Showing 33001 words to 36000 words out of 131687 words
Chapter 12 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
sakata kuka rurus, agaban ƴaƴan nata ya kuma turketa saita gaya masa inda suka kai Lulu koya bata mamaki da hukuncin da bata taɓa zato ba. Ganinfa ruwa ya ƙarema ɗan kada dole Dada ta fayyace komai game da kai Lulu Canada ita da Alh. Sulaiman harma da yunƙurin zubar mata da ciki da sukayi amma bai fitaba sai da ga bayan nan kuma suka gane hakan, sai kuma kiran da Sulaiman yay mata a jiya cewar ya nema su Lulu ya rasa wai wani ya sacesu, amma yasa ƴan sanda na bincike. A yau da safe kuma yake turo mata text message akan yana zargin Yousuf ne da Smart. Da matuƙar mamaki Uncle Yousuf ke kallonta cikin nuna kansa ya ce, “Ni Yousuf ɗin ko wa?”.
“Inba kaiba waye Yousuf anan, munafuki algungumi. Ai dama kana biye damu tunda muka ɗauke ta kai da shegen yaron nan mara kunya dan bakinku ɗaya ne dama. Dan haka saiku fito da ita tunda ankai ga yanda kake so”.
Tuni fa falo ya hargitse, dan sai kawuna kuma suka nema rabuwa. Yayinda Daddy da tunda ya shigo falon baice komai ba ya zuba musu ido kawai. Hakama Baba Garko. Cikin ɓacin ran yin shirun Daddy Uncle Yousuf ya tashi ya fice a falon dan zuciyar ƴan maza ta motsa da gaske a yau. Ganin bazasuyi shiru ba Baba Garko ya katse hayaniyar tasu da faɗin, “Hajarah kije na sakeki saki biyu, kuma ki barmin gidana a yau har sai kun maido Mawaddat idan da yiwuwar ki dawo sai ki dawo”.
Waɗan nan kalmomi masu dukan zukata na Baba Garko ne suka saka falon yin tsitt, yayinda ya miƙe abinda ya shige cikin bedroom ko waiwayen su bai yi ba. Dada kam da taji kanta na juya mata sai ganinta kawai sukai a ƙasa babu numfashi. Cikin tashin hankali sukai kanta. Duk hayaniyar da ake Baba na jinsu amma har suka kwasheta zuwa asibiti bai ki leƙo ba.
Wannan shine sanadin kwanciya Dada a asibiti na tsawon sati biyu tana jiyya, dan hawan jininta ne yay masifar motsawa. Koda ta samu sauƙi kuma Baba yace duk wanda ya kawo masa ita gida a cikin ƴaƴan nasa wlhy sai ya kwashe masa albarka. Duk kuma wanda yazo yay masa maganarta a gidan nan ma sai ya kwashe masa albarka. Wannan ya saka yaran tsorata matuƙa dan sun san wanene mahaifin nasu akan zuciya, balle yanzu ya sake birkice musu irin yanda basu taɓa gani ba. Gashi sunata kiran Alh. Sulaiman dake matsayin babba garesu kuma silar wannan tashin hankali amma sam sun gagara samunsa. Dole dai aka wuce da Dada gidan Uncle Muneer aka gyara mata sashen baƙi....
*_CANADA_*
Labarin Ummita da Lulu taji ya ƙara musu shaƙuwa matuƙa, yayinda Lulu ta fara tunanin buɗe ƙungiya domin taimakon yara marasa zuwa makaranta dan al'amarin yaron nan data taɓa amsar Number a wajensa bisa titi har yanzu yana ranta bata manta ba, tana jin babu daɗi kuma da bata sami ziyartarsa ba. Ƙungiyar zata riƙe abubuwa uku ne. Karatun yara da rashin galihu ya hanasu yi, sai harkar fyaɗe da kuma shaye-shaye. Ɗari bisa ɗari Ummita ta bama Lulu goyen baya game da wannan ƙyaƙyƙyawan ƙudiri nata. Dan haka suka hau tsare-tsaren su kamar waɗanda akacema gobe zasu bar wannan wajen. Lulu ta cigaba da rainon ciki yayinda Usman ke zuwa dubata da bata magungunan ƙarin lafiya ita da abinda ke cikinta. Alh. Sulaiman kuwa na tunanin allurar gubar da zata ruɓar da tayin cikin Usman ke mata. Akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su Lulu da Usman, dan shi ke kawo musu duk wasu bayanai akan Alh. Sulaiman, sai dai a rubuce yake basu, a zahiri kam babu wata alamar dake nuna ko kallon arziƙi sunaima junansu. A haka a haka dai har ALLAH ya kai cikin Lulu haihuwa. Inda ta koma zama da ƙyar tashi da ƙyar. Gaba ɗaya ta canja kamanni saboda kumburin da taɗan yi, dan ma Ummita baiwar ALLAH tsaye take a kanta yanda ya kamata, bata gajiya da yima Lulu da abinda ke cikinta addu'a. Ga Usman na iya bakin ƙoƙarin sa akan komai nasu ciki harda fara shirya musu hanyar guduwa daga tsibirin. Lulu bata taɓa kiran lambar kowa ba tun sanda ta gwada Alh. Sulaiman ya ɗaga. Tunda aka kawosu gidan bai zo ba ko sau ɗaya, hakan ya sasu fahimtar kodai duk cikin takune ko kuma baya ƙasar ne.....
*_UK (LONDON)_*
A ɓangaren Smart wasannin link sun cigaba da tafiya cike da nasarori harma da ƙalubale, inda ALLAH ya ɗaga darajar team ɗin su suka ƙare da maki tamanin da shida, Smart ya jefa ƙwallaye ashirin da bakwai. Hakan ya sashi zama best player na wannan kakar wasa ta bana a ƙasar England, inda ya samu ƙyautar takalmin zinare, team ɗin su kuma ya samu damar shiga babbar gasar premier link na england. A randa su Smart sukai wasan ƙarshe ne ya kasance dai-dai da randa Lulu ta wayi gari da naƙuda. Hankali tashe Ummita tai kiran layin Alh. Sulaiman, amma sai ya amsa mata a daƙile cikin halin ko'in kula. Sai da yaga Lulu na neman rasa ranta sannan yay kiran Usman akan yazo ya dubata, a kallo ɗaya Usman da yay mata ya tabbatar da Alh. Sulaiman cewar dole fa akai Lulu asibiti, dan theatre ya kamata ai mata tilas. Da farko Alhaji Sulaiman ya ɗauki abun babu wasa, sai da fuskanci zai iya rasa damarsa sannan ya amince aka a wuce da Lulu asibiti can cikin gari dan shi tunaninsa mutuwar ɗan a ciki ta jawo hakan. Dai-dai ana shiga da Lulu ɗakin theatre Smart da gabansa keta faduwa ya zira ƙwallo a minti ɗayan ƙarshe da ya rage a tashi wasan. A take garin ya ɗauki ihu, yayinda ya kai ƙasa yay sujida hawayen farin ciki na ziraro masa. Gaba ɗaya teammate ɗinsa sukazo kansa aka rungume juna, suna mai ɗunbin farin cikin shiga a jerin manyan team na duniya da zasu buga primier link kenan, abinda ko'a mafarki ba'a taba kawo musu ba. Amma Alhamdullah sai gashi a dalilin ɗan baiwa kamar yanda suka sakama Smart sun shigo cikin jerin masu nasara. Sosai London City take a hargitse yau anata selebration, su Smart na cikin wata irin doguwar mota mai masifar ƙyau da ɗaukar hankali hannunsu rike da kofin da suka ci suna ɗagawa masoya. Wasu a cikin teammate nashi har cire riguna sukai suna jefama fans. Shi kam dai murmushin sa yake mai ƙayatarwa cike da nutsuwa yana mai ɗaga hannayensa duk biyu, yayinda idan idonsa yakai kan yara yakan ma hannun nasa kiss ya hura musu, sai kaga yaran na maido masa da kisa ɗin suma, jin farin cikin yake tamkar ya zarce na cin ƙwallo a zuciyarsa yau, dan fargabar ɗazun nan da faɗuwar gaba duk ta gudu saboda addu'oin da yake ta yi. Haka suka dinga zagaye cikin London City a wannan mota, inda ta ko ina suka gitta imasoyane ƴaƴa da iyaye harma da kakanni da suka fito domin kallonsu. Sunan Smart Mawashi yasha kira a wannan rana tamkar zai ƙare duk da yanda suke kiran Mawashin abin dariya, sai yaji har hawaye na cika masa ido da wannan al'amari da rahama ta UBANGIJI. A rayuwa ai babbar rahamace ma kaga mutum ɗan uwanka na nuna maka irin soyayya balle kowa yasan Bature akan ƙyamar baƙin fata a zahirance.
Wannan fa nasara ta Smart ta saka hankalin manyan club na ƙasashen turai gaba ɗaya irinsu Italy, Spain, Germany France etc... dawo wa kansa, yayinda aketa kaikawo da cecekuce akan al'amarin yaron a wannan yini, kowacce kafar yaɗa labarai kaje a ƙasar ta England musamman a fanin ƙwallon ƙafa zancen kenan dai Smart Mawashi, Smart Mawashi.. Al'amarin kamar busa usir na alƙalin wasa. Cikin ƙanƙanƙanin lokaci manyan clubs ɗin suka fara ƙwaɗayin nuna zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa........✍️
_To insha ALLAHU dai mun kusa zuwa gaɓar da komai zai cigaba da tafiya a buɗe, ina zazu ɗin nan ne ɗan can mu samesa yanda muke so🥱 dan nasan kunfi kauri acan😜🚴🚴🚴_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣
.........*_CANADA_*
Sosai Lulu ta riga ta sakama ranta tsoron haihuwar ne, duk yanda su Usman suka so ta haihu da kanta hakan na neman gagara. Ga naƙudar tata da gani mai zafi ce, dan tayi wujiga-wujiga a ƙanƙanin lokaci. Tun ma tana hawayen har idanun sun bushe, Ummita dai nata maimaita mata addu'a tana faɗa. Har ALLAH ya isa sai da tama Smart cikin fitar hayyaci😜, akace kuma sai anyi Shari'a da shi yayi jail😂. Abin yaso bama Usman dariya ya dai danne da ƙyar. Dr Lameer yaja Usman gefe cikin damuwa ya ke faɗin, “Ussy inaga fa muyi mata CS ɗin nan kawai, ta riga ta saka tsoro a ranta ga shi kuma jinjirin yayi girma da yawa sosai saboda ciye-ciye data dingayi. Sannan an taɓa taɓa cikin hakan ya raunana mata mahaifa. Amma da ace bata saka tsoro a ranta ba wannan bakomai bane zata iya haihuwa da kanta. Yanzu kam ina tsoron kar wahala tasa mu rasa abinda ke cikinta”.
“No no Doctor bana fatan a rasa babyn nan wlhy, inaga kawai ayi mata cs ɗin”.
“Shike nan babu damuwa, wazai saka hannu a cikinku?”.
“Bara na saka hannun kawai ni”.
Alhamdullah an samu nasarar zaro baby boy a jikin Lulu ƙamshi. Lafiyayyen yaro ƙyaƙyƙyawa da bai baro komai na ubansa ba, ga shi ƙaton gaske masha ALLAH. Dan hatta wani tawadan ALLAH da Smart ke da shi a gefen kunnensa babba shima jinjiri na da shi. Ankai Lulu ɗakin hutu, yayinda Ummita ta rungume yaro tana mai jin ƙaunarsa a ranta kamar jininta. Shi kansa Usman yaron ya shigar masa rai. Bai kira Alh. Sulaiman da ke can yana jiran ace Lulu ta haihuwa ɗa a ruɓe ba, dan yau shine target ɗinsa akan kuɓutar da su Lulun dama. Shi yay duk wani tsare-tsarensa na nemawa Lulu transper da taimakon Dr Lameer zuwa wani ɓoyayyen ƙaramin asibiti a Derby city. A wannan daren aka fita da Lulu cikin ambulance da Ummita, abinka da turai tsaro kaca-kaca hankalinsu kwance suka iso Derby city zuwa gabannin asubahi. Sanin Alh. Sulaiman zai iya bibiyarsu komai ya tafi ne akan tsari da kulawa. Dan wani gida ne a kusa da asibitin aka ajiyesu, acan gefen gari wajen ana noman fruits, sai gidan abinci da ke gaba kaɗan kasancewar babban hanya ce, sannan bature shi babu ruwansa da daji duk inda yay masa alƙarya ce. Komai da Lulu zata iya buƙata na kulawar lafiyarta su Usman ya tanada a gidan, dan bashi da damar barin ƙasar da su a yanzu kasancewar passport nasu na hannun tsule, fita dasu kai tsaye zai zama mai wahala.
Kusan ƙarfe takwas Lulu ta dawo hayyacinta, inda cikin amincin ALLAH ta farka bakinta ɗauke da addu'a. Da sauri Ummita da ke zaune a gefenta rungume da jariri dake ta barcinsa tai saurin kallonta da faɗin, “Alhamdullah aunty kin farka?”. Idanu kawai Lulun ta zuba mata ita da jaririn, sai kuma ta sauke numfashi a hankali da motsa lips ɗin ta tana mai bin ɗakin da kallo. “Ina ne nan Ummita? Miya faru da ni?”. Cike da farin ciki Ummita ta ce, “Aunty an miki C'S ne ga baby boy mun samu, nan kuma sabon wajene da Usman ya kuɓuto damu da ga hannun kawunki.” Lulu batace komai ba sai idanu data zubama jaririn hannun Ummitan, da sauri Ummita ta miƙe zuwa gabanta da jaririn, Lulu ta zuba masa ido zuciyarta na wani irin harbawa na masifa. Dan duk da yaron da sauran ɗanyantakarsa ta kasancewa jinjiri kamaninsa da mahaifinsa a bayyane suke. A hankali ta lumshe idanunta tana sakin wasu irin ajiyar zuciya a jajjere, sai kawai ta samu kanta da sakin kuka. Hankalin Ummita ya tashi, ta shiga jera mata tambayoyi akan ko wani waje na mata ciwo ne? Bata iya bata amsa ba har su Usman suka shigo, Dr Lameer ya dubata yayinda Usman ke faman lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta, insha ALLAH sun kuɓuta kenan, zai kumayi duk yanda zai yi na ganin sun koma gida Nigeria. Ummita ita ta bada shawaran ya kamata ama jaririn huɗuba fa, dan haka suka tambayeta wane suna take so a saka masa. Ita kanta batama san lokacin da ta furta, *_“ALIYU”_* ba. Usman da ya saki wani ɗan murmushi ya ɗauki jinjirin yaymasa huɗuba da suna ALIYU HYDAR ZAKIN FAMA. tare da masa addu'a dan duk lalacewar Usman yanada iliminsa na addini. Kawai zama a waje ne ya sashi zama mara jin magana.
Lulu da idonta ke a lumshe a zuciyarta ta furta (ALLAH ya albarkaci rayuwarka *_Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi_*) sai kuma ta ɗan yamitse fuska kamar wadda take jin hakan banbarakwai a zuciyarta...
_(To muma dai munce ALLAH ya raya Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi. Dangin Smart kar ace bamuyi Barka ba🥱🚴)_
*_NIGERIA_*
Sosai Daddy ke fama da ciwo a tsaitsaye, sai dai yanata dauriyar ganin bai bari ko Mommy ta fahimta ba. Sai dai ya gagara ɓoye damuwarsa akan halin da suke ciki tsakaninsa da ɗan uwansa Yousuf. Yousuf nada matuƙar muhimmanci a garesa ta yanda baki bazai iya furtawa ba. Su fa kaɗaine ƴan uwansa shi da Mommy sai zuri'ar da suka tare a yanzu. Tunda yake da ɗan uwansa bayan rikicin Kasancewar Mawaddat (Maman Lulu) a rayuwarsu baya jin akwai wani saɓani daya taɓa shiga a tsakaninsu kamar haka da Yousuf ɗin ya ɗauki zafi da shi. Ba wai baya son fitowa ya faɗa masa gaskiyar al'amari bane, bai son tada masa da hankaline kawai ko sakashi a matsala. Shiyyasa ya zaɓi shanyewa shi kaɗai a tsahon rayuwa. Amma yana gani a wannan gaɓar in har yana son ɗan uwan nasa ya fahimcesa dolene ya buɗe masa sirrin nan dai da yake ta faman biznewa a tsahon shekaru badan tsoro ba sai don dalilai guda biyu. Na farko baya son tarwatsa farin cikin family ɗin mutum mai mutunci da daraja a rayuwarsa irin Alhaji Sufi Ado Garko. Ya taka rawar gani a rayuwarsa da har a yanzu ake iya kallonsa a nuna a matsayin wane. Duk da yasan wannan rubutaccene daga UBANGIJI ko babu shi ɗin komai zai iya tabbata. Amma UBANGIJI ya sakashi zama matsayin sila. Idan ya kasance mai tarwatsa farin cikin wannan ahali yana jin kamar ya rama sharri ne da alkairi. Na biyu shine kare rayuwar yarinyarsa duk da yasan shi bai isa hana komai ba daga ƙaddarar ALLAH. Tunda gashi nan a sanadin hakan har Lulun ta faɗa shaye-shaye batare da ya iya bata kariya akan hakan ba. Hasalima bai taɓa sanin tanayi ba sai a shekarar nan. Tun daga ranar jikinsa yay sanyi matuƙa da sake tabbatar da wayo ko dabara bata kare maka abu sai UBANGIJIN talikai masanin sirrin fili da ɓoye. A hankali ya kai hannu ya ɗauke ƙananun hawayen da suka ciko masa idanu. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da ɗaukar wayarsa ya rubuta gajeren text message wa Uncle Yousuf ya tura masa, duk da yasan a gajiye yake dan jiya ya dawo daga UK kamar yanda yake ji a bakin Mommy dan shi dai Uncle Yousuf ɗin bai sanar masa ba sam.
Uncle Yousuf na tsakiyar iyalinsa suna kallo, yayinda Deen da Ra'is ke home work text ɗin Daddy ya shigo masa. Kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka ya duba ganin kallon da aunty Saliha tai masa. Shiru yay yana kallon text ɗin da bai wuce layi biyu da rabi ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya dan shima harga ALLAH yana azabtuwa da rashin ɗan uwan nasa a kwanakin nan. Dauriya kawai yake yi. Tunda ya san kansa bai taɓa wayar gari da yini harda kwana baiyi waya da yayan nasa da yakema kallon kamar mahaifi ba. Dan ko baya ƙasar sukan yi waya sama da sau uku a rana. Dan ƙa'idarsa ce duk safiya ko suna a ƙasa ɗaya ko basa nan zai gaishesa, sannan da dare kafin ya kwanta zai kirasa yay masa sai da safe. Idan ma bai kira ba bisa wani uziri na yau da gobe shi daddyn zai kirashi da kansa. Bayan wannan wayoyin biyu na ƙa'ida wasu wayoyin kan shiga a tsakaninsu game da Business ko wani muhimmin abu da ya shafesu. Jin zuciyarsa ta kasa nutsuwa waje guda ya miƙe yana kallon aunty Saliha. “Sweetheart ɗan bani key Please”. Da mamaki ta ce, “Key kuma?. Ina zakaje kaiko a daren nan kamar wanda ke a tarkon mace?”. Karan farko yay murmushin da bai niyya ba. Dan tun a kallon da tai masa sanda text ɗin ya shigo yasan akwai magana a bakinta. Komai baice ba sai wayar da ya miƙa mata. Dan tsakanin shi matarsa akwai yarda mai ƙarfi da fahimtar juna. Duk inda ƙofar zargi ta nema buɗe musu