Showing 69001 words to 72000 words out of 131687 words
Chapter 24 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt
yi kamar suna tare amaryarsa bata zuwa inda yake, amma kuma bai barin itama Dadar tazo. Ko kuma ma ya ƙirƙiri tafiya. Bayan wata ɗaya da dawowar Dada yasa aka saki Alh. Sulaiman shima.....
______★
A ɓangaren uban gayya kam al'amura sai dai Alhmdllh. Dan komai yana tafiya fiye da yanda akai fatansa. Ya zama cikakken ɗan wasan Arsenal da yanzu duniya ke kallo ta faɗa da kiransa *_GWARZON ZAKI_* Sunan Smart Mawashi sake dilmiya yake a duniyar ƙwallon ƙafa. Dan a yanzu haka ya fara taka sabuwar rawa a sabon team ɗin nashi na Arsenal. Duk da kuwa wasanni uku kenan suka buga kacal. Sai dai aduka wasan babu wanda bai saka musu ƙwallo ba. Wannan ya sake jawo hankalin al'umma kansa tako ina a duniya. Ya zama ɗaya daga cikin matasan yara masu tashe a duniyar ƙwallon da ake faɗa ake ma kan faɗa a kowane yini. Al'amarin matarsa bawai baya damunsa bane, ya miƙama UBANGIJI al'amarinsa ne kawai da fatan cinye waɗan nan jarabawoyi kashi-kashi. Shi kaɗai yasan abubuwan da yake jurewa a irin wannan tsukun. Amma yana matuƙar begen matarsa a kusa da shi har ma da gudan jininsa takwaransa.....
____________★
Yau ma a gajiye ta dawo gidan kamar kullum Ummita biye da ita da tarkacenta. Tunda aka kammala bikin buɗe ƙungiyar nan tata bata huta ba. Ga aikin kungiya gana office ga karatun islamiyya ga shago. Dan rainon AA dai bazatace komai ba kusan Mommy da su Afrah ne keyi da Iya Tabawa. Tsakaninta da shi kawai ta shayar da shi. Kasancewar ma yana shan tea da koko hankali kwance bai cika damuwa ba. Shiyyasa ma bata fita da shi ko'ina. Ba kuma ya kuka dan shi ɗin mai iyayene da yawa. Itada kanta ma wani lokacin har tausayi yake bata da rashin samunta yanda ya kamata. Amma yaya zatayi.
Tunda sukai sallama AA da ke a bayan Suhaib na masa doki ya fara zillo. Saukesa yay suna masa dariya. Ya rarrafo da saurinsa zuwa gareta. Kamar yanda suke dariyar itama dariyar takeyi. Daukarsa tai ta jefa sama ta cafe tare da rungumesa tai masa kiss. Shima yay mata a kumatunta biyu. Lakace masa hanci tayi cike da farin ciki da jinjina wayonsa. A kullum kamar ana ƙara masa wayo ne. Baya magana dai sannan tafiya bata nuna ba, amma idan ka gansa bazakace watansa tara ba. AA akwai zafin nama da ɗankaren wayon tsiya. Shiyyasa ɓarna babu kama hannun yaro. Idan aka kaisa hira wajen Daddy har korosa yake saboda ɓuruntu. Hakama Mommy sunta faɗa kenan.
Cikin zubewa a kujera Lulu ke faɗin, “Wayyo ALLAH ku bani ruwa kafin na shiɗe Please”. Amrah na dariya ta miƙo mata ruwa da kofi, kofin ta ture ta ɓalle murfi goran ta kafa kai kawai. Neman ƙwacewa AA yake tana buge masa hannu, bata kulashi ba sai da ta kusan shanyewa ta bar masa ɗan kaɗan sannan ta bashi.
“Wai lallai aunty Lu.. kinji ƙishi fa”.
Cewar Mubeen dake ƙoƙarin ɗaukar AA da ke miƙa masa hannu. Dan shigowarsa kenan shima da ga makaranta. Tace, “Ka bari kawai broth wlhy yau munsha wahala ne. Ai bazan iya driving-driving ɗin nan ba a nema min driver please. Sai dai mai hankali dan ALLAH ban son mai surutu da ƙazanta”.
Dariya Amrah da Afrah da Mubeen suka sanya. Mubeen ke cewa baki son irin su Dallatu yake ko wa ma mai shegen ƙaryar nan ga yalalen haƙora”.
Itama dariyar tayi, dan ta tuna da wanda suke maganar, shine ta kora aka kawo Smart. Akwai shegen surutu da son fafa amma ba tsafta. Aiko yasha marukanta babu adadi. Haka kawai sai Smart ya zo mata a rai. Taɗan lumshe idanu da jan ajiyar zuciya, gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Tsam ta miƙe tabar falon suna cigaba da hirarsu bama su farga ba. Dan Ummita suka shiga bama labarin direbobin Lulun da akasha kala-kala a gidan. Tana shiga ɗakin nata da ke tsaf-tsaf yana ƙamshi mai daɗin gaske dan yana nan a yanda kowa ya sanshi da tsafta, iya Tabawa bata wasa da gyaransa saboda Lulu sam bata son ƙazanta. Abayar jikinta ta saɓule, wando da rigar data saka a ciki suka bayyana. Suma zaresu tai ta shiga wanka. Tana fitowa ta gabatar da sallar magrib da aketa yi. Alkur'ani ta ɗauka tai karatu gwargwadon abinda ya sawwaƙa kamar yanda ta saba a yanzu, kafin ta ɗora da azkar na yamma da bata samun damar nutsuwar yi sai irin iyanzu ɗin. Koda Ummita ta shigo mata da takardun ta da Laptop bata katse abinda take ba, sai ga Iya Tabawa ma da tea da Lulun kesha duk dare AA goye a bayanta. Tea ɗin ta fara ajiyewa a inda Lulun ke zama yin ayyukanta sannan ta matsa gaban gado ta sauke AA ta kwantar a hankali. An masa wankansa an masa shirin barci sai ƙamshi yake yi kamar ba dare ba. Fita sukai gaba ɗayansu suka ja mata ƙofar, dan babu kuma mai sake shigo mata kenan, itama da wahala ta sake fita in ba Daddy ne bai shigo gidan da wuri ba taje su gaisa. Kamar dai yau da suka samu baya a gida bai dawo ba.
Bayan kammala addu'ointa tsam ta miƙe ta maida komai a inda yake tare da zare abayar sallarta ta maidata a inda take ajiyewa. Doguwar riga mara nauyi da bata kai mata har ƙasa ba ta saka mara hannu. Ta ɗan rage gudun acn ɗakin saboda AA mai saurin ɗaukar mura sannan ta nufi gadon nata. Zama tai a hankali gefen da yaron yake da ga can ɗan tsakkiya tana sauke ajiyar zuciya da ɗaukar wayoyinta. Ɗan dudduba massages tayi da miss calls da akai mata ɗazun bata samu amsawa ba. Ta kira wanda zata iya ta share sauran. Sakwanin ma amsa wanda suke da muhimmanci tayi sauran ta barsu. Tana ƙoƙarin ajiye wayar kira ya shigo. Number nan ce dai da ko ta ɗaga ba'a magana tayi masifar har ta gaji, har blocking tayi amma tarasa yanda ake cigaba da kiran nata. Har ta tsinke bata daga ba, aka kuma sake kira. Tasan idan bata ɗaga ɗin ba dai ba dainawa za'ai ba koda za'a jera mata kira hamsin ne, dan haka ma take ɗagawar ta samawa kanta lafiya tunda bata san wane aljani ne ba kuma. Kamar kullum shiru anƙi ace komai, sai dai tana iya jiyo saukar numfashi da fitarsa a hankali. Itama yau sai taƙi yin magana. Haka sukai shiru kusan na mintuna uku kamar ba kuɗi ake ci ba.
“Hummm koma waye dai ALLAH ya shiryesa”. Ta faɗa cikin jin haushi da yanke kiran tana jan ƙaramin tsaki. Wayar ta jefar gefe tare da kai hannu ta gyara ma AA kwanciya, sai ta samun kanta da zubama yaron ido kamar yau ne ta saba ganinsa. Ta ja tsahon mintuna biyar tana ma yaron kallon ƙurillah tare da cakuɗa abubuwa da yawa da ke cimata zuciya. Ganin zata zurfafa tunaninta yay yawa ta sumbaci goshin yaron da sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta masa addu'a ta gyarashi. Miƙewa tai zuwa inda take zaman aikinta ta zauna, sai da ta haɗa shayi sannan ta kunna laptop tare da rage hasken ɗakin, bakajin komai sai motsin keyboard da na ac. Ta kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ta tashi tana faman miƙar gajiya, toilet ta shiga tai uzirirrikanta ta fito tai shirin barci ta haye gado kusa da gudan jininta ta kwanta.....
Washe gari kamar yanda ta saba da wuri tai shirin fita. Dan ma tana ta fama da AA da ya maƙale mata yau shagwaɓa yake ji, sai da Ummita ta shigo ne ta ansar mata shi ta samu ta ƙarasa gyarawa tana faɗin, “Yaro zaka gane kuranka yayeka zanyi ai a cikin watannan”.
Cikin waro idanu waje Ummita ta ce, “Kai aunty wasa kike amma dan ALLAH?”.
“Oh wasa ko zakuga wasa”.
“Kai aunty wata tara fa, baima cika cif-cif ba. Banda ma yanada kirinki da zafin nama ai bai kai a fita a barsa ba”.
“Uhm Ummita kanku fa akeji, wlhy jira kawai nake ya taka na yayesa. Tunda yana cin abincinsa ba wani ya damu da nonon bane sosai ai gara na hutar da kaina ko.”
“Mudai aunty kiyi haƙuri to ko shekara ɗaya mu cika dan ALLAH mun tuba”.
“Ummita kenan, wai baki tausayina ne ma dai ko. Da wanne zan ji?”.
“Aunty damu mana, ai mune farko kafin komai. Dan kulawar mu da ta Abbienmu itace farko”.
Shiru Lulu tai bata sake cewa komai ba. Dan a duk sanda Ummita zata ambaci Abbien AA ɗin takanji zuciyarta na mata nauyi, shiyyasa bata sakewa hirar tai nisa a kansa take basarwa. Ficewa tai a ɗakin tana faɗin, “Bari na duba Daddy zanyi breakfast a wajensa ki yi maza ki shirya kin san munada aiki yau”.
Cikin girmawa Ummitan ta amsa mata da to tare da Binta da kallo tausayi. Sosai ma'aurata ke matuƙar bata tausayi, bata taɓa ji ko labarin irin aurensun nan ba. Auren kusan shekara ɗaya da fin rabi kaɗan babu a biyu amma zaman wata ɗaya cikakken ba'a samu ba, dan ma UBANGIJI mai hikima da ya saƙa zare mai girma na azurtasu da ɗa. Tana ma kanta addu'a, amma gaskiya Lulu na ɗaya daga cikin manyan addu'ointa a kowacce rana. Fatanta ALLAH ya kawo iyakar komai ta koma wajen mijinta da ayanzu duniya ke faɗa da saurara a fanin ƙwallon ƙafa. Ita tasan duk da Lulun bata nunawa tanada damuwa sosai. Dan tasha kamata tana kallon AA kallo mai harshen damo kasancewar sa tamkar photo copy na mahaifinsa. Sannan shi kansa yaron soyayyar da take nuna masa mai kallo yasan ba tashi bace shi kaɗai harda ta Abbien nasa........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣
........A wajen Daddy ta karya kamar yanda ta faɗa. Sunata hirarsu cike da nishaɗi. A cikin hirar ne yake cemata yana son ya je ya ɗan huta kwana biyu da ga nan zaiga doctor ɗinsa da kuma wani business da zai yi a England. Batare da ta kawo komai a ranta ba dan harga ALLAH bata san a ina Smart yake ba yanzu, ta ce, Daddy badan ina akan gaɓar wani case ba ALLAH nima dana bika na ɗan huta kona 1week ne. Da ga nan ina son na shiga U.S ma duba wasu takarduna a gidan can”.
Da ƴar tsokana Daddy ya ce, “To ko na jiraki ne Sweetheart. Kin san fa na daɗe bamuyi tafiya tare ba ina jin kewar hakan”.
Dariya tayi da faɗin, “Daddy karka sa Naseer ya ɗauka na ƙwace masa fadarsa ta autanci fa.”
Shima darawar yay cike da nishaɗi yana faɗin, “Ai yace yanzu shi ba auta bane. AA ne Auta. Banda ƙarfin hali an taɓa ƙwace ɗan wani gida a bama wasu.”
Murmushi Lulu tai da cewa, “Nakune ai Daddy, wake da iko da shi sama da ku?”.
“A'a fa Mawaddat son kai da maida ɗan wani naka. Da haka ne ai da kema na haƙura na barma su Dada. Mahaifinsa na sane da abinsa kafin ya waiwayone kawai. Yanzu dai ki duba idan kinada dama zuwa hutun sai na jirakin, dan nima zan shiga U.S ɗin insha ALLAH. Nanny ɗinki ma ta kirani wai bata da lafiya sosai zata koma ƙasarsu Gambia tai jiyya. Amma nace ta ɗan jirani har naje sai ta wuce”
Sosai Lulu ta nuna tausayawa da mata addu'ar samun lafiya. Da ga haka suka cigaba da hira har lokacin fitarta yayi. Tare suka fito da Daddy ɗin har da Mommy data samesu itama. Ta samu Ummita na jiranta, dan haka bata ɓata lokaci ba ta ɗan tattaɓa AA da masa kiss tana jaddada ma su Amrah su ɗauki saƙon Ammah a ɗakinta idan zasu wuce kai AA ɗin yini can yau kasancewar juma'a ce duk sati can ake kaisa dama. Sun amsa mata da to ta shiga mota suka wuce....
________★
Kamar koda yaushe Ammah tayi farin cikin ganin jikan nata. Dama gashi juma'ar ƙarshen wata ce yaran gidan duk zasu zo. Shima cike da ɗokin ganinta ya maƙalƙaleta dan ya saba da kakarsa kasancewar ana kaisa. Da yaga Asma'u ma haka ya dinga zallo dan ɗan lelenta ne. Su Amrah basu jimaba suka wuce duk da ba haka Asma'u taso ba. Sai dai zasu wuce school ne dole babu yanda zasuyi. Itama yau bazataje bane saboda tun jiya tana kwance babu lafiya. Maryam kuwa tana gidan aunty Bilkisu saboda makaranta tafi mata kusa da ga can yasa tafi zama a can yanzu sai weekend ake ganinta anan gida tunda an zama ƴan jami'a bisa tsayawar Smart, da. Yaran Abba mata basa shiga jami'a sai a gidajen mazansu. Itama ganin an kawo kuɗi yasa Smart cin ƙarfin Abban da ƙyar dai ya amince ta fara. Shi kuma Smart yayi hakane saboda yasan dangin su Ahmad ƴan boko ne na gani kasheni, baya son ƴar uwarsa ta shiga cikinsu ta koma baya. Yanzu ko koba komai taci ƙarfin kusan shekara biyu kafin bikin tunda gashi yanzu tana da shekara kusan ɗaya. Bikin kuma shekara ɗaya aka saka.
Koko Amma ta fara bama AA sai ya ƙi sha ya fara bultso mata shi. Cikin dungure masa kai da faɗin, “Ɗan nema yau kuma kokon ne bazaka sha ba. Kaima dai tsurfa irin ta Babangida yana yaro duk ka iyata.”
Dariya Asma'u da ke kwance take musu. Ta ce, “Kai Ammah yayan ne yay tsurfa?”.
Ammah ta ce, “Tab har ma ana magana. Ai Hydar al'amarin sa daban ne dana kowa. Kinga tashi haɗa masa tea ko zai sha”.
“To Ammah. Amma ƙilafa baya jin yinwa ne.”
“Eh to da wannan kuma. Sai dai kum....” dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammah ɗin. Tashi Asma'u tai ta ɗakko cikin zumuɗi take faɗin, “Ammah Yaya Hydar ne”. Murmushi itama Ammah tayi, dan haka Asma'u ta ɗaga tana gaishesa cikin farin ciki da girmamawa. Da ga can ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta jama'ar gidan tace kowa lafiya yake. Ya tambayeta miyasa bataje makaranta ba ta sanar masa tun jiya bata da lafiya shiyyasa Ammah tace yau kar taje sai monday.”
“Okay” ya faɗa a taƙaice cikin rashin son hayaniyar nan tashi. Har zata miƙama Ammah wayar ya sake faɗin, “Kinje asibiti ne?”.
Amsa ta bashi da cewar, “A'a Aunty Mawaddat ta turomin Doctor ya dubani da dare”.
Da mamaki ya ce, “Gidan tazo?”.
“A'a Yaya ai bata iya zuwa har yanzu, ta kira Ammah ne suka gaisa shine taji Ammah namun faɗan shan magani. Tace mata ta barni bari doctor yazo ya dubani sai yay min allura idan ban son maganin ne”.
“Yayi”.
Ya faɗa a taƙaice. Da ga haka yay shiru. Ita kuma sai ta miƙama Ammah wayar. Ya gaida Ammah cike da girmamawa. Ta amsa masa da kulawa. Dariyar wasan da Asma'u kema AA ya jiyo. Ya ce, “Wake dariya haka?”.
Ammah ta ce, “Babana ne Asma'u kema wasa.
“Yau kuma anan ya kwana kenan?”.
Da ƴar dariya Ammah tace, “Banda abinka Hydar ina mai shan no-no zai kwana wani waje bada uwarsa ba. Yanzu su ƴan biyu suka kawoshi dai. Sai kuma dare sai Mubarak ko Abdull su maida shi. Sai dai nasan yanda baida da rigima kwana nan ma zai iya yi batare da ya damu ba, badai a taɓa gwadawa bane. Da har haƙurinka ya biyo bai bar komai ba shikam”.
Ɗan murmushi kawai Smart yay da ga can da faɗin, “Hummm”.
Sanin halinsa na rashin amsa komai dalla-dalla yasa Ammah fahimtar abin cewar kenan. Dan haka ta ɗora da faɗin, “Hydar baka ganin ya kamata kayi magana su taho haka nan ko ALLAH zai sa a dace komai ya daidaita, duk da dai bata iya shigowa gidan nan har yanzu kuma tana son hakan. Ko tazo sai dai ta tsaya waje shima da ƙyar ake sha dan sai ta tafi da ciwon kai. Amma ƴar albarka kullum bata gajiya sai ta kirani safe da yamma taji lafiyata. Kayan shayi da su sabulu zuwa kayan buƙata irinsu-irinsu sai dai na bama wani. Ai duk wanda yay wannan shiga tsakani na kai da iyalinka bazan yafe masa ba a wannan karon” hawaye suka cika mata ido.
Cikin rauni