Showing 30001 words to 33000 words out of 39319 words

Chapter 11 - AKWAI BAMBANCI Book Complete BY (MRS BB).txt

Mrs BB   

15 Dec 2024

2635

FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


44&45.


"Yaya Adam ina wuni."


Nafee ce ke chart dashi awaya.


"Lafiya lau Amaryar jabeeru,yafad'a tare da turo d'an hoton dariya"


Itama tatura mashi Mai kalar jaa tace"wallahi yaya Adam bafa sunan Sa kenan bah,sunan sa jabeer."


Dariya yaturo Mata sannan ya tanbayi y'an gidan dakuma su baba.
Tace"kowa yana lafiya wallahi, daman yaya jannat yace katuro mana hoton babyn mugani."


Lumshe idonsa yayi yana kallon sunan jannat d'in data rubuto mashi,jiyake kamar ita ce yake kallo zuwacan yayi ajiyar zuciya.
Kallon Mubee yayi tana bata nono yace,


"Maman baby juyo man da ita zantura ma Nafee hotonta tana tambaya na."


Murmushi tayi tace"sun k'agu kenan."


Ta ajiye ta yad'auka,takuma yi kyau sosai don har anrasa wa tad'auko cikin iyayen.
Wani ihun murna Nafee tabuga sadda hoton yazo Mata,
Dagudu ta isa wajen jannat dake can d'akinsu kwance tashiga aguje tana cewa"yaya!yaya! Tashi kiga hoton babyn wallahi bakiganta bah tahad'u masha Allah."


Ansar wayar tayi tazuba wa yarinyar ido,
Nan take taga hancin Adam zankad'ed'e murmushi tayi tace"masha Allah wallahi tayi kyau Allah yaraya ta yasa cikon addinin musulunci ce."
Tace"Amen yaya bari naji yaushe zasu taho don wallahi na k'agu nagansu."


Fita tayi tabar jannat tayi tagumi,
Kwallah suka zubo mata ta share su, tajingina bayanta ga gadon datake ta d'aga hannu tace"Ya Allah narok'eka kacire man wannan A bun danake Ji,Allah kasa kaman kaunar mijin da Zan Aura, kasaka man juriya akan Abunda nakeji Allah ka Amshi rok'ona tarufe fuskarta tana shashshekar kuka.


Kamar yadda Adam yatsara hakan kuwa akai,
Wajen k'arfe goma na safiya saiga Jabeer yasauka Sai lokacin Mubee takejin kamar karta tatafi saboda yadda takejin tun yanzu kewar mijin nata takama tah.


Maijidda tara kota tana cewa" gaskiya zamuyi kewar Ku inama yallabai yace Atafi dani wallahi da naji dad'i."


"Wallahi Maijidda nima zanso haka Amman lokaci yariga yak'ure, sai kuma mungama wanka zamudawo ga wannan kin k'ara wajen hidimar gidanku, kigaida mana dasu goggo iyami ko ma y'ar batazo taganta bah."


"Babu komi inkun dawo zatazo,"
Haka suka rabu suna kewar juna sai takejin kamar sun rabu kenan,itadai wallahi batason tafiyar Amman yata iya dole tatafi hakan shine gatan tah.


Da suka isa filin jirgi kuka take sosai ajikin Adam kamar yace sun rabu kenan,
Jabeer sai yaji sunbashi tausayi har yaji yakasa jurewa yacewa Adam d'in,
"Wai Kai bazaka bari kutai tare bah, tunda hankalinta bai kwanta da tafiyar bah kabari sai kasamu lokaci sai kuzo tare mana."
Kallonsa yayi yana murmushi yace"wallahi Jabeer babu lokaci nan da wata uku ma banda time d'in dazan yi wata doguwar tafiya har naje nayi kwana da kwanaki,gara taje ita acan ayi sunan tayi jegonta can zanfi natsuwa itama haka, akan dai dagani sai ita bamuda wani najiki balle yanuna Mata yadda ake komi, koba haka bah."


Jinjina Kai yayi yace"tabbas maganarka haka take, kiyi hakuri kidaina kukan haka nan,kakwantar Mata da hankali don Allah mana."


Jawota yayi yasunbaci goshinta yace"Am so sorry my angle,insha Allah da nasamu nagama ayyukan dake gabana saidai kawai kiganni nayi maki surprise, kikulaman da baby kinjiko kuzab'a Mata nickname Mai dad'i" haka dai yayi ta lallashi har tayi shiru,baibar airport d'in bah saida yaga tashinsu sai lokacin yaji guyawunsa sunyi sanyi yaji wata mahaukaciyar kewarsu,koda yaje gidan saiyaji yayi mashi yawa, gashi daman yasallami ma,aikatan Mata saura mazan saigidan yayi mashi wani gingirim.


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


Sunsamu tarba ta musanman jannat ta ware kamar komi baifaru bah,
Taja takwarar ta ajikinta koda yaushe tana tare da ita suna wasansu sun bata suna *NIHAL* Mubee koda yaushe suna mak'ale da juna awaya itada Adam,gefe guda kuma mama tazage tana gyare d'iyar tata babu wasa,
Don kusan tare ake masu komi da amaren.


Anyi suna lafiya yarinya tayi goshi don sunsamu kayan baby Masha Allah,
Uwar ma babu laipi tasamu A bun arziki Bayan suna da kwana biyu baban Adam yatusa Mubee har gidan yari taikaiwa mamanta d'iyar tagani,
Kuka suka kamayi kamar ransu zaifita bakamar da mamar take gaya Mata cewar Zainab tagudu tun ranar da aka kawosu,
Sama kuwa anyi nasarar kamashi Wanda yaci dukan tsiya, tasilar haka sukaji mashi rauni yanzu haka yana gidan mahaukata,don kwalwarsa tatab'u Mubee tasha kuka kamar kamar me dak'er aka rabasu Ana jan mamar baba najan Muben haka suka rabu,sosai yatausaya masu halin dasuka samu Kansu.


Biki yataho duk yadda Mubee taso Adam tazo cewa yayi babu lokaci,
Koda baba yakirashi shima haka yagaya mashi don lokaci fah bashida shi,saidai daya nemi excuse babu makawa zai samu niyyar zuwan ne baiba.


Dole jannat tasiyo rigar hakuri tayafa ma kanta,
Don taga dagaske dai wannan Aure babu fashi yinsa za,ai
Cikin abokanta babu Wanda yazo sai mufeeda ta kano,
Hakan yarage Mata damuwar ta saboda koda yaushe suna tare, sai ta rage shiga damuwa balle har tayi kuka.


Cikin satin aka gama komai nagidan Baba dake can abuja,saidai kawai sukaji yace kowa yashirya kayanshi kawai zaid'auka zasu tare sabon gida.
Kowa yayi mamaki da al,ajabin wannan lamarin koshi Baba Alhajin yasha mamaki,
Haka kowa yashiga kintsa kayanshi mama tace mashi"to babansu yazamuyi da kayan mu na nan."
"Mamansu kud'auki Abunda kukasan kunaso sauran kubarsu akwai mutanen dazansa saka."
Haka kowa yakammala d'aukar duk wani Abu nashi Mai muhimmanci,suma mamar jabeer da kakarsa duk hadasu wannan Abu yayi wa kowa dad'i.


Sadda suka koma sabon gida Baba Alhaji har kuka yaringayi akan irin abunda yafaru baya.
Gidafa yatsaru babban gida mai d'akuna kala Kala sai Wanda kakeso, Mubee ta labarta ma Adam duk don yazo.
Yace"Abu yayi dad'i kinturo man hotunan gidan ta what's App."


"Haba Abban Nihal Yanzu duk yadda zanyi kazo bazaka zobah, don Allah kazo naganka kasan kuwa irin kewar danake ciki kuwa."
"Kiyi hakuri mommy baby insha Allahu da angama hidimar biki zanzo, hakan yamaki ko"
Cikin farinciki tace"Kai Amman naji dad'i wallahi kace nafara shiri tun yanzu."
Dariya yayi Mata ganin irin d'okin datake,duk da shima yana cike da kewarsu.
"Sosai ma kuwa kifara shiri, don zanso nazo nasha sabon Amarcin koya kikace Amaryata" yafad'a cikin sigar tsokana.
Kunya ce taka mata kamar yana gabanta jiyai takashe wayar,dariya yayi yace"dama nasan za,arina indai Mubee ce komi saitace kunya yake bata, shikuwa hakan yana kwarar sa wallahi.


*BIKI WAN SHAGALI*


Gida yacika da y'an uwa anata hidima, don kowa bai tunanin bikin zaitara jama,a haka bah don har wanda basuyi tunani bah sunzo.
Hakan kuwa bai rasa nasaba da sabon wuri dasuka yi, kowa yace bari yazo yagani Wanda bai niyya ba ma yazo don ganin kwam.
Amare ta ko ina gyara sukesha idan kagansu sai kayi mamaki, don inkaga jannat bazaka ce itace bah takoma wata jajawur, dama kuma baba ya ba wajen haske ta cire duk wata damuwa aranta, ta rungumi Usman d'inta matsayin mijinta tare da fatan suyi zaman Aure na mutunci da yarda da juna.


*RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA*


cewar wata tsohuwa tana gud'a tana nanatawa.


TAKUCE MAMAN MUHSEE.✍🏻✍🏻


Kuma
Magajiyar kainuwa😉👌🏻
[2/25, 6:25 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: 🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


*46*


Amare sunsha wanka iya wanka,
Gida kuwa yacika da mutane na nesa dana kusa duk sungarzayo,anata shagali ga Abinci nan saiwanda kazab'a kaci Alkubus ne,waina ce,tuwo ne,sinasir ne,dambune,gasunan saika darje hidima kawai akeyi Ango jabeer yasha wankan shadda irin ta amaryar tashi sky blue, babu karya sunyi kyau dayake ba,akai ga d'aura Auren bah maihoto yazo anata kashe d'auri.


Mubee da y'ar d'iyarta Nihal sunsha wanka itama d'in shadda ce Amman maroom Nihal kuma doguwar rigace kalar maroon, tayi wani irin fasifar kyau kamar kasaceta,
Jann ta d'auketa suna can d'akunan baya zamansu da y'an Abokan ta dasukazo.
K'arfe biyu aka d'aura auren Wanda Jannat sanarwar tana shiga kunnenta batasan ta fashe da kuka bah,Wanda ta rasa na meye itadai har ga Allah bata cike da farin cikin wannan Auren.
Mufeeda ce keta lallashinta kankace me har jikinta yad'auki wata masifaffar masassara,cikin lokaci k'an k'ane jikinta yarikice Amai kawai take shek'awa Wanda daman tun safe bata sake saka komi cikin bah,
Duk hankalin y'an gidan yatashi ganin lokaci guda abun na neman rikicewa.
Dole akadanga na da ita asibiti, don jikin yasaki saboda uban aman datake kakari Wanda yaki zuwa,tunda bakomi cikin cikin nata.


Ba wanda bai rud'eba ganin yadda Jaan takoma, dama kuma ga damuwa da tasaka cikin ranta tana cinta kad'an_kad'an hada ita yak'ara saka ciwon ta azzara.
Koda sukaje numfashinta baya fita sosai saida likita yasaka Mata oxygen, hakan ya sake tada hankalin mutanen gidansu,dubata akashiga yi don bata taimakon gaggawa.
Sun d'auki tsawon lokaci babu likitan daya fito, mama da Mubee kuka suke da Nafee, saboda ganin Abun yana neman wuce duk yadda suke tuninsu.....saboda tashin hankalin da suke ciki Nihal kuka take Amman Mubee ba ta ita takeba,kuka take kasa rik'a.....saida Baba Alhaji yazo yad'auketa yashiga lallashinta tare da sab'ata ga kafad'arsa saigashi dan danan tayi bacci.


Kusan awa guda suka d'auka sannan suka fito,
Babban likitan yace baba da Baba alhaji su biyoshi office zai magana dasu....... Bishi sukai kowa zuciyarsa na bugawa don basu san kuma Abunda yafaru bah.....


Waje yanuna masu suka zauna,
Sannan ya natsuwa yana kallon Baba yace"Alhaji yarinyarku tana cikin matsanan ciyar damuwa, wadda ta haddasa mata ciwon zuciya,da kuma neman d'aukewar numfashi saboda aduk sadda zuciyarta tashiga irin wannan matsanancin damuwar komai zai iya faruwa,Amman Yanzu alhamdulillah tasamu bakamar yadda Kuka kawota bah,Abu Mai muhimmanci ne Ku kula da halin datake ciki, saboda yanzu ciwon baiyi wost ba, to don kiyaye gaba sai kukula da halin datake ciki,
Mun Mata duk Abunda ya dace tasamu bacci, zamu rik'eta nan na tsayin kwana uku don ganin yanayin jikin nata ga magungunan da za,a nemo suzata sha natsayin sati biyu insha Allah indai tacire damuwa, zata iya rabuwa da ciwon tunda baiyi yawaba."
Jabeer ne ya anshi takardar yafita yanajin babu dad'i har nawa jannat d'in take da har zata kamu da ciwon zuciya,
Wace irin damuwa ce take ciki har zata jamata wannan ciwon, dole akwai yadda akai, zaiyi k'ok'arin ganin yasan damuwar ta don samun farincikin ta.......


Su mama suna ganinsa suka mike cikin son jin meke damun jannat d'in,
Baisan yazai ce masuba yace"su Baba na fitowa zasuyi maku bayani, zanje nasiyo magani yanzu."
Yawuce yana tunanin yadda auren yazo duk yadda ake tunanin samun farinciki awannan sai A bun yazo yana son fin k'arfinsu.


Koda suka fito Baban Adam ne ya iya masu takaitaccen bayani,
Ai Mubee da Nafee rushewa sukai da kuka har suna d'urk'ushewa k'asa.....Mubee batasan tana son jannat d'in bah saida tashiga wannan halin kwantar masu da hankali,cewar Abun ai baiyi yawaba.


Haka duk suka d'ura cikin d'akin da aka kwantar da ita, tana baccin wuya sai yanzu duk suka ga uwar ramar datayi, kamar tayi shekara tana ciwo.
Baba yace kar Wanda yayi gigin tashinta anason tasamu natsuwar zuciya ne.


Mamar jabeer akabari tare da ita,
Koda suka koma gida yawancin wasu y'an biki duk suntafi, wasu kuma sai gobe saboda ganin halin da gidan yake ciki, amarya guda babu lafiya.


Wata mata cikin dangin mama tace"badole yarinya tashiga tashin hankali bah,duk fitinar bata tashi zowaba sai ranar Auren, saidai kawai taji labarin da zai gigitata."


(Tofah🤔 mekuma yafaru,nasan y'an *ZAUREN MRS BB* ma zasu sojin meyafaru to bari dai muje zuwa wannan amsar tana bakin Baba Alhaji KO baban Adam.)


Jabeer ne yaketa k'ok'arin canza kayansa yaje yawatsa ruwa saboda gajiya,
Can yajiyo ihun wayarsa murmushi yayi yasan Nafee ce zata matsamai kan cin Abinci,sai kuma yaga ba haka ba....sunan ADAM gayani.... Yafasa cire rigar yad'auki wayar yana zama saman kujera.


yace"Ango kasha K'amshi, fatan and'aura lafiya."
ajiyar zuciya yaja yagurzar da iska, sannan yace"Lafiya Amman ba Lauba, yasanar dashi halin da jaan take ciki."


Cikin tsananin tashin hankali yace"what! Jabeer kuma shine zaka ceman kana gida, plzzz ta shi kakoma ka kula da ita,kokuma kacewa mama karsubarta da wasu nurses bazasu iya kulawa da ita yadda yakamata bah..."


Mamaki da dariya suka so kamashi yace"mekake nufi, nizanje nazauna da ita kamar wani mijinta,wai koka manta and'aura Aurenta ne ayau? To banine da alhakin kulawa da lafiyar ta ba,mijinta yazo kuma mama na itama tana tare da ita acan."
Kanshi yaji yasara da wani irin k'arfi,bugun zuciyarsa ya k'aru yakasa cewa komi, saidai yakashe wayar ya jefar da ita har screen d'in yana fashewa...... Jabeer yayi murmushi yace"nizaka wani ce ma haka, saikace kafimu sonta to dai anriga anraba gardama.....


Haka aka agama wannan biki babu dad'i kasancewar duk basu zaune,duk rana acan asibitin suke wuni, Mubee ce kekulawa da ita tabarma mama Nihal tunda tasamu kanta da farkawa,komi yake dawo Mata sabo, Amman kasancewar likitan yaja hankalinta kan shiga damuwa saita daure tana janye damuwar.
Amman Abun mamaki kwanan ta biyu yau KO inuwar Usman da y'an gidansu batagani bah,sosai Al,amarin yad'aure Mata kai har takasa jurewa ta cewa Nafee idan taje gida tataho Mata da wayarta.


Koda ta kawo Mata no. D'in usman d'in tashiga kira lokacin Mubee tashiga toilet daga sai Baby Niha dake hannunta.....akaro na shidda kenan tana kira daga ai rejecting sai ta tsinke ba ad'auka....hakan yasaka mamaki yabayyana k'arara afuskar ta,bata fasa kiranba Amman kuma haryanzu anki d'agawa.....
Mamace da baban Adam suka shigo daidai sadda take ajiye wayar idonta cike da kwallah.... Takalli mamar tace,
"Mama menayiwa Usman kuma?yanzu nake kiranshi yafi sau shurin masuki baya d'auka,wani kiran ma yanke shi yake,kuma mama banji Wanda yace man yazo dubani bah,kigaya man idan nayi mashi laifi yasaka yayi haka". ...hawaye suna zirarowa daga idonta.


Idasa shigowa tayi baban yana tsaye bakin k'ofa,
Zama mamar tayi gefenta Mubee tafito tana gaidasu tace"kekuma kukan namiye, wai miye matsalarki ne jannat kirufama kanki kikuma rufamana asiri, kinkuma ji abunda likita yace dake ko."


"Mubee bai cancanci nashiga wani yanayi bah kenan?kwana na uku yau babu labarin Usman, idan kuma yazo kigayaman kiranshi nake yanzu Amman kwata kwata baya d'agawa.....wai ko wani Abu yafaru bansani bah ta tsayar da kallon ta ga mamar.....


Hannunta tarik'o tace"ki natsu kikwantar da hankalin ki, kinsandai halin dakike ciki baya buk'atar wani kuka KO damuwa,idan kuma kinfison kiyita zama anan to musai mu koma gida kekiyita zaman, tunda haka kikeso ko."
Ta share kwallah tana Jan majina,
"Ni bahaka nakeso bah mama, Amman ai kunsanar dani Abunda kefaruwa ko.."
"Awannan halin zamu gaya maki, kenan muncika marasa hankali kina kwance ciwon zuciya yakwantar dake, sannan mud'auko Abun daya faru baya muhau gaya maki, zuciyar taki taji dad'in bugawa ko."
Babanne take sanar da ita haka,
Sunkuyar da Kai tayi tana sauraren shi yacigaba da cewa,
"Inhar kina son jin Abunda yafaru to ki natsu kisamu sauki har asallameki,koma miye saikiji kinajina Ai ko?.
Ta d'aga Kai kamar k'adangaruwa.
"Magana zakiyi man bawai d'aga kaiba."
Tace,
"To Baba zankiyaye insha Allahu."
"To Allah yayarda."
Mama ta kalli Mubee dake zaune tace"kitashi kibi babanku kije ki shiryawa tar bar mijinki yana hanyar tahowa gida."


Cikin d'okin da batasan tayi bah tace"laaaaa mama dagaske.....saida tayi kuma sai kunya ta Kama ta murmushi baban yayi yajuya yafita,
Tashi tayi tana b'ob'b'oye fuska tasab'i Baby ga kafad'a suka fice dariya tayi Mata kawai... Ta tsayar da idota kan jannat d'in datayi shiru ta rufe idonta.... Tunda taji cewar Adam zaizo kirjinta yacigaba da wani irin bugawa........




Kuyi maleji dashi masoya.


TAKUCE MAMAN MUHSEEN..✍🏻✍🏻


Kuma
Magajiyar kainuwa😉👌🏻[2/27, 4:47 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😍: 🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀


*DAGA ALK'ALAMIN*



*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*


*{MAGAJIYAR KAINUWA}*






*_MARUBUCIYAR LITTAFIN_*
*_RAI DA BURI_*
_*SAFAH DA MARWAH*_
_*SAINA DAUKI FANSA*_
_*RAYUWAR AMEERAH*_
_*AND NOW*_
*_AKWAI BAMBANCI_*




*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


47.


Mubee duk da irin Abincin da y'an aiki sukai wajen Kala uku,Amman bata bi takansu bah, tashiga shirya mashi had'ad'd'ar fride rice tare da fefe chiking,sai lemun ayaba da kankana da strawberry.
Idan kaga yadda tashirya mashi dinner, saika had'iye miyau don nan take zakaji kana buk'atar kaci,Nafee tataya ta suka kammala,Har aka y'an ma Jabeer yaci yana zolayar Mubeena cewa,
"Yanzu duk wannan shagalin na shine, lallai Adam yabar dad'i,yanzu muka gama waya dashi wai har yazo Airport akai mashi kiran gaggawa,yace yakira layinki baisamu bah shiyasa yasanar Dani, wallahi duk sai naji kinbani tausayi."ya fad'a ya na nuna yadda yakejin babu dad'i......ai basusha mamaki bah saida sukaga Hawaye share share ga fuskarta.....Nihal na kuka Amman bangaje ta tayi tana niyar shigewa d'aki.....dariya taciyo Nafee tarik'e ciki tadunga yi babu sassaucii....shima taya ta yake ganin yadda suke son caza mata Kai,dakuma irin wannan dariyar yasa tagane zolaya ce.
Ajiyar zuciya tayi tace"Amman dai Ya Jabeer kad'auki Alhakina wallahi,wai kaji kuwa yadda naji.... Uhm zanrama, wallahi kuwa ni Wanda zanmaku sai yasaka Ku zauci, badai kuna tak'amar zakuyi Amarci bah,to muje zuwa muntsaya one zero."


Dariya sukai Mata ta wuce ta d'auki baby Niha sukai ciki, tabarsu suna soyewa don Jabeer badaga nan bah indai wajen kauna nane don ita kanta Nafee ta shaida hakan,yaba soyayya muhimmanci fiyeda komi shiyasa takeji dashi kamar wani k'wai.


K'arfe takwas aka sallamo Jann daga Asibiti,
Daidai lokacin da yasauka daga jirgi shima,Jabeer yakira yazo yad'aukoshi suka nufo gida,
Yana bashi labarin dramer su da Mubee d'azu, murmushi yayi kawai don shikad'ai yasan yayakeji,soyake yabud'e idonsa yaganshi gabanta,soyake yaji meya jamata ciwon zuciya irin Wanda yake fama dashi,idankuwa har zarginsa gaskiyane jaan tana sonsa to fah KO ankaita gidan usman saiya d'aukota anwar ware wannan Auren Anmaida shi akan shi.
(Ni kau nace bala,i Mai tafiya da cover kturuuu😂w👷allahi Adam d'an bala,i ne kuturuuu😂😂)


Jabeer yagaji da shirun da yake mashi yace,
"Wai man meka d'aukan yazan d'aukoka inamaka hira kamai dani wani dawoo, Aah banason haka fah."


Kwantar da bayansa yayi jikin makarin kujerar yace,
"Sorry hankalina ya lula wata duniyar,mekake fad'a?"


Haushi Yakama Jabeer yace,
"Bansani bah, d'an renin hamutta kawai."
Dariyar da bai shirya ma waba yakwashe da ita, jin Abunda jabeer d'in yace....daga haka kuma suka dayaye suna cigaba da hirar su har sukazo gida...........




Tunda suka dawo tana d'akin mama kwance,
Dama suna dawowa wanka tayi tashiga yin sallar magaruba da isha,i sai shafa,i da wutri.
Nafee takawo Mata coffee don tace shikad'ai ya isheta, sai Baban Adam yasaka maigadi yaje yasiyo Mata gasassar kaza,daidai cin marar lafiya tunda tad'anci saita kwanta duk da bawani bacci takeji ba......


Duk suna falon Baban Adam,Mubee anci wani ubansu gayu itada baby saikace garin zasu bari,mama da mamar jabeer dariya suke mamar jabeer tace"yaran zamani kenan, mu lokacin mu kinxo wanka wama yabaki wannan damar."


Mama tace,
"KO anbaki damar ma bazaki iyaba, saboda kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login