Showing 24001 words to 27000 words out of 59266 words

Chapter 9 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt

26 Nov 2024

3004

sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba.


Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu?"


Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa.


Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata.




Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita.


"Wai ana sallama da mai gidan."
Wani ne yaro ne yake magana a gidan.


Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne?


Luf yayi a d'akin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadi'n." Ka ce gashi nan zuwa."




Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin.




Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko?"


Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi."


Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta.




Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya samu Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah."




Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ?"


Yayi shuru bai ce masa komai ba.


Ya girgiza kansa yana hura 'katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni."


Cike da burga da rashin gaskiya ya d'aga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi k'arfin haka."




Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na mai'ko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi idan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali."


Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa mak'ocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj d'aya na k'okarin d'aura masa ankwa a hannu.


"Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.''


Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun mak'aryaci ne, saboda haka hukuma ce zata raba ni dashi."


Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba.




Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da k'ima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari.


Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis da shi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya."


Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba.




Wai a kace labarin duniya ba ya 'buya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar.




Shahida kam d'aki ta shiga ta ci kukanta ta k'oshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani.




***
"Ranka ya dad'e iyakar ha'kuri nayi kawai abinda na ke so ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani."




Officer ya ce." Saminu kaje ku yi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto."




Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure na ke so nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin ma'karyaci ne na daina yarda da maganarsa."




Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu."


Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana."




Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa."




Yayi jim yana nazari wannan maganar kawai dai ya shata ne ya fad'a amma babu wani dilalli da su ka yi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fad'o kansa a gurin sana'ar tasu.




Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa."


Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa k'aton ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne sheda."


Ya kar'bi zungureriyar takardar ya yi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba.




Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana.




Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai."




Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar maca ce san kowa k'in wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu."


Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake buk'ata daga jikin mace falillahil hamdu.''


Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta."


Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata."


Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za ta yi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin.




*Turkashi!*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


*25&26*
Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.


Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo.


Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."


Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."


"Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne?"




Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje."


Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni.




Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka."


Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa.


Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji."


Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri."


Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai.


Jallabiya yasa ya fita.




Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne.


Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo."




Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba."


Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka."




Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin."
Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa.




'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba.


Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka."


Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah."


Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul sai uban 'kyalli yake.


Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa.




****
Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya.




Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa.
A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara."


"Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci."


Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane."


Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi."


Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina."


Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake."


Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba.




Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin."


Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta.




Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado.




Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu.


Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba.


Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa.
Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar.




****
Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye.


Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa.


Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa.


*Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


*31&32*
"Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar.


Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita.


"Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa!


Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan!




Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali.




Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login