Showing 81001 words to 84000 words out of 131687 words

Chapter 28 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt

09 Dec 2024

7884

Dodo!! Wayyo dodo!!.”
Umma da ke zubama hajiya Naqiba ruwa tana kuka dan ganin abin da bana lafiya bane ta zabura jin aminiyar tata ta sake fasa gigitacciyar ƙara. Dan tana farfaɗowa taci karo da ita a kanta. Yin ƙurin da zatai domin ceton ranta ƙafa ta gurɗe jikake ɓass kamar an ɓalla katako ba ƙashi ba. Sai ta sake zubewa a ƙasa cikin wata irin wahalalliyar ƙarar azaba ta sake sumeya. Duk da abinda ke faruwa kaf ƴan gidan na maƙale ta windows suna kallo har ƴaƴanta da suka rarrabu. Wasu a ɗakin Ammah wasu na Mama. Ita dama aunty amarya da yaranta ɗakin Ammah suka afka suma. Ammah da al'amarin ya jijjiga ma zuciya na zaune a kujera tana cuɗawa da kwancewa. Dan in har lissafinta yayi dai-dai ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya fa a wannan karon. Tukunyar da suka gani tarwatse a tsakar ɗakin Ummah itace asirin da taima su Aliyu matarsa ke ganinsa da mummunan siffa irin wadda suke ganin Umma da ita a yanzun. Abba ne yay hikimar kiran yaranta na ma'auri da su Salim yace suzo babu lafiya. Dan shikam yama rasa ina zai kama a wannan lamari. A yau dai ya sake tabbatarwa Umma na bin bokayen tsubbu, kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya mai kamanceceniya da juna akan al'amarin Aliyu da matarsa da wanda Umma ke'a ciki yanzu. Yau matar Aliyu ta koma wajen mijinta, hakan na nufin komai ya daidaita tsakaninsu asirin ya dawo inda aka aikashi. Dama ai sharri ɗan aike ne, idan ya isar da saƙonka sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Har zai kira Smart sai kuma ya fasa cikin girgiza kai dan a yanzu ya tabbatar dare ne a UK.
Yaran nata ma koda suka iso duk wanda yay tozali da Umma sai gudun ceton rai. Umma ta fashe da kuka da tun ɗazun take irinsa har muryarta ta dishe. Ga aminiyarta kwance ƙafa sai kumbura take kowa ya kasa zuwa a taimaka mata saboda Umma da ke a wajen. Al'amarin dai sam babu daɗi, Umma na cikin tashin hankali fiye da wanda al'umma ke ciki akan ganinta a mummunar halittar da kowa ke ganinta. Ita kuma lafiya Lau take kallon kanta, dan har ɗaki ta nufa ganin kanta a madubi babu wata damuwa ko tawaya tattare da halittar ta sai fuskarta datai kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka ɗauke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi masifar kumbura damm abin zattashin hankali......




*_UK_*



Wahala iya wahala Lulu tasha a wannan dare hannun Smart. Dan zata iya rantsewa ita kam bata ga banbancin sa da daren farkonsu ba, kodan ta saka ma ranta tsoron al'amarin ne oho. Amma tabbas ko a yarda da ita ko kar a yarda Smart namijin gaske ne da ko'a cikin mazan ma zai iya amsa sunan mazaje ne. Sai dai bata sani ba ko ragwantakarta yasa take masa irin wannan kallon ko kuma dan shi ta sani bata san sirrin sauran mazan ba.
Shi kansa sai da ya koma tausayinta, dan magana ta gaskiya fa bai raga mata ba, wahalarsa ta kusan shera ɗaya da wasu watanni sai da ya fanshe abinsa tsaff. Sai dai kuma shi a karan kansa bashi da zaɓin da ya wuce hakan. Bai sani ba ko tsananin begenta da yake a cikine ya sashi jin yau ɗin babu bambanci da wancan daren da ya kasa goguwa a zuciyarsa, amma ako ina kam zaiyi alfahari da baiwa irin ta matar tasa. Dan a wancan dare shima sabo yake, yau kam ya banbance tsakanin aya da tsakkuwa. Ya kuma zaɓi yimata mai gana ɗaya ne dan cire mata tsoron nan da ya lura yay mata tasiri. (Humm gyaran su iya Tabawa bai faɗi a banza ba kenan🥱🤣🚴).
Langyare iya langyare, raki iya raki yasha shi. Kuka kam muryarta har bata fita. Tun ana bashi haƙuri da roko da magiya har dai aka koma kiransa mugu. Yaƙushi da cizo duk ya samu rabonsa kafin duk wani ƙarfinta na neman ceton kai ya ƙare ta koma zallar hawaye da jiran mala'ikan mutuwa (acewarta🥱😜😂).
Shi ya fara farkawa lokacin da alerm ɗin da ke tadashi sallar asuba ya kaɗa. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da ke jingim da barci dan basu wani jima da kwanciyar ba. Hannu ya kai ya kashe alerm ɗin gudun kar AA ya tashi shima. Tunda ALLAH ya taimakesa dai har ya gama bidirinsa na daren jiyan yaron bai farka ba. Idannunsa ya zubama fuskar Lulu dake barci kamar a wahale, shi sai ma ta bashi dariya, dan haka ya ɗan murmusa da kai hannu ya shafa fuskar tata. Baki fal tsiwa da rashin ragiya amma sai tosoro da ragwantaka uwa farar kura. Ɗumin da yaji a fuskarta ya sashi jan bargon kaɗan yasa hannunsa a wunyanta. Zazzaɓine sosai a jikin nata kam kamar yanda yaji. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe da sumbatar goshinta yana sake matseta a jikin nasa cike da tausayawa.
“I'm so sorry Final Choice. Aliyu bazai sake baki wahala ba da ga yau kinji”. Ya sake kai mata sumba a saman hanci yana mai sake jinta sama can ƙololuwa a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya samu ta tashi sai faman langyare take masa da kukan shagwaɓa. Shi dai biye mata yake yana binta da lallashi. Dan ko a wancan karo na farko ba'ai masa wannan langwai ɗin ba. Koda yake wancan ana bori yaushe ma ya samu kanta. Dan haka yau kam ya ƙudiri aniyar rama mata dukkan tattalin da bata bashi damar yimata a waccan ranar ba. Yanzun ma taimaka mata yay ta sake ɗan gaggasa jikinta, duk da dai yasan taimakon da yay mata jiya kawai ya wadatar, yasan kam harda raki da ragwantaka dai koma yace shagwaɓa. Shine ya jasu salla yanzu ma, suna idarwa ya miƙe ya fita, bai jima ba ya dawo ɗauke da kofin tea da soyayyen ƙwai. Da ƙyar ya samu ta sha tea ɗin, kwan ko bata ko kallesa ba balle ta ci, sai maidashi yayi. box ɗin magungunan sa ya ɗauko ya bata na zazzaɓi tasha da rage raɗaɗi. Sai da ya ga ta sake komawa barci ya sauke ajiyar zuciya. Yasan koyaushe AA zai iya tashi shima, dan haka ya haƙura da fita ko'ina motsa jiki ya ɗan yi a gida. Ilai ko bai jima da farawar ba AA ya farka. Rarrafawa yay kan Lulu yana kuka. Hakan ya sakata farkawa. Harararsa tayi, itama kamar zata saki kukan ta ce, “Ni bazaku kasheni ba kai da ubanka wlhy. Kai tayi idan ya jika yazo ku ƙarata”.
Kaf a kunnen Smart dake shigowa, dan haka ya saki murmushi yana ƙarasowa ciki. Tana jin motsinsa ta maida idonta ta rufe kamar barci take. Nanma murmushi yayi kawai da ɗaukar AA dake neman yimasa ƙiwa kamar jiya. Tsaff yama yaron wanka duk da dai da ƙyar akasha, dan sau kusan biyu yana neman suɓuce masa ALLAH dai ya kiyaye baisha ƙasa ba. Ganin kamar yunwa yaron keji yay zaman fara bashi tea da dama ya haɗo ya ajiye tun ɗazun kafin ya shiryashi yana nishi da ƙyar dan bai iyaba. Pampa's ma da ƙyar aka iya sawa sai da ya duba a net.. yaga yanda akeyi. Duk kuma abinda sukeyi Lulu na kallonsu dariya kamar ta kasheta amma ta zaɓi yin likimo wai ya ɗanɗana yaji shima idan da daɗi. Shiko a zatonsa barci takeyi, sai da ta kasa riƙe dariyarta dai tayi sannan ya farga idanunta biyu. Cikin kalar tausayi yake kallonta da faɗin, “Yanzu nan idonki biyu aketa wannan dambarwar amma babu ko taimako Baby luv?”.
“Ku ƙarata nima ta kaina nake”. Ta faɗa tana masa gwalo da jan bargo ta rufe har kanta. “Haka kikace ko? Ba komai zamu rama ne ai”. Bata sake magana ba tai luf a bargo abinta tana dariya har suka kammala ya hawo gadon da yaron yana sauke numfashi ɗaɗɗaya. Sauka da ga jikinsa AA yay zai haye kan Lulu ya riƙoshi yana faɗin, “A'a Sweet heart abar Momy ta huta kaga Papa ya koya mata karatu duk ta jikata”.
“Yaushe ka koyamin karatun?”. Lulu da bata fahimci inda ya dosa ba ta faɗa tana buɗe kanta da sauri harara idonta kamar zai faɗo. Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya ya ce, “Yanzu ma malamin a shirye yake in har za'a barsa ya ƙara ɗora sabon darasi”. Yanzu ne ta farga da inda zancensa yaya dosa. Bargon taja ta sake rufe kanta da faɗin, “ALLAH dai ya shiryeka Aliyu. Ni kutashi ku fita barci nake son yi kun daman”.
“Amin ya rabbi tunda addu'a aka min. Amma fa babu inda zamuje muna nan tare da ke”.
“To ku koma ƙasan carpet kun ishan ALLAH”.
“Anƙi ɗin”.
Harararsa tai shi da ɗan nasa ta matsa can ƙarshen gado ta sake jan bargo dan da gaske jikinta ciwo yake mata sosai, ga zazzaɓi. Murmushi yayi da binta da kallo, dan yasan da gaske bata da lafiyar, yana mata hakane danta saki jikinta dai ne kawai. Wasa ya cigaba da yima AA dake son shi kawai a saukesa yayi ɓarna, sai da ya tabbatar tayi barci ya ɗan janye mata bargon da ga kan fuska danta samu iska. Goshinta ya taɓa yaji da ɗan sauƙin zafin, sai kuma ya maida kan wuyanta. Shima dai alhmdllh ya fara sauka. Sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciya........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣




______________




*3 DAYS CLASS*


Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni


Class ze fara ranar jumaa insha Allah


WhatsApp group 👇👇👇


https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA


WhatsApp 08144147273


👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Maxico Tour visa 1 month


_______________




........Kuka take sosai a gaban mijin nata da ayanzu al'amuransa ke bata tsoro matuƙa. Gaba ɗaya ya sauya mata, sauyawa irin wadda bata taɓa zato ko tsammani ba. Kai koda a mafarki ko lissafin rayuwa bata taɓa tunanin itada Sufiyanun nata zasu kasance a irin wannan ajin ba. Amma a yau sai gashi wai harda mata kishiya sa'ar jikokinta da wannan shekarun nata tsofai-tsofai. Kuma ko kunyarta baya ji yake soyayyarsa kamar wani ƙaramin yaro.
Baba Garko da tunda ta shigo ta zauna bai ko ɗaga kai ya dubeta ba sai ma wayoyinsa da yake hankali kwance. Daya gama wannan zakaga wata ta shigo. Cikin jin gundura da kukan da take rera masa ya ce, “Amma dai kin san kina damuna ko? Please bana son damuwa idan kukanki zakiyi zaki iya bani waje”.
Sake ɓarkewa tai da sabon kuka kamar wata ƙaramar yarinya. A dai-dai nan akai knocking ƙofar falon, ɗan jimmm yay yana kallon ƙofar kafin ya ce, “Ko waye ya shigo”. Mai aikin amaryarsa ce ta shigo a rikice, amma hakan bai hanata kaiwa tsugunne da ga bakin ƙofa ba ta gaisheshi cikin girmamawa sannan ta ɗora da faɗin, “Alhaji aunty amarya ce bata da lafiya, tun ɗazun kuma ta hana azo a sanar mak...” ai mai aikin ma bata ƙarasa rufe baki ba ya miƙe zaram ko nauyin tsufarsa baya ji. Ƙofar ya nufa a hanzarce, Dada da kanta ya nema tarwatsewa ta bisa da kallo galala, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na sake turniƙe mata zuciya. Ba'a ko rufa minti huɗu ba sai gashi ya shigo a rikice, ko kallon inda take baiyi ba ya shige bedroom ɗinsa. Cikin ƴan sakanni ya sake fitowa ya fice hannunsa riƙe da key ɗin mota ya canja zuwa jallabiya. Kasa motsawa tayi a wajen har sai da taji ƴar hayaniya na tashi ta miƙe jikinta na rawar ɓacin rai ta leƙa ta window. Akan Baba garko da ke rungume da amaryarsa ita kuma tana faman yarfe hannu tana kuka idanunta suka fara sauka. A take zuciyarta ta ayyana mata haihuwa. Sake dugunzuma zuciyarta tayi har tana jin jiri na neman kwasarta, batama san sanda ta sulale a wajen ba ta zube saman kujera jaɓar wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, sai kuma ta ɓarke da kuka. Tunda take a rayuwarta, bata taɓa shiga matsanancin baƙin ciki da tashin hankali irin na wannan gaɓar ba. A tsahon rayuwar ƙuruciyarta ko firar kishiya bata so, kai ko ƙawa ko cikin ƴan uwa akaima wata kishiya daina zuwa gidan mutum take saboda yanda ta tsani kishiya. Amma a yau sai gata da ita a wannan shekarun nata, harma da ciki na haihuwa.....


(🤣🤣🤣🤣🤣 Kar kuce dariyar mugunta nakema Dadaras😜)


____________★


Tun Ummah na ɗaukar al'amarin ta ƙarami harta fahimci ya wuce da saninta. Kuka ma da hawaye yanzu ta kasa yinsa. Ƴan gidansu sunzo sai dai me suma ƙarewa sukai da fita da gudu harda masu faɗuwa. Wajen Abba suka koma kowa na maida numfashi, yayanta cikin damuwa ya ce, “Anya ba aljanune suka shigi Yahanasu ba Yaya Mika'il”.
Cikin ɗan taɓe baki Abba yace, “Idan ma sune wajen biɗar baƙar tambayarta ta kwaso su. Ballema bana jin hakanne. Nafi ƙyautata zaton ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Ni yanzu jibirin ban san yanda zanyi da wannan matar ba. Gaba ɗaya ta firgitamin iyali sun kasa sakewa kowa sai zaman ɗaki”.
Cikin damuwa Jibirin yace, “Amma yaya bai kamata kace haka ba. Ƙilama cikin matanka wata taimata haka kasan dai mata akan kishi”.
“Wane matan nawa? A'a ƙarya haramun. Ai duk cikin iyalina babu fanɗararre irin Yaha. Nasan halin kowacce a cikinsu da abinda zata iya. Na jima ina zarginta dama da shigen-shigen nan kawai dai ban taɓa gani da idona bane shiyyasa ban kafa hujja ba. Amma a yanzu na gama fahimtar komai. Ko wannan halin da kaga tana cikin sihirin da taima Aliyu da matarsa ne ya dawo mata...”
“Aliyu kuma Yaya? Aliyu Aliyu dai namu na nan?”.
“Shi ɗin fa”.
“Ikon ALLAH! To shi Aliyu dake matsayin ɗanta kuma zatama asiri. Miye ribarta kenan?”.
“Oho mata, ita ta sani”.
Sosai al'amarin ya girmi kan kowa. Cikin ƙarfin hali Zaidu ya bada shawaran to ko za'a samo malamai suyi addu'a ne. Dan wannan yanayin nata abin tashin hankali ne ga kowa tunda gashi hankalin kowa a tashe, shi wlhy yanzu haka baya jin yau ɗin nan zai iya barci lafiya saboda ganin wannan mummunar halitta da Ummah ta koma. Abba dai yace shi babu ko sisinsa a nema mata lafiya. Hasalima ya kirasu ne su wuce da ita dan bazai iya ba. Hankalinsu ya tashi matuƙa, dan sukam bazasu jajibi wannan halittar ba sukai cikin iyalinsu suna zaune ƙalau. Dan haka suka dage bashi haƙuri da roƙo da magiyar ya barta a ɗakinta cikin ƴaƴanta harta samu lafiya sai aji dalilinta na wannan mummunan al'amari, idan ma matakin sai ɗauka sai ya ɗauka. Anfi ƙarfin Abba ne kawai, dan haka yay shiru. Su suka fita suka zo da malamai, da ga tsakar gida suka tsaya aka kwala mata kira ta fito. Su kansu malaman sai da suka zabura da ganin mummunar halittar dake tunkarasu, ganin tana yo kansu gadan-gadan sukaji fa dauriya ba tasu bace. Ai tuni suka dafe kawuna kowa ya ara cikin ta kare yana jan kula'uzai. Bayan su an sake kawo wasu malaman amma fa kowa yazo yana tozali da Umma sai dai a tsincesa waje ya dafe ƙeya. Al'amari kamar wasa sai ƙara faɗi yake. Dan takai ƴan jarida daga gidajen rediyo har sun fara zuwa neman labari. Sai dai suma fa suna shigowa sukai ido huɗu da Umma labarin bai ɗaukuwa garesu sai ƴar reren gudu...
Tsabar tashin hankali da hawan jini Umma ta koma ko gani batayi da ƙyau. Barci kuwa ya ƙauracema idanunta gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai wata irin muguwar rama mai ban tsoro. Babu abinda ke ɗaga mata hankali sai ganin ƴaƴanta suma gudunta suke da mijinta da ta ɓata tsahon shekarun rayuwarta tana faɗa da faɗi tashi a kansa. tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login