Showing 15001 words to 18000 words out of 39319 words
harkar fashi da makami,
Nayi suna nayi fice bakowa bane face *BALA*
Bala bakowa bane face gawurtaccen d'an fashi da ya iya sata yakuma kware akan harkar kisa,
Shine Wanda yabani wajen zama adakinsa nasauka,
Anan nake komi nawa amman sai insati banga bala bah,
Kullum idan natambayeshi inayake zuwa sai yace man wani aikine,
Haka tafiya tayi nisa ina zaune babu aikinyi,
Duk kudadena nabanki suka kare,
Har takai da bana samun abunda zansaka ga bakina
Sai nawuni da yunwata,
Bala yalura da halin danake ciki sai yaringa barmun kudi
Idan sunkare zaikuma bani wasu,
Saida takai bala babu abunda baya siyaman takalma kayan sakawa masu tsananin tsadar gaske,
Agogo turare karshe rannan saigashi da dalleliyar mota sabuwa vibe maikyau,
Yace tawace awannan ranar nayi murna sosai domin ina bala,in son mota kamar hauka amman sai nace mashi don Allah wane Aikine haka Mai kawo kudi masu yawa haka,
Don Allah kakaini nagaji dazaman vanzar nan kozansamu na kashewa nawa nakaina,
Murmushi yayi yace man indai kanaso maizai Hana kanada zarrar dazakayi irin wannan aikin, amman fah yanada sharadi Wanda idan kaji kowane aikine to yazama wajibi kayi don ba,a fadarsa abanza,
Cikin zakuwa dason inji don nan take naji kwadayin sonyin aikin saboda abunda zansamu.
Jinai yace *fashi da makami*
Wata irin razana nayi har inaja baya,
"AI babu batun jabaya don kariga kaji kuma babu gudu babu Ja dabaya,
Karkayiwa kanka bakincikin wannan gara basar, Adam kanada fasaha ka kware akan harkar computer bazan iya gaya maka iyakar adadin kudaden dazaka mallaka bah awannan lokacin,cikin dare daya zakasha mamakin irin daukakar dazakai,
Bakuma hakanan muke wannan aikinba muna duba masu kudin da suke zaluntar al,ummah ne mufarmasu,muna anshe kudaden azzaluman masu kudi wadanda Kansu kawai suka Sani, Adam nikaina dakagani nan badan inaso nakeyi bah saidan hakan shine yazamar wa rayuwata dole ne,
Tadalilin wani azzalumin Mai kudi narasa iyayena, narasa kanena,
Ina Neman kudin da za,ai wa mahaifina aikin zuciya naje wajenshi don Neman taimako haka ya wulakantani yakoran,
Banyi fushi bah na sake komawa ina komawa yasaka akaiman dukan tsiya,
Gashi ranar ne karshen kwanakin da sukabukaci ai Mata aikin,
Sadda nakoma ina cikin halin taimakon nima amman nasamu tarasu,
Babana saboda mutuwar ta bugai washe gari shima yacega garinku nan,
Bayan sati biyu kuma kanena yadawo daga makaranta wani Mai kudi yabankeshi amman ko waigowa baiba,
Yansanda basuyi komi akaiba saboda yana da babban matsayi,
Karshe kanena akacire Mai kafa ranar da akai aikin shima yarasu,
Wannan shine silar shigata wannan harkar Adam,
Don haka nabaka kwana biyu kayi tunani.
Wannan labarin da Bala yabani yayi masifar tab'ani don yatada man mikin rashin ahalina,
Cikin kwanakin biyu ban tsaya sairaren zuciyar dake Hanani bah kawai na amunce ma bala...........
*KUKASANCE DANI DON JIN CIGABAN WANNAN SARK'AK'K'IYAR*
Takuce maman muhseen.✍🏻✍🏻
_MAGAJIYAR KAINUWA_
[1/30, 2:57 PM] Maman M.: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀
*DAGA ALKALAMIN*
*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*
_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```
25&26.
Washe gari mukatai dashi yakaini wajen ogansu maisuna *barau* nan akaiman register matsayin member,
Cikin kankanen lokaci nazama babban Dan fashi duk gidan dazamuyi fashi ni nake gano mana hanya mafi sauki da zamushiga gidan muyi abunda zamuyi cikin kankanen lokaci mufita,
Dandanan na zama attajirin mai kudi oganmu yabarmun ragamar komi idan zamuje operation ninake fidda yaran da za,atai dasu oganmu yana sona sosai ganin yadda daga zuwana yasaka harkarsu takara bunkasa,
Zuwa wannan lokacin bala yafara kishi dani yana danasanin meyasa yakawoni cikin wannan kungiyar tasu,
Gashinan daga zuwana na anshe mashi matsayi.
Kan tuni nayi suna aharkar fashi kuma kullum banida burin daya wuce nasamu wannan alhajin Yayan babana dashi zanfara,
Nayi kudirin bantaba kisaba aharkar fashi to dashida iyalinsa zanfara
Don lokacin nacire wani Abu washi tausayi acikin raina haka mukacigaba da fashi,
Har watarana bala yasamu wannan mutumen da yayi silar mutuwar kanensa,
Mun tayashi daukar fansar shi don duk wani tattalin arzikinsa saida muka ga bayansa,
Wannan dalilim yasaka muka shirya da bala mukadawo kamar daa can.
Kwatsam wata rana naje nazo tsallaka titi nabanki wani matashi kamata,
Bansan dalilin dayasa naji bana iya tafiya nabarshi gashi naji mashi ciwo akai da kuma kafarsa,
Haka nafito naje nakamashi nakaishi asibiti,
Kullum inazuwa dubashi jininmu yahadu danashi,
Sosai ranar da aka sallamai ranar nake tambayarsa gidansu yace man AI daga hunky yake yazo Neman aiki ne,
Har ma anyi interview yazo tafiya gidan dayake zama hadarin yasameshi.
Nace maizai Hana kazauna gidana saboda lokacin nasamu kudi sosai gidajena basuda iyaka,
Baiman musuba ya amumce zaman damukai da *JABEER* yasan labarina anan yake gayaman ai Wanda nake nema gidanshi yake zaune kafin haduwarmu,
Wannan labarin yayi man dadi sosai to ban nunamai cewar inson zanyi wani Abu akai bah,
Don lokacin nagane Ashe d'an uwana ne nahadu dashi Dan Dan goggo mariya kanwar babana,
Ranar dazai tafi hunkuy zaije gidan yayi sallama dashi,
Sai na ce muje nakaika nayi haka duk Dan nasan gidan,
Amman damukaje nace bazan shigaba kuma don Allah karya sake yafada ma kowa abunda yasani Kai na,
Yayi man alkawarin hakan kuma nayarda don zaman danai dashi Nayarda shidin dan amana ne.
Tunda naga wannan gidan nakuma sake samun information akan Alh Muhammad din nafara tsara yadda Zan farauceshi,
Wata rana yadawo daga wajen aiki,
Nasaka yarana suka tareshi sukai mashi mugun bugu,
Suka kuma bashi wasika Dana rubuta mashi cewar,
_NADADE INA NEMANKA SAIGASHI ALLAH YANUNA MAN KAI,CIKIN RUWAN SANYI KASAKAR MUN BABANA KOKUMA NAYI SILAR AJALINKA.DAGA D'AN HAKIN DAGA RAINA_
sadda sukazo man da labarin naji dadi don sun tabbatar mun da cewar yatsorata sosai kuma yayi masu alkawarin zaiyi abunda akeso,
"Ashe bazaiyi bah din, nasaka yaranmu sukacigaba da bibiyarsa duk wani Abu dayake ciki suka dunga d'auko man rahito,
Ganin hakan bazai man bah mukashirya zuwa gidanshi fashi,
Yaranmu zasu kwashi kudade da gold nikuma Zan farauci Alhajin,
Zuwan damukai nafarko nasameshi nayi mashi barazanar fasamai kanshi,
Akan ina yakai man mahaifina,
KO yafiddoshi kokuma na sakarmai bulet acikin kanshi,
Gaban Matarsa nayi komai.
Yace bayanan gidan akwai wani gidanshi wajen gari can yakaishi,
Yace man gobe bayan isha,i muhadu wajen ganin yanuna man dagaske yake yasaka nace badamuwa sunkwashi kudi kamar hauka
Mukatafi washe gari dagani sai bala da wasu yaranmu subiyu mukatai,
Koda mukaje sai yaturo mana guards dinsa,
Mukafara musayar wuta dasu karshe daker muka tsira da rayuwarmu don har saida sukakashe mana mutun biyun nan damuka tai dasu,
Wannan al,amari yayi matukar tunzirani bansake waiwayar saba sai nabiyo ta hannun wani mutum,
Nasakashi yayi man binciken Halin da Alhaji Muhammad yake ciki dayake yana irin wadannan aikin anabiyan sa,
Nace zanbiyashi konawa take so,
Yafara man binciken don yace man yasamu ganawa da babana amman kuma baikai gayi mashi magana bah yaga kamar za,a kamashi yagudo daker,
Komawa ta biyu da yayi shine nasamu labarin mutuwarsa nayi kuka kamar raina zaifita don nagama hadamai kudinsa kenan don ranar yake gama man aikin,
Kwatsam naga gawarsa a labarai......
Share kwallah yayi amman wasu nasake zubowa kowa yashiga wani irin yanayi don gane dawannan labari da Adam yake badawa,
Jannat kuwa jikinta har wata rawa yaket,
Daker yayi shiru yacigaba da cewa....
"silar wannan mutuwa yasaka nahakura dasaka kowa yin binciken nace zanyi dakaina,
Nagano cewar ashe bama mahaifina kawai yake kamawa bah, mutane dayawa yakama saboda kudi kuma duk Wanda yayi yunkurin tona mashi asiri bazai rayuwaba,
Wannan yasaka nafara kokarin ganin nayi nasara akan shi,
Still mukasake komawa gidanshi wannan karon bamu samai bah saidai kuma nayi gamo da diyarsa awannan ranar,
Hakan yasaka duk abunda yarana suka dauka nace su ajiye nace mata tagaya Mai Dan hakin daka raina yazo Neman shi,
Tun Bayan komawata nakamu da matsanan ciyar soyayyar yarsa *mubeenat* duk wani kwarin guiwar tunkarar Sa saita sireman nafara tunanin hanyar dazan tunkari yarinyar,
Da yan gidansu sai natuna dama basu taba ganin fuskata bah,maizai hana nabiyo masu matsayin Wanda yake neman yarsu insamu muyi aure sannan na bayyana gaban babanta matsayin Wanda yake farautarsa inajin tahaka zamu rabu lafiya harma yazama silar haduwar kawunan junan su.
Da wannan shawarar nayanke hukuncin zuwa gidan da yamma.
Saiga jabeer yazo man da albishir din yasamu aiki anan garin,
Wani company suka daukeshi aiki nayi mashi murna anan yake tambayata aikin me nake ban boyemashi bah nagaya Mai,
Yasha mamakin hakan yayi kokarin ganin yashawo kaina nabar wannan sana,ar zaisamar man aikinyi Mai kyau nace aa bayanzu bah,kuma tsarin kungiyarmu idan kashiga saidai mutuwa ta fitar dakai,
Nagaya Mai halin danake cikin akan diyar wan babana nakuma rokeshi akan karya tonaman asiri har nasamu nawar ware wannan rigimar da ke tsakanin mu dasu. .
Yaban goyon bayan hakan dayaji gudirina,
Nakuma yi mashi alkawarin bayan aurena zanbar wannan Sana,ar hakan yayi mashi dadi sosai.
Shine yarakani har gidan yashiga yasanar cewa mubeenat tayi bako,
Kasancewar Bata yi dawani zaizo wajenta ba tayi ta mamaki,
Har tana tambayar jabeer waye,
Yace mata Wani abokinsa ne yayarta yasaka akaiman iso cikin gidan falon baki aka kaini,
Tare da jabeer suka shigo tana janshi suna dariya inakallon su inajin kaunarta na ratsani tareda ayyana duk rintsi saina mallaketa,
Ta ko ina tayi man shiyasa nakejin sonta yamamaye man zuciya,
Zama tayi tare da ajiyeman juice tazuba taba jabeer yabani,
Gaisawa mukai da ita ban ga wani hali na wulakanci bah munyi musayar no. Waya natafi
Inamamakin saukin kanta bancika zuwa bah Amman muna yawan waya sosai anan naja ra,ayinta tafara sona,
Nikaina nasan tana sona don saida takai mubeenat takori duk wani samarinta alokacin,
Kan kace me munyi nisa cikin kaunar juna,
Bata son duk abunda bana so haka duk abun da nanuna sona dashi zatafini sonsa,
Hakan yasaka nima nakoma haka akanta,
Duk abunda ta ke so inalinka soyayyar fiye da wadda takemai,
Haka zalika idan tanuna tsani Abu Zan tsaneshi fiye da komai Dana tsana,
Jannat yakalla suka hada ido saboda yasan yanuna Mata tsana Kamar Arne da musulmi,
Sadda kanshi yayi don kunyarta ce Takamashi jiyake kamar Ya nitse.
Yacigaba da cewa ganin irin motocin danake hawa yasaka take mamakin wane irin aiki nakeyi,
Don inada motoci sunkusa guda Goma bakuma kanana bah,
Nashiga rudanin sanar da ita don inatsoran tagujeni gashi alokacin jinake bazan iya rabuwa da itaba,
Dole nayanke shawarar gaya Mata gaskiya,
Nace"kibari zuwa weekend inada ishashshen time zanzo muje yawo anan zanbaki labarin komai na rayuwata,
Har akan aikin danake.
Bata nuna komiba ta amunce sai ranar.
*kubiyoni don Cigaba da jin yadda zata kasance*
TAKUCE MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻
_MAGAJIYAR KAINUWA_
[2/3, 11:47 AM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀
*DAGA ALKALAMIN*
*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*
_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```
27&28.
"Ranar weekend watau asabar kenan mukai da ita zamu hadu Amman ba gidansu bah,fita zamuyi da motata zuwa wani resturence duk yadda nashiga damuwar yadda zataji idan nafada Mata,banji Zan iya cigaba da boyewa ba saboda aure nakeson muyi dole watarana zata fuakanci wani Abu har tafara zargina,shiyasa nayanke shawarar sanar da ita komi akaina"
"Ni nazo nadauketa mukatai har muka isa tana man fira nikuwa hankali na atashe yake da abunda zanfada mata,
Bayan mun zauna ankawo Mata lemu da pizza tana ci saida nabari tagama, sannan takallan"Kai bakaci komiba kana ta kallona"
Murmushi nayi Mata"nace aa idan kikaci ma yawadatar dani"
"To inajin ka Allah yasa babu matsala don naga kamar kana jin fargaban sanar dani"
"Agaskiya mubee dole nashiga fargaba saboda abunda zanfada bashida dadin saurare,amman kifahimceni kiyiwa magana ta kyakkyawar fahimata"
"Inajinka kafadi komiye Adam ni bazan taba gudunkaba koduniya tajuya maka baya kasaka aranka mubeenat tana tare dakai,"
"Wannan kalaman yakara sakaman kwarin guiwa akan sanar da ita din,
Haka nazagyara zamana nafayyace Mata kowaye Adam mudassir amman bangaya Mata akwai case tsakanina da baban taba.
kuka take asadda tagama saurarena Amman abun mamaki alokacin mikewa tayi tadauki jikkarta tatafi tabarni nan,
Nashiga tashin hankali mai girma alokacin saboda mubee ta kulleni duk hanyar dazan sameta nakasa saboda kogida nazo haka zangaji dajira intai,
Bata fitowa wayarta idan zanyi kira dubu bata dauka haka text shima konayi bata reply dina,
Saida mukai sati biyu awanan halin.
Sannan wata ranar juma,a tace man tana son ganina nashiga farinciki marar misaltuwa haka tacigayu natafi,
Aranar take sanar dani cewar inhar inasonta inason kasancewa da ita to yazama dole nabar harkar fashi da makami sannan inrabu da duk wani Abu dana mallaka tasilar fashi, inhar na amunce to ashirye take da aurena KO gobe nace"
"Wannan magana itace tazama ga samu ga rashi, saboda barin harkar fashi awajena alokacin bakaramin tashin hankali bane,saboda nayiwa kungiyarmu alkawarin bazan taba fitaba saidai mutuwa,
Sannan natara dukiya maisunan dukiya wadda nikaina bansan iyakar adadin taba,
KO gidaje nawa nakaina inada guda goma duk nabada su haya, ashekara ina amsar kudin haya sun Kai kimanin miliyan ashririn."
"Motocina kana na danake hawa sunkai shabiyu,
Manya kuma da nabada Ana Lodi zuwa legas,sunkai guda biyar kuma duk wata Ana kawoman miliyan guda da dubu dari biyar, sannan duk bayan sati biyu muke fita operation, kuma kalilan kudin damuke samu idan munfita shine miliyan biyu araba aba mu dubu dari bakwai da nida bala muraba yaran kuma abasu dubu Dari uku suraba dayaje subiyu ne,
Miliyan guda kuma ta oga barau ce,
Tunanin wannan dukiyar yasakani tsawon minty biyar bance Mata komiba,
Taya Zan iya rabuwa da duk abunda namallaka idan narabu dasu ta ina zansamu kudin aurenta,inacikin wannan tunanin takatseni dacewar"idan kayarda zaka fita harkar fashi kuma zaka rabu dakomai daka mallaka afashi Zan aureka sannan zansaka babana yasamar maka aikinyi mai kyau"
Ta mike tana daukar jikkarta
"Zantafi duk sanda kayanke shawara kana iya nemana Amman inhar kasan cewar bazaka iya abunda naceba to kadauka aranka bakataba haduwa da wata maikama dani bah"
Tana gama fadan haka tajuya tayi tafiyarta tabarni zaune zuciyata cike da tunanin yazanyi.
"Tunda natafi nake cikin tsananin tunani, narasa wazan tunkara da wannan batun,
Barina cikin wannan kungiyar babban tashin hankaline awajena saboda ogamu yana bala,in sona saboda tadalilina yasaka yanzu basuda wata matsala idan za,fita aiki kuma nakawo masu cigaba fiye da sadda babu ni, kuma nasan hukuncin Wanda yafita daga wannan kungiyar shine kisa,
Duk inda kashiga zasu dunga bibiyarka saisunga bayanka to inaga ni nafita Wanda yanzu nine fitilar dake haske masu gabansu da kuma bayansu."
Shiru yayi kotun tadauki hayaniya akan wannan labari na Adam dayake bayarwa,
Daga masu kuka sai masu tausaya mashi kowa dai da abunda yake fad'a akan wannan labarin mai matukar tsayawa gazuciya,
Jannat takallai shima ita yake kallo,
Cikin sanyi murya da yin kasa da ita yadda shikadai zaiji tace"kaga rayuwa fah, Amman karka damu insha Allah yau basai gobe ba kotu zata wanke ka, kacigaba har zuwa inda asalin abun yafaru"
Alkali yatsawatar sosai sannan sukai shiru,
Alkalin yace"cigaba lokacin sallar ya kusa"
Cikin sanyi murya yacigaba dacewa,
"Nashiga damuwa wadda nadade banshugeta bah saboda duk abunda tafada bazan iya rabuwa da kodaya bah,inson kudina kuma inason aikina sannan itama ina sonta,
Ana cikin haka jabeer yakawo man jiyara,
Anan nakegaya mai halin da akeciki yaceman tunda har tace man zatasaka babanta yasamar man aikin inyi hakuri narabu da duk wadannan dukiyar,don nikaina zanfi kwanciyar hankali kuma tafiddo ka daga cikin masifa saboda na halak dinka kakeci ba,shawara daya kawai kayi abunda tace don shine rufin asirinka,komi kadaukeshi kakaishi gidan marayu kakuma yi istigfari akan aikin dakai,
Saukinka ma bakataba kashe waniba saukin kakenan, ni iyakar abunda zance maka kenan"
"Bayan tafiyarsa nashiga tunani maikarfi Wanda har yaja ranar damukaje wani aiki kadan yahana akafce mu, kuma duk laipina ne fada sosai oganmu yakeyi Wanda baitaba yiman irinsaba Wanda har raina nima yafara baci akan me zandunga surfaman fada haka daga kuskure,
wanda tunda nazo hakan bata taba faruwa bah sai yanzu.
"Nazicciya dagari yawaye duk mun hallara gabanshi zaibamu kasonmu bayan yaba kowa ina zaune babaniba,
Sai cewa yayi Kai saboda laipin dakai Zan baka punishment kudin yau bakada kaso"
Raina yayi mummunan baci nace" akan haka zaka rikeman hakkina, to karike indai kudine banason nikuma bari kaji nawa hukuncin akan abunda kayi man gaban wadan nan shashashun,
*NI ADAM MUDASSIR DAGA RANA IRIN TAYAU NABAR HARKAR FASHI, NABARTA HAR ABADAN BAZAN KUMA DAWOWA CIKIN TABA KAMAR YADDA BAZAN KOMA CIKIN MAMA NA BA HAKA NABARTA KUMA BABU WANDA YA ISA YAMAI DANI CIKI*
nabarku lafiya na mike nabar gidan,
Zuciyata tafasa kawai takeyi akan abunda oga barau yayi man,
Nakumayi alkawarin nabar wannan aikin har abada koda zanyi yawo tsirara,"
Gidana naje nadauki ATM card Dina natafi banki, duk wasu kudi dake cikin account dina ranar saida naciresu bantsaya KO inaba sai gidan marayu,
Nabadasu dacewar aikoni akai kuma ance karna fadi suna.
"sannan nayi waya da masu man haya suma nace inason ganinsu gobe suduka,
Washegari saigasu bantsaya dogon turanciba nace Kai kallamu Kaine mai iyali dakuma yara gashi idan kabar wannan aikin bansan inazakaba don haka kadauki motar dake wajenka halak malak nabaka kacigaba da ciyar da iyalinka,
Har kuka yayi man akan wannan kyauta saida nadakatar dashi sannan,
Sauran kuma nace subani makullin motocin,
Nace suje Zan nemesu.
Nasaka motocin akasuwa bakaramin kudi sukaiba don nikaina mamakin hakan nayi,
Duk yadda zuciya taso sakaman soyayyar kudin haka nakauce natai narabar ma mabukata haka naitayi duk wasu kadarorina saida nasayar kaf narabar da masu bukata,
Gida guda nabari Wanda zankoma saboda tsaro don nasan tabbas bazasu kyaleni ba,don dama tundaga ranar yake kirana yake turoman text naban hakuri akan nadawo cikinsu,
Vanma bitakan wayar ba balle har nasaurari kalaman dayake fadaman,
Gidan danake ciki ma nasiyar narike kudin don tsaron laluri,
Gidan danakoma babu Wanda yasanni dashi,
Shiyasa basu zo wajenba sannan nacanza layi number mubee kawai nadauka nakarya su duk ukun danataba anfani dasu,
Alokacin sai akejina sayau kamar nasauke wani gungumen dutsi daga saman Kai na,
Lallai cin haram ba karamin tashin hankali bane,
Sai lokacin na tabbatar *AKWAI BAMBANCI* kudin halak dakuma kudin haram,
Duk yadda kake murna dasamunsu don kashe kishirwar gabanka bazaka taba natsuwa bah,
Saida nayi sati sannan nakira mubee akan cewar nacika umurninta,
Ashirye nake da aurenta wannan labarin bakaramin dadi yayi Mata bah,
Ana take gayaman irin kewata datayi kuma dama tanaji garanta zanyi abunda tace don ta San bazan iyajure rashinta bah,
Bayan sati biyu tace man inzo gida mahaifinta nason ganina........
Alkali yace"andakatar da wannan karar har sai anyi sallar la,arsar za,Acigaba.....
*kotu! kotu!! motu!!!*
*nima Zan dakata anan don yin nawa uzirin sai munhade ga next page*
TAKUCE HAR KULLUM
MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻
Love u all my fans
Amrita, Ruky, khadija lawal Aminatu Sambo,hadiza musa, Shema,u Salis,Ruky m gee,
Zubaidat Mrs Salis,ammin sultan, maman ameer,
Sophash,maman Aminu,Anty ushe, deejah,Fatima Salis,Mrs barrister, Zainab,Hafsat sgr,Aisha musa,
_DON GIRMAN ALLAH DUK WADDA BATAJI SUNAN TABA KARTADAUKA DON BATAYI NE AA BABU LOKACIN ZANOKU DUKAN KU, AMMAN KOWACE INA ALFAHARI DA ITA KUMA INA SONTA KAMAR YADDA KUKE SONA_
_MAGAJIYAR KAINUWA_👌🏻😉
[2/4, 6:17 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀
*DAGA ALKALAMIN*
*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*
_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our