Showing 57001 words to 60000 words out of 131687 words
Chapter 20 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
gama min hutu a wannan karon ban saki jiki da shi ba, bai damuba bai kuma daina kulani ba. Tun daga wannan lokacin naga Felix ya daina zuwa gidan. Ba irin tambayar da bamma Mah-mah ba sai tace min yayi tafiya ne mai nisa. Akwana a tashi na fara mantawa da Felix a zuciyata, sai wataran katsam gashi, a lokacin inada shekaru goma sha kusan uku, dan kaɗanne ya rage na ƙarasa tunda har secondary na shiga, duk da dai su kasan karatun nasu bawai kamar namu ne na Nigeria ba, shiyyasa ma na kammala karatuna da wuri gaba ɗaya a ƙarancin shekaru. Zuwa lokacin na manta da shi, shiyyasa ban wani sake masa ba, ga shi kuma na fara hankali. Yaso jana jikinsa amma sam naƙi sake masa, idan ma yazo gidan ko fitowa falo bana yi sam. Ni ban san ashe wannan abun naci masa rai ba har yanama Mah-mah korafi, takanyi dariya tace masa na girma ne yanzu na zama ƴammata na fara kuma mantawa da shi..
A wata ranar asabar Mah-mah ta wuce wajen ibadarsu sai ni kawai a gida da mai aikinmu. Ina ɗakina na baza books na makaranta ina dubawa, jikina daga ni sai ɗan bomshot da best, kaina ko ɗan kwali babu sai jin mutum nai kawai ya faɗo min. Raina ya ɓaci ganin Felix. Dan ko sanda inada ƙuruciya baya shigamin ɗaki ai, balle yanzu da a iyayin tashi cikin jar fata yake sakani jin na zama ƴammata ni da ƙawayena. Cikin masifa nace mizaisa ya shigo min ɗaki, ya fita bana son shirme. Maimakon ya fitan sai ya tsaya kawai yana kallona, dan gaskiya inada tsiwa sosai tun da ƙarancin shekaru na. Dariya ya shigayi irin ta shaƙiyanci, batare da ya damu da masifar da nake masan ba ya murzama ƙofa key ya nufoni. Da farko na ɗauki al'amarin nasa wasa, sai da naga yana yunƙurin rungumoni jikinsa ne raina ya ɓaci, duka na shiga kai masa ina janye jikina, ganin bazan bashi haɗin kai a yanda yake so ba ya kamani ya ɗaure, hankalina ya tabbatar min da yana son wulaƙantamin rayuwa ne. Ina kuka da roƙonsa da magiya amma bai sauraren ba ya ciremin kaya kaf shima ya cire nashi. Aliyu wlhy ban taɓa sanin minene tashin hankali ba sai a wannan ranar, tsabar tsoratar da nai da ganinsa babu sutura ban san na suma ba, sai da ya ɗiba ruwan sanyi a Despenser ɗin ɗakina ya sheƙamin na farfaɗo. Zaginsa na shigayi cikin matsanancin tashin hankali bayan dawowa a hayyacina ina tofa masa yawu a fuska, shiko ya shiga marina yana dariya, da yaga na ƙi daina zagin nasa marin ma bazai masa ba ya cire belt dinsa ya dinga dukana da ita, tamkar ya samu wata babbar mace yay min duka na hauka, har yanzu da sauran tabbunan dukan a jikina wasu basu ƙarasa ɓacewa ba. Ga jini a sayin inda ya bugeni, ga kumburin fuska data sha mari da fashewar baki, ga haɓo da dukan da yay min a gefen ido duk bai duba wannan ba ya nema haike min. Na riga na suma saboda firgita dan ya na gab da cimma burinsa na suman, shiyyasa ban san yanda akai Mah-mah ta samu nasarar shigowa ɗakin ba, ita ce ta kuɓutar dani batare da ya samu nasara a kaina ba. Kiciniyar kwanceni da dukan da yake mata ya sani farfaɗowa, sai dai kafin ta ƙarasa kwanceni ya kaita ƙasa da duka itama. Ina kuka da zaginsa a saman lips dan ko magana bana iyayi dan wahala ya kekketa mata suturar jikinta ya ɗaureta kamar yanda ya mun, a gaban idona ya keta mata mutuncinta ta hanyar mummunan fyaɗe, ya kuma juyata ta baya nan ma ya wulaƙantata. Suma ta biyu ko a lokacin dan tashin hankali. Ban taɓa sanin ana suma a dawo a suma a dawo ba sai a wannan ranar. Kaina ya dawo yana wata ƴar iskar dariya da tabbatar min sai ya wulaƙanta min rayuwa fiye da yanda yay ma Mah-mah dake kwance cikin jini face-face bata ko numfashi sosai. Ban san yanda akai wani irin ƙarfi yazo min ba na halbesa da ƙafata a gabansa, azaba ta sakashi duƙewa, pen ɗina da nake aiki da shi kafin shigowarsa na ɗauka na buga masa a wuya, banyi tunanin zai iya mutuwa ba, a haukana hakan da zan masa ai zai tashi idan aka kaisa asibiti kamar yanda naga a film yana faruwa. A take ya saki razananniyar ƙara da zubewa a ƙasa hannunsa ɗaya riƙe da gabansa ɗaya ya riƙe wuyansa. Dai-dai nan mai aikinmu ta shigo, ashe matsiyacin aikenta yay kasuwa dan ya samu damar min illa ALLAH ya kawo Mah-mah ta dawo gidan. Ihunsa ya sata shigowa, koda ta shigo taga a yanda muke mu duka ukun sai itama ta fasa ihu da komawa da gudu, itace tai kiran ƴan sanda, abinka da inda akasan kimar ɗan adam, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu sun iso, a gaggauce aka tattaramu duka zuwa asibiti muduka ukun. Ban dawo a yahhacina ba sai bayan kwana biyu, a hakan ma ko yaya namiji yazo kusa dani na dinga firgita kenan harda ihu ina roƙon karya cutar dani, duk wanda ya ganni sai ya tausaya min sosai. Ashe nawa wasane, dan Mah-mah ita gaba ɗaya ma brain ɗinta ta birkice, ga wata irin jijjiga da jikinta keyi, a taƙaice dai kamar ta haukace ma kawai..... Felix Kuwa ashe abinda nai masa ya mutu. Ƴan uwansa sunce bazasu yarda ba tunda kashesa akayi, wannan dalilin ne ya saka aka maida hankali akan bama Mah-mah kulawa harta ɗan dawo hayyacinta, an tattara case zuwa kotu. Daddy bai zo ba, Uncle Yousuf bai zo ba har sai da muka samu kusan sati uku a asibitin, zuwa lokacin an miƙa case kotu har an ajiye ranar zaman shari'a. Ana gobe fara shari'ar Daddy ya iso Germany, ya shiga matsanancin tashin hankali da ɓacin rai akan abinda Felix ya aikata, a ranar bai zauna ba sai da ya samo ƙwararren lawyer, washe gari aka shiga kotu. Mah-mah, bata wani bari shari'ar ta ɗauki lokaci ba ta ce itace ta kashe Felix saboda yayi mata fyaɗe ta ƙarfi. Duk yanda naso faɗar gaskiyar abinda ya faru bani da dama saboda tun a daren jiya ta roƙeni akan kar nace komai, na rufa mata asiri kar Daddy yasan ni Felix ya fara hara, dan hakan zaisa ya kalli rainon da tai min a matsayin sakaci, koma ya ɗauka dama a haka take sakaci da al'amarina tun can baya. Kawai idan anje kotu zatace a wajen cetonta ne Felix yay min wanna dukan. Yanda ta tsara ɗin haka ta faɗa a kotu, bayan gama saurarenta da lawyer da dangin Felix suka kawo alƙali ya yanke hukunci, wannan yanke hukunci ne ya sake birkita ƙwaƙwalwar Mah-mah take a wajen ta shiga wani yanayi irin na masu taɓin hankali sosai, a gaggauce aka maida ta asibiti kamar yanda alƙali ya bada umarni, hakan bai wa dangin Felix daɗi ba, dan ba haka suka so ba, sai dai babu yanda zasuyi. Sashin masu taɓin ƙwaƙwalwa aka kaita, ana kula da ita yanda ya kamata bisa tsayawar Daddy. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa game da halin da ya ga Mah-mah ta shiga ciki, sai dai rashin sanin yanda abin ya faru yasa shi bai yi tunanin da yanzu fa akaina abin zai faru ba, tunda Felix ni yaso ketama mutunci ba, ya ɗauka kawai wajen son ceton Mah-mah ɗin nawa ne kamar yanda ta faɗa na samu wannan mahaukacin dukan, wai dan ma na samu sauƙi sosai a lokacin. Kwanan Daddy uku da zuwa Germany Mah-mah ɗina ta mutu, ta bar duniya tana kuka da sunana bakinta....”
Kuka ne yaci ƙarfin Lulu, ta sake ƙanƙame Smart da tun ɗazun idanunsa sun kaɗa sunyi jazur alamar yana kukan zuci ne. Sake ƙanƙameta yay shima jikinsa na wata irin tsuma, ji yake kamar zuciyarsa zata fashe, kukanta na sukar masa zuciya da ruhi. Tayi kuka sosai kafin ta cigaba da faɗin, “Wannan al'amari shine sanadin barowata Germany, na fahimci Daddy kamar yana tsoron maidani Nigeria ne a wannan halin saboda su Uncle You, ya maidani U.S, in da aka sake sama min sabuwar Nanny sai dai baƙar fata ce, asibiti aka sake kwantar da ni a can farko dan nima dai ina abu tamkar brain ɗin nawa ya taɓu. Na samu tsahon lokaci ina ganin likita kafin na ɗan rage firgita har Daddy ya saka ni a makaranta. Wannan shine ƙalubale na biyu, sannan sanadin abubuwa da yawa na rayuwata. Na ƙudiri niyyar yin karatu tuƙuru na zama lawyer domin kai ƙarshen irin masu halayyar Felix. Sannan kuma na kasa sakin jiki da kowa a yanzu ciki harda sabuwar Nanny ta. Banda aiki sai kuka, zaman ɗaki, a class bana shiga sabgar kowa. In har babu malami ma ina daga can gefe a takure. Duk yanda Daddy daya kasa tafiya ya barni ke lallaɓani da jana a jiki na kasa sakewa, depression yay min tasiri matuƙa. Wannan yanayin nawa ne ya jawo hankalin Alice da Luna gareni, tun bana kulasu har na ɗan fara amsa musu magana, ba komai ya jawo hakan ba sai ganin suna maida hankali a karatunsu, sannan suna nuna min suma suna cikin damuwa amma suna magance damuwarsu da wasu abubuwa shiyyasa ba'a ganewa........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣
........A hankali suka cigaba da shiga jikina da nuna kulawa har takai na amshi maganin da suke yawan kwaɗaitamun na sha wai zai min maganin damuwata, wannan shine sanadin komai, domin kuwa a randa na sha na farkon sai na fahimci na samu sassaucin damuwata, har takai bana iya tuna komai na wani ɗan lokaci, da ga haka aka fara, a hankali, a hankali al'amarin ya fara tasiri har aka farga damu. Malamai sun tsawata mana, saboda shekarunmu sunyi ƙaranci da shaye-shaye, sai dai babu alamar zamujisu, daga ƙarshe suka nema iyayenmu. Nanny na ce taje, amma koda muka dawo gida na tabbatar mata idan ta bari Daddy na ko Uncle You suka sani a bakin aikinta. Tasan zan iya, kuma Daddy na jin maganata, ga shi kuma ina nuna bana sonta dama. Dan haka taja bakinta tai shiru. Ni kuma sai na ɗauki matakin daina shan komai sai da dare, kafin safiya ya sakeni. Sai a week end ne nake sha da rana, wataran a gidan su Luna wataran gidan su Alice anan gidan dai bana taɓa yarda suzo ma balle musha wani ya gane, sai takai har week end ina zuwa gidajen su Alice da Luna. Sai da Daddy ya farga ne hankalinsa ya tashi, yayma Nanny na tas da tabbatar mata in fa har bata kula da aikinta ba zai sallameta. Ni kuma ya rufe ido yamun tas da faɗa dan ya fahimci na fara wasa da karatu, ya kuma haɗani da Uncle You shima yay nashi. Har lokacin babu ruwana da ko mazan ajinmu, ƙawayena biyun nan dai sune Luna da Alice. Faɗan da su Daddy sukai min ne ya dawo dani hankalina akan karatu sosai, sai kuma burin dake raina shima na ƙaramin himmar hakan matuƙa har muka kammala karatun. Mun samu damar shiga jami'a ni su Alice kamar yanda muka tsara, hakan ya sake bamu lasisin cigaba da shaye-shayen mu da yawon clubs. Sai dai inata taka tsantsan ta yanda babu wanda ke fahimtata har lokacin. Kula maza da su Luna suka fara ne ya fara sakamu fara samun matsala, sunyi-sunyi suja ra'ayina akan hakan amma ya gagara, sai ma saɓani da muka fara samu da su. Akwai wani yaro a depertment namu da ya takura min, duk da bashi kaɗai bane sauran dana karta musu rashin mutunci sukan kama kansu. Shiko naci yaƙi ya barni na samu sakat, har takai ya fara shiga jikin su Luna domin su shawo masa kaina. Amma hakan ya gagara. Ganin bazai samu nasara ba suka haɗa baki da shi aka bugar da ni, matsalar da aka samu ni ba komai ke sani buguwa irin ta galabaita ba, mukan sha abu tare da su su fita a hayyacinsu sosai amma ni ina normal sai dai ɗan yanayi, wannan yasa na fahimci manufarsu a kaina. Wannan shine sanadin daya sa na karta musu rashin mutunci irin wanda basu san zan iya ba, na kuma rabu da su dan su basu san nai mugun tsanar maza irin haka ba. Bayan rabuwa da su nasa Daddy ya canja min makaranta, naso barin shaye-shaye a lokacin sai dai hakan ya gagara dan ya shiga jikina matuƙa, sai dai ina kiyaye duk wani yanayin da wani zai iya fahimtar halin da nake a ciki, zuwa lokacin bani da Nanny, sai masu aiki, sai kuma wata yarinya da aka kawo da ga Ghana wai ɗiyar abokin Daddy ce tazo karatu. Babu ruwana da ita dan ko harakar ta bana shiga, sai mu kwashe sati biyu ban mata magana ba, koda tamun ma sai ma gadama nake amsawa. Duk ina mata wannan abunne saboda tsanar ƙawaye da nayi, bama na son ta shiga jikina da har zamuyi shaƙuwar da zata kaimu ga wani matakin kuma, sannan bana son ta san ina shaye-shaye. A haka na gama karatu da ƙyar, dan a wasu lokutan sai nayi kamar zan ɓaras saboda yanayin da nake ciki sai kuma dai na dawo hankalina da ƙyar na maida hankali. Alhamdullah na samu result mai ƙyau saboda inada kaifin basira, kuma na saka zuciyata ga abin. Na yi wasu courses da ban da ban da suka shafi karatuna har na tsawon shekara ɗaya da wasu watanni, da kaina na ce zan dawo Nigeria nayi service, dan haka kawai nake jin kewar asalina, na dawo Nigeria a tsagerata, dan bana iya ragama kowa sai Daddy Uncle Yousuf, Mommy ma rashin ɗaukar halina yasa nake shakkarta, Aunty Saliha da Aunty Naja'atu kuwa soyayyar da suka nuna min da kulawa tasani jin ƙaunarsu a lokaci guda. Dan naje Abuja ne gidan Uncle Khamil nai hidimar ƙasa ta, sai kakata Dada dake nuna min soyayya irin ta uwa, tana mun gata sosai da yimin duk abinda nake so. Case ɗin wata yarinya akan fyaɗe ne ya zama sanadin fara aikinna a Nigeria, raina ya ɓaci da abinda ya faru, har takai Aunty Naja'atu na sanar min ai wannan ba komai bane da ga cikin tarin cases na fyaɗe a Nigeria. Musamman ma a yankinmu dan gwara nan Abuja akwai wayewar kan da iyaye basa bari. Amma tacan wajen gida akan rufe zancen wai dan kada yarinya ta rasa miji ko ahalinta su tozarta sai dai iyayen baƙin ciki ya kashesu, itako ta ƙare rayuwarta a cikin ƙunci da baƙin ciki. Wannan al'amari ya tayar min da hankali sosai, sai ko na ɗauki ɗammarar zama kan ƙafafuna domin hana samuwar irin waɗan nan mata tasiri, da kuma kai duk wani shegen daya ce shi mace ce abar wulaƙantawarsa ta hanyar fyaɗe prison ya ƙare rayuwarsa acan ko ƙuruciyarsa.. Wannan shine jiyan na Aliyu. Banda baƙin ciki da takaici mi kaji a cikinsa? Babu wani abun birgewa ko ƙayatarwa”
Smart ya kasa magana, sai kukan zuci kawai, a ransa yana auna tsakanin Lulu da mahaifinta waye yafi wani zama a ƙalubale?. Sai dai duk da haka tabbas Daddy yayi sakaci da al'amarin ta, dolene a faɗi hakan, amma tunda har ya amsa laifinsa da tabbatar da kuskurensa shikenan. Lallai a yau ya koya darasin rayuwa a labarin Daddy da Mawaddat, bai taɓa tunanin ko hasashen za'a iya samun wanɗan nan al'amuran ba masu gogayya da juna. Sai dai shi fa har yanzu zuciyarsa na bashi dole akwai hannun Sulaiman akan al'amarin Lulu. Daddy bai farga bane a wannan gaɓar saboda yarda da kansa da yayi na ganin tako ina, ta kowanne motsi yana dabaibaye da al'amarin Sulaiman ɗin, ko kuma dama ya riga ya gama shirya hakan kafin shi Daddyn ya fara nashi shirin. Ya kuma haɗa da wannan itace ƙaddararta babu wata dabara ko tsaro da zai hana hakan. Duk da kuɓutar da itan da Daddy yayi hakan bai hanata fuskantar ƙaddararta da yake gudan mata a inda aka haife ta ba. UBANGIJI kenan, gagara misalin masu misali. Shi kaɗaine masanin gaibu a zahiri da baɗinin rayuwa.... Sai da ya firzar da nannauyar iskar bakinsa a kusan karo uku sannan ya ɗago Lulu da ke hawaye har yanzu a jikinsa a hankali. Sosai idanunta sun kumbura abin tausayi. Nasa juyayyun idanun ya zuba mata, tare da riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa duk ya fara goge mata hawayenta da babban yatsun sa da faɗin, “Kalleni” cikin sarƙewar muryarsa da ke nuna tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki.
A hankali ta ɗago nata Lulu idanun ta saka cikin nashi, a take gabanta yay wata irin masifar faɗuwa. Kanta ya sara. Yanayin da take jin kanta da jikinta tun a jiya ya shiga sake zafafa gudanar jinin jikinta da motsin numfashinta. Shi kam Murmushi mai sanyi ya sakar mata batare da ya fahimci halin da take ciki ba. Cikin ƙanƙanin lokaci kamaninsa suka juye mata zuwa wani abu daban kamar a mafarki. Baya taja jikinta daya fara ƴar rawa-rawa da sauri. Cikin mamaki Smart ke kallonta, kafin ya iya cewa wani abu a bazata kawai ta fasa wata iriyar gigitacciyar ƙara da ta saka su Daddy dake ƙofa na saurarensu shi da Uncle Yousuf shigowa a firgice. Hatta Abbah da Ammah da Mamy ma a ruɗe suka iso ɗakin. Riƙetan da Smart yayi sai take neman sume masa ma. Al'amarin ya bama kowa