Showing 39001 words to 42000 words out of 59266 words

Chapter 14 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt

26 Nov 2024

3008

kayi aure idan ba haka ba to jama'a ba za su daina zargin ka ba."


Murmushi ya yi ya ce." Na kusa aure Hajiya insha Allahu kiyi min addua."


Fuskarta cike da annuri ta ce." Alhamdulillahi haka nake so na ji to ubangiji Allah ya baka tagari.''
Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina."




********


Tsabar fargaba da tashin hankali ya haddasa masa matsanancin ciwon kai! wanda duk dauriyarsa sai da ya kwanta! hankalin Talatu ya tashi domin ko banza idan ya fita ya samo wani abu yana rage mata wata wahalar gidan! ta shiga nan, ta fita can. yawon cin bashi domin samun abinda za su ci da yara.




Ganin saura 'yan kwanaki wa'adin ya cika ya sanya ya yanke shawarar sanar da ita halin da ake ciki ko da taimakon da za tayi akan lamarin.


Tashin hankali kenan! maimakon ta tausaya masa halin da yake ciki sai ta shiga surfa masa rashin mutunci da tsiya iri-iri da tozarci! a cewarta shi ya sayi hakan da kud'insa saboda haka ita babu wani taimako da za tayi masa domin shi kadai yake cin kud'insa hakkinta da na yara baya saukewa! saboda haka matsalarsa ce! a halin da ake ciki 'ya'yansa ne kawai suke tausaya masa domin sune suke jinyarsa! Talatu ba ta bi ta kansa harkokin gabanta kawai take.




Jamila ce ta yanke shawarar zuwa ta fad'a mata halin da mahaifin nasu yake ciki na rashin lafiya, da kuma irin tashin hankalin da suke ciki.




Kasa hakuri tayi hawayen takaici suka k'wace mata! ko shakka ba tayi fargaba da tashin hankali ne suka janyo masa ciwo! me za ayi da wannan hali irin na mahaifinsu, duniya ta sani suma 'ya'yansa sun sheda cewa abinda yake aikatawa haramun ne, anyi anyi dashi ya bari ya'ki! kullum sake tsunduma kansa yake a masifa! yau shine cin bashin wancan. gobe shine cin bashin wannan. kuma kudi ba kad'an ba! to yanzu dai yayi kankat! gidan da yake tutiya dashi ya sarayar dashi kuma bukatarsa ba ta biya ba, dama karshen kwad'ayi jin kunya! Mutumin da ya sayi gidan ya bada notice saura 'yan kwanaki, kana kuma ga wani can a gefe yana jiran miliyan daya da rabi wannan wane irin tashin hankali ne?




Ido jawur! ta fito tsakar gidan da hijab a hannunta, Jamila na biye da bayanta itama kallo d'aya za kayi mata ka hango damuwa a tare da ita.


Baba dake tsige alayyahu ya kalle su tana girgiza kanta, babu shakka ruwa baya tsami banza duba da yanayin fuskokinsu, bayan haka kuma ta zargi wani abu ne yake faruwa da mahaifin nasu duba yanda ta ji suna magana 'kasa-'kasa kamar ba sa so wani ya ji abinda suke tattaunawa.


Cikin dushewar murya! da yanayin harshenta ta ce." Baba zan je na duba babanmu bashi da lafiya shine Jamila ta zo ta fad'a mini."


Cikin alhini ta ce." Allah sarki to ai ba kuka za ku yi ba addu'a za kuyi masa Allah ya tashi kafad'arsa ai cuta ba mutuwa ba ce; shin wai me yake damunsa ?" ta karasa maganar tana kallon jamilan dake kokarin mayar da k'wallar idonta.


A sanyaye ta ce." Ciwon kai ne mai tsanani! amma da likita ya duba shi ya tabbatar mana da cewa jininsa ne ya hau?"


"Allah sarki! ai abinda ake ta fama dashi kenan. Allah ya bashi lafiya."


Gabad'aya suka amsa da "Ameen."


'Dari biyar ta mi'ka wa Shahidan da fadin." Kuyi kudin mota amma ki dawo da wuri kar ki bari dare yayi miki kin ji ko ."


A sanyaye ta ce." Insha Allahu." Hanyar fita suka nufa ta ce." Jamila ki gaishe min da mai jikin kinji ko."


Ta ce." Insha Allahu zan fad'a masa."


Girgiza kanta tayi bayan fitar su, tausaya musu take na rashin samun nagartaccen uba! idan Jamilu bai yi hankali ba yanzu ba to yaushe ne zai yi ? gashi Allah ya bashi zuria duk mata wannan shine abin dubawa.


Lokacin da suka isa gidan yana bacci shi kadai a dakinsa, ita kuwa Talatu sai sabgoginta take, Hadiza bata nan ta je bikin 'kawarta, gidan a bushe 'kamas! yanzu ne Talatun take kujuba kujubar d'ora girki bayan ta je tayi fafutukar ciyo bashi a mak'ota!


Babu arziki ta kalle su da fadin." Au! ita ki kaje kika jajibo me za tayi? ko kuma za ta iya biya masa bashin dake a bin sa ne."


Ta ce." Haba Talatu wannan ba magana bace dani da Anty Shahida duk d'aya muke kuma itama tana da hakki na je na fada mata ne domin ta zo ta duba shi saboda yana matsayin mahaifinta.


Tsaki! ta ja ta shige dakin girki ta bar su a tsaye a gurin da takaicin ta.




To sai gefin magriba ya tashi daga baccin babu laifi da dama-dama jikin nasa. fitowa yayi domin daura alwala nan ya gansu a zaune a tsakar gidan sunyi jugum jugum! jikinsa ya k'ara yin sanyi! kunyar had'a ido yake dasu, da sauri ya dauki buta ya kama hanyar band'aki. Sai suka dinga rige rigen yi masa sannu! kansa kawai ya iya daga musu yayi saurin shiga band'akin Talatu ta bishi da zabgegiyar harara!




"Baba ya jikin naka?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Da sauki alhamdulillhi wanene ya fada miki bani da lafiya?"


Ta goge hawayen da ya zubo a fuskarta ta ce." Jamila ce ta je ta fada min shine na ce bari na zo na duba ka, Baba Asabe ma ta ce ayi maka sannu.''


"Ina amsawa ai na ji sauki ki tashi ki tafi kada dare yayi." Ya fada yana dan kallonta ganin yanda take kuka sai abin ya bashi tsoro lallai baya shakka ta samu labarin abinda yake faruwa; sai kawai ya sunkuyar da kansa 'kasa ya san takaicin abin ke damun zuciyarta.


Aikuwa ya tsinkayi maganarta. "Baba wace irin rayuwa ka jefa kanka a ciki? wace irin rayuwa kake so ka jefe mu a ciki shin wai baka tausaya mana ne?"


Shuru yayi bai ce komai ba.


Ta ja majina! tare da cigaba da cewa ." Gabadaya ka zubar da kima da mutumcinka a gari, babu wanda bai san irin harkar da kake ba, shifa arziki na Allah ne, wallahi ubangiji ba zai ta'ba azurtaka da haram ba! ko ya azurtaka din 'karshen nadama da jin kunya! shin meye ribar abinda kake? gashi ka jefa kanta cikin masifa da bala'i ka jefe mu a ciki, a yanzu ina muka ga miliyan daya da rabi? babban tashin hankalinmu wannan gidan da ya rage maka shima ka sarayar dashi yanzu da mu da kai ina zamu kama?"
*BINTU**MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


pege
43&44
"Ranka ya d'ad'e wannan mutumin da ka sa na yi maka binkice a kansa har ila yau magana d'aya ce kamar dai wancan lokacin; ma'kotansa da jama'ar unguwa ba su ba da kyakykyawar sheda a kansa ba, duk wanda zai bud'e baki yayi magana baya fad'in alherin sa, ranka ya da'de wannan shine labarin da nasa mu a kansa cewa d'an ca-ca ne wasu ma suna zargin yana harkar bariki."
Cikin ladabi Sule ya 'karasa maganar da yake tafe da ita.


Jaridar dake hannunsa ya ajiye a gefansa, ya mayar da hankalinsa gare shi ya ce." Sule ka tabbatar da Gaskiyar maganar nan? kasan duniya ta lalace mutane basa kunyar sharri! yarda da amincewa ne yasa na sanya ka gudanar min da wannan binkicen, ba naso daga baya wata magana fito."


"Ranka ya dad'e hakane wallahi ba za a ta'ba had'a baki dani a cutar da kai ba, duk maganar da na fada gaskiya ne akan Hujaj sai dai ma'kotansa sun bada sheda arziki akan mahaifinsa, sun tabbatar min da cewa shi mutumin kirki ne domin har ya rasu bai ta'ba aikata alfasha ba."


Ya ce."To godiya nake Sule za ka iya tafiya."


Har ya niyyar tashi sai ya koma ya zauna yana d'an shafa 'keyarsa tare da sinne kai.


"Sule Ya akayi ne? da alama akwai magana a bakinka ."


'Dan murmushi yayi ya ce." Ranka ya dad'e na jima ina mamakin al'amarin tun a karon farko da ka sanya ni wannan aikin, sai nake tunanin wani abu, na ce kodai mun kusa samu uwar d'aki ne?"


Maganar ta sanya shi dariya ya ce." Sule ai na d'auka za ka bukaci zuwa gida ne domin dubo iyali ashe ba hakan bane.?"


Da murmushi a tare dashi ya ce." Da wannan maganar ma Alhaji amma ina bu'katar ka bani wannan amsar idan babu damuwa."


Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce." Hakane maganar ka Sule, yarinyar mutumin nan nake so na aura insha Allahu."


Da walwala a tare dashi ya ce." Ma sha Allah Alhamdulillhi ranka ya d'ade Allah ya sanya alkairi yasa za ayi damu Allah kuma yasa abokiyar arziki ce."


Ya amsa da "Ameen suma ameen."


Shuru gurun yayi na minti biyu kafin ya ce." Amma Alhaji baka ganin hakan zai janyo maka wata matsalar duba da cewa uban yarinyar bashi da kirki! akwai ma'kiya wad'anda suke jiran 'kiris su samu abun yayatawa a gari."


Murmushi yayi ya ce." Sule kada ka damu da hakan, insha Allahu alkairi ne zai biyo bayan al'amarin, ba mu nufi kowa da sharri ba, duk wanda ya nufe mu dashi to babu shakka sharrinsa zai koma kansa."


Ya ce." Wannan haka yake fatan alkairi Alhaji tabbas idan hakan ta kasance za mu fi kowa farin ciki."


"Ma sha Allah." Abinda ya fada kenan; ya dauki jaridar da ya ajiye ya dan kishingida kan kujerar da yake zaune, ya ce." Ina fatan ka shedawa Labaran cewa bayan sallar la'asar za mu fita."


Yana k'o'karin tashi ya ce." Eh Alhaji na sheda masa umarinka tuntuni."




To bayan fitar Sule da minti goma kira ya shigo wayarsa.


Koda ya ga wanda yake kiran sai ya ajiye ya cigaba da abinda yake.


Sai da ta kira sau uku tukkuna ya daga, shuru yayi bai ce mata komai ba.


"Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya.


A dakile ya amsa.


Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji."


Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?"


A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata.


"Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?"


"Ba haka bane Daddy."


Ya ce." Nayi 'karya kenan."


"A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take."


Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana."


Tana kuka take bashi hakuri!


Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba."
Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace!




Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo hanyar warware matsalarta.




****
"Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa."


Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi da safe.


Ta d'an 'bata fuska da fadin." Har kin manta ko?"


Girgiza kanta tayi ta ce." Ke shahida magana mai muhimmanci ita nake ajiyewa a cikin raina domin abubuwan da suka dame ni suna da yawa." Ta 'karasa maganar tana kokarin kwance lalitar dake d'aure a k'ugunta.


Sunkuyar da kanta tayi idonta yayi ja! alamun ranta ya 'baci!


Ita kuwa Saliha dariya kawai take mata tana 'yan 'kananun maganganu wanda ta san ba za ta ji ba.


Wutar nepa a ka kawo Saliha da sauri ta kunna musu fanka domin zafi ake a garin.


Ita kuma Shahida ta je ta dauko hijaban ta domin ta goge.




Ta kalle ta da fadin." Kin san dutsen gugar nan yana da jan wuta Shahida da ki bari na gama kallon labarai idan an gama sai kiyi gugar ki."




Ta ce."Baba idan su ka dauke wutar fa.''?


Ta ce." A'a ba zasu dauke ba insha Allahu, ke Saliha kunna min talabijin din NTA KANO zaki kai."


Ta ce." To." da sauri ta janyo 'yar yawo (cover socket) ta jona kayan kallon tana kokarin gyara Area domin hoton ya fito.


Shahida d'aki ta shiga ta kwanta ta shiga tunanin masoyinta.




An gama labaran, 'karshen kawai suka riska.


A in da mai gabatarwa yake fad'in kanun labaran 'karshe, cewa wannan Attajirin d'an kasuwar Alhaji Saddiku wanda aka fi sani da *'Dan gaske* zai yi rabon shinkafa a babban company sa dake sharad'a, za a fara rabon abincin da karfe hudu har zuwa karfe goma na dare.


Baba Asabe ta ce." Wannan karon ma sai na je ko Allah zai sa na da ce."


Saliha ta ce." Da rabon kiyi asarar kudin motarki, har kin manta 'bakar wuyar da ki kasha a wancan lokacin"


Ta ce." Wuya ai mai shigewa ce 'yar nan a wannan zamanin shinkafa 'yar gwamanti babban buhu ai ko kwana zanyi a gurin ba zan damu ba mutukar zan samu, saboda haka yanzu ma zan tashi na shirya sai ki kula da masu shige da fice.


Girgiza kanta tayi a zuciyarta ta ce." Wanda ya 'ki sharar massalaci ai yayi ta kasuwa! samun shinkafar nan ai sai mai tsananin rabo.




"Baba ina za ki je kuma?" ta fada tana kokarin tashi zaune.


Tana gyara hijab din dake wuyanta ta ce." Unguwa zani amma ba zan dade ba insha Allah."




Ta ce." To don Allah kiyi sauri ki dawo kada kuma ya zo ba kya nan."


"To." kawai ta ce ta kama hanya ta fita da sauri tana mamakin wautar yarinyar.




****
Gurun cike yake da mata da maza dattijai da matasa matan aure kai harda 'yan mata, dama irin wannan na faruwa mutane babu uzuri sai su tarkato 'ya'ya da jikoki a zo a bi layi kowa kansa ya sani idan kai ka samu ba zaka bari d'an uwanka ya samu ba, wannan shine abinda yake cutar damu wato son kai.




Gurin yayi cikar kwari! hayaniya ce kawai take tashi wasu ma fad'a suke yi akan bin layi mussaman mata wasu babu kamun kai! don ma da akwai masu tsaro (securities) da abinda za ayi a gurin sai yafi haka.


Duk yana kallon abinda yake faruwa ta cctv camera ya umarci yaransa cewa su je su raba number kowanne ya san matsayinsa lokaci yana cika afara rabo."


Abinda ya faru kenan mutum goma ke raba number 'bangaran maza mutum biyar 'bangaran mata mutum biyar.




Baba Asabe dai ita ce ta dari hud'u da talatin da shida😂 ta tambayi cewa ita ce ta nawa ? ya fada mata cewa sai an bawa mutum dari hudu da talatin da biyar kana za a zo kanta, amma bata sare ba! ta gyara tsayuwarta a gurin tana adduar Allah yasa tana da rabo.


Wasu na fita wasu na shigowa haka ake ta turmutsutsu! a gurin, duk wanda rabo ya zo kansa ana bashi yake jan buhun ya fita daga gurin da yake kan titi ne abun hawa baya wuya.


Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da farar dara irin ta larabawa ya nade da farin hirami sai k'afarsa dake sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi.


Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi.


Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. *"Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! bangon sukari kowa ya jingina sai ya lasa! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka 'DAN GASKE!* *'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya."*


Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu.


Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi.


Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta d'aga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka."


Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi."


"An gama ranka ya d'ad'e."


Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita.




Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login