Showing 42001 words to 45000 words out of 131687 words

Chapter 15 - FURAR DANKO PART 2 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt

09 Dec 2024

7902

shirin, yayinda zuciyarsa ke masa kai-kawo akan sakkowar Daddy da sauri haka. Sai dai baicema Uncle Yousuf komai game da wannan ba. Ya daiyi murmushi da cema Uncle Yousuf batun Alh. Sulaiman wannan wasan nashi ne. Jin wai Lulu kuma tace a sakama yaron sunansa ya sakashi sake yin murmushi da lumshe idanunsa, dan harga ALLAH baiyi tunanin hakan daga gareta ba. Irin farin cikin da Smart ke ciki yau da banne a rayuwarsa, dan ko randa sukaci nasarar cin ƙwallon nan baya jin farin cikin sa yakai koda kwatar haka. Ya kira Abbah da Ammah cikin zumuɗi, inda suma suketa tsokanarsa cike da farin ciki tare da masa barka da arziƙi. Ya ce, “Ammah shiyyasa kullum sai naita mafarkin yara, ashe takwarana yana isarmin da saƙon ya kusa zuwa duniya ne”. Dariya Ammah keyi, cikin tsokanarsa ta ce, “Oh ni Hydar ko irin ƴar kunyar ɗan farin nan babu ma?”. Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da rufe fuskarsa da fillon kujera kamar yana gabanta, ya ce, “Ammah sai anjima to nayi shiru”. Itama dariyar ta shiga yi masa sosai cike da jin shauƙi da tarin ƙaunar tilon ɗan nata namiji........✍️




_🚴🚴🚴Yau fa dangin Smart an cika mu da iyayi, to ɗa dai bara mu bada ba ehe dan zufarmu ce😏_






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣






........Koda ya ajiye wayar miƙewa yay zuwa cikin bedroom ɗin sa. Alwala yay domin gabatar da nafilar godiya wa UBANGIJIN talikai mai ƙyautar da kuɗi ko ƙarfin mulki baya badawa a duniya. Gaskiya tunda yake a rayuwarsa baya jin an taɓa masa wani suprice mai taɓa zuciya da jijjiga jinin jiki irin na yau. Bayan ya idar ya jima yana kwararoma ɗan nasa da Lulu kanta addu'oi, tare da fatan ALLAH ya kawo musu dai-daiton wannan al'amari da ƙarshensa cikin sauƙi su cigaba da rayuwa a inuwa ɗaya tamkar sauran ma'aurata. Wayarsa ya sake ɗauka ya dawo falon.


A karan farko Smart yay kiran number Daddy yau tunda yabar Nigeria. Sun gaisa cikin mutunta juna da nuna jin nauyin juna musamman ma shi Smart ɗin. Daddy ne ya fara masa barka, shima Smart ɗin yay masa barkar. Da ga haka Daddy ya bashi haƙuri akan abinda duk ya faru a baya da masa bayanin akwai dalilin yin hakan, zai masa bayani amma ba yanzu ba sai sun haɗu. Sai batun ɓoye masa ciki da inda Lulu take nan ma ya bashi haƙurin kamar yanda Uncle Yousuf ya bashi da masa bayanin dalilin yin hakan. Cikin girmamawa Smart ke roƙon Daddy da ya daina bashi haƙuri shi bai taɓa riƙesa a ransa ba ko ganin laifinsa. Yana masa kallon uban ne da kuma uzuri dan yasan koma minene yanada dalili, ya kuma fahimci hakanne tun a randa Alh. Sulaiman yasa aka satoshi, shiyyasa ma ya haƙura da halayen Lulu ya sake komawa aikin gidan. A yanzun ma yana roƙon Daddyn da ya bar wannan wasan a hannunsa ya kwanta ya huta ya haifa masu masa yaƙin ai, fatansa kawai in har bai shiga hurumin daba nashi ba yana son jin tushen matsalar ne kawai. Murmushin jin daɗi Daddy yayi da ga can har Smart yana iya jiyosa. Da ga haka ya shiga sanya masa albarka da tabbatar masa in sha ALLAH zai sanar masa komai, sannan ya ɗauki kansa matsayin ɗa a garesa koda wasa ya daina jinsa daban a cikin family ɗin sa. Bama shi da suka haɗa jini ba a yanzu ko ahalinsa sun zame musu ahali ai suma. Sosai Smart yaji farin ciki da waɗan nan kalamai na Daddy, tare da sake jin kimarsa da mutuncinsa a zuciyarsa.. da ga haka sukai sallama cikin mutunta juna.
Bayan sun ajiye wayar Smart ya ɗakko laptop ɗin sa ya saka flash ɗin nan a ciki. Ba komai bane face videon yaronsa mai tsananin kama da shi sai Mawaddat ɗinsa da keta kallon jariri tana wani munafukin murmushi tare da motsa lips ɗin ta sai dai baya iya jin mi take faɗa, sai matashiyar matar da ke gefenta tana tofama yaron addu'a. A hankali ya lumshe idanunsa da sakin wata irin raunananniyar ajiyar zuciya ƙwallar ɗinbin farin ciki na sake cika masa idanunsa. Shi yama rasa mizaiyi domin nuna farin cikinsa akan wannan ƙyauta ta UBANGIJI mai tsadar gaske da kuɗi ko alfarma bata badawa a wannan duniya.. ji yake inama zai iya tauntsuwa ya gansa gabansu, kai shi koda muryarta ne yaji ma ta waya zai rage masa nauyin zuciya. Ƙasa haƙuri yay ya turama Uncle Yousuf saƙo akan neman number ta. amma sai ya samu reply cewar babu waya a hannunta amma akwai ta yaron da ya kuɓutar da su mai suna Usman zai tura masa. Duk da ya ɗan ji kishin nasa ya motsa sai ya danne...


*_NIGERIA_*


Sosai ta yi wata irin rama data sake bayyana tsufarta sosai gamai kallo. Ga shi bata da isashiyar lafiya sakamakon tsangwama da rashin kulawar da take fuskanta a hannun matar ɗan nata. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai gara rayuwar surukan nata data jima tanayi a shanun talla. Musamman ma ita matar Uncle Manner ɗin. Itama kuwa sai gashi ALLAH ya bata damar ramawa. Abinda yafi yima Dada ciwo a zuciya makircin Hajiya Aneesa, dan in har Uncle Manner na gida bai isa gane komai akan matar tasa ba, kulawa take bama Dada kamar uwarta mahaifiya, amma yana gusawa kashi ma ya fita daraja. Ta dinga gasa mata azaba da magana kenan masu zafi har sai hawaye sun cikama Dada ido. Ga shi ta hana ƴaƴanta raɓar Dadar sai ubansu na nan, daga bayama ko uban nasu na gida sai basa zuwa, da tayi magana kuma za'ace makaranta ce ta ɓoye su. Kaɗaici da damuwa sunma Dada yawa, ga kewar mijinta da rashin ƴancin data saba dashi na tsawon shekaru, babu irin kalar kiran da bataima Baba Garko da tura masa saƙo ba amma tamkar ma baya ganinta. Abinci kuwa sai wanda aka gadama ake bata dan nata daban ake dafa mata garo-garo su kuma suci lafiyayye. Idan Uncle Manner ya gani kafin ma yace wani abu matarsa ta fara zayyana masa zancen Dada ce tace ai mata, sunyi-sunyi kuma ta kafe harda musu tsiya. Sanin halin mahaifiyar tasa da yayi da irin hantara da ƙyarar da takema matar tasa tunba yanzu ba saya baya maida hankali ko ƙin yarda. Idan kuma ta saka masa kuka da nuna son ita dai a canja mata gida ko'a roƙar mata mijinta sai zuciyarsa na bashi son komawa wajen baban nasu ke damunta kawai. Yakan zauna yay mata nasiha da nuna mata illar biyewa zuciya da ɗan uwan nasa da tayi, yanzu gashi nan ya barta a halin ƙaƙa nakayi, tunda ko Nigeria ya ƙi zuwa, hasalima yaji ƙishin-ƙishin tattare iyalinsa da yake shirin yi su bisa inda yake a ɓoyen saboda tsoron umarnin mahaifinsu akan duk randa ya diro ƙafarsa Nigeria tun a airport a kamashi. Ga kuma tashin hankalin rashin sanin ina Lulu take a yanzu. Dan zuwa yanzu ta gama tabbatar ɗan nata nada manufa akan al'amarin da nasa. Ga Baba yasa an cafke Tajuddeen da ya shigo Nigeria a watan daya gabata, saboda bakinta daya furta cewar tare da shi ake komai ai. Iya binciken Tajuddeen anyi amma ya rantse shi bai san ina ubansa ya kai Lulu ba, ya dai san da su ake komai da farko amma shima kansa bai farga akwai wata manufa a ziciyar mahaifin nasa ba sai bayan na son ya aura masa ita. Sai a randa ya rabosa da Canada ya kwashe su Lulun. Ya kuma rantse a yanzu bai san ina yake ba, dan ya ɓoye kansa ne. Amma sam Baba Garko yace bai yarda ba, ƴan sanda su cigaba da riƙe Tajuddeen ɗin har sai Alh. Sulaiman ya miƙa kansa koya sako Mawaddat. Baba Garko yayi hakane kuma dan ya jima da sanin Tajuddeen shine zuciyar ɗan nasa. Kamar kuma ya sani dan hankalin Alh. Sulaiman na can a tashe game da kama masa yaro, dan haka ya baza mutanensa suketa shige da ficin ganin an saki Tajuddeen ɗin amma hakan ya gagara. Dan Baba ma da babansa, duk ƙarfin ikon da suke jin suna da shi da alfarma a ƙasar Baba Garko ya taka su ya shanye. Wani lokacin ma da bazarsa yake rawa.
Waɗan nan abubuwa marasa daɗi sunka haɗu suka tararma Dada a zuciya dan haka sam ta kasa lafiya. Ga shi a lissafinta wannan watanne na haihuwar Lulu in har Alh. Sulaiman bai salwantar da cikin ba kamar yanda yay niyya tun farko, sannan iddarta ta kusa cika, tana cika kuma hakan na nufin sun rabu kenan, dan tasan irin kafiyar Nana garko, sai idan da rabon su koma ne ma sai an sake ɗaura mata aure da mijin nata na auren tun jajayen sawu. Kwanciyarta asibiti kusan uku a tsakanin nan, a yanzu hakan ma tana asibitin tun shekaran jiya ƙarƙashin umarnin likita, sai banka mata allurar barci suke dan ta samu nutsuwa...


★Tsaf Alhaji Garko na biye da al'amarin matar tasa, kuma ya maida aurensu tun a randa ya saketa kodan tausayin yaransu. Amma ya zaɓi yin biris da ita dan lamarin jikar tasa na ci masa zuciya. Ya kuma ɗauki alƙawarin hukunta ɗan nasa akan wannan al'amarin. A yanzu haka ya baza cid suna kan bincika masa inda yaje ya ɓoye kan nasa, dan yanaji a jikinsa a duk inda yake Mawaddat tana tare da shi....


__________★


Kamar yanda bokanta ya sanar mata ta koma sai da tai yanda tayi wajen hillatar Abba ya sake barinta fita yau suka koma ita da Hajiya Naqiba. Sun gurfana a gabansa suka gama masa bayanin komai, cikin jinjina kai da bugun ƙasa ya ce, “Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari kuma iyayensa sun sani, sai dai an gargaɗesu da sanar wa kowa shiyyasa sukaja bakinsu sukai shiru. Kamar yanda na sanar muku tun farko bawai yaron zai gagaremu bane, kawai dai tsaye yake da ƙafafunsa wajen bautama ALLAH tamkar mahaifiyarsa. Bata gajiya kuma da nusar da duka ƴaƴanta ta wannan fannin. Shiyyasa cin galaba a kansa kamar baya abune mai wahala. Amma zamu gwada sa'armu mu gani a yanzun ma sai dai akan matarsa duk da itama tana nata ƙoƙarin . Sai dai maganar gaskiya ban gano abinda zai iya tasirin rabashi da nasarar da ke tunkarosa ba game da abinda yake yi ɗin. Dan lokacin hakanne yayi. Kunsan ance mai laya kiyayi mai zamani. Abinda kawai zan iya muku aiki a kansa shine nisanta shi da al'amarin matarsa itama kuma a nisantata da duk abinda ya shafesa, wannan zai iya zauta masa zuciya ƙila har al'amarin ƙwallon nasa ma ya iya taɓarɓarewa duk da dai abune mai wahala hakan ta kasance. Sannan kuma ko akan wannan farraƙun tsakaninsa da matarsa in ma anci nasarar sake nisantasun fa na gano akwai haɗari a ciki, kuma haɗarin zai iya dawowa ne matsayin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya gareki. Yaya kika gani ayi ɗin?”.
Ɗan jimmm Umma tayi yayinda Hajiya Naqiba ta zuba mata ido da mata signal ɗin ta yarda kawai babu abinda zai faru ai sune masu nasara. Wannan ƙarfin gwiwar data hanga a idanun aminayar tata ya sata jin jina ma malamin nasu kai da faɗin, “Babu ma abinda zai faru malam in sha ALLAHU. Ni in sansamu ne ma har uwarsa da uban ai musu kalar asirin nan dan na tsani buɗe ido naga Hafsatu a gidan nan wlhy, sauran sakarkarun basu daman ba, dan babu wacce tasha gabana sai ita. Na rasa wane shegen boka ke mata aiki haka”.
Murmushi malam yayi kawai. Sai kuma zuwa can ya nisa da cewa, “Maganar iyayensa gaskiya bamai yiwuwa bane kamar yanda na faɗa miki. Dan matar nan a tsaye take fa wajen bautama ALLAH. Ke dai kawai ai miki na yaran ma zai baki duk nasarar da kike buƙata in har ba'a samu kuskure ba”.
“Bama za'a samu ba malam ayi kawai.” Hajiya Naqiba ce mai maganar. Malam ya amsa musu da to, tare da gaya masu adadin kuɗun da aikin zaici, babu musu ta ajiye masa duk da da ƙyar ta ƙwaƙulesu a hannun Salim, sai da tasha ƙunƙunai ma da ƙananun magana sannan ya bata. Amma da yake tana so haka ta amsa tana sanya masa albarka......


Koda ta koma gida dukkan yanda akace mata ta aiwatar tayi cikin kulawa da taka tsan-tsan, daga haka ta koma gefen kallon yaya wasan zai fara kuma.........✍️


_(Ni dai nace Hummm Ummah kenan🚴😵‍💫)._






_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070




*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗






𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻




𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣






.........*_CANADA_*


Kwanaki Uku kenan da mata cs ɗin, amma Alhamdullah da alamun fara samun lafiya tattare da ita kasancewar bata da ƙan jiki, sai dai kuma Lulu akwai raki. Mahaifiyar Usman da yake kira da Mamy tazo tana tare da su tun shekaran jiya. Hakan yasa take sake ƙara samun kulawa ita da jinjirinta. Ga Ummita na iya ƙoƙarinta itama tako wane fanni. Hakama Usman da Dr Lameer. Tayi mamaki matuƙa da ganin ɗunbin kayan baby da Mamy ta kawoma Aliyu ƙarami. Sai dai yanda matar ke kulawa da su cikin haba-haba ya sa Lulu kasa cewa komai akan hakan. Duk da wannan gata da kulawar da take samu wajen abokan arziƙi zuciyarta a cinkushe take da rashin ahalinta ko guda ɗaya a kusa da ita. Hatta shi kansa uban tafiyar yakan zo mata a rai, duk da a duk sanda yazo ɗin takan yamutse fuskar cikin nuna halin ko'in kula. Sai dai hakan babu alamar zai turesa a ran nata, dan data dubi ɗan jaririn nata zuciyarta kan harba mata, balle kuma idan tana shayar da shi takan zuba masa idanu da tafiya cikin tunani mai zurfin gaske akan al'amarin mahaifinsa. Kasancewar Mamy babbar mace ta jima da hango halin da Lulun ke a ciki, amma bata cewa komai saboda lokacin cewar bai isa ba...


A ranar da su Lulu ke cika kwanaki biyar da zuwan baƙon duniya su Abba da Daddy suka iso ƙasar Canada, tafiyar da tai masifar tada hankalin su Ummah dan Abba yace musu zasuje duba Smart ne zuwa ƙasar England. Jidali iya jidali rasar su Aunty Amarya sun gani wajen Ummah, dan su Asma'u ma basa gidan Ammah catai su tafi gidan yayunsu har sai sun dawo su dawo. Dan haka suka tafi gidan Aunty Bilkisu da shirin idan suka mata kwana biyu sai su koma gidan Hawwah itama su mata kwana biyu. Babu irin zagin da Ammah bata sha ba ranar har maƙwafta sai da suka shigo, inda mutane da yawa suka fara fassara al'amarin Umman da hassada. Dan sukam basu ga wani abin tada jijiyar wuya a nan ɗin ba...


Oho su Ammah ma basu san tana yi ba, dan suna can a hanya hankalinsu kwance. Ƙasar England su Abba suka fara yada zango wajen Smart. Wanda zuwan nasu yazo masa a bazata sosai, dan sam Uncle Yousuf bai sanar masa ba. Tsabar farin ciki baima san lokacin da ya rungume Ammah ba. Turesa tai cikin jin nauyi da faɗin, “Kajimin ja'irin yaro abinda ka koya a ƙasar turawan kenan kuma?”. Cikin dariya da shagwaɓa Smart ya ce, “Ammah nafayi missing ɗinki ne, ALLAH sai nake ganin kamar mafarki nakeyi”. Tsinguli ta kai masa da faɗin, “Bari na tabbatar maka idonka biyu”.
“Ouch!” ya faɗa cikin turɓune fuska yana kallon Abba a marairaice. Abba ya riƙo masa hannu yana hararar Ammah. Daddy da Uncle Yousuf dai dariya sukeyi, dan basu taɓa zaton Aliyun taɓararre bane a wajen iyayen nasa sai yau. Smart ya gaishe da Daddy cikin girmamawa, Uncle Yousuf kam ai baida maraba da aboki duk da yanzu ana ƴar kunyar surukuta kaɗan-kaɗan. Sosai mazaunin Smart ɗin ya ƙayatar da su Ammah, suka shiga godiya ga UBANGIJI a zukatansu da mamakin wannan rahama ta UBANGIJI. Sunci sun sha daga abincin da Smart ya tanada musu a cikin ƙanƙanin lokaci, dan abinci ne na ƴan Nigeria. Bayan kowa yaci ya ƙoshi suka ɗan tattauna, sosai zaman ya sanyaya ran Smart, inda ya fahimci surukinsa sosai a yanzu ya kuma sakko daga fushin daya tafi. Sun tafi zuwa masauki aka bar masa Ammah da Abbah nan. Hakan ya musu daɗi su duka, dan sun sami damar tattauna abinda ya shafesu sosai shi da iyayen nasa. Inda ya ƙara warware musu cigaban da ya samu da wanda yake fatan samu anan gaba. Ƴan uwansa kaf bai manta da kowa ba sai da ya tambaya, har maƙwafta da abokan arziƙi. Ranar dai ansha hira, dan duk rashin yawan maganar Ammah da Smart yau dai sun sha hira abinsu kamar suyita kasancewa a haka suke ji...


Washe gari da yamma suka wuce Canada har da Smart dake jin wani irin faɗuwar gaba lokaci-lokaci, yakanyi sauri ya ambaci sunan ALLAH. Wannan ziyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login