Showing 36001 words to 39000 words out of 59266 words
Chapter 13 - MAJANUNI Book by Binta Umar Abbale.txt
da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
Pege
41&42
Cike da fuffuka! irin ta rashin gaskiya ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi."
A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai."
Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi."
Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa."
Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa."
To in ban da rigima irin ta Talatu ya za su yi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma su yi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna.
A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi.
Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta.
A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa!
Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa duk a cukurkud'e!
Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi.
Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo.
Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani ne domin al'amarin ya 'bata tsoro mutuka!
Maganarsa ta dawo da ita hayyacin ta. "Shahida ni ne Baban-baba kina mamakin gani na ko?" da d'an k'arfi yayi maganar saboda ya san lalurar ta.
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke har yanzu da ragowar tsoro a tare da ita ta ce.'' Baban Baba kai ne da gaske ko dai idona ne yake min gizo."
Ya sake matsowa kusa da ita a nutse ya ce." Ni ne dai masoyinki na san kin yi kewata ko? nima ina can hankali na yana kan ki."
Wasu hawaye masu zafi suka 'kwace mata ta ce." Alhamdulillahi Allah Na gode maka daka 'kar bi addu'a ta."
Yana murmushi ya ce." Ai d'azu akan idona kuka fito tare da wata abokiyar ki sai na ga fuskokinku cike da damuwa! ganin haka ya sa jiki na yayi sanyi na ce lallai akwai abinda yake faruwa, wannan dalilin ya sa na ce sai na zauna na jira dawowarki kafin na tafi."
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta.
Ya dan sake matsowa daf da ita da fad'in." Ko ba zaki iya fad'a min damuwarki ba?"
Ta kalle shi tana girgiza kai.
Ya tausasa murya da fadin." Ina sauraranki ki sanar dani abinda yake faruwa domin ganin ki cikin damuwa da tashin hankali ya sanya ni cikin wani hali."
Ita dai a tsorace take dashi dan sai waiwayen bayanta take.
Shima ya fahimci hakan ya ce." Kina jin tsoro na ko?
Zuciyarta ta karye sai kawai hawaye suka shiga gangarowa ta sanya hannu tana sharewa wasu na biyo baya! sai jan majina take.
Wani irin ciwo zuciyarsa take masa. tuntuni ya tsani zubar hawayen ta ita ce ba ta fahimci hakan ba.
Ya rasa yanda zai yi a gurin yana jin kamar ya rungume ta ya rarrashe ta, sai dai ya daure ya shirya kalaman rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har ya samu ta daina kukan.
Ta kalle shi; nan ta fahimci cewa yana cikin damuwa da kukanta, sai ta sassauta fuskarta ta d'an yi kasa da kanta ta ce." Ka fara fad'a min ya akayi rayuwarka ta sauya ? wani almajiri dai ya tabbatar min da cewa an tashe ka daga gurin da kake rayuwa to tun daga lokacin ba a 'kara ganin ka ba. shin dama kai din ba mahaukaci bane?"
Murmushi yayi, ya ce." Ni ba mahaukaci ba ne Shahida." Da sauri ta kalle shi tana mamakin furucinsa, koda yake ba abun mamaki bane a gurinta tunda dama can ita ba ta yi masa wannan kallon.
Ya cigaba da cewa " Rayuwa ce ta mayar dani haka amma yanzu alhamdulillhi na gode Allah tunda ya mayar min da alkairi ya had'a ni da uban gida wanda ya dauke ni aiki a garin abuja, ina masa gadin gidansa ni nake kula da masu shiga da fita! wannan shine ya sauya min rayuwata na dawo cikkaken mutum kamar kowa tunda bani da fargabar ci da sha da kuma gurin kwanciya komai ya d'auke min, nutsuwa ta zo min ban yi tunanin kowa ba sai ke domin ina ganin zaki iya amincewa mu rayu a inuwa d'aya."
Hannu tasa ta rufe fuskarta kunyarsa ce ta rufe ta.
Ya raunata murya da fadin." Ko kina ganin nayi miki tsufa ne? ko kuma kina gudun kada 'yan uwanki da 'kawayenki su yi miki dariya."?
Hannunta ta cire tana girgiza kai ta ce." A'a wallahi bana shakka kuma bana jin kunyar mutane su gan ni tare da kai! so na gaskiya nake maka, kuma wallahi zan iya rayuwar aure da kai a cikin kowane hali, ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninmu."
Ya amsa cike da walwala da farin ciki.
Ya ce." To yanzu ya za a yi nayi magana da mahaifinki domin jibi nake so na koma bakin aiki na."
Shuru tayi tana Nazari!
Ya ce." Shahida akwai matsala ko?"
Kanta ta d'aga murya a sanyaye ta ce." Mahaifi na yana cikin matsananciyar damuwa da rashin lafiya! gashi bama jituwa da juna kullum cikin yi min tsawa! yake tunkararsa da wannan maganar zai yi wuya domin bashi da fahimta, ita ma Baba Asabe tana da tata matsalar.
Ya ce." Ko zan iya sanin matsalar.?"
Shuru tayi tana jin nauyin fad'a masa! dole duk d'an halak yayi kishin iyayansa.
Ya ce." Ki daina shakkar fada min damuwarki Shahida ni dake mun riga mun zama d'aya."
Shuru tayi ta kasa magana.
Ya d'anyi murmushi da fadin." Ki fad'a min kada kiji komai, ni mai rufa miki asiri ne a kowane yanayi."
A sanyaye ta fara bashi labarin abinda yake faruwa.
Shuru yayi na minti uku kafin ya ce." Ina ganin wannan ba a abun damuwa bane insha Allahu, ni zan yi iyakar bakin 'kokari na akan al'amarin ina da alfarma sosai a gurin maigida na zai nemi alfarma a gurinsa insha Allah ba za ku tozarta ba."
Ta ce.'' Kudin fa suna da yawa." yayi murmushi da fadin." Ba zai gagara ba insha Allahu rabbi.''
Ta dinga kallonsa ta na tunanin yanda za ayi har a samu a biya wannan kudi masu yawa, to amma tunda ya ce Allah ya gama magana.
Har 'kofar gida ya rakata suna tafe suna hira ta fahimtar juna sosai ta saki jikinta dashi, ta kuma samu sassauci a kan fargaba da tashin hankalin da take ciki.
Sai dai har yanzu tana mamakin sauyawarsa.
Cike da farin ciki biyu ta shiga gidan.
Sai kawai ta riske su a tsaitsaye a tsakar gidan har da kawu Musa a cikinsu, da alama akwai maganar da suke.
Gabanta ne ya fadi! ganin fuskokinsu babu walwala ko kad'an!
Kafin ma tayi magana ya rufe ta da fada! ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.
Sai kawai ta fashe da kuka ta durkushe a gurin tana shashshe'ka!
Baba Asabe ta ce." Ka kyale ta haka tunda dai Allah yasa ta dawo lafiya shikkenan magana sai ta wuce."
Ya ce." Idan gidan uban nata take so ta koma ai sai ki had'a mata kayan ta, amma idan ba haka ba mai zai sanya ta dinga wahalar damu, kawai ina zaman zamana an taso ni a tsaye 'karfe goma na dare idan ba shashashan uba ba waye zai bar 'yar sa tana gantali a hanya irin haka."
Ta ce." Na ce ya isa haka don Allah kada mak'ota su ji abinda yake faruwa, tunda dai ta dawo magana sai ta mutu."
'Kwafa! yayi da girgiza kai ya kalle ta da fadin." Ni zan tafi gida sai da safe."
Ta ce." To Allah ya tashe mu lafiya"
Ya kama hanya ya fita da takaicin abin a cikin ransa.
Saliha kuwa bayan fitarsa tsaki ta ja ta shige daki tana surutai!
Ya rage da ita sai Baba Asabe a tsakar gidan.
Ta ce." Ai sai ki tashi kuma kukan da kike bashi da amfani domin sai da na ce miki kada kiyi dare duba da yanayin garin da kuma lalurarki idan shi Jamilun bashi da hankali to mu muna dashi"
Cikin b'acin rai na yanda suke cin fuskar mahaifinta ta ce." Baba ku daina daukar alhakinsa haka don Allah."
Sai ta ri'ke baki da mamaki a tare da ita ta ce." 'Karya akayi masa kenan?"
Girgiza kai tayi ta ce." Tuntuni na dawo fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min."
Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare."
Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa!"
Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?"
Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane."
Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take.
A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa.
Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi."
Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.?
Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata."
Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba."
A hankali suke maganar dan kada ta ji."
Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a.
Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran.
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
WANDA BAI JI BARI BA...!
39&40
To ko da ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo domin ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. sai wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance!
Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama gidan a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da yake sanya rai a kansu duba da cewa malaminsa ya tabbatar masa da samuwar su.
Alhaji Sammani ya nu na rashin amincewar sa akan hakan. A cewarsa ya za ayi yai masa wasa da dukiya duba da cewa shi a dunkule ya bashi, amma zai tsinka masa kud'i a cikin miliyan biyu da rabi an bashi miliyan d'aya mai zai yi da ita a wannan lokacin da yake bukatar kud'in masu kauri da zai yi order amma za a zo masa da wasa! ba tare da 'bata lokaci ya nufi police station. domin shigar da 'kara mutukar akan kudi ne baya saurarawa kowa ciki kuwa har da 'yan uwansa.
"Alhaji Sammani ban yi tunanin za kayi min haka ba wallahi, yanzu ni ka kawo police station? na d'auka ai kai mai rufa min asiri ne a kowane hali. Alhaji Sammani me akayi akai miliyan biyu da rabi da har zaka tozarta ni."
Murmushi ya yi ya ce" Alhaji Jamilu ni kaina ban so hakan ba amma duk kaine ka janyo duba da ganin yanda kake min yawo da hankali alhalin na sheda maka cewa ga bukatar da zanyi da kudin nan. shin wai ko so ka ke ka talautani ne kamar yanda ka talauta kanka."
Murmushin takaici ya yi ya ce." Kana da damar da zaka fad'i duk abinda kake so, amma ka sani sai kayi nadamar abinda kayi min.''
Ya zakud'a kafad'arsa da nuna alamun bai damu ba ya ce." Kud'i na kawai nake bu'kata a yanzu gani a zaune ga kuma Yalla'bai shi zai zama shaida zan kar'bi miliyan d'aya ba don raina ya so hakan ba sai don samun maslaha a tsakaninmu, sabida haka ka fadi lokacin da zaka cikan kud'i na."
Shuru yayi gumi sai karyo masa yake.
D.P.O Ya ce." Alhaji Jamilu kai muke saurare."
Kansa ya d'ago ido jawur! ya ce." karshen watan nan insha Allah zan biya Alhaji Sammani Kud'insa."
D.P.O yayi rubutu cikin wata takarda ya bashi ya sanya hannu.
Ya kalle shi da fadin." Wannan shine 'karshen magana Alhaji Jamilu, iyakar adalci anyi maka kada lokaci ya cika ka zo da wata magana, hukuma ba zata saurare ka ba idan baka cika al'kawari ba to zamu d'auki mataki na gaba."
Ya ce." Babu damuwa Allah zai rufa asiri." Daga haka bai saurari jin wani abu daga gare su ba ya tashi fuuuuu! ya fita daga ofis din. Duk suka bi shi da kallon mamaki!
****
A shirye ya fito ya same ta zaune a falo tana kallo. kafin ma ya yi magana ta riga shi da fadin." Ranka ya dade ina son magana da kai." Tunda ya ji haka sai yayi murmushi ya nufe ta ya samu guri ya zauna tare da fuskantar ta. cikin zuciyarsa yake raya cewa maganar dai d'aya ce amma ba zai yi saurin yanke hukunci ba tukkuna.
Ta gyara zaman ta da fadin." Hajiya Fatima ta kawo k'arar ka akan Shukura wai ta samo mata aiki amma ka hana shine nake so na ji dalili."
'Bacin ransa ya danne ya ce." Hajiya ki cire kan ki a cikin wannan maganar don Allah. domin ba ni da wannan ra'ayin, babban buri na shine Shukura ta samu miji nayi mata aure amma ni ba zan yarda da wannan tsarin ba."
Ta ce." Sabode me? kenan karatun da tayi ya tashi a banza?" Ya ce." Bai tashi a banza ba mutukar za tayi amfani dashi ta hanyar da ta dace. nufi na anan shine ta tarbiyan tar da yaran ta sannan tayi biyayyar aure."
Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Hakane kai ma kana da hujja amma ai har yanzu ba ta samu tsayayye ba, mai zai hana ka bar ta domin ta ci gajiyar karatun da tayi."
Girgiza kansa ya yi, alamun bai amince ba. ya dan kalli agogon dake daure a hannunsa ya ce." Wannan maganar mu bar ta kawai Hajiya kawai ki cigaba dayi mata addua'a."
Ta ce." To shikkenan Allah ya za'ba mata miji nagari." Ya amsa da "ameen."
Kallonsa tayi lokacin da yake kokarin tashi ta ce." Yanzu kuma ina ka nufa? kwana biyu dai na ga ka zauna a gida ka huta sosai na ji dadin hakan."
Ya ce." Kano zan tafi amma iyakaci na kwana biyu zuwa uku zan dawo saboda akwai tafiyar da zanyi zuwa Spain insha Allah."
Ta ce." To Allah yayi jagora ya tsare ka a duk in da zaka shiga. Sai dai ba zan fasa yi maka maganar aure ba, Alhaji Habu mutukar ka naso ka cika cikakken mutum to dole