Showing 57001 words to 59266 words out of 59266 words

Chapter 20 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt

26 Nov 2024

3016

ya jefa mata towel din a jiki.


Sai ta bi towel din da kallo tana mamakin abinda yayi. kallonsa tayi. suka had'a ido sai tayi saurin kawar da fuskarta.


Ya tashi daga kan keken ya nufi gurin cin abinci ba tare da ya ce mata komai ba.


Ganin haka sai ta ajiye masa towel din ta kama hanyar fita tana neman tsari dashi.




Sunanta ya kira tana daf da fita.


Ta juyo tana kallonsa fuskarta sam! babu fara'a.




"Zo ki zuba min abinci" hankalinsa na kan wayarsa yayi maganar.




Girgiza kanta tayi ta koma da baya domin bin umarinsa.


Ta had'a masa komai ta ajiye a gabansa kafin ta ce." Zan iya tafiya?"


Kansa ya girgiza alamun A'a. sai ta tsaya tana kallonsa da jiran umarni na gaba.


Sai da ya mula tukkuna ya ajiye wayar hannunsa kafin ya kalle ta a sakarce ya ce." Kinyi kyau cikin hijabi."


Tayi shuru dai ba tace uffan ba.
Gabadaya girmansa ya zube a idonta.


Ya ce'' Na ga kina ta wani rufe-rufe me ki ke b'oyewa ne?"


Ta ce." Babu komai."


Girgiza kansa yayi ya ce."Ban yarda ba gaskiya, ba zaki fita ba sai kin cire wannan hijabin na duba ki."


Taji wani irin fad'uwar gaba! ta kalle shi idonsa k'ur! a kanta kamar tsohon maye!


Ta ce" Shigowata ban kai minti goma ba kuma iyakata nan falon me kake tunanin zan d'auka?"


Ya daga kafad'a da fad'in." Ni dai ban yarda ba saboda haka ki cire idan kuma kinyi gardama to zan cire miki da kaina.




Cikin rawar murya ta ce." Kai fa uba ne, ka haifa kasan mai kyau da mara kyau, yanzu idan akayi wa 'yarka abinda kake min za ka ji dad'i?"


"Ba zan ji dadi ba gaskiya" Serious ya fadi maganar.


Ta ce." To mai yasa ka keyi min haka?"


Shuru yayi be ce komai ba illah kofin shayi da ya d'auka yana kur'ba!


Ta ce" Zan iya tafiya?"


Ya ta'be baki "A'a nifa har yanzu ban yarda dake ba, mutukar zaki shigo nan to ki dinga sa mayafi wannan hijabin akwai munafurci a ciki.


Cike da takaici da mugun haushinsa ta ce." Ba hali na bane sata, kuma ba zan fara anan ba, don haka ka daina d'aukar alhakina.


Bagarar da maganar yayi ya cigaba da kur'bar shayinsa.


Yanda ya ke wulakantata hakan yana yi mata ciwo mutu'ka! sai kawai ta kama hanyar fita a karo na biyu ya dakatar da ita da fadin." Har yanzu ban baki izinin fita ba don haka dawo ki tsaya."


Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta tsaya tana facing d'in shi, ya 'kura mata mayunwatan idanuwansa masu je fata cikin tashin hankali.


Sai da ya gama karyawa tsaf! sannan ya tashi ya fito daga tsakanin kujerun ya nufi gurin da take tsaye.


Ta ji fad'uwar gaba sosai! amma ba ta karaya ba, domin kuwa tasan duk shaid'ancin mutum bai fi karfin addu'a ba, tana da tabbacin cewa sai ta samu rinjaye a kansa.


Daf da ita ya tsaya yana lumshe mata shu'uman idanuwansa.


Ta kawar da fuskarta tana cigaba da nanata addu'ar neman rinjaye a bakinta.


Ya sanya hannu da nufin cire hijabin jikinta.


Ba tare da jin nauyi ba ta buge hannunsa da karfin gaske! bahaushe ya ce ." Idan babba ya zubar da girmansa yaro zai iya hawa kai ya tattaka.


Ya dube ta da fad'in" Ba ki ji nauyin abinda ki kayi ba?"


Zum'bura bakinta tayi tana d'an ture shi da 'kokarin so ta fita daga tsakaninsa domin ya babbake gurin yayi mata rumfa.




Ya sake kama 'kasan hijab din a karo na biyu, sai ta sake wancakalar da hannunsa, ta tsinci kanta da nuna shi da yatsa da fadin" Wallahi zan baka mamaki yanzu nan!" cikin zafin zuciya ta fad'i maganar jikinta na wani irin karkarwa!


Bai wani tsorata ba, sai ma sake matse ta da yayi jikin bango (garu) ya tallafo fuskarta da hannunsa d'aya, aikuwa karan hancinsa dake daf da bakinta ta gartsawa cizo! tana nema ta gutsire masa saman hanci! babu shiri ya matsa gefe yana shafa gurin da ta cije shi wanda yayi sheda tare da rurucewa!


Zazzafar harara! ta buga masa kafin ta ja masa dogon tsaki! tana 'kun'kuni! ta wuce ta bar shi a tsaye a gurin yana bin ta da kallo har ta bud'e 'kofa ta fita.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


*Ga hanyar da za a biya kudin littafin....Normal group #500 posting sau daya a rana, Vip group 1k posting sau biyu a rana. account number.... 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp da wannan lambar.07084653262....Mutanan Nijar za ku tura dala dari. Vip jakka daya, za a turo mini ta WhatsApp. Allah ya yassare.*


55&56
A nutse ta d'an tsaya a jikin daya daga cikin kujerun cin abincin, amma bata yarda ta kalleshi ba, kanta yana 'kasa, sai dai a jikinta ta ji yana kallonta. gabanta ya dinga fad'uwa tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! 'kadaicewarsu, a falon su biyu yana nufin abubuwa da yawa, saboda haka sai tayi ta maza! ta d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yalla'bai ko kana bukatar wani abu ne?"


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari.


Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata.


Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma k'afafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba.


"Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba.


Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita.




Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta.


Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa.


Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane!


Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan.


Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa!


Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce.


_"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_


Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka.


_Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_




Ya dawo mata da amsa kamar haka.


_"Maigida na ya wuce komai a guri na, ba zan iya yin jayayya dashi ba saboda haka kiyi hakuri kawai"_




Kasa bashi amsa tayi sai uban kukan da take shirga! wai shin ita ya za tayi ne? wannan lamari da faru ya fara sanya ta cikin shakku da fargabar zama a gidan.






Kwana tayi cikin zullumi da tunani da kuma rashin madafa, amma tasa a ranta cewa Allah shine madogara a gare ta.




Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe.


Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai.


Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo."


"Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari.


'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima.


Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana.


Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske.


Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin haushin abinda yayi mata jiya.




Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa.




Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya.


Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita.




Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi.


Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa.




A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?"


Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba.


Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi.


Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa.


Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa.


Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin.




Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba.




Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama."


Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai!


Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba.


"Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido!


A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta.


Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta.


Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba.




Ya ce." Ya hannun naki?"


"Da sauki." tafada a ta'kaice!


Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata.


Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?"


Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta.


Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci."


A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba.




Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai.


Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci."


Ta kalleshi da tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai




Fita tayi daga tsakanin kujerun.


Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba.


Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na.




Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali.


Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba.




Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na.


Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa.




Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba.


Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa.


A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta.






Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita.


Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin.


Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login