Showing 63001 words to 66000 words out of 131687 words

Chapter 22 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt

09 Dec 2024

7895

hakannan? Ai nazata ko'a hanya kika ga jinina dana Aliyu kya gudu dan kunya. Baku so ba ALLAH yayi, Aliyu ɗan Aliyu Mawashi ya tabbatar muku shi ɗan halak ne. Kuma ki sanarma ɗayan Mugun ni da shi wasa yanzu zai fara...”
Rawa jikin Dada ya farayi kamar mazari. Tuni hawaye sun cika mata idanu, muryarta na rawa ta ce, “Mawaddat ni kike ma irin wannan ɗibar albarkar haka? Saboda namiji? Namijin ma da bai damu da ke ba bai taɓa sonki ba sai da akai masa tallarki da sunan auren yarjejeniya. Kin bar gidansa bai nemi inda kike ba...”
Cikin ƙyaɓe baki Lulu ta ce, “Wannan gurgun tunaninki ne Dada. Shiyyasa kika zabgan ƙarya Aliyu ya sakan ko kunya baki ji ba saboda kina son na auri shashashan jikanki da baida freedom ɗin kansa sai na ubansa. Yo ai ko maza sun ƙare a duniya gara na mutu babu aure dana auri wannan shakatafin da ko ƙirrar mazan ƙwarai babu a jikinsa soƙai-soƙai kamar wani ɗan talo-talo. Aliyu ya soni ko karya soni wannan ba matsalarki bace ba, jeki fara gyara naki matsalar auren da ya rage saura kwanaki hope ɗinki ya kufce inba haka ba wlhy azumin bana sai mun buga miki gwauruwa tashi gari ya waye....”
“Mawaddat!!”.
Daddy ya faɗa da ɗan ƙarfi cikin tsawatarwa. Cikin girmamawa ta ce, “Na'am Daddy”.
Kansa ya girgiza mata alamar ta bari. Harara ta ballama Dada ta ɗauke kanta. Mommy da Uncle Muneer abin ai ya girmi kansu. Yayinda Dada ta saki kuka tana nuna Lulu. “Ni zaki cima mutunci Mawaddat saboda na zo gidanku ganin ɗanki. Ni kike nunama kin haihu kin san zafin ɗa?”.
Baki Lulu ta murguɗa mata da taɓe baki. Uncle Muneer ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyara zaman AA a cinyarsa da yin gyaran murya ya dubi Dada. “Dada ya isa haka dan ALLAH miye abin wani kuka anan. Mawaddat yarinya ce ai, sannan irin wannan ranar nake gudun mana dama shiyyasa nake nuna miki ki daina biyewa Yaya da al'amarinsa. Yarinyar nan itace dai zata zauna da Tajuddeen, tun farko da aka ƙulla tace muku bata so, amma kika damu kanki, kuma godema ALLAH rabon yaron nan na namiji ne, da mace ne wlhy komai zai iya faruwa ciki harda iya rasa rai....”
“Yanzu dai Manneeru kana sake goyon bayanta ta cigaba da zagina kenan?”. Dada ta faɗa cikin kuka. Da sauri ya ce, “Sam ba haka nake nufi ba Dada. Taya zan giyama Mawaddat baya ta zageki kuma. Amma kuyi haƙuri. Ina son a gyara kuskuren nan ne saboda gaba. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba yarinyar nan ta kuɓuta a hannun Yaya mi kike tunanin zai faru? Ko kuma data rasa ranta a wajen yunƙurin zubar mata da ciki. Yaya yayi amfani da ke ya barki a ciki. Sannan da mijin yarinyar nan fitinanne kina ganin zai ƙyaleku ne akan yunƙurin zubar masa da ciki har sau biyu? Ga shi kunje kunce mata mijinta ya saketa! Shin aure kan aure kukai shirin mata komi ma wai shin ni na kasa gane muku?”.
Tsigil Lulu ta ce, “Abinda suka shirya mun kenan Uncle, kuma wlhy a lokacin na ƙudiri aniyar suna ɗaurashi zan kashe Tajuddeen ɗin ne sai dai nima a kashe ni!”.
Babu wanda bai kalletaba yanzu ma a razane. Itako hankalinta kwance tama miƙe tana hararar Dada da cigaba da faɗin, “Kuma ko yanzu ba haƙura nayi ba. Dan bana barin bashin gaba. Sulaiman sai yamun bayanin alaƙata da shi da ya addabi rayuwata data mahaifina, dan haka ku jira sammacin kotu dan sai munyi shari'a, idan Aliyu ya iya muku haƙuri da kawai ci ni bazan barku ba”. Daga haka tabar wajen fuuuu. Dada ta zabura zata bita Uncle Muneer ya riƙeta yana girgiza mata kai. Sai ta ƙara fashewa da kuka ta maida faɗan a kan Daddy. Wai duk shi ya kitsama Lulu taci mata mutunci tasan Lulu bata da wannan wayon. Daddy dai ko tari baiyi ba, sai Uncle Muneer ne ya shiga mata magana cikin ɓacin rai akan shi da yasan abinda zatayi kenan da bai kawota ba. Yanda yake faɗa zai tabbatar maka ransa ya ɓaci, dan sosai take cima Daddy mutunci da masa gori. Amma ko tari bai mata ba balle aje ga batun ramawa. Su Amrah ne dai suka sake zuwa suka kira Lulu. Aiko sai gata a fusace. Ranta yafi na kullum ɓaci akan abinda Dada kema mahaifinta, atake na ƴan ƙwayar ya motsa ta rufe ido taima Dada tas har sai da ta gudu dan kanta saboda ganin buyagin Lulu fa ya haifi nata. Dan yanda Lulu ke ruwan bala'i zaka rantse bata taɓa sanin Dada ba a rayuwarta balle tuna qlaƙarsu. Uncle Muneer ransa ya kai matuƙar ɓaci, da yasan abinda Dada zatazo tayi a gidan mutane wlhy dabai kawota ba. Aiko ƙin kaita yay gidan Alh. Sulaiman da tace zata duba Tajuddeen shima.
Lulu kam da bayan fitarsu Daddy ya hauta da faɗa sai ta sakar masa kuka. Dole ya fice cikin ɓacin rai dan duk da yayi shiru kalaman Dada sun matuƙar zafar masa zuciya shima, amma bazai so Lulu ta cigaba da mata tsiwa ba matsayinta na kakarya. Ya danne ne kawai saboda dattako. Lulu na komawa ɗakinta kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Ɗauka tai kawai ta fashe masa da sabon kuka. Ƙirjin Smart yay wata irin harbawa. Dan dama kiran nashi ne bana Uncle Yousuf ba. Haka yake yi sai ya kirata da layin Uncle Yousuf ɗin yaƙi magana. Taita faman sallama yay shiru har sai ta gaji ta katse, wani lokacin tabi kiran wani lokacin ta share. Ko tabi baya ɗauka kuma sai dai ya bama Uncle Yousuf ɗin. Dama shi burinsa jin muryartane, wani lokacin ma yakanyi sa'ar jiyo AA na kuka musamman idan darene a Nigeria kasancewar AA ɗin ya dage da musu kukan dare yanzu. Da ance ɗaya tayi babu sauran zaman lafiya kuma sai anyi sallar asuba. Wani lokacin har Daddy fitowa yake ya ɗaukesa aita masa addu'a da rirriga amma yaron nan ko'a jikinsa. Mommy tayi, Ummita tayi Iya Tabawa tayi. Lulu kam sai dai tayi tagumi kawai yana kallonsu, wani lokacin ma ba'a tashinta sai idan kukan yayi nisa ne sosai ace ta tashi ta shayar da shi. Amma yaron nan ko'a jikinsa, wani lokacin ma dan zuciyar tsiya irin ta uban baya ko kamawa.
Kasa sauraren kukan nata Smart yayi ya yanke kiran, cikin tashin hankali da damuwa ya nufi Uncle Yousuf kamar zai fasa kuka ya ke faɗin, “Kuka takeyi, ka kira kaji mike damunta Please Uncle”.
Shima Uncle Yousuf hankalinsa ya tashi, dan yasan duk abinda ya saka Lulu kuka ba ƙarami bane. Wayar ya kira tare da saka Hans-free. Kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauka. Tambayoyi Uncle Yousuf ɗin ke mata cike da kulawa batare da ko jiran sun gaisa ba. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa. Smart ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa da suka kaɗa sosai. Shi dai tunda ba wani abu ne ya sameta ba ai da sauƙi. Lallashinta sosai Uncle Yousuf yay, sannan ya mata faɗa da nasiha akan rashin kunyar da taima Dadan. Ya ce karta sake babu ƙyau hakan. Dada tamkar mahaifiya take a gareta. Ta bashi haƙuri da tabbatar masa bazata sake ba. Amma a ranta fa tasan ita da Dada fa ai haihata-haihata (🤣😂 ALLAH ya ƙyauta su Lulu an san daɗin ɗa🥱🚴👏).
Cikin tsokana Uncle Yousuf ke duban Smart yana faɗin, “Darun matar nan taka sai kai Aliyu, ni dama nasan wlhy bazata ƙyale Dada ba. Kuma duk a wajensu ta kwaso wannan masifar ai dan mudai a family namu babu mafaɗaci”.
Murmushi kawai Smart keyi, a ransa yana sake jinjina hali irin na Lulu. Yasan tabbas yaransa sun bani da masifa tunda shima dai ba raga masa ake ba. Wani lokacin idan tana faɗa har mamakin wai kanta baya ciwo yake yi. Tana da tsiwa sosai, ga shi sam babu tsoro a idanunta. Ita dai kawai zaman lafiyarka da ita kada ka shiga gonarta ne kawai..........✍️






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣






.......Alhmdllh sosai jego yayma Lulu ƙyau, ga Iya Tabawa na mata wani sirrintaccen gyara irin na mutanen da cikakke da ke zama a jikin mace duk da bada kanta ta haihu ba. Gefe kuma Aunty Saliha ta sake kawo wanda sukai mata gyaran aure na nasu suma yanzu. Mommy ma na nata ƙoƙarin. Sai ruwan addu'oi wajen Malam na Yakasai da ake amsowa Lulu na tsarin jikin da yanayin da take ciki game da Smart. Wannan ƙoƙarin Ammah ne da Abbah. Dan ita kanta Ammah kan zauna da kanta tai mata addu'oi a cikin ruwa da ma ruwan zam-zam shima AA ana bashi.
Sai Daddy da ya kawo mata malama har gida tana ɗora mata karatun addini saboda Ummita zataje ganin gida itama. Da yake Lulu tasa abun a ranta hatta Mubeen zaunarwa take ko su Amrah su ƙara mata karatun. Gefe guda kuma tana ta ciku-cikun yima ƙungiyarta rigester shima da taimakon Daddy da Uncle Khamil na Abuja da shima ya bata goyon baya. Koda wasa bata son tuna Smart, dan ko AA ta kalla babansa yazo mata a rai kanta ya dinga wani irin masifar ciwo kenan dake tayarma kowa na gidan hankali. Inda aka yankata Alhmdllh yana sake warkewa, Aunty Khadijah matar Coach ce ke zuwa dubata kullum babu fashi, idan abinda ya kama taje asibiti ne kuma sai ta shirya Mubeen ya kaita suje suga likitan su dawo. Da Ummita zata wuce shatara ta arziƙi Daddy ya haɗa mata, itama Lulun ba'a barta a baya ba, Uncle Khamil ne da yazo ya wuce da ita duk da dai jirgi sukabi zuwa Abuja tare, dan Lulu ta gargaɗeta zuwa ɓagwai saboda gudun mutanen Alh. Sulaiman kar su cutar da ita ko iyayyenta.


★A ɓangaren Ammah tsaye take wajen kaima UBANGIJI kukanta akan dai-daituwar zaman waɗan nan ma'auta. Tare da yawaita sadaka da azumi. Yaranta kaf basu zauna ba har ƴan uwanta kasancewar suna da haɗin kai. Yayinda itama Ummah ta kasa zaune ya kasa tsaye wajen sake lafto sabbin asirai kala da iri akan Ammah da Smart kai harma su Aunty Amaryar ba bari tayi ba. Dan a kwanakin nan da ƙyar suka samo kan Abba da aka nema juyarma da kai. Sai Alhmdllh al'amarin baiyi nisa ba ya sake shi, hakan ya tada hankalin Ummah kam sosai, dan ba ƙananun kuɗi ta kashe a aikin da akaima Abban ba, amma sai gashi ya tafi a banza cikin ƴan kwanaki ƙalilan....


*_UK LONDON_*


Hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk abinda UBANGIJI ya ƙaddara shi a matsayin naka babu wani mahaluki a duniya da ya isa canja wannan ƙaddarar. Dan kuwa a lokacin da Ummah ke can tana faɗi tashi akan abinda bata iya jayayya da shi ba anan ƙasar England ƙaramin labari ne ke neman canja kansa akan Aliyu Mika'il Idris Mawashi, wato Smart Mawashi zuwa babban gaske gagarumi. Dan fa manyan clubs da ke zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa sun fara bayyana kansu a fili yanzu. Wannan yasa aketa faman kai kawo da dambarwa tun barowarsu Canada shi da Manager ɗinsa Uncle Yousuf. Sosai ake ta kai ruwa rana da bata kashi a tsakanin Coach's ɗin mayan clubs ɗin. Shi dai Smart ya duƙufa gayama UBANGIJI da neman zaɓinsa. Dan bashi da wani zaɓi sai nashi. Yayi alƙawarin duk inda ya tsinta kansa zaiyi aiki tuƙuru in sha ALLAHU duk da a cikin zuciyarsa yana da club ɗin da yafi so da ƙauna kuma gashi a cikin masu zawarcin nasa. Amma sai bai Zafafa ba ya bar ma UBANGIJI komai sai su Uncle Yousuf da keta kaiwa da komowa shi da Coach ɗinsu na Queen City da duk manyan masu faɗa ajin club ɗin.
Sosai mahawara ta ɗauki zafi a tsakanin manyan clubs guda uku da suka riƙe wuta fiye da sauran, dan kowa ya gagara janyema kowa. Sannan duk sun zuba manyan kuɗaɗe akan Smart ɗin masu girgiza zuciya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta sake zama babba. Dan manyan gidan jaridu na duniya musamman a fanin ƙwallon ƙafa sunyi ƙur da idanunsu akan wannan batu domin ganin wazai ɗauki wannan lu'u-lu'un a cikin juji. An buga an turza an kai matuƙar kai ruwa rana kowa yaƙi sakarma ɗan uwansa, dole aka tafi mataki na biyu wato jin ra'ayin Smart game da wane team yafi sha'awa shi a ransa. Tun farko Smart nada ra'ayinsa dama, amma ya zaɓi barma UBANGIJI zaɓinsa. Har a yau da aka kai wannan matakin na jin ra'ayinsa bai ji zuciyarsa ta canja da ga abinda ta ke so ba tun yana da ƙuruciya. Dan haka bai wani basu wahala ba ya faɗa musu zaɓinsa wato *_ARSENAL FC_*. hankalin sauran clubs biyun da sukai gogayya da Arsenal ɗin ya ɗaga, a take suka ƙara kuɗi akan wanda suka saka a farko, amma dai Smart nakan bakansa Arsenal ɗin dai, dole suka haƙura dan aikin gama ya gama Arsenal tayi nasarar siyensa da kuɗi kimanin dala Miliyan arba'in.
Duk wani masoyin Smart a wannan rana yana a cikin matuƙar farin ciki mara misali, Ammah duk dauriyarta sai da tai hawaye lokacin da Uncle Yousuf yay kiransu yake sanar musu al'amari fa ya kai girman da aka daɗe ana fata. Sai kuma addu'ar cigaba da samun nasarori ga Smart ɗin. Amma wannan tsanin kam an haye sama ƙololuwa.


Sun ɗanyi zaman meeting meeting da ƴan cike-cike na tsarabe-tsaraben da aka san ƙwallo da shi su da Manager ɗin sa Uncle Yousuf da shi kansa Smart ɗin. Kafin dai a ƙarƙare ya saka hannu a ƙarshe. Da ga haka akaje matakin duba lafiyarsa ciki da bai. Alhamdullah nan ma normal an samesa da cikakkiyar lafiyar jiki dama ta sassan jiki. Bayan kammala waɗan nan ya ziyarci Arsenal camp domin yin hotuna da gabatar da shi ga teammate ɗinsa. Ya samu tarba fiye da yanda yay zato da tsammani ga teammate ɗinsa. Dan tunda suka shiga cikin camp ɗin bakinsa bai bar ambaton ALLAH ba. Kwarjininsa da hasken musulunci ya sake ƙawatashi a garesu da girmama mutuncinsa. Sunyi hotuna da duk abinda ya dace a wannan ranar kafin a wuce mataki na gaba. Wato gabatar da Smart Mawashi ga fans.


Duk wani masoyin Arsenal ya halarci babban stadium ɗinsu da ke a cikin birnin London. Wasuma da ga ƙasashen ƙetare suka zo domin ganin sabon yaron na Arsenal da za'a gabatar saboda soyayyar da sukema club ɗin. An cika matuƙa da har sai da Smart ya dinga jin kansa na sara masa. Ga kuma masu kallo a television. Amma ya daure bakinsa na cikin ambaton ALLAH ya fuskanci masoya. Wani irin ihu da stadium ɗin ya ɗauka lokacin da yake shigowa fuskarsa ɗauke da sassanyan murmushi yana mai ɗaga musu hannayensa biyu yay dai-dai da wanda su Mubeen suka ɗauka suma a cikin falon gidansu da Lulu ce kawai babu tana can ɗakinta tana barci. Hatta AA na a hannun Daddy dan har shi ake wannan kallo. Fitowa tai a ruɗe, sai dai ganninsu duk suna kallon ƙwallo a tv kuma duka gidan ya sata tsayawa turus cikin dafe kai da jan tsaki. Babu ma wanda yasan tanayi dan hankalinsu bama ya wajen. Cikin jin haushi ta juya ta koma duk da tayi mamakin ganin harda Daddy da su Iya Tabawa wai ake kallon ƙwallo yau a gidan. Abu ne ita dai da bata taɓa gani ba. Ta dai san Mubeen nayi da su Hussain idan sun zo. Amma kosu Amrah ta sha jin suna faɗa da Mubeen idan zai kalla ƙwallo ya hanasu su kalla film. Amma wai yau sai gashi ƙwai da kwarkwatar gidan ta gani. Abinda ma Lulu bata lura da shi ba shine harda masu wanki duk suna a falon, dan suna da ga ƙasa ne zaune yasa bata gansu da ƙyau ba... Kamar yanda a gidan Daddy suke kallo a gidan su Smart ɗin ma hakane. Dan su Mubarak ne suka cika gidan da abokansu da samarin anguwa. Yayinda ba'a bar Abba a baya ba da ga shi har Ammah da sauran yaran gidan sun cika a falonsa danƙam dan shi yasa a tattaro kowa yazo. Ran Umma da Mama a mutuƙar ɓace yake. Zuciyar Umma bata nema fitowa ta baki ba sai da aka nuna Smart na shigowa cikin tsakkiyar tarin tawagar turawan nan yana ɗan wasa da ƙwallo, stadium ɗin ya ɗauki ihu kamar zai tsage. Sai kuma sanda aka ɗaga rigarsa mai lamba tara yanda suka ɗauki ihu mai jijjiga kunne ita zuciyarta suke jijjigawa, dan a bazata kawai sai ta fashe da kuka. Da farko babu ma wanda ya lura da ita sai da Huwaila ta ce, “Ummah ke kuwa miya sakaki kuka? Ko duk farin cikin ganin Yaya Hydar ɗinne?”.
Lokacinne hankalin kowa ya koma kan Umma. Sai dai kafin ma wani ya iya cewa wani abu ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login