Showing 75001 words to 78000 words out of 131687 words
Chapter 26 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
shine dressing nata. Batare data kallesa ba ta wuce gaban mirror ɗinsa dake cike da turarruka da mayukan gyaran gashi sai abinda ba'a rasa ba. Gashinta taƙe ƙoƙarin tifkewa. Kwanciya ya gyarama AA tare da miƙewa, dai-dai tana tattare gashin cikin hannunta bayan ta zare ribbon ɗin data ɗaurosa da shi sukai ido huɗu da shi a bayanta. Yay wani tsaiwar ƙasaita irin na isassun maza yana kallonta da mayatattun idanun nan nasa. Sosai ta ƙara jin ƙirjinta ya motsa, tai azamar janye idanunta tamkar bata ganshi ba. Idanun ya rufe ya buɗe a lokaci guda yana ɗan ƙara matsawa jikinta daf ya mata runfa, sai kuma ya ƙarasa rungumeta a hankali tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. A tare suke ja numfashi da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Yanda yake wani bin wuyanta da shinshina idanunsa a lumshe ya sata jin tana neman zubewa a ƙasa, saurin riƙo hannayensa duk biyu da ke zagaye da ita a saman cikinta tai, hakan ya sakashi sake ƙanƙameta tsam-tsam kamar za'a ƙwace masa ita ya wani busa mata numfashi a cikin kunne....
Harga ALLAH bazata iya ɗaukar wannan salon nasa ba, dan haka tai ƙoƙarin jan jikinta da saurin faɗin, “Wai nikam minene haka?” cikin rawar murya data lips. A cikin kunnenta ya raɗa mata “Saƙon barka da zuwa mana. Haka ya kamata ki tarbi mijinki _My Final Choice_”.
Kanta ta matsar gefe tana taune lip ɗinta na ƙasa, cike da basarwar nan tata cikin son janye jikinta ta ce, “Kama nemo Final Choice ɗin naka bana son iyayi”.
Sake ruƙota yay sosai yana murmushi. Idanunsa ƙyar a kanta ta cikin mirror ɗin ya ce, “Kowa yasan na nemo abita ai tuni. Dan duniya duk ta san Mawaddatan'warahmah ce Heart controller ɗin Aliyu Hydar Mika'il Mawashi”.
“Kai dai ka sani”.
Ta faɗa tana janye jikinta a nashi. Bai hanata ba ya saketa tare da harɗe hannayensa a ƙirji. Kallonsa tayi ta ɗauke kai da rusinar da idanunta. A hankali ta ce, “Malam matsamin na wuce”. Dan ya tsare mata ko ina. Bai matsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta sama da ƙasa ba. Kallo irin mai haka mutum sukuni ɗin nan da ji iska ma na maka wahalar shaƙa. Ƙoƙarin raɓasa tayi ya tare, ta sake komawa ɗayan ɓangaren, nan ma ya tare, ta koma tsakkiya nan ma ya tare. Sai kawai ta zabga masa harara tana tunzura baki. Hannayensa ya warware da ƴar murmushi har sannan a fuskarsa ya ɗan matsota, baya ta matsa ta manne da mirrorn. Shima sai ya dafe hannayensa a mirror ɗin ta gefe da gefenta ta koma tsakkiyarsa, ya ranƙwafo sosai yana busa mata numfashinsa a fuska. Ga son su haɗa idanu da yake faman yi. Cikin daburcewa ta furta “Aliyu!”.
“Uhmyim Mawaddat!”.
Ya amsa mata kafin ma ta gama rufe bakinta, sai taji ma ta sake daburcewa dan yanda yay kiran sunan nata da amsawa acan ƙasan maƙoshi da busa mata numfashin yasa ƙafafunta ma suka fara rawar son kasa ɗaukarta. Ɗago idanunta da suka tara ƙwallar da ita kanta bata san dalili ba tayi, hakan ya bashi damar ɗaura lips ɗinsa akan nata kamar dama abinda yay target kenan. Kafin tai wani yunƙuri ya tallafi kanta da ƙyau da hannun damarsa, ɗaya hannun kuma ya saukesa akan bayanta. Sam bata da wani sauran ƙarfin yin wani yunƙuri, dole ta haƙura dan tasan wani buyaginta bazai sa ya fasa ba in dai shi ne, sannan ita kanta kawai ƙarfin hali ne tana buƙatar mijinta. Jin tsaiwar na neman gagararsu yay ƙoƙarin tattarota zai ɗaga. Da sauri ta tattaro nata ɗan hankalin waje guda itama ta kai masa ɗan duka a gefen cikinsa....
“Ouch!”.
Ya faɗa yana sakinta yana dafe wajen. Sai kuma hankalinta ya tashi ganin yanda ya duƙe, cikin rikicewa ta ruƙo hannunsa dake riƙe da inda ta bugesan duk da dai ita tasan kaɗan ta masa. Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Please kayi haƙuri ALLAH ban san zai maka zafi ba, wayyo ni”.
Sake langaɓewa Smart yay kamar gaske, ta kamashi ta jinginar da mirror ɗin tare da ɗan daga rigarsa tasa hannunta a wajen tana murza masa a hankali. Sake langaɓe murya yay yana faɗin, “Wayyo zafi Ammah kizo ta targaɗa miki ni”. Harga ALLAH Lulu ta ɗauka da gaske yake, dan haka ta sake ruɗewa har idanunta na tara ƙwalla, duk yanda yaso riƙe dariyarsa hakan na neman gagara, dole ya saketa dai-dai tana kwantar masa da kai a kafaɗarta.
Galala tai tana kallonsa ga hawayen da suka cika mata ido na neman fara zubowa. Cikin son danne dariyar da ke ƙara tunƙuro masa ya ce, “Dama haka kika damu da Aliyu? Madam!”.
Hararesa ta ballara masa da raɓawa ta gefensa ta wuce tana jan ƙafa da ƙyar dan ji take tamkar zata zube ƙasa ma. Shima sai yaja nasa jikin yana murmushi zuwa ƴar ƙyaƙyƙyawar kujerar dake gefe da ɗan table mara tudu dai-dai ita da zaka iya miƙe ƙafa a kansa ya zauna yana sauke numfashi da ƙaramar dariya. Sai da ya bada kusan mintuna biyu hankalinsa ya dawo jikinsa sannan ya tashi zaune da ga kwantar da bayansa da yay ya buɗe idanunsa a kanta. Tama kwance kusa da AA ne idanunta a lumshe ta wani dunƙule jikinta waje guda kamar wata baby. Ƙaramin murmushi ya saki da miƙewa ya fara zame kayan jikinsa da faɗin, “Ya kamata ki fara cin abinci kafin ki kwanta barcin ko”.
Shiru kamar bazata amsa masa ba, sai can a takaice ta ce, “Ba buƙata”.
Bai sake cemata komai ba ya nufi bathroom. Da kallo ta bisa, sai kuma rashin sake cewarsa koman ya bata haushi ta wani tura baki da hararar bayansa tana murguɗawa ta maida idanunta ta rufe. Ya ɗan jima kafin ya fito ɗaure da towel yana goge jiki da ƙarami. Kai tsaye wayarsa da ke ring ya nufa yana ɗan yamutsa fuska da kallon agogo. Bai niyyar ɗauka ba, sai dai ganin Ahmad ne ya sashi ɗagawar tare da ɗaukar bluetooth ya manna a kunnensa ya cigaba da abinda ke gabansa da alama Ahmad ɗin yake saurare.
“Ka kira dai kayi gulma ɗan sa ido”.
Dariya Ahmad ɗin ya kwashe da shi da ga can. Ya ce, “Ai kai dama ba'a maka abin arziƙi. Ni yarona na kira naji yaya yazo bai jigataba dai ko?”.
“Ga shi nan na samesa yana kwasar barci dan sun shigo gidan na fita. Yaya kun gama da mutanen?”.
“Har yanzu dai ana cuɗawa, naga sun ɗauki burin duniya sun ɗaurama wajen. Amma dai za'a dai-daita in sha ALLAH dan naga da Yaya yace zamu haƙura kuma kamar sun damu.”
“Oh kuma dai?”.
“Ai kasan dama irin wannan matsalar ba daga masu kayan bane masu sayarwar ne”.
A hankali ya ɗan furzar da iska da faɗin, “To duk yanda kukai dai?. Ya batun wancan aiki? Yaushe ne kuma shigowar taka?”
“Ai maybe ma na fasa, dan business ɗin bai faɗa ba har yanzu, kasan abinda ma lura da shi komai suna fara yinsa ne a tsare kafin su sakeshi a kasuwa, amma dai shi guy ɗin nan ya tabbatar min zai haɗani da ogan nasu saboda nace masa ni dila ne, sannan pharmacy ɗin nan ya kamata aikinmu ya fara ta kansu dan na sake zuwa da takardar nan still sun saida min jiya. Kaga tabbacin maganarka kenan ta fito”
“Hummm aina faɗa maka dama. Sai dai inaga kafin hakan ya kamata musan mai pharmacy ɗin. Sai Companyn da yafi kawo musu kaya. Dan ina son mu fara da mutuminka ne”
“Uhm wannan ma tunani ne mai ƙyau, sai dai kuma kamar abin zai mana wahala nake ga. Kasan fa kai ka fini dabaru ta irin waɗan nan fannin”.
Murmushi Smart yayi yana ɗan lumshe ido. Cikin ɗan furzar da iska yace, “Kaima zaka iya Ahmad. Ka nutsu na maka bayani, yaro zamu samar da zai nema aiki a wajen, ta silar yaron ma zamu samu abinda bamu hasaso ba ma. Plan a kenan, idan wannan zai ja mana lokaci plan b muja yaro ɗaya dake pharmacy ɗin a jiki, ta hanyar masa alkairi kasan dai yanda mutanenmu suka ɓaci da wannan karɓar na goran, a cikin biyun nan zamu dace da ɗaya”.
“Yess boss na fahimce ka, kuma tabbas wannan dabaran yayi, shiyyasa nake sonka”.
“Ɗan iska waye boss ɗin naka?”.
Dariya Ahmad ya sanya da faɗin, “Kai mana. Zanyi ƙoƙarin nan daga nan zuwa next week, Dan Cameroon ma nake son zuwa kawo shanun nan dai. Ya kamata ka shigo ayi harkar nan da kai ALLAH, dan na hango za'a samu alkairi a ciki.”
“ALLAH mutumina! Kaifa nasan baka wasa dama da harkar ƴan canji. Yanzu yaya za'ayi?”.
Cikin dariya ya ce, “Masheranci, kaima naga ai bawasan kake da su ba. Muyi magana kawai idan ka samu time, yanzu karna shiga lokacin Madam tana amaryarta. A huta lafiya tsohon ango”.
Kafin Smart yace wani abu ya yanke kiran. Ya ɗan lumshe ido da girgiza kansa yana furzar da iska. Yana ƙoƙarin cire bluetooth ɗin idonsa ya sauka akan Lulu ta mirror da ke kallonsa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣
.......Sai dai yana waigawa ta rufe idanun ita a dole barci take. Nasa idanun ya rufe da sakin guntun murmushi ya ƙarasa shiryawa ya miƙe. Wando yasa 3quater da ƴar riga armless yasa turare. Baice da ita komai ba ya fita domin duba mima zai bata taci ne duk da yasan halinta bawai ta damu da abinci bane. Ganin babu wani abinda zata iya so sai kawai yay mata order na gasashen kifi da abinda yasan zata iya so. Cikin abinda baifi mintuna ashirin da biyar ba aka danna bell ɗin gidan. Tashi yay zuwa ƙofar dan yasan abinda yay order ne aka kawo. Shi ɗinne kuwa. Mai kawo saƙo ɗin na ganin shine ya wani washe baki, cike da zumuɗi da farin ciki ya ce, “Smart Mawashi”.
Murmushi Smart yay masa. Shi kuma ya zaro wayarsa yace Please ya bashi dama suyi hoto ɗaya. Kai ya jinjina masa alamar babu damuwa. Ya gyara sukayi sai farin ciki yake yi. Shi kuma ya amsa kayan ya koma ciki. A falon ya ajiyesu ya nufi bedroom ɗin.....
*_NIGERIA_*
Kamar yanda ta saba a ƙarshen kowane wata take sake ƙulla silin zare ɗaya a jikin battar da malamin ya bata game da asirin da taima Smart da Lulu. Yau ma cikin nishaɗinta ta jawo battar hannunta riƙe da farin zaren kirtani tana ɗan raira waƙarta ta barmani coge alamar dai tana a cikin nishaɗi. Dan bayan Aunty Amarya da Ammah ta sanar mawa babu wanda yasan yau Lulu ta koma wajen mijinta a gidan.. Wani irin kwance-kwance ƙirjinta yay ya yanka lokacin da take jawo battar idanunta ƙyar akan zararrikan data ɗaura zube ƙasa a warware. Battar ta tukunyar ƙasa ƴar ƙarama ta wani tsage daga sama har ƙasa. Tana ɗagata ta rabe biyu tsokokin nama biyu da suka wani tsotse a waje guda tsire da allurai suka zube a ƙasa. Ƙara ta daddage ta fasa na tsananin fita hayyaci da tashin hankali batare data farga da ɓaranɓaramar da take neman yi ba. Su Huwaila dake falo suna kallone farkon shiga a ɗakin nata a gigice. Ganinta kwance wanwar a ƙasa babu numfashi ga wata ƴar tukunya-tukunyar tsafi zube a ƙasa harda allurai a jikin tsokar nama ya sasu suma fasa ƙararar data ankarar da su Ammah. Kusan a tare suka afko ɗakin tare da gayyar yaran gidan. Babu wanda idonsa bai gane masa wannan tarkacen tukunya ba idan ya shigo, har Abba da ya shigo a ƙarshe dalilin kiran da Salis yaje yay masa akan tarkacen ya fara sauke ido kafin Ummah dake kwance wanwar ana sheƙa mata ruwa amma babu alamar numfashi tattare da ita.
Wani irin harbawa ƙirjinsa yayi tare da jin kansa ya sara. Yana sake maida idonsa akan Ummah ya ga ta koma masa wata irin mummunar hallita. Da sauri ya kauda kansa yana mai ambaton sunan ALLAH. Yanda yay baya zai faɗi sai da Ammah ta tarosa tana faɗin, “Ya Salam Abbansu yi ahankali”.
Hannun Ammahn ya riƙe yana jujjuya mata kai, muryarsa na rawa ya ce, “Hafsat fiddani a ɗakin nan kaina zai fashe”.
Furucin Abba yasa gaba ɗaya hankalin sauran yaran da su Aunty Amarya dawowa kansa. Sai kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin halin da Abba ke a ciki. Amma mi abin mamaki yana fitowa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya da sakin kan. Kallonsa Ammah tai da faɗin, “Yaya dai Abbansu?”.
Kamar bashi ya gama cewa kansa kamar zai fashe ba ya ce, “Wlhy Hafsat kinji kuma ya saki kamar ba'ayi komai ba.” Sosai abin ya ɗaure kanta. Bata gama fita a mamaki ba kuma sai ga yaran na fitowa da ɗaɗɗaya hannayensu dafe da kansu. Wasu ma a guje suke faɗin, “Dodo! Dodo!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya gama rikicewa. Kowa ya fito a ɗakin Ummah, da kuma sun fito sai su jisu sakawai kamar an zare musu komai. Umma da hayaniyarsu ta sakata farfaɗowa cikin tashin hankali tabisu da kallo ganin yanda suke fita a guje. Ganin babu kowa sai taga damace ta sameta ta tattare kayan nan. Da sauri ta tattarasu jikinta na mazari ta ɗaure a ɗan kwali ta tura ƙarƙashin gadonta. Sannan ta fito cikin ƙarfin hali. Tana sakko ƙafarta waje yaran suka shiga yanka ihu suna kwasa da gudu zuwa ɗakunan iyayensu da faɗin, “Wayyo Umma ta zama dodo! Ummah ta zama dodo!”. Ba yaran kawai ba sai ga su Aunty Amarya suma duk sun rufta ɗakunansu. Abba ma har tuntuɓe yake na barin wajen sai Ammah ce ke kallonta da ambaton addu'oi a bakinta. Dan itama kam yanzu a wata irin mummunar siffa mara ƙyan gani tane kallon Ummahn. A nutse ta nufi nata ɗakin itama aka bar Umma ita ɗaya a tsakar gida cikin tashin hankali da mamaki. Sai kallon jikinta take taga minene sukema gudu amma bataga komai ba. A take jikin nata ya kama rawa. Ɗakinta ta koma ta jajibi waya tai kiran Hajiya Naqiba....
*_★UK★_*
Cikin mamaki Smart ke kallon Lulu da ta buɗe gasashen kifin ta maida ta rufe da sauri fuskarta a ɗan yamutse. Dan shi dai a sanin da yay mata tana son kifi sosai. Shi kam baya so, dan ko a yanzu haka dauriyar shaƙar ƙamshinsa kawai yake yi. Da farko yayi tunanin halin nata ne ya motsa, sai ya so ɗauke kansa. Amma ganin yanda ta tura baki da faɗin, “Nifa bana cin kifi yanzu” ya sakashi zuba mata idanunsan nan.
Cike da shagwaɓa ta ce, “Ni ka daina kallona da wannan idanun”. Ƙaramin murmushi yayi da janye idanun nasa, da kulawa ya furta, “Yaushe kika daina cin kifi kuma Madam?”.
Harararsa tai saboda Madam ɗin da ya kirata da shi, sai ya riƙe kunnuwansa alamar sorry. Mikewa tai tana ƙara tura bakin. Hannunta ya riƙo da sauri dan yasan kaɗan daga aikinta tace zata koma bedroom ɗin da da ƙyar ya samu ta fito. Saman cinyarsa ya zaunar da ita, cikin lallashi kamar wata ƴar yarinya ya ce, “Faɗa min yaushe kika daina cin kifi?”.
A ɗan tunzure ta ce, “Da cikin ɗanka”.
“Woow really?!”.
Kanta kawai ta jinjina masa da yunƙurin tashi ya hanata damar hakan yana dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Oh oh like father like son. Babie luv anya akwai wanda ya kaini sa'ar nasara a ƴakin ƙasa da ƙasa kuwa?”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa tana kallonsa a karo na farko. Gira ya ɗage mata tare da kwantar da kasa a kirjinta ya ce, “Aliyu ɗan Aliyu a suna. Aliyu ɗan Aliyu a kamanni. Aliyu ɗan Aliyu a hallaya. Ya kamata ki bani Award na gwarzon shekara ALLAH kuwa.”
Ƙoƙarin ture masa kai take ya riƙe hannun, cikin mamaki ta ce, “Wai dan ALLAH yaushe ka lalace haka Aliyu? Ko abinda zama cikin turawan ya koya maka kenan kai?”.
Idanunta da suka canja launi ya ɗago yana mata wani irin narkakken kallon da ya sanya jininta da tsigar jikinta yamutsawa a lokaci guda. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kece kika lalatani fa Mawaddatan'warahmah.”