Showing 45001 words to 48000 words out of 59266 words
Chapter 16 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt
matsayinki na mai hankali bai kamata kiyi masa haka ba, ban ji dadi ba wallahi." ta kai karshen maganar cikin rawar murya.
Ta ce." Rashin kunya za kiyi min Shahida?"
Ta girgiza kai "A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai kuskuran ki nake nuna miki."
Ta ce." Ai ba tun yau ki ka saba nuna min kusukura na ba Shahida ki cigaba da yi min abinda ranki yake so.
Ta share hawayen da ya soma fita ta ce." Allah ya baki hakuri! dama zan fada miki ne cewa. Za muje can gurin Babana tare dashi."
Ba tare da ta kalle ta ba ta ce." Sai kun dawo."
Ga mamakinta sai ta ga ta juya ta fita.
Suka kalli juna ita da Saliha ta ce." Gatse fa nayi mata."
Saliha ta ce." Don girman Allah Baba ki kyale 'yar iskar yarinyar nan da mahaukacin mutumin nan jiki magayi."
Baban ta shiga girgiza kanta tana tu'ajibun al'amarin.
Gidan duhu sosai! babu haske. dukkaninsu suna rumfa a zaune yunwa na sasakarsu! yau Talatu dai ta ranste tace kowa ya ci aljihunsa! domin ta gaji yawon cin bashi gashi babu mai ko anini a cikinsu, tunda ba sana'a suke ba, bahaushe ya ce duk lalacewar mutum yana da rana. Talatu tana iyakar bakin ko'kari a kansu, yau dai ta gaji! 'kokari take ma ta biya bashin da ta ci a baya wanda kullum ta Allah ake mata sallama ba dare ba rana.
Motsin shigowarta gidan ya sa Hadiza tayi saurin kunna fitilar wayarta tana fadin." Waye?" Ta ce." Ni ce Shahida." Talatu tayi karaf ta ce" Wa ce Shahida kuma. ba dai kurmar yarinyar nan ba, domin na ji kamar muryarta."
Hadiza ta ja tsaki mai tsayi ta tashi ta shiga daki ta kwanta. tunanin yanda za a yi ta samu abinci kawai take, tana ganin saurayinta kawai zata kira a waya ta fad'a masa halin da take ciki.
A wulakance ta kalle ta kafin ta ce." Ke kuma daga ina da wannan daran?"
"Da ga gida nake." tafada a takaice.
Ta ce." Ayyo! to ina fatan dai lafiya?"
"Gurin Babanmu na zo tare da wanda zan aura za su yi magana."
Gabanta ya yanke ya fad'i! ta ce" Waye wanda zaki aura din? wane sakarai! asararran ne mara mafad'i."
Jamila ta ce."Haba Talatu abinda ki ke fa bai dace ba, kefe uwa ce idan ba zaki fadi alheri ba to kiyi shuru."
"Rufe min baki ba'kar munafuka algunguma." ta katse ta a zafafe!
Jamila ta mik'e ranta duk a 'bace ta kama hannunta suka fita tsakar gidan.
"Don Allah Aunty Shahida kiyi hakuri da abinda Talatu take miki wallahi ba na jin dad'i."
A jiyar zuciya ta sauke ta ce."Jamila Mahaifiyarku ba ta k'aunata ban san abinda nayi mata ba. amma ki sani wallahi ta na cin albarkacin ki, da ba don haka ba da tuni na dauki mataki a kanta."
Ta ce.'' Ki cigaba da hakuri watarana sai labari yanzu ina mutumin da ku ka zo tare?"
Ta ce." Yana can waje a tsaye kuma wallahi da gaske ya ke aure na zai yi."
Ta ce.''Amma na ji dadi wallahi. mu je na gaishe shi kafin Baban ya dawo"
Tare su ka fita suka same shi a tsaye a jikin bango (garu) yana danna 'karamar waya nokia da aka d'aure ta da kyaure.
Jamila wani irin kallo take masa a tsorace! kwata-kwata mutumin bai kwanta mata a rai ba, ganinsa wani iri babu sutturar arziki gashi tsoho gemunsa da tsalli-tsallin furfura!
"Ina wuni." Ta fada tana dan sunkuyar da kanta.
Ya amsa fuskarsa a sake yana dan tsokanarta.
Tana 'yar dariya ta ce." Ga aunty na nan; don Allah ka rike mana amanarta! kaga tana da lalura ta rashin ji a kula mana da ita.
Murmushi yayi ya ce." Kada ki damu 'kanwata zan ri'ke amana insha Allahu; yanzu ina so ne nayi magana da babanku domin da gaske na ke."
Tana k'okarin magana Hujaj ya k'araso gurin! kallonsa yayi sama da 'kasa da fadin." Malam menene? ka tsaya min a kofar gida tare da yara na."
Ya d'an rusuna da fadin." Barka da dare Baba." A takaice ya amsa da "Barka dai"
Gurin yayi shuru dukkaninsu jikinsu yayi sanyi!
Ya kalli Shahidan da fad'in."Waye wannan ki ka kawo min?"
Ta ce." Shine wanda nake so na aura, mun daidaita junanmu shine ya ce yana da kyau ya zo ya gaishe ka, kuma akwai alherin da yake tafe dashi."
Bud'ar bakinsa sai ya ce." Ni da kai na nace ki fito da mijin aure, amma kin san dai a yanzu ba ni da kud'in da zanyi miki wata hidima ko? don haka maganar aure a tattara a ajiye a gefe guda. idan kuma zai aure ki babu kayan daki falillahil-hamdu."
Ya ce."Babu komai Baba Shahida nakeso ita kanta ba wani k'yale-k'yale ba, buri na kawai ka bani ita.
Wani irin kallo yake masa yana raya abubuwa da yawa a ransa! wannan mutumin da yake gabansa da ka gani talaka ne duba da yanayinsa, amma kuma ya yaba da nagartarsa kuma ba 'karamin yaro bane, Shahida 'yarsa ce mai rangwamin ga ta, shiyasa bai wani ci buri a kanta ba, amma zai so nagari ya aure ta ko dan ya kula da ita saboda lalurarta.
Ya ce." Na baka yarinyar nan amana. sai abu na gaba wane alheri ne yake yafe da kai bayan wannan."
Fuskarsa cike da annuri ya ce."Alhamdulillhi na gode sosai insha Allah zan kula da amanarka. bayan haka kuma Shahida ta shaida min irin halin da ka ke ciki na rayuwa, zanyi iyakar bakin kokari na akan lamarin.
Ya ce." Wane irin taimako za kayi min? da ka ganinka dai talaka ne, wanda baka ajiye ba, baka bawa wani ajiya ba, shin ko akwai wata hanyar da ka ke samun kudi a b'oye kake yawo a tsiyace! kana da hanyar miliyan biyu da rabi ne?"
Ya girgiza kai cikin rashin jin dadin maganganunsa ya ce." Eh insha Allahu, ina da alfarma a gurin maigidana, mutum ne shi mai tausayi da taimako insha Allahu zai duba uzuri na."
Nan da nan fuskarsa ta washe ya ce." mutukar kuwa hakan ya tabbata baka da matar aure sai wannan yarinya na baka ita halak malak."
Bai yi mamakin jin haka daga gare shi ba, ya ce."Shikkenan Baba na gode sosai, yanzu abinda za ayi shine ka bani number wayar mutumin da yake bin ka bashin kud'in koda maigidana zai bukaci magana dashi idan na koma can abujan."
Ya ce." Don ta lamabar waya ai babu matsala sai na baka yanzu.
Ya shiga fad'a masa lambar shi kuma yana d'auka a 'kwara'babbiyar wayar dake hannunsa da aka d'aure ta da kyaure.
Sai bayan ya gama fada masa lambar wayar ne ya kalle shi da fadin." Da gani kai ba yaro bane ga alamun shekaru nan a tare da kai. shin kana da aure ko kuma yarinyar nan ita ce matarka ta farko?"
Ya ce." Nayi aure shekarun baya har 'yata ta girma ta zama budurwa amma tana can garinmu."
Ya ce." Ina kenan?"
"Katsina a cikin karamar hukumar jibia, nan ne mahaifata.
Ya ce." Ma sha Allah. kayi kokarin ganin ka fitar dani a wannan masifar ni kuma nayi maka alkawari sati guda yayi yawa gurin daurin auranka da yarinyar nan.
Ya ce." Insha Allahu zanyi kokari."
Gidan ya shige zuciyarsa fes! yau haihuwa za tayi masa rana.
A tsakar gida ya same ta a tsaye. kamar wacce take jiran shigowarsa babu sannu da zuwa ta ce." Maganar da Jamila ta zo fad'a min gaskiya ne?"
A lalace ya kalle ta kafin ya ce." 'kwarai kuwa yau haihuwa za tayi min rana dake da yaranki kun zama yuyuyu! sakarkaru kawai."
Yana 'kare maganarsa ya bude dakinsa ya shiga ya bar ta a tsaye a gurin cike da d'umbun mamaki!
A hanyar su ta komawa gida take tambayarsa ashe ya ta'ba aure har da haihuwa, ya tabbatar mata da gaskiyar magana ya ce." Amma yarinyar ta na can garinsu kamar yanda ya shedawa mahaifinta.
Cike da 'kauna da begen juna su kayi sallama da juna tare da alkawarin cewa gobe da wuri zai zo ya gaisa da Baba Asabe kafin ya tafi.
Lokacin da ta shiga gidan, muryoyinsu ta ji a can cikin daki harda Kawu Musa. gabanta ya fad'i! jin kawu Musa a gidan ba alheri ba ne.
Saliha ta fito tsakar gidan ta sameta a tsaye ta kasa shiga dakin.
Ta dan d'aga muryarta da fadin." Matar mahaukaci kin dawo kenan?"
Kallonta kawai tayi amma ba tace mata komai ba, ba don ba taji haushin kalaminta ba.
Suka fito daga dakin a tare, Baba Asabe na sake jadadda masa matakin da zata dauka akan al'amarin, ya yin da shi kuma yake nuna mata cewar tabi a hankali domin ba ta da k'arfi akan yarinyar kamar ubanta.
Ya kalle ta suka had'a ido! sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa.
Ya d'an bud'e muryarsa da fad'in." Shahida wannan rayuwar ki ka za'bawa kanki ko?"
Shuru tayi hawaye na 'kok'arin kufce mata.
Ya cigaba da cewa." Shin me ki ka hango a tare da wannan mutumin wanda shi ba mai hankali ba kuma ba mahaukaci ba, a matsayin ki na mara lafiya zaki za'bi wannan rayuwar da mara galihu. wanda ba a san asalinsa ba."
Baba Asabe ta d'ora da fadin" Yo idan ba rashin hankali ba ina ke ina auran mahaukaci mutumin da ba a san daga ina ya ke b......gurin ta bari tana wani irin kuka! duk suka bita da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu.
*An fara biyan kudin littafin masoya*
*Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce #500 Vip 1k 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*Dubbun Godiya zuwa ga:*
*Hajiya Hadija Marad'i (Nijar) Ina godiya da abin alheri Hajjaju🥰🙏🏻*
49&50
'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta ke yi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda su na yi.
Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya.
Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Saliha kuwa sai dariya take mata addua take a zuciyarta Allah yasa mahaukacin ya nuna mata tumasanci!
Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa domin ita Hadiza ma yawon gantali ta tafi da saurayinta.
Da magariba Hujaj ya shigo gidan; 'kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba.
A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba."
Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na."
Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam."
Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai."
'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa.
A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai."
D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya!
Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba Asabe. ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki.
Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna.
Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba.
Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa.
Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido.
Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min."
Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba.
Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye."
Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito."
Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa".
Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri.
Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki."
Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a."
Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce."
Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.''
Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki."
Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya ba mu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa.
Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta.
Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri."
Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua."
Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri."
Sosai suka rungume juna suna ta kuka!
Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba.
Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita.
****
To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta.
Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta.
Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya