Showing 18001 words to 21000 words out of 55178 words

Chapter 7 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt

25 Nov 2024

4316

yasan ta damu da abinda yakeyi" ganin haka yasa ya fara zazzaginta da cewar idonta ya fara budewar da har zata iya girka abinci ta hanashi" wata dariya ce da takaici suka zowa ZAINAB lkc guda,tama kasa jin 6acin rai bare ta tanka masa" ganin haka yasa RABI'U dagota daga kwance da take ya shek'a mata wani wawan mari hadi da tambayar ta wa kika mayar mahaukaci?............










*KARUWAR GIDA*






*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*


*SADAUKARWA GA:*
*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*


*TSOKACI*
*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*


*~GODIYA TA MUSAMMAN GA:~*
*_DR KAMAL U. MAIKUDI_*
*_DR HUSSEN MOHMD YAK'IMA🤙_*




*🅾8⃣*




Dafe kuncinta tayi had'i da binshi da kallon mamakin da ya hanata furta komai bare tayi kuka bisa marin da yayi mata" komawa tayi da niyar sake kwanciyar sai ji tayi ya sake fezgota yana k'ara tambayar ta kamar yadda yayi a farko da was kika mayar mahaukaci?"shiru ZAINAB tayi hadin da sunkuwayar da kanta k'asa dugun kar ta d'ago ya k'ara mata wani marin" jin shirun tayi yawa ne yasa RABI'U kara matse mata hannuta da gangan da ta furta wata kalma ya sami damar da zai jifgeta amman babu dama" fusukatar hakan ZAINAB itama daga gareshi shi yasa tayi shiru"bugu da k'ari dare ya shuda babu mai kawo mata dauki sai Allah shine babban dalilinta na kin tankam masa kamar kumar" sai da taji zafin rokon tsaurin da yayi mata sannan ta fizge hannuta ta kwanta ba tare da tace masa komai ba" ganin haka yasa RABI'U ya k'ara zage dantse wajan zazzagin ZAINAB babu k'auk'autawa kamar wanda ya sha kwaya" shiru tayi kamar mai bacci" tana jin shi har ya dan lafa da sage_zagen nashi ya sami guri ya zauna kamar mai gadi sam ya k'i kwanciya bare ZAINAB ta sami dama/dama" ganin bashida niyyar dainawa ne yasa ZAINAB ta mike jiki a sanyaye ta fita ta d'auro alwala duk da tsoran da take ji ta dawo dakin kenan zata tayar da kabarar sallah sai jin wani irin ciwo tayi tunda tsakiyar kanta har zuwa tafin kafafuwanta duk sun daure ga wani abu da yake mata zuge a gadon bayanta zuwa k'asan mararta banda rad'adin da takejin zuciyar ta tana yi mata"' salati ta fara a hankali ta sanna ta zauna akan daddumar da ta shinfida zata yi sallah takai wani tsawan lkc tana jin ciwan, bayan ya lafa mata ne ta mike a hankali ta tayar da sallah na filar da tayi niyya" ta dade tanayi tun tana iya lissafa iya raka'oin da tayi har ta daina"fatan ta ubangiji ya k'ara kawo mata dauki da kafita a koda yaushe,domin tasan babu wanda ya isa ya yaye mata damuwar da take ciki sai ubanginta mabuwayi gagara musali tunda tasan yana sane da zamanta. Shi kuwa RABI'U ganin ZAINAB ta kama salla ba tare da tace masa komai ba, gashi batayukukan marin da yi mata ba, kuma bata tanka masa ba shine abinda ya k'ara k'ular dashi ya dinga masifar ta mayar dashi shaidan kenan raba daren wanna ranar yayi yanamasifa da aibatawa a gareta" ko kallonshi batayi ba ta mayar da kanta ta kwanta ba tare da ta kalli inda yake ba,hmmm ranar ZAINAB ta k'ara tsinkewa da lamarin RABI'U sosai"kuwa har ya kai hak'ark'arinshi makwancinshi ya sake tashi ya dawo kan ZAINAB ya k'ara ce mata yanzu kika fara ganin wulak'anci na,ai daman hausawa sunce babu mace mai wulak'antuwa gurin miji sai wacce ta yadda ta bude gindinta da haihuwa sanna ya dawo ya kwanta kamar shink'inkin kamar gawa" ZAINAB taso bashi amsar kalmarshi ta kashe sai ta fara domin tasan haka yakeso shi yasa ta fasa ta k'aleshi itama ta juya ta cigaba da juyayin halin da take ciki. Ka shegari ZAINAB bata fito da wuri ba tunda ta iddar da sallah asuba bacci ne ya dauke ta daga baya sai da rana tayi sosai sannan ta fito ta nemarwa yara abinda zasuci, sai da ta tabbatar yaran duk sun koshi sannan ta dauko maganin ANAS ta shi yasha ko wanne,sanna ta koma ta juye musu ruwan wanka su ta farayiwa ANSA da bai da lfy, sanna MARIYA taje tayi nata"ita kuma ta kama aikin gida ta kammala bayan tashi gama taje tashi yi nata wankan, sai da ta shirya ne ta sannarwa MARIYA ta zauna ita da k'anainta zataje ta dawo" ba dadewa zatayi ba"amsawa MARIYA tayi da toh" fita tayi ta barsu a gidan. Tana fita bata zame ko ina ba sai makarantar da yaran nata suke yi tana shiga ta tambayi office din shigaban makarantar aka nuna mata,sallama tayi" ya amsa sannan yayi mata umarnin ta shigo hadin da nuna mata gurin zama" shiga ZAIANB tayi ta zauan suka gaisa ya da shi sannan ta gabatar da kanta a matsayi mahifayar su MARIYA"shiru ya d'anyi kadan ya kalleta da cewar MARIYA RABI'U ko?" kai ZAIANB ta daga hadi da ce amsa eh ita" mamaki ne ya kamashi asarari yace ikon Allah ai na dauka yaran marayune ko kuma basa tare da mahifiyarsu, duba da yadda yaran suke da hazak'a amman sam basa samun kulawar da ta dace tun daga uniform dinsu zuwa kayan karatunsu,duk babu wata kulawar kirki sai nake ganin kamar kin taka muhimmiyar rawa wajan tauye musu jin dadin karatunsu bai kamata yara masu hazak'a adinga watse da su ba" shiru ZAINAB ta d'anyi sanna tace hakane gaskiya amman ina iyar kokarin akansu a matsayina na mahaifiyarsu sai dai nak'ara, kuma insha Allah daga yanzu zan k'ara akan wanda nakeyi" shugaman makarantar yaji dadin alkawarin da ZAINAB tayi masa na bawa yaran kulawar da ta dace a sarari" godiya tayi masa itama" sannan tasa yayi mata lissafi kudin da ake binsu na Makaranta,ba tare da ya 6ata lkc ba ya janyo fayin yaran ya duba ya sanar mata da yawan kudin" lissafo ZAINAB kudin tayi ta mik'a masa", yasa hannun ya kar6a sanan ya rubuta mata rasit ya mik'a mata"ta karba tayi godiya" sannan ta sanar masa da cewar MARIYA ce kade zata dawo a goben ba tare da k'aninta ba shi bashida lfy" amman da zarar ANAS din ya sami lfy shima zai dawo" amsawa shuban Makaranta yayi da cewar Allah kaimu ya kuma bashi lfy,ZAINAB ta amsa da amen. Sannan ta fito daga office din ta koma gida. Tana dawowa ta sanarwa da yaran inda taje" MARIYA ta kama tsalle hadi da murnar lbr baya musu kudin makaranta"ba ita k'ade ba hatta ANAS da yake kwance sai da yayi murnar lbr da mahifiyar tasu ta zo musu dashi, yayi fatan Allah yabashi lfy ya koma Makaranta" amsawa sukayi da Amen" wani sabon tausayi yaran ne ya k'ara kama ZAINAB domin tasan duk duniya basuda wanda yafita a gurin su" wannan hujarce tasa take shanye duk wani wulak'anci da cutarwar mahaifinsu domin tasan wata rana sai lbr,uwa uba basuda wata mafita daga ita har yaran wacce ta wuce suyi hakuri da halinsa har Allah ya ganar dashi. Haka dai ZAINAB taci gaba da bawa ANAS baya kulawa ta musamam da kudaden da k'awarta ta bata tunda ranar da suka gamu a hanyar kai ANAS asibiti" tayi hakan ne sakamakon bayanin da Dr yayi musu na yanayin ciwan da yakeyi". Tak'ara fita harkar RABI'U bata bi ta kanshi daga ita har yaran babu wanda yake shiga sha'aninshi" ganin haka yasa shima sai yaga dama yake kwana a gidan tun daga lkc." Babu abinda yafi damun ZAINAB face wani irin ciwo mara da rik'awar baya ga wani irin ciwo da take ji yana taso mata daga cikin (pravet part )nata watau farji ta" kasa daurewa ZAINAB tayi ta shirya bayan yara sun tafi Makaranta ta nufi gidan RYKAIYYA domin ta shaida mata irin yadda take ji a jikinta sai dai kash tana zuwa gidan ta tarar bata nan sai a lkc ta tuna tace mata zata shiga aikin safene awatan gabaki daya babu yadda ta iya haka tayi kwana ta nufi titi ta tare mai mashin din adaidaita sahu tanufi clinic din da RUKAIYYA take aiki" a daddafe ta sakko daga mashin din ta mik'awa mai mashin kudin shi" ya kar6a"ya bata chanjinta" ta nufi office din RUKAIYYA take aiki tayi sallama"RUKAIYYA ta amsa sannan ta nunawa ZAINAB gurin zama" ZAINAB ta zauna fuska babu walwala ta kalli RUKAIYYA suka gaisa"kallo d'aya RUKAIYYA tayiwa ZAINAB tasan babu lfy a tare da ita, tasowa tayi daga kujerar da take zaune ta zagayo ta zauana a kujarar da ta take gefe ZAINAB ta k'arewa ZAINAB kallo da cewar yadai?" Cije leben ZAINAB tayi kamin ta bawa RUKAIYYA amsa da cewar k'awata banida lfy naje gida ki dubani bak'ya nan shine dalilin biyoki nan" sannu rukiyya tayi mata sanan ta tambayeta abinda yake damunta" bayani ZAINAB tayi mata da cewar tana jin ciwon mara da rikewar baya ga wani irin kai da kuma wani ciwo da take ji a farjinta" shiru RUKAIYYA ta dan yi kada'an da cewar na gane" amman ki tashi muje office din babban likita ya dubaki,ba wai bazan iya bane amman yana da kyau ayi miki bincike mai kyau tunda kin anbaci (pravet part) naki duba yadda kika fasalta ciwo,tunda abune da yake buk'atar duba na tsanaki" toh kawai ZAINAB tace ta mike a hankali" RUKAIYYA ta wuce gaba ZAINAB na biye da ita abaya" wucewa suka yi RUKIYYA ta kar6arwa ZAINAB kati sanna suka hanyar office din babba dr""daya daga cikin kujerun da suke gefe office RUKAIYYA ta nunawa ZAINAB tace ta zauna ta shiga ta nemi izinin ganin shi tukunna"amsawa ZAINAB tayi da toh ta zauna da k'yar sakamakon jin wani irin ruwa da ya fara zubowa daga cikin wandonta har ya fara sauka kan cinyoyinta amma sam bata gayawa RUKIYAYA ba gudun kar ta k'ara rikita ta kuma tunda sunzo inda za'a sami makarin abin" juyawa RUKAIYYA tayi ta karasa bakin kofar office din dr tayi sallama RUKAIYYA tayi hadi da kwankwasa kofar office din babban Dr" ya amsa da yes coming" RUKAIYYA ta bude ta shiga ta fara da gaishe shi"ya amsa da cewar ah Hajiya RUKAIYYA kece Kika bugu kofa kamar wata bak'uwa?" Murmushi tayi sannan ta masa da cewa nice sir" kallonta yayi ya da cewar lfy ko?"amsawa tayi da lfy sanna tace Dr sister ta ce bata da lfy shine na rakora domin ka dubata" murmushi yayi da cewar ai kema Dr ce mai hana ki dubata?" Murmushi tayi da cewar sir ai gaba da gabanta shine dalili?" Yaji dadin girmamashin da RUKAIYYA tayi ya amsa da cewar ko toh nagode jeki shigo min da ita" amsawa RUKAIYYA tayi da hakane mana Dr amman bari naje na shigo da ita din" Dr ya amsa da okey" tana fita ta sami ZAINAB har ta sauka daga kan kujerar da ta barta ta durk'ushe kasa kamar mai nak'uda" da sauri ta k'arasa inda take ta dagota" hadi da cewa sannu ZAINAB menene yayi zafi haka?" Sai da ta tallafota sanna taji danshin a jikin ZAINAB din" rikiwa tayi hadi da tambayarta menakeji haka a jiki jikin !!?" Amsawa ZAINAB tayi da k'yar hadi da cewar nima tunda kamin na zauna naji abin ya fara biyomin cinyoyi na tun ina zaune shine har zaman ya ga gara domin duk zubowar nan da yakeyi sai marata ta karta min da ciwo" sannu tayi kara yi kata sanna ta kamata suka shiga office din Dr" suna shiga ya nunawa RUKAIYYA gadon da yake cikin office din yace ta kwantar da ZAINAB akai" amsa tayi da toh" a hanzaarce ta karasa da ita inda gadon yake ta taimaka mata taho" ture tarin takardun da suke banshi yayi na marasa lfy da yake dubawa ya k'araso inda ZAINAB take kwance yace mata sannu" ZAINAB ta amsa da k'ayar" tambayarta ya fara da cewar menene abinda yake damunta?" amsawa ZAINAB tasakeyi da cewar ciwan mara da rik'awar ba hadi da ciwan kai mai tsanani ga wani irin ciwo da nake jin daga al'urata, yanzu kuma bayan shigo asibitin nan shine wani irin ruwa yake fitowa dag ciki" amsawa Dr tayi da cewar okay toh bari mu duba ko" juyo yayi ya kalli RUKAIYYA da cewar ta miko masa safar hannu a drower set din shi" ta amsa da OK ta tafi da sauri ta dauko ta bude kwalin ta ciro ta mi'ka masa" ya kar6a ya saka, sanna ya yi mata nuni da ta miko mishi sauran kayan aikin nashi" tasake komawa ta dauko masa su,ta ajje a gefe"itama ta koma kusa da kan ZAINAB ta tsaya tana kallon yadda Dr yake ta ta faman kokarin saka taimakawa k'awar tata" hannu shi guda daya wanda ya sakawa safar ya ware d'an yatsa daya ya zuwa a(pravet part) din watau farjin ZAINAB tana cije le6e yakai yatsa na biyu duk da ruwan da yake fitowa daga ciki da kyar ya zurashi ya shiga" wani k'aramin ihu ZAIANB ta saki sakamakon jin zafin da ta k'ara ji gun yanayi mata"hakuri ya Dr yabata da cewar sorry" kai kawai ZAINAB ta dan motsa tayi shiru domin kuwa ita kad'e tasan irin zafin da takeji domin ji take kamar k'ara mata zafin ciwan mara da takeyi da dr yake acikin jikin nata" sai da yagama duk wani bincike sanna ya ciro yan yatsunshi daga ciki,sanna ya dako kai ya kalli ZAINAB da cewar shekarki ki nawa rabonki da aure?" Mamakine ya kamata akan tambayar Dr me ya hada cutar ta da rashin aure"kamar yasan abinda take tunanin kenan"yes abinda nake nufi kenan cutar ki tana da alak'a da rashin aure" dururu da ido ZAINAB tayiwa lkita domin batasan masar da zata bashi ba" yanjuyowa yayi ya kalli RUKIYYA ta cewar Hajiya tun wanne lkc ne yar uwar taki takai rabonta da namiji? Dan naga tana jin kunyar amsa min tamabayata?" Murmushi RUKIAYYA tayiwa Dr da cewar ai tana da aure" mamaki ne ya kamashi da cewar what?" Daga kai RUKAIYYA tayi da cewa Dr yes da gaske nake?" Asarari ya k'ara baiyana mamakinshi da cewar okey,babu damuwa binken da nayine a yanzu ya nuna kamar ta dade rabota da d'a namiji, duba irin ruwan da take fitarwa daga jikinta launshin ya nuna kamar na wacce ga rabo da namiji tsawan lkc, amman bari na k'arasa sauran sai nayi muku bayanin komai" toh kawai RUKAIYA tacewa Dr" ta cigaba da kallon yadda yake gudanar da aikinshi cikin kwarewa da ta sanin darajar ilimin kanshi, wannan ce k'ara bawa Dr wani matsayi na musama a idon sauran likitoci yan uwanshi" daukar abin gwaji yayi ya fara gwada (BP) ZAINAB sannan ya dawo ya bude idonta, ya bata umarni ta bude bakinta ya gani" ta bude" ya buda sannan yayi bata tambayar shekarunta na haihuwa" ZAINAB ta amsa da cewar sunkai 30 zuwa da d'aya" Dr ya amsa da okey"ya cigaba da yi mata tambayoyin yadda takejin yanayin nauyi jikinta" ZAINAB ta bashi amsa iyakar saninta" sai da ya gama yasaka d'agowa ya kalli RUKAIYAYY da cewar zanso ace kamin na baku masa da shawarrin da yadace wanda yar uwarki zata bi na fara tattaunawa da mijinta idan da hali"yana kai maganarshi ta k'arshe a tare ZAINAB da RUKIYYA sauka had'a ido da bakin ciwa baya gari matafiyi ne" da sauri dr ya d'ago ido da cewar amman nayi mamakin halin da take ciki koda yake matafiyin yana kaiwa shekara nawa ba yanan?" K'asa da kai kowacce tayi daga cikinsu daga ZAINAB din har RUKAIYYA" jin sunyi shiru ne yasa Dr shima yayi ya koma ya kan kujerarshi ya zauna sanna ya janyo katin ZAINAB yayi rubuce_rubece da zaiyi akai" sanna ya sake cewa RUKAIYYA ta taimakawa ZAINAB ta sako daga kan gadon ta dawo kujerar da masa lfy suke zama yayi musu bayanin komai a tak'aice hadi da bata shawarwarin da suka dace"toh RUKAIYYA tace wa dr" ta kamo ZAINAB a hankali suka k'arso har kujerar da take fuskantar tashi" Ya gyara zama yayi sosai ya kallosu su duka biyun sanna ya fara da cewar kunji ina Alak'anta ciwon da maganar aurataiya ko?"suka daga kai da almar eh?"ya cigaba da cewar ba abin mamaki bane idan na fadi haka domin kuwa bincike ne ya nunamin haka?" Domin nayi iyakar bincike na bata da( high BP)da ta ambaci ciwan kai mai tsanani,kazalika kuma binken ya nuna batada cutar (ucler)da ta ambaci rikewar baya d.s.......shine as abinda yasa na k'ara matsa mata da tambayoyi hadi da k'ara bincikar shekarunta na haihuwa da tambayar matsayi aure, nasan ke RUKAIYYA ba abun mamaki bane a tare da ke ammn ita dole zatayi" RUKAIYYA ta amsa da cewar hakane Dr" mumushi yayi da cewar insha Allah komai yazo da sauki tunda har an gano meye matsalar" amsawa sukayi su duka da masha Allah a tare"bayani ya fara kamar haka da cewar ita mace wata hallitace wacce Allah ya sirrita ta kamar haka,idan mace takai mamakin balaga tana da wasu(humous)a jikinta watau jiyiwon sex,mana'a jijiyon shawarta ga da namiji basa budewa sai ranar da ta fara sanin namiji a rayuwatar wanda da zarar tasan shi ne cikar matantakarta,kuma shine take sabawa da shi, a duk lkc da suka matse junansu basa buk'atar komai sai sex watau jima'i da zarar sun samu toh mace zata zauna lfy ba tare da sun takura mata da ciwo ba,idan basu samuba shine,mace zata ringa jin zafin sha'awa na firgata, har ta kaita da cin ciwon mara da rikewar baya hadin da ciwon kai mai tsakani wani, sometimes yakan haifar da sarkewar tunani ga macan da ta dade bata samu sex ba,watau saduwa da namiji a hausancen"duk bayanin da Dr yake ZAINAB da RUKAIYYA suna jinshi." Numfasawa yayi kadan da cewar wannan itace matsalarki a ta farko"matsakarki ta biyu watau zubar ruwan da kikeyi daga (pravet part)naki shima matsalace a likitance domin hakan ya faru ne sakamakon wancan bayanin da bayi miki ba farko,duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login