Showing 126001 words to 129000 words out of 131687 words
Chapter 43 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
ahali. Kafin kowa ya samu nutsuwa a dalilin farfaɗowar Lulu. Ba'a bari an shiga inda take ba sai Smart kawai. Dan shikam a ranar ma tare suka kwana. Ko yaya ta motsa ya dinga tambayarta minene damuwarta kenan har saita sakar masa murmushi. Sai washe gari ƴan uwa da abokan arziki suka samu ganinta. Daddy ji yake kamar ya haɗiyeta dan farin ciki. Duk wani masoyinsu da uban gayyar sai yau suka samu nutsuwar kallon baby's. Yayinda aka koma kuma taya juna murnar samun ƙaruwa.
Salim shi Smart yasa yayma yara huɗuba a kasancewarsa babba. Itama Lulu sai a ranar ta samu ganin abinda ta haifa. Cikin ƙarfin hali da magana ƙasa-ƙasa take faɗin, “Mr A wannan karon ma kamin wayo, su duka kai suka biyo”.
Murmushi ya sakar mata yana wani ɗage gira sama da amsa mata da cewar, “Hakan na nufin na fiki jarumta a filin yaƙin ƙasa da ƙasa kenan. Next time ma ƴan uku zakiyi in sha ALLAH”.
Da sauri ta kauda kanta gefe tana faɗin, “Ai kai dama ba'a hirar arziƙi da kai. Mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kake wani kira masa haihuwar ƴan uku”.
Dariya ya sanya mata Nadiya na tayashi. Dan duk tana ɗakin suke wannan taɓarar... Dada da ciwo ya sake fidda tsufarta ta taƙarƙara da ƙyar tazo asibitin da duba Lulu. Lokacin da taga ƴan tagwayen nan sai da hawaye suka cika mata ido. Dole abubuwa su rincaɓe musu dan rabon yaran nan kaɗai ya isa ya zama sanadin kaudasu a duniya. Gashi nan cikin shekara biyu da rabi a auren nasu Lulu nada yara uku...
Alhmdllh Lulu ta samu kanta sosai kasancewar jikinta mai ƙyau ne baya riƙe ciwo. Kwananta shida aka sallamesu suka koma gida. Dan ta matsa akan ita a sallameta ta gaji da zaman asibitin nan bata son warin. Haka aka sallamota suka nufi gida. Sai dai maimakon gidan Abba sai taga an wuce da ita katafaren gidan da mijinta ya gina batare data sani ba. Duk da sun taɓa wucewa ta gaban gidan kasancewar a anguwarsu ta hotoro GRA ne har taita santinsa. Ashe wai nasu ne. Koda ta jiyo tana kallon Smart sai ya kama kunnesa yana wani ɓata fuska kamar AA na fushi. Murmushi kawai tayi tana mai sinne kanta dan suna a tsakkiyar mutane ne.
Gida bai sake rikita kowa ba sai da suka shiga cikinsa. Abun ba'a cewa komai kawai. Lulu na son keɓewa da mijinta sai dai babu dama. Dan gidan cike yake kasancewar su Ammah sunce fa sai anyi taron suna. Washe gari aka raɗama ƴan biyu suna. Inda sukaci sunan *_Ayshatul-humairah da Hafsatul-Ikram_*. Ƴan biyu Aysha da Hafsat sunyi goshi matuƙa. Dan kwai da kwarkwata na dangin Lulu da Smart musamman ƴan FURAR DANƘO C-BOX. AREWABOOKS, ZAFAFA FANS dama ƴan bayan katanga masu karatun bati sun zo a gayyar SOƊI🤣🥱 (A daure azo a biya 400 ne, duk 1k babu yawa bama son halin dangin Sulaiman Tsule ƴan bati. Dan nidai babu ruwana biyana za'ai🤪😜). An raƙashe an ƙwalle a wannan taron suna yayinda amaryar jego da jariranta sukasha ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon badaga baya ba kam. Munci hinkafa iya hinkafa. Munha zoɓorodo harda kajin gidan gona masu tsokar gaske. Ga halawa da biskin duk an bimu da su a ledoji. Kai al'amarin dai ba'a cewa komai dan an nuna halin girma. Sai muce ALLAH ya raya Ayshatu da Hafsatuwa....
Har washe gari gidan nan cike yake da mutane. To su Xoxo anga hinkafar banza anƙi tafiya🥱. Huguma da Rano da Mamu kam harda rantsuwar su sai Lulu tai arba'in zasu wuce, yo anga gida ginin gilashi🤣. Nace kunji abin kunya Zafafa dai sai an nuna hali a ko'ina😏🚶, alhalin hinkafar nan fa dai kowa nada a gidansa, gilashi kuwa kowa akwai a windown gidansa. Amma dai bari mu bincika o'e da o'e kodai-kodai 🥱. (I love you Zafafa's😘😘😘❤️💞🙏).
Shatara ta arziƙi kam dai Lulu ta sameshi a wannan haihuwar. Dan Nadiya da Ummita da amaryar Baba Garko da Maryam amarya sune tsaye akan duk wani gift data samu. Tun a wajen hotuna bata sake saka mijinta a ido ba sai a daren na washe gari ya fidda kunya dai ya shigo har ɗakinta. Su Ummita dake baje suna buɗe gifts suka suka fara rige-rigen fita. Idanu Lulu dake da ga kwance AA na gefenta zaune yana fitinar a bashi Baby ta ɗago a hankali ta sauke a kansa. Shima ita yake kallo da yaransa guda uku dake gabanta reras. Lallausan murmushi ya sakar mata yana mai lumshe ƙyawawan idanun nan nasa da take kira na maciji tare da ɗaga kafafunsa a sannu-sannu ya cigaba da nufota cikin takun ƙasaita da kasala tamkar mai irga steps ɗin nashi. Dai-dai yana isowa ta yunƙura zata tashi zaune ya girgiza mata kansa yana mai kaiwa zaune a bakin gadon da kama kafaɗunta ya maidata ya kwantar yana kaɗa mata kansa. Bata da zaɓin daya wuce komawar ta kwanta. Baice da ita komai ba sai hankalinsa da ya maida kan AA. Cike da kulawa ya ce, “Waya saka Baban Ammah kuka ne?”.
Cikin shagwaɓa AA ya nuna Lulu, dan har yanzu shi maganar tasa sai a hankali ce. Dan ma ɗan zamansu a Nigeria ɗin nan ya fara samun bakinsa kasancewar gidan Abba gidan yarane. Balle shi da ko yaushe yana hannun yaran gidan kowa ji yake da shi saboda ƙyautatawar iyayensa. Kaɗan Smart ya ɗan waro idanu waje da faɗin, “Kai-kai Maah-maah ce”. Kai AA ya ɗaga masa yana wani sake ƙwaɓe fuska.. “Ayya Kakan Papa yi shirunka ƙyale Maah-maah kaji ko. Bazamu saya mata kayan daɗinmu ba ai ko?”. Nan ma AA ya ɗaga kansa dan yana jin magana sarai abinsa. Gyara masa zama Smart yayi tare da ɗaukar Hafsat dake a kusa da shi ya ɗauramasa a saman cinya, sai dai bai sakar masa ba tana a hamnunsa. A take yaron ya hau dariya yana nuna Aysha wai itama a ɗaura masa. Haka Smart ya biye masa itama ya ɗaura masan. Ita dai Lulu na kallonsu kawai, dan a yanzu tana sake fahimtar irin so da ƙaunar da mijin nata kema yara ta dabance. Sai da yaran suka ɗan jima a cinyar yaron sannan ya saukesu ya kwantar da su yace ya kwanta kusa da su ya musu wasa.
“Ni dai kada ya tsokale min idanun yara gaskiya. Har yanzu ban gama dawowa a hayyacina ba fa”. Lulu ta faɗa cikin shagwaɓa harda wani ɗan tura baki. Dariya ta bashi ma shi, dan haka ya juyo yana kallonta gira a ɗage ya ce, “Oh really?!”.
“Kai ne shaida ai, tunda kai kafi kowa shan kuka”.
Kansa ya kauda gefe yana murmushi da faɗin, “Oh ni Aliyu. Na shiga tara kuma da gorin yarinyar nan. Ke da baƙya raye a lokacin ya akai kika san haka?”.
Murmushi ta saki mai bayyana haƙwara. Ta ce, “Likimo nayi fa duk ina jinka. Dan na sake tabbatar da wanene mijina. Ashe ragone shi a kan lamurana”.
Yanzu kam dole dariyarsa ta fita da sauti. Ya zuba mata mayun idanun nan nasa yana sakar mata wani murmushi mai sanyi da fasa zuciya. A can ƙasan maƙoshi yana mai dimtse hannunta cikin nashi da ƙyau ya ce, “Kin san kuwa matsayin da Mawaddat Jiƙamshi ke da a zuciyar Aliyu! Wannan sirrin ALLAH ne kawai yasanshi Baby luv. Kin fa gama mamaye ko'ina da ina baki ragema wata koda ƙanƙanin fili ba. Har tsoro nake ji kada wataran ƙaunarki ta fasa zuciyar ɗan bawan ALLAHn nan ma”.
Tuni ƙwalla sun cika mata idanu, zaune ta tashi tana mai juya kwanciyarta zuwa jikinsa. A tare suka saki ajiyar zuciya da lumshe idanunsu suka buɗe duk a lokaci ɗaya. Akan yaranta ta fara sauke nata kafin ta juyo gareshi hawayen da suka taru mata na sakkowa a hankali bisa ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Da sauri ya wara idanunsa zaiyi magana sai ta sakar masa murmushi da girgiza masa kan alamar kada yace komai.
“Aliyu!”.
“Uhyim Mawaddatan'warahmah!”.
“Kai ɗan aljanna ne da izinin ALLAH”.
“Tare ai zamu shige in sha ALLAHU”.
“Da'ace wani ɗan adam nada damar buɗema ɗan uwansa nan dana buɗe tawa ka ga matsayin ka a ciki” tai maganar tana ɗaura hannunsa a saitin zuciyarta. Idanunsa da sukai rauni sosai ya lumshe da sake buɗewa a kanta. “Kin mallaki Aliyu Hydar da komansa Mawaddatan'warahmah. Na jima da sanin kema kin mallaka masa zuciyarki. Sai dai ban san miyyasa kika zaɓi ɓoyewa ba baby luv. Salonki na azabtar dani matuƙa”. Dariya ta ƙyalƙyale masa da ita tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Sai ma sake matseta da yay cikin jikin nasa har sai da tai ƴar ƙara da faɗin, “Wash ciwona”. Da sauri ya saketa a rikice, ta ko kwashe masa da dariya tana masa gwalo. Sai ya ƙwaɓe fuska cike da shagwaɓa ya ce “Zan rama ne ai”.
“Sai dai wani karon wannan kam nayi winning”.
“Ba komai, ai da kai da kaya duk mallakar wiyane.” yay maganar yana mai lakace mata hanci. Ita kuma taja kumatunsa da faɗin, “Yaushe Aliyu ya fara ɓoyewa Mawaddat sirrikansa?” ta ƙare faɗa tana kallon ɗakin. Ya fahimci mi take nufi. Dan haka ya saki ɗan murmushi da kallon ɗakin shima. “Aliyu bai taɓa ɓoyema Mawaddat sirrinsa ba. Ya mata hakanne kawai domin supricing ɗinta, kuma Alhmdllh burinsa ya cika, wannan shine gidan Mawaddatan'warahmah da Aliyu da zuri'ar da zasu tara in sha ALLAH.”
Hawayene masu ɗumi suka gangaro a idanun Lulu dake kallonsa ko ƙyafta idanu batayi. Kallonta yay da sauri. Zai yi magana ta ɗaura yatsarta akan lips ɗinsa ta ce, “Shiii!!. Lokacin Mawaddat ne”.
Yanda tai maganar cikin raɗa sosai ya sashi sakin murmushi.....✍️
😁😁😁😁To nima bari na ɗan murmusa
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣5️⃣
________
*_INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN 😭😭😭_*
_ALLAH yayima *MARUBUCIYA FAREEDA ADO GACHI* rasuwa. Ya rabbi ka gafarta mata ka yafe mata kura-kuranta. Ayyukanta na alkairi su zama fansata domin rahamarka ya *UBANGIJI. MARUBUCIYA* ce data taka rawar gani a harkar rubutu da alƙalami da duniyar rubutu bazasu manta da ita ba. Tana cikin tawagar manyan marubutan nan na *MACE MUTU* a littafinsu mai suna *HANNU DA YAWA.....* da wasu ire-iren su. Ta rubuta littatafai ita kaɗai kamar haka._
*MEKE NAN?*
*RAYUWAR MATA*
*ƳAN UBA*
*NI KO SHI*
*RA'AYINA NE*
*TUBALIN TOKA*
*_ALLAH kai mata RAHMA damu baki ɗaya. 🙏🙏_*
*_MADUBINA A HARKAR RUBUTU TA TAFI 😭😭😭🙏_*
_____________
.......A bazata ya ji saukar lips ɗinta akan nasa. Daburcewa ya nema yi kasancewar anfa jima ba'a haɗu ba. Dama ɗan Ammah a wuya yake. Sai da ta gama rikita masa lissafi da salon da bai taɓa sanin ta iya ba sannan ta nema janye jikinta. Shi kuma a sannan yace bai san zancen ba. Dan ta riga ta ɓallo MAZAN FAMA. Murya a sarƙe yana ruƙota ya furta “Please Mawaddatan'warahmah”.
Murmushin mugunta ta sakin masa tana kai bakinta a saitin kunnesa ta furta, “Jego muke fa”.
“Bayan kin gama jigata ni”.
“Yada karaya haka MAZAN FAMA”.
“Ki ɗauka kawai na zama rago ko MATAN FAMA”.
Dariya Lulu ta kwashe da shi. Kamar zai saki kuka ya ce, “Ki kasheni ki huta kawai”.
“Idan na kashe Aliyu dawa za'a ganni a filin yaƙin ƙasa da ƙasar kuma ni Mawaddat”.
Harara ya ɗan sakar mata yana kaiwa kwance dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi. Yaransa ya zubama ido kawai dan AA ma yayi barci a kusa da twins.. Mintsini ta kai masa, yay shiru, ta sake ya sake mata shiru, ta sake kai hannu a karo na uku ya damƙe hannun tare da birkiceta. Rikitata ya shiga yi tare birkita mata lissafi da zazzafan salonsa. Sai ga Lulu na roƙonsa harda kukanta akan ya rufa mata asiri yau fa kwananta tara da haihuwa. toshe kunnuwansa yay kamar baya jinta, sai da ya tabbatar ta tsorata matuƙa sannan ya harareta yana komawa gefe. Sai kuma ya koma yimata dariya ganin yanda ta gama fita a hayyacinta da tsoro. ƙaramar ƙwafa yay da faɗin “Gobe ma ki sake takalata zaki sha mamaki dan sai kinga ƙarshen tsokala.”
Baki ta tura masa tana harararsa, da sauri ya kai mata cafka, ta dire da gudu daga gadon. Dariya ya kwashe da ita harda hawaye itako tana harararsa baki a sama.....
Duk shagalin da aka sha sai da aka kaima Umma labari, hawaye kawai take zirararwa. Ga shi dai Aliyu yakai inda ta jima tana yaƙin, yayinda ita take kwance sai an kwantar an tayar. Miji ya saketa ƴaƴan nata ma sai wanda ya ga ALLAH yake tausaya mata. Gashi su dukansu sun koma ƙarƙashin alfarmar maƙiyin nata. Kallon Ammah kawai na ɗaga mata hankali. Dan daka ganta kasan Alhmdllh komai ya zauna dole a kirata uwar sarkin gida. Suna da matsayin data jima farautar samu. Huwaila harda nuna mata video ɗin gidan Smart. Nan ma saita ɓarke da kuka. Babu kunya Huwaila ta sanya dariya tana faɗin, “Su Umma dai ana kwancen ma baza'ai dana baƙin ciki da cigaban wasu ba”. Tana gama faɗa ta miƙe da cikinta tirƙai-tirƙai da ke saka jinin Umma sake hawa a duk sanda ta kalli Huwailar tayi wucewarta yayarta na mata faɗa bata ko saurareta ba.....
★★★
Duk yanda Smart yake kwaɗayin zama kusa da iyalinsa dole ya shirya ya koma saboda cikar kwanakin da aka bashi. Ya tafi ya barsu da kewa kamar yanda shima ya tafi da kewarsu. Haka Iya Tabawa ta cigaba da kula da Lulu. Yayinda Asma'u ta dawo nan dan gidan yay masu girma duk da an zuba ma'aikata kamar su maigadi mai gyaran filawoyi mai wanki harma da driver da mai share-share da sauransu. Sannan Huwaila ma kusan tana anan ne ita da Nadiya. Hakan ya ɗan ragema Lulu raɗaɗin rashin mijinta a kusa da ita. Sai dai akoda yaushe suna maƙale a waya ana video call. Ammah na leƙosu akai-akai, hakama aunty Saliha. A haka sukai arba'in zuwa lokacin ta gama gyagijewa. Ga gyaran Iya Tabawa tana samu mai lafiya dan ita kanta tana jinta on top. Ta zagaye dangi itace har Abuja, kafin ta fara shirin komawa dan Smart ya ishi kowa da damuwarsa. Ammah dai data gaji da yawan ƙorafinsa ta ce ta shirya ta tafi wajen mijinta kozai barsu su huta. Kunya abin ya bama Lulu ma ita. Shiko ta fahimci ko'a ƙwallar rigarsa. Tare da Asma'u suka wuce da Iya Tabawa. Mai gayya da aiki ne da kansa yaje tarbarsu airport, da mamaki yake kallon Asma'u dan bai san da ita za'azo ba. Lulu bata taɓa sanar masa ba har taima Asma'u komai-da-komai na tafiyar. Bai iya cewa komai ba ya kwashesu suka wuce yana ɗauke da yaran duka, sai da Asma'u ta amsar masa AA dan taga sun masa yawa. Tsaff suka samu gidan nasu harda abinci ya tanadar musu. Dan haka babu ɓata lokaci sukayi wanka suka baje. Asma'u ce ma dai keta faman ƙauyanci da santin gidan suko suna mata dariya. Shi dai Smart na manne da yaransa kamar wani yace zai ƙwace masa su, dan gaba ɗaya hankalinsa na kansu ne.. Sai narkakken kallon da yake bin matarsa da shi lokaci-lokaci a kaikaice wanda ita kaɗai ta fahimci abinta. Dan haka taɗan shiga tsoro dan tasan yau kam saita ALLAH wai biri a hannun bamaguje. Gashi tasha gyara kala da iri da ita kanta tasan sai tayi bayani da yaran Jiƙamshi yau kam.
Kamar yanda tai hasashen kam ta ɗanɗana kuɗarta, yayinda Smarty ya rikice mata tare da sanya mata albarka babu adadi. Tattali kam ta shashi a wannan yinin, gashi dama babu inda ya fita dan haka suka yini a ɗaki da ƙyar yake barinta ta leƙa su Iya Tabawa kodan Asma'u dake fama da baƙunta. Yayinda ya barta da jin kunyar Iya Tabawa, shiko ko'a ƙwallar rigarsa. Bayan dawowarsu da sati uku ya fara nemawa Asma'u gurbin shiga jami'a ta fara, sai dai kullum tana manne da waya suna shan soyayyar su da Hussain ɗin ta, idan kuma ya bushi iska yakan shiryo yazo UK ɗin ya mata kwana biyu. Tayi farin ciki da hakan sosai dan ita mai son karatu ce dama. Shima AA an sakashi makaranta, sai dai ba boko bace ta addini ce da wani balarabe maƙwafcinsu ya ɗan buɗe domin yaran musulmai. Lulu ta cigaba da shayar da yaranta cikin ƙoshin lafiya da kuzari, yayinda suketa ƙara wayo da ƙyawu masha ALLAH. Kamaninsu da mahaifinsu da AA nata ƙara fitowa....
_________★
Sosai bashi da lafiya. Ya wani irin fita a hayyacinsa tare da yamushewa kamar wani tsoho dan ko Baba Garko bazai nuna masa tsufa ba a yanzu al'amarin zammamaki. Duk wanda yasan Sulaiman ya ganshi a yanzu zai iya dire rantsuwa da bada tabbacin bashi bane. Ya bushe a tsaye ƙwarai da gaske. Tunda aka gama shari'arsu aka kaisa wani mugun jail