Showing 54001 words to 55178 words out of 55178 words

Chapter 19 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt

25 Nov 2024

4322

kuma, ko kin dinga karya cutane kullum?" karara wayarta ce ta yanke mata tunanin da takeyi da sauri ta k'arasa inda ta ajje wayar tata, gani wacce take Kiran nata ne yasa ta daga wayar cikin sauri da zumudi da cewar hello k'awata nayi fushi dake!! Sabida Allah ace tunda kika tafi wayar mu batafi sau biyu ba sannan ko an kiraki bakya daga wa meye haka? " dariya HAFSAT dayi da cewar korafinki ba karbuwa zaiyi anan ba k'awata domin idan nabar gari nayi tafiya irin wannan bana sauraron kowa har sai naga abinda ya turewa buzu nad'i" amsawa ZAINAB tayi da cewar babu hmmmm naga alama ai ba sai kin min dogon bayani ba toh ya kike da fatan kina lfy? "amsawa HAFSAT tayi da cewar normal wallahi kefa?" amsawa HAFSAT tayi da cewar Nima haha k'awata ashe kinga sak'on!" dariya HAFSAT ta sake yi da cewar ganin na shine ma yasa nakiraki banda kaba ai da sai na dawo keda jin muryata ta Kara da tambayar ZAINAB cewa lfy kike son yin magana dani ta gwaugawa Kamar yadda naka kin barmin sako inbox nawa?" murmushin karfin hali ZAINAB tayi sannan ta amsa da cewar lfy kalau k'awata sai dai Ina cikin zullumi tun jiya da AG ya sanar min zai dawo kano wallahi banyi bacci ba a zaune na kawan Sabida tsabar tashi hankali domin a yanzu haka shirin fita nake zanje gurin shi tun jiya ya takura sai min da kira akan yana jirana a yau dinan kinga kuwa ai dole ne na damu"" hmmm HAFSAT tace sannan ta Kara da cewar toh wai meye abin tashin hankali a wannna maganar? Kaji abin haushe wallahi na dauka ma ko sabani kuka samu toh tunda ma kin shirya kije mana aiy bazai cinye duka a yau ba zai rage na gobe har da na jibi ma ta k'are tana dariya" " amsawa tayi da cewar bazaki gane bane k'awata Ina zullumin yadda zan kasance masa ba, ba kuma wannna be damuwar ba idan yayi min ciki fa!! ya kakeso nayi dashi? wanna ne babban tashi hankali na gaskiya" dariya HAFSAT ta sakeyiwa ZAINAB da cewar banza mara wayau ai wannan ba damuwa bace domin kuwa koda hakan ta faru ai akwai hanyar magancewa domin ko ni nan sai da na cire cikin kusan sau Sha daya kuma ba tare da wani yaji ba, kinga kuwa damar barin shi tana hannunki sai kin so za'a sani dan haka ki ware jiki kiyi harka ki, nifa bana Son sanya dalili kuwa ni a harkallolina da nakeyi komai bashi hakkinshi nake ya kamata ki dau hannu daga gareni duk da ba'a nunawa kuruciya baka" jin HAFSAT tace mata hakane yasaka kwsahe da dariya tace gaskiya k'awata Ina missing naki domin wallahi dan bayanin nan da kika yimin har yasa naji kwarin gwaiwar tafiya" amsawa HAFSAT tayi da cewar Yaww ko kefa ai nasan kina gane wannan yaren shi yasa na fito miki a haka" dariya ZAINAB tayi da cewar toh nagode da kuwalar ki gareni" amsawa HAFSAT tayi cikin zolaya tace amen yar gidan AG a da mana da tsarabar lbr" dariya ZAINAB tayi da cewar baki isa kiji sirrin mu ba koke kin gaya min naki ne? Waya ma tana neman ta gagara a tsakanin mu bare fadar sirri" dariya HAFSAT tayi da cewar shikenan kowa ya rike nashi hadi da cewar sai kin dawo ana jirana nikam" OK ZAINAB mata hadi da cewar nagode toh " amsawa HAFSAT din tayi da cewar babu komai keda sai kin dawo din bari ma na kirashi na ce masa ya wasa wukarshi da kyau domin yau zai kwashi babbar tsoka ta yanke wayar ba tare da tajira mai ZAINAB din zata ce ba ta gudu." Dariya kawai ZAINAB tabita da ita sanna ta ajje wayar a gefe ta Kara gyara fuskar sanna ta dauko mayafi da takalmai da jaka ta saka ta fito" tana fita ta gidan SAMIRA ta fara biyawa tayi mata karyar zataje bakin kanne HAFSAT Kawarta hadi da bata sallahon mukuliin gida koda bata dawo da wuri ba idan su MARIYA sun dawo suna da bukatar daukan wani abu ta basu su dauko su rufe mata gidan " amsawa SAMIRA tayi da cewar Allah ya sanya alkairi hadi da Karba dan mukulin tace mata a dawo lfy" amsawa ZAINAB tayi da cewar tagode sai ta dawo din ta fito" a hankali ta k'arasa bakin layin unguwarsu hadi da tare mai mashin din adaidaita sahu taho tace masa ya kaita Kanar( A. T. C)ya amsa mata da toh hau mutafi" ZAINAB ta shiga ta zauna" Shi kuma yaja suka kama tafiya "Basufi muna uku da fara tafiya ba wayar ZAINAB ta hau Kara da sauri ta bude jaka ta ciro hadi da daga Kiran tace hello" amsawa yayi ALHAJI GARBA yayi da cewar zazzafa ta kina Ina a daidai yanzu? " murmushin tayi ta kama magana Kamar rada da cewar gani a cikin a daidaita sahun da zai kawoni ATC Idan na karasa zan kiraka" amsawa yayi da OK -OK babu damuwa sai kin Karasa din"ok tace sannan ta yanke Kiran ta cigaba da nazarin yadda zata ga AG din ko yaya yake oho!!!"
Cigaba da hakitoshi a zuciyarta Jim kadan suka k'arasa gurin da tace ya kaita mai adaidaita yaci burki hadi da cewar Hajiya anzo fa" firgigit ZAINAB tayi da cewar toh!! Hadi da tambayar shi nawane kudin shi" ya amsawa mata da gaya masa abinda zata bashi" ciro kudi tayi a jakatta ta mika masa sannan ta sakko"karba yayi hadi da ciro mata chaji ya miko mata da cewar Hajiya ga chanji" mubarshi tayi Sannan ta amsa masa da cewar ya basu kawai" godiya yayi mata Sanna ya ja mashin din ya tafi." Waige_ waigen ta Ina Wanda zai zo daukarta ZAINAB ta fara yi" tana shirin cirowa wayarta ta kira AG ta sanar masa gata ta karaso sai ganin kira ta yi ya shigo wayarta da bakuwar lambar dayawa tayi cikin sauri hadi da yin sallama jin murya da bata sani bace tasa ta tambayar waye?" amsawa yayi da cewar nine driver da aka turo nazo na daukeki, gani nazo inda a kayimin kwatance zan sameki ki kina Ina?" fada masa tayi daidaita gurin da take tsaye hadi da sanar masa kalar kayan da da ta saka" Kamin ta gama rufe baki sai ganin wata zungureriyar mota tayi a gabanta ta tayi parking rufe motar take ruf da bakin gilashi ta ko Ina, fitowa driver yayi hadi da yawa ZAINAB sanu"ta amsa masa tambayar shi tayi da cewar Kaine aka turo ya daukeni" amsawa har yana rusunawa da da cewar haka ne Hajiya nine aka aiko" OK ZAINAB tace masa" Shi kuma ya juya da sauri ya bude mata gidan baya hadi da cewar Hajiya shigo" tabawa ZAINAB tayi a hankali ta k'arasa ta shiga cikin motar" ganin ta shiga ne ya driver ya zagaya da sauri ya bude mufin bangareahi ya shiga hadi da tayar da motar yaja suka tafi......




~AMENAT KABER KIRU~

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login