan yahana bullet din dasuka harbo yasameni ga Kai sai Allah yatsare,
Haka mukaita tseren gudu dasu bisa hanya har sukai nasarar tura motarmu cikin wani rami,
hakan yaja nasamu mummunan ciwo har karaya nasamu ganin mufada cikin wannan ramin yasaka sukajuya,
Daker da taimakon wasu masu kiyo cikin wannan dajin suka fiddo mu cikin ikon Allah motar bata mutuba Amman glass din baya dana gaba dana gefen danake duk sunzube,haka babu fitilar motar tadauke duka, ganin bazan iyayin tukiba yasaka ta anshi motar duk da ciwon dake jikinta itama, hakadai muka karasa cikin garin Abujar,
Asibiti mukatsaya saida akai Mata dressing din Goshinta da hannunta nikuma akaiman gyaran karayar,
Sannan mukai gida saida nayi wata da watanni sannan nawarke, munata waya da sagir akan cewa yasamu shiga wajen saidai inda yake boye da mutanen akwai hadari awajen, don wajen zagaye yake da waya wacce kuskure kadan yasaka kataba ta to shock ne zakamata saidai kamutu awajen,
Nayi mashi kashedi da tunkarar wajen nace yabi wata hanyar Amman banda wannan,
Yace inbashi nan da kwana biyu komi zaizama normal.
Haka nacigaba da sauraren sagir gefe guda mubee tasaka damuwa aranta nayi duk yadda zanyi nayi Mata maganin ta abun yafaskara.dole nasaka Mata ido.
kwatsam rannan, jabeer yasanar Dani rasuwar sagir,
Nayi kuka nayi bakin ciki naji kwata kwata rayuwar natsaneta, kenan babu Wanda zainemi fallasar asirinsa saiyayi sanadin mutuwarsa yasaka akashe shi,nashiga damuwa Mai tarin yawa haka nahakura nacigaba dayiwa mahaifina addua akan Allah yatsare manshi shikadai yarage man Allah kakare shi,
Ganin irin damuwar da mubee keci ki yasaka na tilasta Mata akan saitagaya man abunda yake damunta idan bahaka bah kuma nima zanyi fushi da ita,
Tana kuka take sanar Dani cewa"yan gidansu sungano ni Dan fashine dadynta da mamanta sun tilasta ta akan sai tarabu dani itakuma tace bazata iya rayuwa babu niba, shine maman tace inhar bata nemi Saki wajena ba to zata gamu da bala,in da dole tagujeni,hankalina idan yayi dubu yatashi jikina har rawa yake alokacin kaina har sarawa yake,
"Nace haba meyasa zatayi haka mama, bayan tasan irin son damukewa juna ehy, kuma baki gaya Mata cewar nabar wannan sana,ar ba kigaya Mata nabarta wallahi tunda nabarta bansake marmarin komawa bah,hawaye yake shatata daga idona saboda inason matata banason duk abunda zai rabani da ita,
Shikenan ni duk abunda nake dashi sai narasashi,
Nataso babu uwata ina rayuwa hannun yar uwata naduketa tamkar mahaifiyata,itace komi nawa na rayuwa itama na rasata na dan gana na rungumi k'addarata, nacigaba daka sancewa da baba na na sadaukar daduk lokacina akan shi don inaganin shikadai garan vanida kowa,
Shima kaddara tarabani dashi,
Yanzu kuma matar danake samun farinciki gareta itama anson rabani da ita............. Kuka yafashe dashi Mai tsananin kunci da taba zuciya duk Wanda yake cikin wannan kotun indai Mai imani ne dole yatausaya wa Adam halin dayashiga,
Dayawa kukan suke tayashi karma jannat taji labari,
Don har saida tadurkusa tana shashsheka,
Tsawon minty biyar sannan yashare hawayensa yana kallon mubee da ta duke itama kukan takeyi,
Nadama da dana Sani suke cinta meyasa tabiyewa mama da Zainab meyasa Tayiwa mijinta irin wannan butulcin,
Cikin dashewar murya yacigaba dacewa,
"Ina zubda kwallah nace mata mubenat kece kadai nakesamun farinciki daga gareki narokeki karki rabu dani kece shaida Allah ne shaida tunda nabar wannan sana,ar bansake mararin komawa bah, kina ganin irin yanda suke bibiyata akan rashin komawa cikinsu kigaya masu nadaina kinji"
Kukan take itama tace"Adam yazanyi tun da mukaje gida mukadawo nakecikin wannan tashin hankalin,saboda haka mane dady yayi fushi Dani akan nace bazan iya rabuwa dakai bah,
Kowa yadaina daga kirana idan nakirasu naboye maka ne saboda tunanina daga baya zasu fahimceni,
Jiya dady yake ceman tunda Kai nazaba sakaka akoreka daga aikin yakuma anshe komi dayabaka sai nazauna da kudin fashin dakake cidani.... Kuka yaci karfinta tace shiyasa nakecikin tashin Hankali wazan zaba cikin kaidasu Adam gayaman kowane inasonsa rungume juna sukai suna cigaba da tsanan ta kukansu,
Daker yayi shiru yahau lallashinta,
"Nace mata shikenan mubee kikwantar da hankalinki Allah yakaimu gobe kishirya muje kanon ninsan yadda zanyi yayi hakuri suma suyi hakuri,karkidamu taso muje mukwanta."
Awannan ranar tun safe aketuro man text na barazana da rayuwata,
Bama shine karon farkoba tun zuwanmu Garin babu ranar da ba,aman text akan nadawo cikin harkar damuka Fara kokuma sujefani cikin bala,in da bazan taba fitarshiba,
Naboyewa mubee saboda ganin halin datake ciki tana fama da damuwarta vazanso Kara jefata cikin wata ba.
Ranar kafin dare wayata text bazan kilga yawansu bah waidan ma ina gogewa,
Dayashigo saboda kartagani
Koda muka kwanta hankalina baya kwance saboda text din dasuka sake turoman,
Cewar tunda har naki basu hadin Kai to inshirya tarbar mummunan sakamako,Tashi nayi nakama zarya cikin dakin duk nashiga tashin hankali,
gashi jikin mubee yadauki zafi don dama duk kwanakin tana fama da zazzabin dare,
Wajen karfe biyu nayi niyar kwanciya,
Saiga wani text din yasake shigowa ga Abunda text din yace.
_*ADAM KENAN KAYI KUSKUREN AIKATA ABUNDA KAYI,ATUNANINA IDAN NARINGA BINKA DA LALLASHI ZAKA DAWO SAINAGA BAKAJIN LALLASHI DOLE TASAKA NABIYO MAKA TAHANYAR DAZAKA FI GANEWA,DON HAKA IDAN KASHIRYA CETON RAN SIRIKINKA GAMUNAN KOFAR GIDAN SHI ZAMU SHIGA MUKASHESHI,KAZO KACECE SHI AWA UKU MUKA BAKA SAIKAZO*_
Wata mahaukaciyar zufa nakeyi nan take bantsaya sake wani tunani bah,
Nacanja kaya bakake nasaka nadauki bindigata,
Nasaka Mata bullet biyar nadaiyi shirin danakeyi idan zamuje operation,
Kallon ta nayi kamar intadata saikuma tausayinta yakamani gashi jikin yayi zafi sosai sai nakyaleta nasumbaci goshinta,
Hakanan nakejin kamar zanyi bankwana da ita,
Ganin lokaci naja yasaka nafito cikin hanzari nashiga mota,
Maigadi yana magana bansama abunda yake cewaba,
Burina inganni cikin kano don ceton wan babana kuma sirikina Wanda matata takewa wata irin soyayya,
Gudu nake Wanda motar har tsalle take,
Duk nashiga tashin hankali burin baiwuce naganni na isa bah,
Amman duk gudu danake bansamu isa kano bah sai karfe biyar darabi anata sallar asuba,
Bansamu motarsu bah haka nabi katanga nahaura cansaman kwanon su inda mukataba bi muka shiga
Bantsaya KO inaba sai dakinsa,
Saidai bankai gashiga cikin dakinba nazube bakin kofa, saboda abunda nagani yayi masifar bugar Dani,
Kwamce yake cikin jini ga alamar harbin nan ga kirjinsa dakuma cikinsa,
Harbi uku sukai mashi,
Dararrafe nakarasa gabanshi kirjina bugawa kawai yakeyi,
Don lokacin dasauran numfashinsa hannunsa yaketa mikoman,
Bansan sadda wasu zafafan kwallah sukafara zarya ga fuskataba,
Cikin Jan hali yafara man magana cewa"Adam kayafeman duk abun da kaganayiwa babanka bani nasaka kainaba, zuci.... Ce dakuma waccen shaidaniyar.....numfashinsa yafara daukewa yana dawowa,
Yace babanka yana nan cikin koshin lafiya acikin drawer kayana akwai wani akwati nanan duk abunda kukeso yana ciki .....rikeni yayi sosai idonsa yana niyyar kafewa,
Yadaga hannunsa daker yana nunaman kan wata loka.
Sadda zanwaiga insake maido kaina gareshi yariga yacika.....
Wani irin kuka yakucceman jijjigashi nake ina kuka natashin hankali...abunda yake nunaman naje nadauka,
Mukulline dakuma wata wasika dayayi rubutu ajikinta,
Haka matarsa tazo tasamemu dagani harshijikinmu yabaci dajini,
Jinai tafasa wata Kara tana ihu azo acecesu ankashe Mata miji,bakina nasaki ina kallon ikon Allah kankace me gidan yacika makil,
Har yansanda sunzo babu jimawa suka sakaman unka babu abunda take cewa sai shine shine nasamu yaharbeshi harbi uku yayi Mai,
Mugu azzalumi karkukyaleshi kukulleshi wallahi shine ya kasheshi,
Tundaga nan komi yajuye dani haka suka dunga dukana babuji babu gani,
Akan saina amsa laipina nikuma nace kozasu kasheni bazan amsa laipin daban bah...... Kunji asalina dakuma asalin abunda yafaru....
Kotun tadauki hayaniya sosai yayinda mama da Zainab suke cikin tashin hankali,
Tabbas babu makawa asirinsu yatonu zufa kawai sukeyi idonsu yayi luhu luhu saboda rashin gaskiya.
Alkali yace"ganin wannan sharia bazata iya kammaluwa yau ba,dole sai dai gobe don haka iyalan marigayi Alhaji Muhammad yansanda surikesu ga hannu,
Don gudun matsala watau matarsa dakuma yaranta macen da namijin,
Idan Allah yakaimu gobe zamu dasa Still Adam yazama karkashin kulawar yansanda saboda tsaro,
Karfe goma na safe zamucigaba da sauraren wannan karar"
Yabuga gudumarsa *kotu! Kotu!!kotu!!!*
*anan zantsaya aradu nagaji fah*π
TAKUCE MAMAN MUHSEEN.βπ»βπ»
_MAGAJIYAR KAINUWA_ππ»π
[2/7, 10:28 AM] MAGAJIYAR KAINUWAπ: πππ
*AKWAI BAMBANCI*
ππππ
*DAGA ALK'ALAMIN*
*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*
*{MAGAJIYAR KAINUWA}*
*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
33&34.
Su mama sun shiga cikin tashin hankali,ko k'adan basu kawo haka yanzu bah,Amman lokaci guda reshe nashirin juyewa da mujiya,idanu kawai take rabawa kamar ansace ma karya y'ay'a.
Haka y'ansanda suka tusa k'eyarsu har cikin mota jabeer ne suke tafe da Adam zuwa wajen motar da akazo dashi,
Daka kalleshi zakasan yafara samun natsuwa yace"nagode Jabee..."ba na hana ka yi man wannan godiyar bah wallahi duk abunda zanyiwa Kai na da wanina haka yazama wajibi agareni Adam,don haka kabar yiman godiya munriga munzama d'aya."
Har bakin motar yakaishi yabude mashi gidan gaba ya zauna yace,
"To ina zakuje kukwana kenan,don gaskiya ban yarda kubi hanyar zuwa gida yanzu bah."
"Eh dama bazamu tai gida ba, inada isassun kud'in dazan kama mana d'akuna a hote, karkadamu."
D'an sandan dazai wuce dasu yashigo yaja motar sukabar wajen,
Har motar tabace idonsa yana kan jannat datake tsaye nesa dasu kad'an,duk yadda yaso suhada ido abun yagagara.
Saida tasan motar tawuce sannan tasauke wata irin ajiyar zuciya,
Mama tace "lafiyarki kuwa"
"Wallahi mama gajiya nayi sonake kawai nakwanta nahuta jikina ciwo take man"
"Bari jabeer yazo muji yaza,ai"
Daidai isowar Sa kenan yace"mama bazamu iya isa gida yanzu bah kinga duhun mangaruba yasauko, don haka kuzo muje kawai cikin gari mukama hotel kafin safe."
Baban jannat da duk abun duniya ya isheshi akan wannan Al,amarin kunya yakeji bakad'an ba daker ya iya cewa"Jabeer ni bari zan kwana wajen maigadin can, kuje kawai don gaskiya zaka kashe kud'i dayawa."
"Aa baba kata ho muje bana son wani Abu yafaru da d'ayan mu mafi A,Ala mutai wajen dazamu fi samun natsuwa kar kadamu inada