Showing 36001 words to 39000 words out of 39319 words
k'ok'ari kike mijinku yayi maki abunda bai mata ba,ko kuma tayi Duk abunda zatayi don ganin takawar da hankalin mijin akan d'ayar matar.
Wannan ba daidai bane, akodayaushe murink'a anfani da wannan *Hadith d'in wanda Akace layu,uminu ahadikum hatta yuhubbul akhihi ma yuhubbul nafsihi* imanin d'ayan mu baya ciki har sai mun soma d'an uwanka abunda Kake soma Kanka,don haka mata muji tsoron Allah muyi abunda zai zama alkhairi gare mu,ba mu nemar ma kanmu Sheri ba.)
Adam yayi wa Allah godiya da ya bashi mata masu hankali,wanda burunsu suyi Abun da d'ayansu bazai Cutuba,
A haka lokacin ta fiyarsu yazo, iyayen suka zaunar dasu suka sake masu nasiha mai shiga jiki,wadda Mubenat da jannat suka kama kuka, daker Su mama suka lallashesu.......wajen rakiya hada amaryar Nafee da angonta,idan ka gansu zaka sha mamaki, sun wani yi fresh dasu Sunyi b'ulb'ul, Adam sai tsokanar jabeer yake, ana dariya y'an gida basu bar filin jirgin ba saidai sukaga tashinsu.
Sai Nace amaryar Jaan da uwargida Mubee, sauka lafiya.
kuyi hkr da wannan Insha Allah zuwa gobe zanmaku paging k'arshe.
TAKUCE MAMAN MUHSEENβπ»βπ»
[3/14, 9:44 AM] Maman muhseen: πππ
*AKWAI BAMBANCI*
ππππ
DAGA ALK'ALAMIN
*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*
*(MAGAJIYAR KAINUWA)*
*littattafan marubuciyar*
ππ»
*Rai da buri*
*Safah da marwah*
*Rayuwar Ameerah*
*Saina dauki fansa*
And Now
*Akwai bambanci*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
___________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
50.
Zaune Suke d'aki shi da Mubee, sun gama cin Abincin dare hira suke suna k'yal-k'yala Dariya,baby Nihal tana wajen Su mama.
Magana yake mata akan koma warsu Lego's,shagwab'a take ta zuba mashi yana biye mata,wayarsa Tayi K'ara yayi saurin zarota daga Aljihun rigarsa yana dubawa.
"kin gani baba ne d'a gani na ansa kiran."
Cikin girmamawa yace,
"to baba ganinan......to..... Eh.... to sai munzo. "
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Mubee,
Itama kallon nasa take tace,
"lafiya dai. "
Mik'ewa yayi yace,
"kira ne daga baba,yace muje nida Jaan."
Wata irin fad'uwa gaban ta yayi,don wallahi ta manta shaf da cewa Jannat yanzu matar Adam ce, miyasa ta yi haka anya kuwa ta kyauta,ko sau d'aya bata nusar da shi ba, sun shagala da soyayyar Su sun manta da ita.
Bata San fitar sa ba ta dai dawo daga tunanin taga ba shi nan.
Gaban sa ke ta faman Duka,don tabbas ya san tatsiniyar gizo bata wuce ta k'ok'i,magana zai mashi akan yadda ya nuna halin ko in kula akan Jaan.
Har ya isa bakin k'ofar d'akin da take yana sak'awa da kwancewa, sallama yayi bakin k'ofar yaji shiru kasancewar yau aka mik'a Nafee d'akin mijinta.
Ba yadda ya iya dole ya shiga......... Daidai fitowar ta daga wanka kenan tana d'aure da d'an k'aramin towel iya kar sa cinyarta.
tsorata tayi zata ruga yayi saurin fizgota, wanda kad'an ya hana towel d'in bai kunce ba,matse ta yayi yana kallon Cikin Idanunta,ranta inyayi dubu ya b'aci ta fizge jikinta cike da masifa tace,
"dalla malam Miye haka!fitarmun anan taya zaka shigo mani d'aki babu Sallama."
Kallonta yake cike da Madaki, shi bama masifar ce ta bashi mamaki ba, illah yadda yaga gaba d'aya ta canza mashi kamar ba ita ba....... Shigewar ta toilet ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya matsa kusa da toilet d'in yace Cikin sanyin murya,
" *Jaan* kifito baba fah ya turo ni na kira ki plz kisaka kayan kifito Ina jiranki. "
Har Cikin ranta haushi yake bata,yadda yayi buris da lamarin ta ya nuna da ita da babu Duk d'aya,tsaki taja tace,
"ka iya tafiya tunda ba cewa yayi ka d'auko ni na."
Jingina bayan sa yayi jikin k'ofar bayin yana lumshe ido,don yadda lokaci guda wasu feelings su kai mashi dirar mikiya,k'ara sausauta muryar sa yayi yace,
"cewa yayi kar na bari ki wahala,na goyoki ga baya na Don haka Ina nan Sai kin fito "
Runtse ido tayi tana jin irin yadda zuciyarta ke bugawa,jarumta ta aro ta yafama zuciyarta sannan ta iya cewa,
"wallahi inhar sai na fito za muje to sai dai ka bushe a nan,don bazan fito ba."
Duk yadda yaso tafito ya sake kallon ta,abun yaci tura dole ya Hakura ya tafi yabar ta don kar baban yayi ta jiran su.
Sai da ta tabbatar ya tafi sannan tayi saurin fitowa ta Fara kokowar saka kayan, ko mai bata tsaya shafawa ba ta zari abayarta ta fice.
Zaune ta some su baban yana kan kujera Adam yana gefensa k'asa,
Itama d'ayan gefen ta samu ta zauna tare da cewa,
"baba Ina wuni. "
Kallonta yayi yace,
"kema bazan amsa ba murjanatu."
Cikin zaro ido da mamaki tace,
"baba lafiya! minayi kuma, ni dai nasan lafiya muke tun wayewar garin yau. "
Harara ya sakar mata yace,
"kad'an ya hana ban kwana da fushin kuba,saboda naga kuna neman watsa mana k'asa ga ido."
Kanta ta sadda k'asa,don ta gane meyake nufi.
Shima Adam din sadda Kai yayi kamar wasu munafukai,cigaba yayi da cewa,
"kabani kunya Adamu, Don ban zaci haka daga gareka ba, nad'auki d'iya na baka amman kana nuna mana bamu isa ba ko?
To kayi daidai ko nace kunyi daidai,matsayinka na babba baka jata jikinka ba, baka zauna da ita ba balle ku fahimci juna asamu daidai to, Ashe soyayyar da Kace kana mata ta k'arya ce!kaban mamaki kuma kaban kunya."
"kema kuma kin taimaka mashi ta wajen halin ko inkula da yayi dake, saboda bakya gaidashi, Idan d'ayan ku yazo waje sai d'aya ya tashi,to kun kyauta tunda kun kasa had'a kanku tun anan, hakan na nufin can ma haka za kuyi, Don haka gara a warware Abun kowa ya huta,kaje ka kawo mani takardar sakin ta yanzu. "
Babu wanda zuciyarsa bata bujawa,
don basuyi tunanin hakan ba tuni Adam ya jik'e da zufa,Jannat kuwa jikinta rawa yake idonta yaciko tabda kwallah, Cikin kermar Muryar k'iris takejira ta fashe da kuka tace,
"baba badan na raina kuba,har ga Allah ganin ya shareni yasa nima nakyale shi, tunda ya nuna mani bai damu dani bah......... Sai hawayee shatter suka zubo mata.
Nan da nan jikin Adam yayi sanyi,tausayinta ya kama shi ji yake kamar yaje ya rarumota ya rungume yana lallashi.
baba yace,
"yi hakuri murjanatu daina kuka, tunda Baya sonki yaje ya kawo man takardar sakinki, Allah zai baki wanda yafishi insha Allahu."
A hanzar ce ya rik'o kafar baban yace Cikin karyewar zuciya,
"kayi hakuri karkace haka.!wallahi Ina sonta baba, banyi don naci fuskar ta ba,abunda yasa nayi haka saboda Mubee kar taga na fifita ta akan ita, na bari na shawo kan Mubee d'in kafin na juyo gareta,Amman idan hakan ya sosa maku kuyi hakuri. "
Sosai Baba yaji dad'in kalamin sa saidai dole ya nuna masa darajar jannat d'in Don yarik'eta da kyau.
Kara had'e fuska yayi yace,
"Aa Adam gara dai ka saketan,sai kaje ka kula da matar ka da kyau, tashi kaje maza Ina jiranka."
Ya fad'a tare da mik'ewa kamar zai bar d'akin.........cikin azama ya rik'o hanunsa yace,
"baba kar kayi haka, na rok'eka kayi hakuri wallahi zan gyara,kar ce zakaa rabamu tana sona nima haka In Allah ya yarda zan gyara."
Duk ya rikice ya susuce, Jaan kuwa babu abunda take sai shashshekar kuka,
Dawowa yayi ya zauna yace,
"inhar ka Amunce zaka gyara to kayi Mani alkawarin kwatan ta adalci tsakaninsu,ka tsaya tsayin daka kalu da kowacen Su........cikin zumud'i ya katse baban da cewa,
"nayi wallahi nayi baba, bazan karya alkawari ba insha Allah. "
dariya yaba baban murmushi ya kucce mashi,
Mik'ewa yayi yace"to indai ka d'auka karka fito sai ka lallasheta, ka kuma bata hakuri"
Ficewa yayi ya barsu nan,
Inda take ya koma Ya d'urkusa ya Kama kunnensa yace,
"Na tuba princess kaina bisa waya, kiyi Mani komi kikeso indai zaki huce,Amman pls kibar kukan haka nan kar yasakar maki ciwon Kai...........Ai Indai kaine hawan Jini ma zaka saka man, miyasa ba zaka kasheni na huta ba, wallahi da inada ikon dazan ciro zuciyata na cire wahalallen Sonka da kasha mamaki,don banga anfanin sa ba....... Hannu ya saka ya rufe mata bakin, ya durk'usa gaban ta tare da rik'o hannuwanta yace,
"karki ce haka, tab'a nan Kiji yadda sonki yake walagigi da zuciyata,kiyi hakuri ki ya feman,wallahi nayi maki alkawarin kulawa dake har sai kince kingaji"
Mik'ewa tayi zata bar d'akin............. Saidai tajita kawai ajikinsa yace,
"wallahi inhar baki ce kin hakura ba, saidai mu dawwa ma anan. "
bole tace ta hakura yana rik'eda hannunta suka fito,
Har d'akin ta ya raka ta ya gyara mata shimfid'ar gadon sannan yace "muje na taya ki canza kayan,"
Hararar sa tayi yace"wallahi kika sake hararana saina cinye wannan sweet lips d'in daketa tsole Mani ido tun d'azu"
Shi ya zab'o mata kayan bacci wata shegiyar rigace mai had'e da pant, wadda ita sai zafi ya kankama sannan take Sata,shima da tasa Zara rufe k'ofarta don gudun shigowar wani, shine yanzun zai d'aukota.
Shan mur tayi tace,
"don Allah malam katafi wai Miye haka, to wallahi bazan saka taba kuma ma Ina ruwanka da kayan da zansaka, kaje matarka ta sama Duk wadda kakeso Amman banan ba."
Rungumo bayanta yayi yana shinshinar wuyanta, nan da nan tsikar jikinta ta tashi,dole ta lumshe idonta tana Jan numfashi, Cikin low voice d'insa yake mata magana Cikin kunne,
"ke ma mata ta ce,duk abunda zanyi da Mubenat, kema zan iyayi dake don haka karki sake man magana Cikin rashin d'a,a don wallahi kika kaini karshe yau zan anshe budurcin inga ta tsiya,don haka ki kame bakinki kafin nayi aika aika gidan nan."
Shiru tayi tanajin saukar muryarsa har Cikin y'an cikinta, jikinta wata fitinanniyar kasala ta sauko mata, tana jikinsa yake zare kayan jikinta, takasa jurewa wannan munafukin salon nasa, jikinta ko Ina rawa yake, don lokaci guda taji wasu fitinannun feelings suna taso mata, Wanda rabon da ta tsinci Kanta irin haka ta dad'e ba tayi aune ba taji ya rabata da duk kayan, sai pant Kawai don sadda zata wajen baba sauri bai barta ta saka wata bra ba,
sadda ta ankare tayi saurin fixge jikinta, ta ruga bayi ta datse k'ofar tana sauke numfashi daker,
Kad'an ya hana bai zube kasa ba,,saboda yadda jikinsa yake tsuma ita d'in kawai yake murad'i. Meyasa zata ruga, wani naushi ya kaiwa bango don ba haka yaso ba, bai San iyakar tsawon lokacin da ya d'auka d'akin ba sannan ya tafi.
*saura page biyu nagama insha Allah.*
Takuce Maman muhseen.βπ»
[3/14, 9:44 AM] Maman muhseen: πππ
*AKWAI BAMBANCI*
ππππ
DAGA ALK'ALAMIN
*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*
*(MAGAJIYAR KAINUWA)*
*littattafan marubuciyar*
ππ»
*Rai da buri*
*Safah da marwah*
*Rayuwar Ameerah*
*Saina dauki fansa*
And Now
*Akwai bambanci*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
___________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
52.
Sun samu gidan tsaftace Don tun kan Su taho yayi waya dasu,akan ashirya masu tarbar ta musanman akuma sanar da masu aikinsu matan sudawo bakin aikinsu kafin Su ISO.
Jannat tayi mamakin wannan uban gida haka, ta jinjina irin d'aukakar da yasamu yanzu, jikinta asanyaye suka isa cikin main falon gidan, babu abunda ke tashi sai k'amshi ta kowace kusurwa, don komi saida Adam ya saka aka canza saboda zuwan habibatyn sa Jaan.
Tunda ta zauna masu aikin keta zuwa gaidata,
Mubee ce ta sauko daga sama b'angaren Adam, saida ta gama kintsashi sannan yace taje ta shigo da Jaan d'in.
"kin wani jeb'e waje guda sai Kace Wata bak'uwa, taso muje sama."
Kasa tanka ta tayi saboda har ga Allah wata kunyar mubeen takeji,gani take kowa zaginta yake akan wannan auren.... Bin bayanta tayi tana maijin babu dad'i,sadda suka k'arasa saitaga ai can bataga komi ba, Wata daulace ta daban, ta jinjina Kai kawai, saboda daka gani Kasan babu k'arya Adam yana samun kud'i.
Zama tayi saman Wata lumbutsestiyar kujera, wadda tana zama taji talume ciki,
Mamaki ya ka mata dama akwai irin wad'annan kujerun, lallai daji zasuyi kud'i.
Tare da Mubee suka fito yasha wanka kaya bacci me lemon green jikinsa,yayi masifar kyau Duk yadda take yana kwayar idonta satar Kallonsa, abun yaci tura har saida ya kamata tana Kallonsa, Hararar wasa yasakar mata ya cewa Mubee,
"my love kiyi mata magana tabar satar kallona."
Sadda Kanta jaan tayi tana jin kunyar mubeen tana walagigi da ita,
Jitai tace masa"to Kai hubby da wane Idon Kasan ta kalleka,in banda kaima Kallonta kayi."
Yace"au goyon bayanta kike ko? To Shikenan munb'ata."yafad'a yana shagwabe fuska.
Dariya tayi tana wucewa k'asa don ashigi masu da kayansu....... Suduka binta sukai da kallo har tafice,
Ya dawo da Idon sa akan jaan yana canza salon kallon zuwa Na zazzafar k'auna......tasowa yayi daga inda yake ba tayi aune ba ta ganshi durk'ushe gabanta, duk hannuwanta yarik'o yana k'ok'arin saka kwayar idonsa cikin tata,amman taki bashi damar hakan, matse hannun nata yayi taji zafi wanda dole ya d'ago ta Kallai.
Ajiyar zuciya suka sauke tare, Amman tashi tafi bayyana, duk da haka saida yaji tata.
Motsin shigowar da taji za, ai yasaka tayi saurin tashi tabarsa anan,
Mubee ce d'auke da baby, tana ganin jaan taita mik'a hannu har saida ta ansheta.
Har wasu d'akuna Mubee takai jaan tanuna mata komai tace takintsa ta kuma huta kan agama dinner.
Wanka tazuba Tayi shigar doguwar riga light pink tasha adon fulawoyi da a Kayisu da stone's sai walwali Suke.
Koda tafito suna nan babban falon sun baje k'asa ga abinci nan kala Kala sai wanda Kazab'a ga uban naman Kai nan ga Kilishi, dasu yanciki ferfesun Su,
Tunda tafito idonsa yake Kanta, yakasa d'aukewa tazbihi yakewa Allah akan bashi mata zafafa irin wad'annan,Mubee nunawa Tayi kamar bata ga me yakeba,abincin take zuba masu,
Har jaan ta iso idonsa kamar zai fado k'asa shiyasa Itama duk ta takura,
Mubee tace"gaskiya kallon ya isa haka, wannan ai saka saka tafad'i Abban baby."
Tafad'a cikin wasa tana Hararar sa.
Murmushi yayi yana shafa kansa,
Mubenat ta gama hada komi tace"kowa yasaka hannu yad'auki spoon don nidai yunwa nakeji wallahi,ga bacci da gajiya basu barni ba,don haka nidai da wuri zan kwana."
Jaan dai takasa tankawa sai tsakurar abincin take, Wanda rabinsa duk namane.
Lura tayi da yadda takasa sakewa tace" mommy Nihal kisaki jikinki kici,ohhh kina jiran angonki ya baki ko,?to bari kigani........ Plet ta d'auka ta zuba nata ta d'auki komi, sannan ta mik'e Kunga nayi nan saida safenku.......
Cikin sauri jaan ta rik'ota tace cikin sanyin murya"don Allah karkayi haka kizauna ni ba fa haka nake nufi ba,kizauna wallahi bazanji dad'in hakan ba Idan kikatai."
Murmushi yakeyi yak'i cewa komi,
Harara tawurgamai"Abban baby kazo Kaja amaryarka ni tafiya zanyi sai kuyi soyayyar cikin natsuwa, tunda naga kunyata kukeji.. "
Mik'ewa yayi yanufo Su yana cewa"wakejin kunyar taki, kinsan dai ni banda wannan sai dai Idan kanwar taki. "
Hannun jaan Yarik'o ya zaunar kan kujera, yace muje my love Na rakaki......
Fita sukai suka barta tana jin kirjinta yana dukan tara tara,
Tausayin mubeen ya kamata tasani K'arfin hali take, duk don ta basu kwarin guiwar kasancewa da juna,
Hakika jitake Idan itace mubeen bazatayi dukan wannan ba, zadai tayi iyakar Inda zuciyarta ta iya.
Har bedroom d'inta Na k'asan bene yakaita,
Duk yadda taso danne kukanta abun yaci tura, dole tafashe da wani irin Marayan kuka,
Lallashinta yakeyi sosai da kalamai masu kwantar da hankali, tare da nuna mata irin muhimmancin ta gareshi, da irin Kaunar da yake mata bai baro wajenta ba saidai tacinye Duk abincin, ta yi shirin bacci sannan ta kwanta,yayi mata addua tare da kunna mata karatun Kur,ani don sakamata natsuwa...... Sannan yafito.
Koda yadawo tayi bacci d'aukar ta yayi yakai d'akinsa sannan yadawo yad'auki holandia da naman yakai,
Kayanta ya shiga ragemata tai firgigi tatashi,
Tana tureshi saidai ya matseta jikinsa sannan ya idasa cire mata Su.... Kunya kamar ta tsaga bango tashige,
Ganinta daga ita sai pant kawai..... Wata arniyar rigace wadda da ita gara babu ya d'auko yasaka mata dakokowa,
Tana ta kwallah ita bataso haka yasa mata ita, aiko tashige bargo don komi ya bayyana kansa Na jikinsa,
Tun yanzu duk yarud'e don har jikinsa ya fara Wata rawa rawa....amman ya danne ya shiga bata ga baki naman daker ta d'anci kad'an tasha hollandia dad'an yawa....... Suka shiga sukai brush, tare dayin alwallah,,
Yasaka after sukai sallah tare da yiwa Allah godiya daya mallakama su junan Su.
Bayan sungama yayi mata wannan adduar allahumma Ummii as, Kayla khairaha wa kairama jabltaha alaihi wa auzubika minsharriha wa sharri ma jabltaha alaiki.
Yagama yace taje ta kwanta.
Can k'arshen gado ta koma Talullube har ya gama hidimarsa yazo yakwanta tare da kashe wuta,ya kunna dumlight....amatukar tsorace take dashi sadda taji ya jawota jikinsa...... Cikin kunnenta yake mata magana mai tsananin rikitar da sassan jikinta.
"baby love Inason anuna man irin Kaunar da akeman, Inga da gaske jaan d'ina tana son wannan Adam d'ina. "
Tsikar jikinta tatashi saboda yadda yake sauke numfashinsa cikin kunnenta, tare da k'ara matseta da yake ajikinsa...... Shiru tayi tanajin wani irin yanayi da ta dad'e rabonta dashi...... Jitai yana yawo da hannunsa ajikinta,dandanan ta rud'e don dama kad'an takejira duk da gabanta yana dukan uku uku, Amman jikinta yana karb'ar sakon, saboda irin abubuwan da sukaita banka,
Wannan dare sun raya shi cikin amincin ubangiji,Adam yama rasa da kalmomin da zaiyiwa Allah godiya,
Don jaan kuka Shima kuka saidai zamuce nata na Shan wuyane, shikuma abun saidai arufe baki (π€π Su adamu ansha miyar amarya jarda kuka π€£π€£π€£ )
Har gari ya Waye yana lallashi daker yasamu bacci yayi awon gaba da ita, sannan yasamu natsuwa yaje yayi sallah yana zuba adduoi bila dadin,akan Allah ya zaunar dasu lafiya da matanshi tare da zuria Dayyiba...............
ππππππππ
soyayya sabuwa ta bud'e tsakaninsu don har sun rasa Waye yafi son d'an uwansa,
Saida Mubee tabasu kwana goma cif,sannan ya raba masu kwana, Duk bayan kwanakin uku uku.
Hakan yayi masu sosai, don jaan tace itadai kwana biyu yayi mata