Showing 54001 words to 57000 words out of 59266 words
Chapter 19 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt
WhatsApp da wannan numbers.. 07084653262.or 08089965176. BINTA UMAR ABBALE*_
59&60
Ya jima yana jinyyar karan hancinsa kafin ya daina masa ciwo, sai dai sa'i da lokaci idan ya tuna abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar sai yayi murmushi! cikin zuciyarsa yake addua'a akan Allah yasa ta cinye jarrabawarsa, domin d'an zaman da su kayi tare sonta da k'aunarta ya gama mamaye jini da gangar jikinsa.
A na ta 'bangaran kuwa daina walwala tayi a gidan, motsi kadan za ta tsorata, domin tana fargabar kada ya kawo mata farmaki har gurinta.
Bata sake saki jikinta ba sai da su Hajiya suka dawo sannan. ta warware amma duk da haka Hajiyan sai da ta lura da wani abu, sai take tambayarta ko akwai abunda ke damunta ta daina sakewa, da sauri ta ce "babu komai wallahi kaina ne kawai yake ciwo." Hajiya ta ce'' Ai fa na ga alama saboda ba haka muka tafi muka bar ki ba, to amma kin shedawa mijinki domin naga kina da k'wauron baki''
Murmushi tayi ta ce." Eh na fada masa har ya siyo min magani na sha."
Ta ce."To Allah ya raba lafiya." domin ita Hajiyan a tunaninta ko ciki ne da ita.
Ta ce." Ki je ki kwanta ki huta ai sai da lafiya ake komai."
Sosai tayi farin cikin hakan, sakamakon ganin saukowarsa tasan tabbas idan yana gurin ba zata iya sakewa ba.
Ya zauna kujerar dake fuskantarta. sai ta sunkuyar da kanta a hankali ta ce." Ina kwana?" ya d'aga mata hannu ba tare da ya amsa ba.
Hajiya ta kalle shi da fadin." Yarinyar nan bata da lafiya har nake zargin ko ciki ne da ita?"
Gabansa ya fad'i ya kalle ta da fadin." Wane irin ciki kuma Hajiya duka-duka yaushe su kayi auran?"
Murmushi tayi da fad'in." Yo tsakanin mace da miji ai sai Allah, ai yanzu kamar tuntu'be akeyi dashi a hanya, shine nake tambayarta mijinta ya sani, ta ce" Eh har magani ya siyo mata."
Ya kalle ta tare da bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce" Ke da gaske ciki ne dake?"
Kunya duk ta rufe ta, sunkuyar da kanta tayi tana jin nauyi don gani take kamar maganar tayi kama da ta rainin hankali! kwana d'aya kacal da aurensu ya dauk'e mata miji ya kai shi uwa duniya, zai zo yana tambayarta sai dai idan shine yayi mata cikin. ita da zuciyarta take magana.
Hajiya Saude tasa dariya da fadin." Kai ma dai da wani abu, to idan shine a tunaninka za ta fad'a maka ne? ni ma hasashe kawai nake.
Ba tare da ya ce komai ba ya dubi agogon dake daure a hannunsa, ya kalle ta da fadin " Hajiya zan fita"
Ta ce" To Allah ya bada sa'a." ya amsa da "ameen yana kokarin tashi. Shukura ta fito daga d'akinta.
Sai ya tsaya yana kallonta, ta ce." Daddy ina kwana?" ya amsa babu yabo babu fallasa.
Ta ce."Hajiya ta fad'a maka sakon mommyna."
Ya kalli Hajiyan domin jin 'karin bayani.
Ta ce" Neman magana ne kawai irin na Hajiya Fatima, mun shirya dawowa gida ne shine take ba mu sa'kon gaisuwarta gare ka.
Bai ce komai ba ya kama hanyar fita, sai suka bi shi da kallo jikinsu a sanyaye Hajiya ta riga tasan halinsa tun yana yaro mutukar ya bar abu to bar shi har abadah, wannan dalilin ne yasa take tausayawa Hajiya Fatima duba da irin wahalar da take sha a kansa ya'ki sauraranta, shekara da shekaru da rabuwar auransu, ta'ki aure ita lallai tana jira yazo ya mayar da ita d'akinta, in da shi kuma ya ci alwashin sai dai ya mutu babu aure mutukar sai ya zauna da ita ne. 'Yan uwa da ita kanta kakar tasa sunyi-sunyi har sun ha'kura, domin mai daki shi ya san in da yake masa oyoyo, shi kadai ya san irin wahalar da ta bashi a lokacin da suke tare.
****
BAYAN KWANA BIYAR
Tana zaune 'kasan kafet tana cin abinci wanda ci kawai ta ke yi saboda ta kori yunwa ba wai don abincin babu dadi ba, A'a sai don ta san mutukar ta kwanta da yunwa to tabbas zata tashi a galabaice! shiyasa take tuttura abincin tana had'awa da ruwa. Motsi ta ji ana kokarin bud'e kofar shigowa, gabanta ya yanke ya fad'i! ta tsirawa kofar ido tana addua a zuciyarta, domin ba ta kawo cewa mijinta bane ta fi tunanin maigidan ne da yake kai mata hari a duk lokacin da su had'u sai ya san yanda yayi ya ta'ba jikinta, wannan abu yana yi mata ciwo mutuk'a! ita ba abun ta zazzage shi ba tana cikin gidansa, sai dai duk sanda ya ta'ba jikinta ko ya cire mata dankwali sai ta yini tana share hawayen takaici wanda ya ajiye ta ma bai ta'ba ri'ke mata hannu ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta.
Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje!
Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta.
Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba.
A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba.
Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta.
Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu.
Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar.
Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani.
Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta.
Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take.
****
"Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba.
Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan."
Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki."
Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta."
Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida.
Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba.
Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri.
Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen"
*****
_"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_
Wannan shine abinda Saliha ta rubuta.
Tana hawaye take tura amsa kamar haka.
_"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_
Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba.
Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa.
Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali.
Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta.
Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah.
Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.''
Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari."
Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da har zai farauce ki, to shikkenan misali a ce maganarki gaskiya ce, ni na amince ki bashi kanki a madadina domin bani da wata cikakkiyar lafiyar da zan kwanta dake, na fad'a miki wannan mutumin ya fi karfin komai a guri na, saboda haka na amince a duk lokacin da ya buk'aci
wani abu a gurinki ciki kuwa harda kwanciya dake, to kada kiyi masa jayayya domin yin hakan na barazana da auranki, ki amince masa kai tsaye kuma ki sakar masa jiki sa'anan kiyi k'o'karin faranta masa, ki ji a ranki kamar kina tare dani, wannan shine abinda za kiyi ki faranta min rai.
*WASA FARIN GIRKI!π₯°*
Ko ya zata kasance? ina fatan za ku biyo ni domin karanta cikakken labarin, don wannan sominta'bi ne, kada ku manta akwai labari a 'kasa jingim! don haka masoya kada ayi 'kasa a gwiwa gurin biyan kudi domin jin yanda za ta kasance. Ni ce taku a koda yaushe
*BINTA UMAR ABBALE*
MARUBIYAR
*1-NANA KADIJA*
*2-YARO DA KUDI*
*3-GIMBIYA BALARABA*
*4-BABBAN YARO*
*5-MASHAHURI*
*6-LADIDI KWADAGA*
*7-RUWAN DARE*
*8-SADAUKI OMAR*
*9-NIDA YAYA SADAM*
*10-YAR BANGAR SIYASA*
*11-DA WATA A KASA*
*12-MADADI*
*13-KWARYA TABI KWARYA*
*14- GA IRINTA NAN*
*15-MATSALARMU A YAU*
*16-GOJE*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALEπ*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
*ABACHE POULTRY FARM*πππ
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*
57&58
A tsorace take kallonsa a lokacin da yake 'kokarin zuwa gurin da take tsaye.
Cikin wata irin tafiyar isa da ta'kama! ya tsaya daf da ita hucin numfashinsa na dukan fuskarta.
hannu ya sa cikin aljihu. kafin yasa d'aya hannun ya rungumota jikinsa! rikon tsauri! yayi mata da hannu d'aya yana sumbatar gefen fuskarta.
Wani irin hauka da buge-buge! ta shiga yi duk domin ta 'kwaci kanta daga hannunsa! ta samu gefen kafad'arsa ta gartsa masa cizo! wanda yayi sanadiyar sakinta, sai ta matsa gefe tana mayar da numfashi tare da wani irin kuka! mai ciwo! jikinta na kyarma! tsigar jikinta gabad'aya ta tashi.
Kallonta yake da idanuwan da suka sanja launi! ta zabga masa muguwar harara! cikin tsananin jin ciwo da takaicin abinda yayi mata ta ce." Wallahi ka ji kunya! ashe dama baka da kirki ko?"
Ya tsira mata rikitattun idanuwansa dake cike da tsantsar fitina ta shekara da shekaru! gabad'aya yarinyar ta gama tayar masa da hankali.
Ta je ta rarumi gwangwanin turare a kan madubi ta jefa masa tana kuka ta ce." Sai Allah ya saka min abinda kayi min, kuma sai na fad'awa mijina."
Ya 'bata rai! kafin ya bud'e muryarsa sosai ya ce" Kafin ki fad'a masa ni zan riga ki, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka ki fice min daga daki" Da k'arfi ya k'arasa maganar yana nuna mata hanyar fita da hannunsa.
Ta sake d'aukar wani gwangwanin ta je fa masa wanda ya sauka a goshinsa, tana zubar da hawaye ta ce" Ban yafe ba daka ta'ba ni." yanda ta ke rawar jiki da yanda take kuka har cikin ranta ya tabbatar masa da cewa ta ji ciwon abinda ya yi.
Sai ya mi'ke da azama ya nufe ta, ta zabura! a guje tayi hanyar fita, garin kici-kicin bud'e kofar ta zame ta fad'i a gurin, rintse idonta tayi ganinsa a tsaye a kanta ya yi mata rumfa.
Ta rufe fuskarta da tafin hannunta "Don Allah kada ke ta min haddi, ka dubi darajar aure kada ka sake ta'ba ni." tafad'a jikinta na wani irin rawa.
Hannu biyu yasa ya d'ago ta ta mi'ke tsaye, ya tsirawa fuskarta ido, hawaye sai tsare suke a saman fuskar, harshe yasa yana tsotse hawayen, gabad'aya k'afafunta suka kasa d'aukarta, sai k'o'karin zubewa take a gurin, yana tallafota.
Yanzu ma haukan ta sake yi masa tasa dukkanin 'karfinta ta dinga dukansa a k'irji har sai da ya saketa, ta zube a gurin tana wani irin kuka mai cin rai!
Tayi tur! da wannan rayuwa da take. tayi Allah wadai da ita.
Ya tsuguna gabanta tare da k'okarin daidaita yanayinsa ya ce." Ko na kwanta dake mijinki babu abinda zai ce, saboda iko na ne, ke kuma baki da wata daraja! sannan na ji kina maganar aure! to ki daina daukar wannan auran naku da mutunci, domin duk ina da labarin yanda akayi shi, da kud'i na aka fansheki a gurin mahaifinki, saboda haka ina da iko da damar nayi duk abinda nakeso dake.
Wani irin kallo take masa bakinta ya mutu murus! gabad'aya ta rasa a wane mizani za ta ajiye maganarsa.
Ganin tayi sanyi ta gagara magantuwa yasa ya mi'ke tsaye, anan ne ta girmansa ya bayyana sosai! ya tashi, saboda yanayin kayan dake jikinsa masu kwanciya a jiki ne, wannan dalilin yasa girmansa fitowa, gaskiya ta tsorata! da yanayin, sai tayi gaggawar d'auke idonta tana kiran sunan Allah a zuciyarta, tunda ta ke, bata ta'ba ganin girman namiji irin haka ba sai akan wannan mutumin da yake kokarin keta mata alfarma.
"Tashi ki fitar min a daki.''
Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta tashi har dankwalin kanta yana fad'uwa, anan ne ya ga tarin sumar kanta, ya sake shiga rud'ani, domin a rayuwarsa yana masifar son mace mai gashi, kawar da kansa yayi daga barin kallonta ya nuna mata hanyar fita da fadin." Yanzu nan zan kira mijin ki na sheda masa irin zagi da cin mutumcin da ki kayi min." Ya fadi maganar ne yanda za taji.
Muguwar harara! ta buga masa kafin ta ja dogon tsaki! ta fita ta barshi a tsaye da kwantaccen murmushi a fuskarsa.
Jiki a mace ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, gabad'aya jikinsa ya rikirkice sha'awa ta shekara da shekaru ta taso masa, bai san ya zai yi ba a halin yanzu.
Yinin kuka da damuwa tayi, duk ta tsargi kanta da kanta, sa'i da lokaci idan ta tuna al'amarin sai gabanta yayi ta fad'uwa, adduar kariya kawai ta lazumta domin ita kad'ai ce magani a gare ta.
Wajejan goma da rabi na dare ya turo mata text cewa ta kiyayi 'bacin ransa idan ya dawo domin ya ji labarin abinda tayi wa maigidansa saboda haka tayi gaggawar zuwa ta bashi hakuri.
Amsa ta bashi kamar haka; "Da kasan abinda ya faru a tsakanina dashi ba zaka fad'i haka ba maigidanka mutumin banza ne don haka ni ba zan bashi hakuri ba.
Sai ya bata amsa da cewa; Ashe kuwa auranki yana gargada domin kuwa mutukar ba ki je kin bashi hakuri ba wallahi zan iya sakin ki."
Jikinta yayi sanyi jin abinda ya ce. sai tayi shuru tana tunanin yanda za ayi ta je ta bashi hakuri bayan tasan shine mara gaskiya.
Ya sake turo mata da wani sakon, cewa; "Lallai kada ta tsallake umarninsa a daran nan taje ta bashi hakuri.
Agogo ta duba sha d'aya saura na dare, ya za'ayi ta iya fita a wannan daran. gaskiya sai dai da safe, shima don ba yanda za tayi ne.
Yau cikin hijabi har 'kasa ta shirya jikinta, babu walwala a tare da ita nufi cikin gidan.
Zaune a falo ta same shi kan wani keke irin na motsa jiki, yana sanye da singileti da wando iya gwiwa, cigaba yayi da motsa jikinsa ba tare da ya kalle ta ba.
Tsugunawa tayi a gefansa da fadin." Ina kwana?" shuru yayi be amsa ba ya cigaba da abinda yake gabansa.
"Don Allah kayi hakuri." Tafada cikin yanayin maganarta, gabadaya duk tayi sanyi ta fara nadamar wannan auran.
Ya cire 'karamin towel din dake rataye a wuyansa. fuskarsa ya goge! kawai