Showing 30001 words to 33000 words out of 55178 words
Chapter 11 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt
kallonki haka kika lalace kuma baiyi yun kurin yi miki magana ba ke kuwa?" Murmushi ZAINAB tayi da cewar ai shine ma silar lalacewar komai nawa da kika gani" amsawa HAFSAT tayi da cewar kamar yaya? Yanzu fisabilillahi shine zai zauna yayi miki gyaran gida da na daki da sauran kulawarka da duk ta dace?" Hmmmm kawai ZAINAB tace sanna ta dora da cewar da dai banyi niyyar gaya miki hujjar hakan ba, amman yanxu tunda har kina gani baki yadda ba toh bari kiji dalilin da yasa nace hakan kwashe lbr komai da yake guna tsakaninta da RABI'U tayi tun daga lkc da ta fara samun matsala da shi har kawo wannan lkc da take ciki duk wata cutarwa da yake mata ita da yara babu abinda ta boyewa HAFSAT har zuwa yau da take bata lbr" koda ZAINAB tazo karshen lbr ta ta dago ido domin tambayar HAFSAT meye nata laifin sai tayi arba da ita tana ta faman zubar kallah da share majina" bude baki tayi da kyar ta cewa ZAINAB sannu a gaskiya ko kwatar hakurin da kikayi ni bazan iya ba amman ki barshi idan yasan wata, ai biasan wata ba ,ba dai shi karuwan namij ba? toh da hannushi zaiyi nadamar abinda ya aikata miki a rayuwar shi ta duniya" zaro ido ZAINAB tayi da cewar a'a k'awata nifa tsoro gareni domin wallahi RABI'U ya wuce inda kike tunani ni dai ki rufa min asiri" amsawa HAFSAT tayi da cewar ai rufin asirinki kenan ki tashi tsaye tun kina raye basai takaici ya kasheki ba,irisu zuma ne sai da wuta, idan kina ganin zai baki matsala kiyi k'arshi zuwa kotu mana"sake zaro ido ZAINAB tayi da cewar kin manta da sharad'in da nace miki MALAM tayi min tun kamin ya rasu?" Amsawa HAFSAT tayi da cewar haka naji kince a cikin lbr da kika bani,toh ya zame miki wajibi tunda girmanki, ki samarwa kanki mafita tun kamin dare yayi miki domin hausawa sunce mace kamar ruwa take idan aka tsare mata hanya sai yiwa kanta, dan haka ki shirya d'amarar yak'ar bakin ciki d'a namiji daga zuwaciyar ki" wani dogon numfashi ZAINAB tayi da cewar toh ta yaya k'awata" hmmmm HAFSAT ta fara cewa sanna ta budi bakin tace toh ki zama karuwar gida mana domin yanzu wanna harka ita ce Sana'a mafi sauki domin majority matan yanzu ita suke dalili kuwa a matan da suke gidajan aure25% ne suke zaune da mazajen su lfy sauran duk rubabine kinga kuwa idan nace miki 75% karuwar gida ne kar kiyi mamaki domin maza basuda tabbas sune silar jefa matansu zuwa ga neman kudi ko ta halin k'ak'a" dafe k'irji ZAINAB tayi da cewar haba kawata sam wannan kalmar bata kamaceki ba domin wannan shawarar taki sai nake ganin bayi ba" amsawa HAFASAT tayi da cewar OK sai ki zauna zafin sha'awa ya kasheki da taikaicin d'an namiji wallahi kawata sam baki san yadda rayuwa ta juya bane" wani sabon numfashi ZAINAB ta k'ara saki da taji maganar HAFSAT kamar al'mara ta rasa bakin magana" ganin haka yasa HAFSAT tace ai k'awata ko dan ki rama abinda RABI'U yayi miki kya aminta da magana ta kuma ai karuwanci gida shine domin kuwa ko cinki aiki babu wanda zai gane tunda da aurenki,ke nifa wallahi matsalar da na samu da nawa mazajan sam bata doshi irin taki ba amman na nuna bazanyi zaman auren ba akan me zan zauna takaici ya kashe ni?shine dalilin ma da kika ga yanxu banida aure karena nake ci babu babbaka banida wanda zai matsamin nayi" amsawa ZAINAB tayi da cewar gaskiya k'awata bazan iya ba" jin haka yasa HAFSAT fusata tace ai sai ki zauna takaici ya kasheki!! hadi da mikewa ta bude Jakarta ta zaro kudi yan dubu2 ta mikawa ZAINAB hadi da yi mata sallama tace ta tafi" karba ZAINAB tayi tai mata godiya ta kara da tambayarya sai yaushe?"tabe baki HAFSAT tayi da cewar sai na sake samun time zan kewayo ku" godiya ZAINAB ta k'ara yi mata sanna tayi mata rakiya har zaure.
Shikuwa RABI'U tunda ya 6usa yaga da jini ai can ya tare gurin JAMCY ko waiyayar ZAINAB bayayi daga ibedi sai garesu na gyaran mota haka rayuwarshi ta sauya ko tsoran Allah bayayi bare tausayi maraicin ZAINAB" suna zaune a garejin su masu aiki nayi masu hira nayi irin wacce aka saba ta yau da kullum,guda daga cikin su ya nisa da cewar kai bari na tashi na shiga kasuwa tun kamin na shagala da hirar na" farat kuwa RABI'U ya amsa da cewar me zakayo a kasuwa yanzu? kamar wani mace" amsawa tayi da cewar wallahi tunda zan fito iyalina ta sanar min da cewar kayan abinci mu sun taho k'arewa"shine yanxu na tuna da maganarta toh kaga ai na hanzarta naje na sayi komai tun kamin dare yayi ko?" Wata dariyar mugunta RABI'U ya saki ya kalli na gefenshi da cewar kaji mutumin ka fa wai har wani rawar jikin shiga kasuwa yake madam ta gaya masa kayan abinci ya kusa k'arewa amman dan shine kaluluwa sarkin d'oki bazai jira ya k'are din ba amman kaji zaije ya sake sayo wasu"wancan ya bushe da dariya mugunta yace ai kasan mijin tace ne" mik'o hannu RABI'U yayi suka tafa yace wannan bai san mata ba abin tausayi bane wallahi ai mace tsakani ka da ita shine ta biya ma buk'ata malam amman da zarar ka nuna kana tausayinta babu d'an iska rinka kasan Allah ni dai yanzu a gidana bazan iya sayan kayan abinci da za'ayi sati ana ci ba" mikewa wancan din yayi da cewar oga RABI'U duk naji dalilanka dan haka kayi rayuwarka da iyalainka yadda kaga dama, nima ka barni nayi yadda nake so ya juya ya barsu ya tafi" yana juya suka sake kallon juna suka bushe da dariyar RABI'U ne har da cewar a haka zaka k'ara d'an wahala.
Ita kuwa ZAINAB tunda HAFSAT tabar gidan ta take ta tunanin maganar ta hadi da jinjina al'amarinta na ko kadan bataji nauyi irin shawarwarin da take bata ba? Wanna ai gurguwar shawarce ta yaya ma za'ace ita din tayi hakan, domin a ganina tuni mahaifinta yake guje mata faadawa rayuwar da batada ammafani,a tunanishi rashin aurene yake haddasawa ashe ba anan gizon yake sak'ar ba.........
~AMENAT KABER KIRU~
*KARUWAR GIDA*
*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*
*SADAUKARWA GA:*
*_HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMED)_*
*_Kuna Raina Kamar kudin haya yasen🤾♀_*
*yadomma mohmd Bello,my zuk,Sadiya I. Baso matar kirki, zainab sarki Mustapha Kiru, zainab b. Sani kiru(ta rabe), 🤭yar yola karuwar gida fans,Fatima Abubakar abaza life,Hauwa'u Umar Mohammed karuwar gida fans, Abdul h2, my bro amaccid'o Abubakar, Yaya hayat, Bashir sardauna mashek'i & mawasgi😜Ina gaisuwa kamala Bala yaron kirki Ina yinku over Kuna k'albina😘🥰*
*12*
Kadai ZAINAB ta wani tana juya maganar HAFSAT a zuciyarta............ Domin kuwa yanzu abin ya wuce tunanin duk wani mai tunin"haka dai ta yini tana jinana maganar Kawarta ta. "Allah sarki rayuwa (Ina ya Allah babu ya Allah sarkin iko da buwaya k'asaitaccan sarki gagara misali) a cikin wannna daren ranar ne Allah ya sake sakkowa da ANAS cutar ciwan ciki ya sake damk'arshi haha dai ZAINAB ta sake kwanan zaune har gari ya waye basuyi bacci ba daga ita har yaron " Kamin gari ya waye ANAS ya suka kusan sau hudu zuwa biyar wannna ce tasa ZAINAB ta Kara rikicewa da shiga rud'u domin batayi tsammanin ciwan nashi har zai kaishi ga suka ba" k'agara tari gari ya waye domin ta kaishi asibiti"tun ZAINAB tana kuka a sarari har yakita da tana na zuci domin kuwa ji tayi ruwan idonta ya dauke baya iya zubowa ko kadan, haka dai tai ta zarya da yaron a hannuta daga d'aki zuwa tsakar gida"a haka har gari ya waye.....
Gari na wayewa ta shirya ta fita domin Kai ANAS asibiti" tana zuwa cikin gwaugawa likitoci suka kar6eshi ba tare da sun tsaya neman wani bayani daga bakin ZAINAB ba."domin kuwa tana shigowa dashi cikin asibiti ya sake someway, wanna ce tasa aka wuce dashi emergency domin duba lfy sh"wani irin kukan zuci ZAINAB takeyi domin kuwa ta rasa yadda zatayi sau kinda MA Allah yasa jiya HAFSAT ce ta Bata kudin da tazo asibitin dasu wannna ne ya takaita tashi hankalinta"shi kuwa ANAS tun bayan da aka tafi da shi dakin gwaugawa likitoci ne suka taro akanshi domin ceto lafiyar shi"bayan ya farfado daga suman da yayi ne babba Dr yace ta kaishi dakin bincike na musaman domin yana son ya k'arayin bincike akan matsalarshi duba da yadda cikinshi yayi wani irin girma Kamar ba cikin k'aramin yaro ba." gani an sake fito dashi daga 6angaren da aka kaishi yasa ZAINAB tayi saurin zaburowa daga inda take zaune tana tamabayar likita da cewar Dr ya jikin nashi? "kallonta yayi Shima cikin tausayawa yace ai yaji sauki zamuje dashi d'akin bincike na musamman ne domin sake dubashi dan gano asalin matsalar shi" amsawa ZAINAB tayi a hike a sanyaye da cewar toh Dr Allah yasa a gane din" amsawa yayi da cewar amen" Sanna yaruba yabi bayan k'ananun likitoh cin da yabasu umarnin sukai mass ANAS din d'akin bincike"bayan sun shigar da ANAS din suka daurashi a Kan gadon daya daga cikin gadajen da suke d'akin Kai tsaye sukai wa ANAS (x_ray)watau hoton cikin ya dauka"Kamin wani lkc Dr ya fitar da sakamakon da aka samu daga hoton cikin nashi da akayi." Bayan ya fitar ne ya Bawa daya daga cikin k'ananan likitocin da suke gefenshi yace ta Kai masa office gashinan zuwa"toh tace ta fita a hanzarce"shi Kuma Kuma ya k'ara komawa inda ANAS yake kwance yasa a aka dagoshi daga kwanciyar inada ya k'ara tamabayarshi ya yake jin yanayin nauyi cikin nashi da Kuma yanayin murdawar da yake masa?"amsawa ANAS yayi da cewar baya jin wani ciwo a halin yanzu dai dai Yana jin cikin Kamar ansaka masa dutse a ciki " sorry Dr ya k'ara cewa ANAS Sanna ya ce wa sauran litocin su dauko shi su kawo masa shi office" amsawa sukayi da toh sanna ya fita " Yana fita kuwa sunayin arba da ZAINAB wacce ta taho a sukwane gaba Dr" da sauri tace Dr Yaya jikin Nasha dai?"amsawa ya sakeyi cike da kulawa yace haba ai ya ji sarki " wata ajiyar zuciya ta saki da fad'in masha Allah" kallonta yayi cikin tausayawa Dr ya k'ara da cewar ki biyoni office yanxu"toh ZAINAB tace sanna ta bashi. "
Yana shiga office din nashi itama ta shiga hadi da yin Sallama" amsawa yayi hadi da nuna mata gurin zama",, ZAINAB ta zauna tana sauraron abinda zai ce mata"Kamin ya fara bata bayanin dalilin cutar ANAS sai gashi sauran likitoci sun shigo dashi tare da yin sallama"a tare suka amsa"musu sallamar tasu"suka k'araso inda ZAINAB take zaune suka mik'o Mata ANAS din"tasa hannu ta karbeshi ta daurashi akan cinyartahadi da rumgumeshi tayi musu godiya"suka amsawa suka fita."Bayan fitar su ne Dr Shima ya dawo da hankalinshi zuwa ga ZAINAB wacce ta k'ago taji abinda Dr zaice mata akan cutar ANAS din"farawa yayi da cewar bisa bincikin da mukayi akan ciwan cikin da yaronki yakeyi, ba wani abu bane ila(Ascites) na taruwar wani ruwa a cikin shi hakan Yana faruwa ne Idan mutum ya kamu da wasu irin cuttutuka Kamar haka cutar k'ada da Saifa, da hanta,a jimalance muna Kiransu da shine(Abdominal da cavity)shine yake tara ruwa a wani 6angare na cikin mutum, Shine dalilin da yasa yaronki ya kamu daya daga cikin cuttutukan da na lisafa Miki a Fargo watau(chronic liver disease) a turance"toh wanna ita ce karshen nan bi ma'ana ciwon hanta, itace take haifar masa da wanna cowan cikin mai tsakanina Wanda ya hada har da taruwar ruwa a cikin cikin shi, toh Kinga yana da kyau a bashi jinya ta musamma mai domin tarar ciwon da wuri sabida Kar yazo yana samun damuwar da tafi wacce yake ciki a halin yanzu"ya daga Kanshi yana kallon ZAINAB wacce tuni ta gama kid'imewa da bayanin da yayi mata"wata irin ajiyar zuciya ZAINAB ta saki sannan tacewa Dr duk na gane bayabinka sai dai na karshen ne bangane da kace jinya ta musamma"eh Dr yace abinda nake nufi shine zaku zauna anan dashi domin bashi kulawar da tace"murmushin karfin hali ZAINAB tayi da cewar Dr Kamar yaya? " Amsawa Dr yayi da cewar eh Ina nufi Idan kina da sarari sai mu baku gado anan domin yayi jinyarshi Koda kuwa ta kwana biyu ce, Idan Kuma babu sai na rubuta miki ganin da duk ya dace yasha tare da dokinkin da za'a kikaye"amsawa ZAINAB tayi da cewar gskiya Dr banida sararin da zan biya kudin d'akin da za'akatar damu domin bashi jinyar ta musamam sai da a rubutamin maganin da kuma gayamin dokokin da zanbi domin bashi Kariya " Dr ya fuskanci iyar gaskiyar ZAINAB Kenan wanna dalilin ne yasa ya janyo katin ANAS ya rubuta mata magani yace taje pharmacy ta sayo su ta dawo" kar6ar katin tayi hadi da godiya ta dauki ANAS din ta fita." ko dar ZAINAB bataji ba wajan tunkarar pharmacy da yake cikin asibiti tana zuwa ta mik'a musu Kamin " suka karba tun Kamin su hado mata magungunan suka gaya mata kudin da batayi tsamani ba, domin kuwa ce mata sukayi kudin ya kama 15k Ina magani da allurori da aka rubutu" wani irin Jeri ZAINAB taji yana shirin damk'arshi, da kyar ta samu ta iya bude baki tayi musu bayanin cewar ita fa iya 6k ne a jikinta sai d'ari biyu da ta rage mata zata hau adaidaita sahu ya mayar da ita gida, dan haka ta roki alfarmar su Bata Wanda zaifi muhammanci subar sauran ta Saya daga baya " nuna mata sukayi da cewar ko wanne mai amafani ne, dan haka ta ciko kudi su Bata magani kawar shine yafi sauki" magiya ZAINAB ta shiga yi musu da cewar su fuskanci halin da take ciki ita da yaron duk duniya iya abin da take dashi Kenan " ganin magiyar tata tayi yawa yasa dole suka bata iya na kudin ta suka rabu da ita" karba tayi taimusu godiya ta juya ta koma office din likita sagale da ANAS a kafad'arta. "tana shiga tayi sallama" Dr ya amsa hadi da dakatar da rubuce2 da yakeyi ya kalleta da cewar kin dawn? "ZAINAB ta amsa da cewar eh nadawo ga magungunan ta mik'a masa" yasa hannu ya kar6a hadi da cewa ta zauna bayan ta zauna ya cirosu daya bayan daya, sanna ya d'ari ido ya Kalleta da cewar ai basu cikaba"sosa k'aya ZAINAB tayi da cewar eh Dr wallahi duk kudin hannuna sun k'arene shine nace su bamu iya wadan nan daga baya Idan na samu sai da sayi wadan da ban Saya ba " kallonta yayi da cewar haba madam ya kike saka wasa a cikin al'amuran ciwon yaron nan naki ai nagaya miki ba cuta ce Kamar saurancuttutuka ba yana da kyau Idan anyi muku bayani ciwo toh ku tsaya ku hankanta ku kuma yak'i cutar ta hanyar shawarrarin likita da sayan maganin da aka rubuta muku, ganin halin da kike cikine yasa ban bari an rubuta miki duk wani kudin gwaje2 ba amman yanzu kuma ga magani yana neman gagara ki Saya gabaki daya"murumushi karfin hali ZAINAB ta k'akaro da cewar Dr nima nasal kayi naka kokarin kuma nagode!! Amman yana da kyau ka fuskanceni wallahi banida sararin Sayan maganin duk kansun wannna shine dalili"amsawa Dr Yaya da cewar Ok amman yana da kyau kayi kokarin samun kudin da zaki sayi sauran kamin nan da kwanan uku ace suma sauran ya fara amfani dasu, Kamin lkc da zaki dawo mana dashi muga yadda jinkin nashi Yaya idan har ruwan da ya taru a cikin nashi bai tsiyaye ba ta hanayar shan maganin da aka rubuta muku toh sai ta kai ga matakin zuke Masashi da na'ura ta hanyar yi masa aiki na mustafa, Shima kuma ba abune mai sauki ba, shi yasa nake mai baki shawarar da ki gaggauta sayan sauran magaungunan kamin lkc dawowarmu Yayi nan da sati uku masu zuwa"jinjina Kai kawai ZAINAB ta shiga da tayi bayanin da Dr yayi mata tace toh insha Allah za'a Saya ta amsahi maganin hadi da yi masa godiya ta fita.......
~AMENTA KABER KIRU~
*KARUWAR GIDA*
*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*
*SADAUKARWA GA:*
*_HAJIYA ZALIHA_*
*_YOLA(MMN AHMED)_*
*_KUNA BAWA ZUCIYATA SHAUKI A KODA YAUSHE_*
*_AMENA SALES, UMMU USANAISA_*
*13*
Tana fitowa ta tare dan mashin din adaidaita sahun da zai mayar da ita gida."
Shi kuwa RABI'U yana ta bacci a d'akin JAMCY sai ji yayi tana zungurar kafarshi" a gigice ya tashi duk ya shar6a da gumi ya kalli JAMCY da jajayen idanunshi da cewar wai dan Allah bazaki barni nayi bacci ba Kenan!!"kalloshi tayi a wulak'ance da cewar ai kuwa bazakayi bacci cikin jin dadi ba a yau Kam, domin ai nasanar kama cewar Ina son zanyi gyaran d'akin nan tun wanccan watan amman kayi shiru dani matuk'ar baza bani kudin da na buk'aci kabani ba,toh wallahi zan dauki mumaman mataki na hanaka shigomin daki gaskiya"jin hakan daRABI'U yayi yasa ya k'arayin ya zaro kudi a aljihunshi na gefe da cewar wallahi banida abinda ya wuce 35k din kud duk duniya nace ki kar6i wannna din da zarar na samu zan cika miki sauran a sati nan"murguda baki tayi Wanda ta cikashi da cingum tace haba Kai kuwa ta Yaya zan yadda na kar6i 35k bayan hidimar da zanyi ta zarta Hakan ka duba ko(AC) kad'e a nawa zan Sayota? Inason sayan kayan kallo ma ga sauran gyare2 da zanyi, kudin da nake son kashewa d'akin nan nawa ai ya tasamma 120k amman sai ka bani 35k me zan Saya dasu?"kallonta tayi da cewar ai nace kiyi hakuri zuwa k'arshen sati duk matsalar da ta kawo min rashin kudi a tsakanin nan bata wuce ta k'arancin aiki da muke fama dashi a garejin muba amman kiyi hakuri nayi al'k'awarin baki duk kudin da kike so da zarar aiki mai tsoka ya samu" murgud'a masa baki tayi" hadi da yin far da idanunta sannan ta sunkuya ta kwashi kudin da ya ajje akan katifarta ta ta"tawuce ta dauko