Showing 33001 words to 36000 words out of 59266 words
Chapter 12 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt
ba zaka watsa min 'kasa a ido ba."
Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.''
"Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita.
Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba."
Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko?
"Yes na sa ni da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah."
Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta."
Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace!
Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin.
Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya.
*******
Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya!
Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba."
Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na."
Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki?"
Jin abinda Baban ta ce yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa."
Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar ta yi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka!
Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko za ki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne."
Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa."
Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi."
Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa."
Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai.
Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban."
Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."
*******
"Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa.
Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin dai Hujaj! gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa.
Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata!
Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa ya yi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa!
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*Mutane masu karamci da mutunci ina godiya da adduarku tare da 'kwarin gwiwa💯❤🔥*
_*JAMILA YUSHA'U*_
_*FAUZIYYA MU'AWIYYA*_
Tun a farkon fari muke tare. ina ro'kon Allah ya had'a fuskokinmu da alheri🙏🏻
*35&36*
Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin ya yi shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun.
Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu?"
Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku."
Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi."
Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.?'
A sanyaye ta ce." Ki yi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta ya ge kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a b'ace ta yi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau.
Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben.
Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya.
Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole.
Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar."
Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari."
Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta.
A gaggauce ya shigo gidan. sai kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo.
A tsaye ba tare da ya risina ba ya gaishe ta. itama fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa sai ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa.
Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba."
Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa?"
Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba."
Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi.
Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta"
Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga.
Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta.
Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da ya ji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu ya fi su rinjaye da yarinyar.
Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta.
Ta fito da hijabi a wuyan ta.
Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta.
Zum'bura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa."
Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.?
Murmushi tayi tana kawar da fuskarta.
Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin *SO!* dole tayi wa yarinyar uzuri.
Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce."
Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami!
****
Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a.
Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar.
Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa.
Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni."
'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci wani abu a tare dashi, sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannnunta.
Ba zato ta tsinkayi maganarsa." Kin tafi kin barni da tunaninki."
Kallonshi tayi tana so ta tabbatar da maganarsa.
Ya lumshe ido tare da daga mata kai "Nayi kewar ki My dear."
Gabanta ya fad'i ta dinga kallonsa tana mamakin kalaman dake fitowa daga bakinsa kamar ba wannan mai tabin hankalin ba.
A sanyaye Ta ce." Ga abinci nan kayi hakuri nima kwana biyu bani da lafiya shiyasa ban zo ba."
"A jiki na naji hakan domin tare muka kwanta ciwo nima bani da lafiya my dear amma ganinki a yanzu ciwon ya tafi."
A d'an tsorace ta ce ." Don Allah waye kai nifa har yanzu zuciyata bata amince min da cewa kana da tabin hankali ba, haka kawai nake tausayinka.
Shuru yayi bai ce mata komai ba. A lokacin ta fahimci sauyawa daga gare shi, sai ma ya shige 'kasan motar ya bar ta a tsugune a gurin.
Ta mike tsaye tana 'karkade jikinta tana juyawa taga yara sun fara taruwa a gurin, da sauri ta tsallaka titi ta shiga layinsu cikin sassarfa.
Washe gari ma da safe ita ce ta kai masa abin kari, sai dai lokacin da ita isa bakin titin baya nan, sai dabbobi a kwance akan buhun da yake kwanciya duk sunyi kashi da fitsari! gurin sai wari yake ga shara nan birjik da bawon lemo da sauran tarkace! Tsigar jikinta ta tashi! ta tsani ganin kazanta a rayuwarta, wai yanzu a ce mutum mai rai! wanda Allah ya daraja shike kwanciya a gurin, ta girgiza kai tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata, kofin kunun ta ajiye a can gefe in da babu k'azanta! ta juya gaba da baya tana duba gurin, da yake yanzu garin ya waye babu mutane sosai amma dai wandanda ke sana'a a bakin kasuwar sun fara fitowa yara 'yan makaranta da wanda ke cikin ababan hawa suna ta wuce wa suna kallonta lokacin da take kokarin korar dabbobin dake kwance a kan shimfidar buhun nasa.
Wani almajiri ya zo ya tsaya da roba a hannunsa.
Kallonsa tayi idonsa cike da 'kwansa da alama tashinsa kenan daga bacci ya fito neman abinda zai sa a bakinsa.
Cikin yanayin da Allah ya halliceta take masa magana."
Ya ce." A she baki sani ba ai jiya da daddare wani mutumi ya zo wai ashe shine mai wannan motar." Ya fada yana nuna katuwar akori kurar da ta jima a gurin. ya cigaba da cewa." Ya gargadi Baban-Baba cewa lallai ya kwashe tarkacensa daga gurin zai turo kanikawa su kwance motar ya siyar da ita.
Gabanta ya dinga dukan uku-uku! baki na rawa." Ta ce.'' Yanzu ina yake."?
Cike da rashin fahimta ya ce." Waye?
Murya a sama ta ce." Baban-Baba."
Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa."
A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata.
A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji."
Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan."
Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba."
Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko?"
Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin.
Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka.
Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida."
Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka.
Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba.
*Jama'a tafiya tana kara nisa kada dai ku manta cewa wannan littafin na kudi ne adalci guda da nayi muku tsawaita free peges har book1 ina fatan za ku yi kokarin sayan littafi na biyu, domin karanta cikakken labarin.*
Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce...#500 Vip 1k 0542382124..Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ki dauko hoton katin mtn ki tura mini ta WhatsApp, mutanan nijar kuma za ku turo da dala dari Vip jakka daya, katin airtel za ku tura min da shi ta wannan number
07084653262
Allah ya ba mu sa'a da rabo mai amfani.
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana