Showing 51001 words to 54000 words out of 131687 words
Chapter 18 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
tun a haɗuwata da shi ta farko. Dan haka na zauna na karancesa yanda ya kamata, sai dai rashin sanin abinda ke a tsakaninku yasa ban taɓa wani yunƙuri ba. Amma tabbas na jima da lura da duk inda nake ana biye da ni, hakama ƙannena, na shiga tashin hankali saboda a tunanina Sulaiman ne, sai daga baya na fahimci ƴan sanda ne, sai dai babu irin bibiyar da ban musu ba sunƙi gayamin wanda ya sakasu, sai nai tunanin ma ko Uncle Yousuf ne ko Coach a lokacin, shiyyasa na zaɓi musu shiru a ganina wataran ai zan sani. Kamar yanda na faɗa maka ina son ka bar wannan case ɗin a hannuna yanzu, sannan ina son na bada shawara....”
Cike da kulawa Daddy ya ce, “Ina jinka Aliyu, ka faɗi komi ke'a ranka kai tsaye tsakaninmu babu wani ɓoye-ɓoye”.
Kai Smart ya jinjina tare da furzar da iska mai nauyi. “Wato Daddy irin su Sulaiman da hatsabibancinsu yaƙin sunƙuru yake buƙata a farkon fara wasa. Kamar yanda ka ɗauki masa salon shekarun da suka gabata na nuna baka san mi yake ciki ba wannan salon zamu cigaba a yanzu har zuwa wani mataki. Domin idan har akace za'ai masa fito-na-fito a shirye yake da wannan tun ba yanzu ba. Jirace yake da kai kace kule yace cass. Sannan mahaifinsa da kai hallacin shanye komai daminsa zai iya samun bugawar zuciya wlhy in har yaji kasuwancin da yake yi da kuma ketama autarsu mutunci da yayi. Ko kuma shi da kansa ya shirya hanyar halakasu idan yaga zaka cimma burin tona masa asiri. Kaga anyi gudun gara kenan an faɗa gidan zagon dai. Dan haka mu ajiye batun fito-na-fito ɗin nan mu lallaɓa Baba Garko ya sakar masa ɗansa, ka cigaba da nuna masa kana shakkar tasa, sauran yaƙin ka bar mana zamu ƙarasashi ni da Mawaddat da Uncle Yousuf in sha ALLAHU”.
Idanu kawai Daddy ya zubama Smart, yama rasa abin faɗa akan wannan yaro. Lallai farar haihuwa tayi, dan shikam dole ya kira wannan yaro da farar haihuwa ga iyayensa. Smart ne da yaga kallon da Daddyn ke masa yay ƙasa da kansa yana murmushi kawai....
__________★
Yau kam Ammah da kanta ta wanke ɗan jikanta ta gyarashi ɗaras ɗas. Yayinda Mamy ta gyara Mawaddat ita kuma Ummita ta shirya abinci. Lulu da ke jin jikinta wani iri tunda garin ALLAH ya waye cikin damuwa take sanarma Ammah ta mata addu'a gabanta sai faɗuwa yake. Jawo hannunta Ammah tai ta zaunar kusa da ita cikin damuwa da kulawa ta fara mata addu'oi, a hankali Lulu ta dinga samun nutsuwa har ta ɗan sha tea ta kuma shayar da AA abincinsa. Sun kammala kenan Ummita na gyara mata gashinta su Smart suka iso niƙi-niƙi da kayan da ya siyo bisa jagorancin Usman. Da mamaki Lulu ke kallonsu su da kayan, Usman ya nuna Smart cikin ɗaga hannu yana ficewa acewarsa bari yay kiran Dr Lameer.
Lulu da ke jin faɗuwar gabanta na dawowa tun shigowar Smart ɗin ɗakin cikin dauriya ta ce, “Good morning” a takaice. Bai amsa mata ba sai da ya ɗauki AA tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake a gaban gadon ya ɗan ma yaron kiss a goshi da kumatunsa sannan ya dubeta idanu ƙasa-ƙasa. Kamar wanda baya son motsa lips ɗinsa ya furta, “Haka ake gaishe da miji? Kamata yay kizo da gudu ki rungumeni da bani ƙyaƙyƙyawar sumba ki ce good morning rabin raina” yay maganar cikin kwaikwayon muryarta. Harara ta zuba masa da saurin faɗin, “ALLAH ya kiyasheni. Miye wani rabin rai babu ko daɗin ji.....”
“Ki rantse ni ba rabin ranki bane”.
“Kana buƙatar ganin likita kam”.
Murmushi ya saki da ɗan lumshe idanunsa yana gyara AA da ƙyau. “To muje a hakan, idan tai wari maji ai. Ina fatan kun tashi lafiya ke da baban Ammah?”.
Cikin ɗan marairaice fuska ta ce, “Wane lafiya bayan ya hanamu barci, ka masa faɗa gaskiya ni bana son damuwa. ALLAH nima sai da nai kuka duk ya ruɗamu ga Ammah tayi tafiya ta gaji ya sata tanata faman jijjigarsa”.
Gaba ɗaya neman harmutsa masa lissafi take da salon nata. Ƙaramin gyaran murya yay saboda jin yawu na neman sarƙeshi. Hakan yasa Lulu zuba masa ido, sai yay saurin janye nasa da ke neman canja launi cike da basarwa ya ɗan lakace kumatun AA da faɗin, “My Grandpa miyasa ka hanamin Mata barci? To da ga yau karna sake ji kaji Sadaukina. Kuma ka bama Maah-maah haƙuri” Sai kuma ya ɗago ya dubi Lulu data zuba musu ido, a yanayin ɗan ɗage gira ya ce, “Koda yake ni ya kamata ma na bada haƙurin nan a madadinsa” ya ƙare maganar yana tasowa. Ƙoƙarin sauka tai a gadon tana faɗin, “Ni dai ban gayyaceku ba”.
Cikin ɗan murmushi ya ce, “Oh oh har ma takai gudunmu akeyi. Haƙuri da kawai zamu baki”.
“Na haƙura basai kunzo ba”.
“Please mana Baby luv ko ɗuminki ki bari muji mana”.
Dama ta fahimci wayon nasa kenan, dan haka ta maƙe kafaɗa kamar wata ƴar baby da faɗin, “Naƙi ɗin. Kai koma kunya bakaji a gaban ɗanka sai kayi taɓara. Ka rage halin nan wlhy rashin jin magana zalla”.
Komawa yay ya zauna yana dariya da faɗin, “Kema ai rashin jin ne ya kaiki ga samo AA Mawashi. Haka kawai kin lalatama Ammah yaro, sai kawai ta ganki da yaro a hannu kuma dai tasan a inda kika samo.....”
“What!!”
Ta faɗa da sauri cikin daburcewa kamar Ammah na gabanta. Aiko ya shiga yin dariya a hankali. “Ni dai ai kowa yasan ni babu ruwana salihin ALLAH. Ina zaman zamana kikace sai anyi yaƙin ƙasa da ƙasa. Tsabar zalama baki fito a filin dagar ba sai da ganimar yaƙi wannan yarinya sai a barki kawai amma dai gaskiy....”
Fillon data ɗauka zata jefa masa ya hanashi ƙarasawa, cikin ɗaga hannaye sama da sauri alamar surrender ya ce, “Yi hakuri nayi shiru, ke kam akwai kawaici nine zalamammen ga shi ma AA ni yabiyo tabbacin haka”.
Hararsa tai da ajiye filon ta koma ta zauna. Sai kuma cikin damuwa da marairaicewa ta ce, “Da gaske dan ALLAH su Ammah suna ganin bani da kunya ko? Wata goma da kwanaki dayin aure na haifi yaro, wlhy nima abin na damuna, sai nake ganin abin yayi kusa da yawa kamar wata mayyar miji”.
Daƙyar Smart ya iya danne dariyarsa. Dan ya fahimci tsakaninta da ALLAH take tambayar. Cikin kaɗa kai ya ce, “Kai kai baza'a suce ba Madam. Sai dai ma a kiraki da jaruma mai matuƙar hazaƙar ɗaukar darasi a wajen malaminta. Ammah kam ai zata so nan da wasu watannin goma masu zuwa ki sake santalo mata wata baby girl ma again”.
Sosai ta waro manyan idanunta kamar zatai kuka. “Hydar wane fatan tsiyane kuma wannan dan ALLAH mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kamar wata akuya. Kasan miye rainon ciki da haihuwa kuwa?. Wlhy akwai wahala, ni da ga ɗayan nan ma na gama gaskiya”.
Tsam ya taso da ga inda yake zaune ya dawo kusa da ita. Cikin nuna damuwa ya ce, “Da gaske akwai wahala? Bani labari yaya kika kasance?”.
Lumshe idanunta tai a hankali tana mai ƙara shaƙar ƙamshinsa mai masifar daɗi, duk da dama dai tun ɗazun take shaƙar, kusancin da suka samu yanzu ne ya ƙara ƙarfinsa sosai a cikin han nacinta. Hannunta ya ruƙo tare da murzashi a cikin nasa a hankali. Idanun ta buɗe tsigar jikinta na tashi. Ta kalli hannayen nasu ta ɗan sake lumshe idanun nata da sake buɗewa. Cikin ƙara ƙasa da muryarta batare da ta farga da canja salon harshen nata ba ta furta, “Ai ya wuce kuma, share kawai”.
“Please ina son ji nidai”.
Ya faɗa yana murza mata hannu a ɗan marairaice. Hannun taso janyewa dan yana sata a wani yanayi salon nasa, amma ya hana hakan, sai kawai ta saki ajiyar zuciya a hankali ta furta,........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣
.......“Humm akwai wahala sosai da bata da misali. Na ƙara jin ƙaunar mahaifiyata da jinjina mata wahalar da tai dani a dalilin wannan cikin. Ko abinci bana iya ci, da naci sai amai, ko wani abu na sha sai nayi amai. Gashi nan ko yanzu dana haihu magani ma ya gagareni sai dai allurai ake min dan in naga magani amai nake ji. Kunun gyaɗa ne kawai ya zama abincina kwana da yini. Gaba ɗaya dai abin babu sauƙi kawai dan ba'a iya misaltashi ma Aliyu. Balle naƙuda Hummm......”
Duk da a dunƙule ta bashi labarin ya fahimci dai ciki ya hanata shaye-shaye, sai kunun gyaɗa daya zamar mata abinci kawai. Cikin ƙara sanyaya murya da jin tausayinta da farin ciki ya ce, “Addu'ata dare da rana UBANGIJI ya tasirantar da itane atare da gudan jinina, ya ƙarasa min aikin dana fara kenan, sannan a kowane awa bayan awa yana tuna miki Abbiensa ne ta hanyar shan abinda yafi so fiye da komai.” yanda ya ƙare maganar da ƴar dariyar tsokana ya sata ɗan harararsa da taɓe baki, sai dai batasan hararar tata ba ta juye ne zuwa wani sassanyan kallon dake neman hargitsama Smart lissafi da hankali.
“Ita hararar nan tana son tada zaune tsaye ne fa. Zakuma ta iya takalo yaƙin ƙasa da ƙasa a taƙaice rigakafi yafi magani”. Ya faɗa a wani irin kasalance yana ƙasa-ƙasa da idanu. Ba fahimtar zancensa tai ba, amma salon da yay maganar da yanda yake wani narke idanu da murya ya sata janye jikinta a nasa cikin basarwa duk da saƙon nasa ya isa ga manyan mata fiye da yanda yay tsammani. Shima kawai sai ya basar cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Yanzu miye shirinki akan suna gobe idan ALLAH ya kaimu?”.
Cikin mamaki ta ce, “Suna kuma? Da suwa za'ayi sunan to? Bayan naga idan za'ai suna a gida Nigeria taruwa dangi sukeyi da matan anguwa, in dai ban manta ba haka na gani a sunan Deen ɗin mu fa anyi, anan kuma mu yanzu wa garemu da zai zo?”.
“Mu mana, iya mu ɗin nan ma ai mun wadatar muyi suna bawai wajibi bane sai antarun kamar yanda kika gani a sunan Deen, in sha ALLAHU kuma za'a yanka masa rago kamar yanda ake yankama kowa. Ƙyautar da ban san da itaba ce ba fa a hannuna, taya bazan nuna godiyar ALLAH ba nikam. Sannan ni so nake daga nan mu wuce kawai basai kin koma Nigeria ba”.
“Hanyoyin nuna godiyar ALLAH ai suna da yawa ba sai ta hanyar yin taron suna ba. Sannan idan ban koma Nigeria ba ina kake son naje banda neman magana irin taka. Kuma ni nama faɗa maka na shirya cigaba da zama da kai ne? Auren contract akayi kuma ya ƙare it's ok”.
“Hakane kam, Alhamdullah suma waɗan can godiyar UBANGIJI ɗin duk na kamanta su, amma duk da haka dai ina son muyi shagalin suna. Kinga koda ƙannensa sun zo nan gaba suma shi bazaiga an musu ba'ai masa ba”. Ya ƙare maganar batare daya amsa maganartata ta ƙarshe ba.
Hakan ya bata haushi, dan haka a tunzire ta ce, “Miye wani ƙanne? Malam ka san abinda kake faɗa fa! Na gaya maka ni na gama auren nan”.
Dariya ta bashi ganin yanda tai maganar a gatsire, amma sai ya danne da ƙyar yay murmushi kawai da faɗin, “Naki tsarin kenan wannan ai”.
“Kamar ya nawa tsarin kenan?. Amma kasan dai ba haka akai da kai ba ko?”.
“Humm” yace kawai. Baice komai ba akan maganar tata yanzun ma, sai ma ya nuna mata ledojin da suka shigo da shi. “Kuyi haƙuri da waɗan nan babu yawa, sauran abinda ya dace duk na damƙashi a hannun Usman. Munyi magana da Daddy akan suna son a turaki Saudiya ki zauna a can na wani lokaci saboda Kawunki Sulaiman, dan bazai taɓa ƙyaleki ba zai cigaba da bibiyar al'amarin ku. Ke yaya kika gani?”.
“Ni babu inda zani, shi ɗin banza da zan cigaba da masa wasan ɓuya. Ko wannan ɗin ma da yaga yaci nasara saboda Dada ne wlhy, sannan ina kan sani na cigaba da biye masa bayan nasan manufarsa. Nayi hakkanne kawai domin sake tabbatar da shi ɗin waye. Amma har miye wani Sulaiman can”.
Murmushi yayi kaɗan, a zuciyarsa yana ayyana (ashe a wajen Daddy kika gado wannan taurin ran naki da kafiya) a zahiri kam sai ya nisa cikin ɗan cije lips ɗinsa ya ce, “Zamu iya tunanin shi ba abin tsoro bane ba, sai dai idan muka shagala da hakan zai mana illa a ƙanƙanin lokaci cikin salon duka ta inda bazamu taɓa iya sosawa ba balle mu rama. Mawaddat Kawunki ya wuce duk yanda kike tunani a kansa. Domin ya jima biye da rayuwarki tun kina ƙarama. Bana raba ɗayan biyu shine ya koya miki shaye-shaye. Kuma shine ya taɓa harar rayuwarki ta hanyar keta miki haddinki har kike firgita kika tsani maza....”
Da wani irin sauri ta kallesa, sai kuma jikinta ya fara tsuma. Dan danan annurin fuskarta ya ɓace gaba ɗaya. Cikin yanayin faɗa-faɗa ta ce, “Aliyu rayuwata ta baya ta zamar maka abar bibiyane ko mi?”.
“No ko ɗaya, mizai sa na bibiya bayan na gama fahimtar komai. Sannan Mawaddat nake so ba halayenta ba. Ruwana ne na maidata a irin halayyar da nafi buƙata kona barta da wanda na ganta a ciki. Mawaddat ki sani shure-shure baya hana mutuwa, duk yanda kike jin zaki iya ɓoye abinda ya faru a baya wataran zuciyarki bazata iya ɗauka ba. Kiyi haƙuri ba ina tilasta miki bane sai kin sanar min, kidai sani cigaba da riƙewar zai iya sake nakasaki akan shaye-shayen nan. Doctor ya jima da tabbatar da idan kika cigaba zaki cutu, sannan a yanzu ke ɗin Uwa ce Mawaddat, taya kike tunanin idan yaron mu ya taso yaji wannan ɗibi'ar koda a labari ne zaiyi farin ciki. Mahaifiyarki mutuniyar kirkice data shinfiɗama rayuwarta alkairai da dama da a yanzu sune ke bibiyarta da ke kanki har maƙiyanki da nata suka gagara cin galaba a kanki. Taya kike tunanin naki ɗiyan zasu samu irin wannan kariyar idan har baki zama uwa ta ƙwarai ba Mawaddat. Please ina so ki canja, canjawar taki kuma zata tabbatane kawai ta hanyar fidda abinda ke zuciyarki, dan shine yay miki nauyin da har kike jin abinda kike sha zai iya danne miki shi. Taya za'a gyara ɓarna da ɓarna banda wautarki......”
Wani irin kuka mai tsuma zuciyar da ta saki ne ya saka shi yin shiru, a hankali ya furzar da iska tare da miƙewa ya koma daf da ita, matsota yay ya saka a jikinsa ya rungume. Sai kawai ta sake sakin masa kuka da iya dukkan ƙarfinta da baƙin cikin dake cinkushe da zuciyarta da ƙwaƙwalwa. Bai sake mata magana ba ya barta tai kukan mai isarta dan haka zai rage mata nauyin zuciyar. Tako yi kukan sosai dan sun kai kusan awa guda tana abu ɗaya har sai da taji kanta na sara mata sannan tai shiru ta koma shashsheka. Cikin son kauda yanayin ya ce, “Uhm nace ba! Yau dai anan zan kwana ko? Naga ai gadon zai ishemu”.
Da sauri ta ɗago tare zuba masa harara da kumburarrun idanunta da suka sha kuka. Murmushi yayi da marairaice face yana shafa kai. “Nifa bance wani abu ba Madam. A wajen kwanciyar ma na yarda sai ayi kai da ƙafa AA a tsakkiyar mu. Kinga dai ai babu batun kawo harima balle ace da wata manufa nazo”.
Filo ta ɗauka ta maka masa. Ya shiga karewa shi kuma yana ƙyalkyala dariya. Dai-dai nan Usman yay sallama. Hararar ƙofar Smart yayi cikin dafe kai. Hakan ya saka Lulu dariya ta amsa da cema Usman bismillah shigo. Babu kunya yana shigowa Smart ya hararesa da faɗin, “Kai wai miyasa baka iya zaɓar lokacin zuwa bane ɗakin mutane?”.
“Oh ba'ai farin ciki da zuwana ba kenan na koma?”.
“Eh gaskiya koma anjima sai ka dawo, wannan ai shiga tsakanin masoya ne”.
Ita Lulu abin harya bata kunya tana