Showing 15001 words to 18000 words out of 55178 words

Chapter 6 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt

25 Nov 2024

4313

sauki da ZAINAB ta samu d'aya ne babu wani abu da zata nema dag RAB'U sai yarjewarshi zuwa kai ANAS asibiti" duk ranar da yaga dama ya barta ko kuma ya hanata" hatta yawo daren da yakeyi ya dawo da yin abinshi." Haka ZAINAB ta cigaba da hakuri da yanayin da RABI'U ya koma duk dan abinda yake hannuta haka ya tasama k'arewa dole ce ZAINAB sake shiga cikin wata damuwar" shi kuwa ko kadan baya kallon ZAINAB a matsayi mace tunda ta haihu gashi har ta tasama wata na uku da haihuwa, yanke shawara ZAINAB tasakeyi na tun karara mijinta ko dan ssauke nauyin da yake kanta nashi" tasa ZAINAB zaman jiranshi a wannan dare,koda ya dawo tayi masa sannu da dawowa"ya amsa a ciki kamar baisanta ba,ko kadan ZAINAB bata kiyeyeshi ba,sai da ta shigar da buk'atarta ta bashi hakkinshi" wata harara ya wurga mata da cewar Ashe ganin buzu a masallaci bazai sa tunkiya taji tsoran Allah ba?" Ke wai waje mara fashinta ce? Nace miki ina buk'atarki ne? Ko nace miki ina sha'awar kwantawa da ke ne?" Ni banza ne kenan da zan k'ara kusantarki"ai tun daga lkc da nace miki muje a cire cikin wannan yaron kika k'i naci alwashin daina kwanciya da ke" wasu zafafan hawaye ne suka ziyarci kumatun ZAINAB hadi da zafin rai dana zuciya"yi tayi kamar taci kwalar RABI'U tace ya saketa kawai ta huta,sai ta tunda da maganar mahaifinta na cewar ko da wasa taja sanadin da mijinta ya saketa ko bayan ya mutu bai yafe mata ba" wannan hujar ce tasa ZAINAB mik'ewa tsaye tsam ta har kusa da RABI'U ta kuma yiwa kanta al'k'awarin ko zafin sha'awa zai zama shine ajalinta bazata k'ara zuwa gareshi ba itama" Ganin haka yasa RABI'U shima ya fita a rayuwar ta" duk abinda ya zama wajinbinshi ya daina bata sai yaga dama kama daga sabulun wanka da na wanki da dai duk wani kayan tsafta wanda ZAINAB zatayi amfani dashi ya daina bayarwa tunda yana ganinta dasu,kuma bai ta6a tambayarta waye wake kawo mata ba." Ko kadan ZAINAB bata gaban RABI'U abin har ya dain 6ata mata rai da zuciya' fatan ta Allah ya dawo dashi kan hanya a kullum addu'ar ta kenan.


ZAINAB na cikin wanna gallazawar ta mijinta Allah ya saukar mata da maraicin rashin iyaye duk biyu dare daya,hakan ya farune sakakon annobar amai da guduwa da ta sami iyayen nata cikin daren da bazata ta6a mantawa dashi ba!!! ZAINAB tasha kuka ita da k'anneta da suka ragemata kamar basu daina ba". Haka dai sukayi ta kuka har suka hakura" bayan an k'are saman makokine dangin mahaifin ZAINAB da na mahiafiyar ta suka raba k'anneta a tsakaninsu,ranar ne ZAINAB ta k'ara tsikewa da labarin duniya!! Tun kamin kowa ya watse aka yanke shawarar zuba yan haya a gidan mahaifin ZAINAB din" kowa ya aminci tsakanin dangin duba da MALAM bashida d'a namiji babba duk mutuwa suka ringa yi,sai daga kan ZAINAB 'ya'yan nashi suka fara zama"gashi har sun koma ga Allah basu sake samun haihuwar namijin ba.
Haka dai aka yanke shawara,kowa ya amice ZAINAB tasha kuka mai isa gani za'a tafi da k'anne nata danginsu"ba iya ita ba hatta dayan sunyi kukan suma duk da ba wani wayo suka cikaba" haka dai suka rabo da juna kowa yana kuka. Ko kadan RABI'U bai tausaya ZAINAB ba bisa rashin iyaye da tayi haka ya cigaba da cisguna mata" dole tasa ZAINAB sake tunkararshi dan sanin matsayinta amman ko kallonta baiyi ba' wanna dalilin ne yasa ta shirya taje nufi gidan iyayenshi"ko da taje bata sami mahifinshi a gida ba ya fita, kunya da nauyi ya yabata zaiyanawa mahaifiyar mijinata komai, ta dai dan gaya mata wasu abubuwan da suke faruwa a tsakanin su" musamam janye hakkin kwanciyar aure a cewar ZAINAB tun kamin ta haihu rabinsu da juna" tafa hannu mahaifiyar RABI'U ta shiga yi da cewar haba ZAINAB na dauka wani gagarumin abune?" Ke ko kunya bakiji na kallona ki sanar dani laifinshi ba duk da irin kyautatawar da yake miki?" haka zaki fara yawan kawo k'arashi daga muguwar iyayenki ko tausayi kanki bakya yi" toh ai sai kiyi hakuri ta wuyu ma tausayinki yake shi yasa ma ya kaurace miki badan wani abu ba,banda zamani ina ke ina iya fitowa kice baya kusantarki"wallahi mu adacan ko k'awace zaki iya sanar da ita wanna maganar ba,bare ni da nake a matsayin mahaifiyarshi,sunkuyar da kai ZAINAB tayi tana jin surukar tata tana ta faman motar maganar" hakance ta hana ZAINAB dadewa a gidan tunda ta fuskanci mahaifiyar mijjn nata bata son a fadi alaifin d'anta,ta baro mata gidan." Tunda ZAINAB ta baro gidan surukar tata,ko da wasa mahaifiyar RABI'U bata gayawa mahifinshi ba,bare yayi binke a matsayinshi na namiji" ganin babu sarki sai Allah yasa ZAINAB ta rungum k'addararta ta faulawa Allah" duk wani kaso dakesamu na hayar gidan mahaifinta akan hidimarta da taranta ta ke k'arewa ko kadan ZAINAB bata k'ara gajiyawa da hakan ba tunda ya zame mata jiki duk da yawan rashin lfy da ANAS yakeyi" tana cikin wanna halin ne gwamnati ta bijiro da aikin titin da zai ratsa ta unguwarsu anyi ittifak'in gidajan da za'a ruguje cikin kuwa har da wanda mahifinsu ya bar musu gado" nan hankali ZAINAB ya kara tashi sosai, da taji wannan lbr." Bayan gwamnati ta rushe gidajan nasu ta raba musu diyya,idan aka raba musu ita da k'anneta"ita aka damk'a mata nata a hannuta,haka ta ringa d'ibar nata kudin da kadan_kadan tana yin hidmar yau da kullum saura ta k'ara a jarinta. Tunda RABI'U ya ga ZAINAB ta kara samin wannan kudaden ya k'ara matse hannunanshi babu wani abun da ZAINAB zata gani na ciki ko n sha,ko na sha'awa nata ko na yaransu" taiya tunkarshi da maganar ya sai musu' tsawan shekaru takwas kenan wannan ce ta k'ara kasaara ZAINAB din" duk lkc da tayi tunk'urin bijirewa wasiyar mahaifita sai ta kasa, ba wani abu take k'ara tunawa ba illa iyakar gamuwarta da mahillicnta uwa uba ga tausayin rayanta da taki a duk lkc da ta kalli idon yaran sai taji bazata iya barisu ba ita ma,wannan ce tasa ZAINAB daura dammara zama da RABI'U duk wuya duk rintsi. Tana cikin wannan haline Allah yasa RUKAIYYA kawata suka dawo gari ita da mijinta tunda duk su biyun ma'aikatane"cikin ikon Allahkusa dasu ma suka dawo run dag lkc RUKAIYYA ce take taimaka mata akan komai wanda baifi karfinta ba,hakan take k'ara bata shawarar duk rantse kar ta sake ta rabu da yaranta" tana kaiwa k'arshen tunanin ta tuni ta jike fuskarta da hawaye Sai a lkc ta lura da dawowa k'awartata tun tsawan lkc tana tsaye kanta...............






~AMENAT KABER KIRU~












*KARUWAR GIDA*






*STORY WRITEEN BY✍*




*AMENAT KABER KIRU*


*SADAUKARWA GA:*


*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*





*TSOKACI*


*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*




*🅾7⃣*




Tsaiwar Hajiya RUKAIYYA bata hana ZAINAB cigaba da kukan da takeyi ba" sunk'uyawa Hajiya RUKAIYYA tayi tatallafo kan ZAINAB da cewar haba kawata yaushe zaki daina wannan kukan naki?" Ya kama ace kin saba da halin da kike ciki duk da cewar manzo Allah sallalahu _alaihi_wasalam yace (babu wani bawa da jure cutar bayi yana ji, idan ba Allah ba.) Amman duk da haka inason karki manta da ubangiji mu,domin shine ya kaddara miki komai tun daga ranar da aka haifeki har zuwa ranar mutuwarki tsararrene a gurin Allah babu wani bawa da ya isa ya ketarewa k'addarasa" abibda nake so dake shine ki k'ara hakuri akan wanda kikeyi"cikin shashshek'ar kuka ta amsa da insha Allah zanbi duk shawarar da kika bani" Ganin ZAINAB ta d'an lafa da kukan da takeyi ne yasa RUKAIYYAN tace mata bari taje ta kaiwa Dr mugungunan da ta sayo wa ANAS a phamarcy ya duba"amsawa ZAINAB tayi da toh" wucewa RUKAIYYA tayi office din Dr" sallama tayi kaitsaye" Dr ya asma da sannan ya k'ara nuna mata gurin zama" RUKAIYYA ta zauna had'i mik'a masa maganin da ta sayo" yasa hannu ya karba ya duba komai yabata amsa da cewar duk sunyi, ya k'ara da bata shawarar akan bawa ANAS kulawar da ta dace" amsawa RUKAIYYA tayi da toh mungode" tayi masa sallama ta fito" ta dawo inda ZAINAB take zaune da ANAS akan cinyarta da kanta ta sunkuya ta dauki ANAS din sannan ta kalli ZAINAB da cewar tashi mu tafi" toh kawai ZAINAB tace tana biye dasu a baya",har suka isa idan RUKAIYYA tayi parking din motarta ta,a hankali ta mikowa ZAINAB ANAS ba tare da tace mata komai ba" hannu ZAINAB tasa ta karbeshi" sannan RUKAIYA ta bude musu motar ta koma nata 6angaren" ZAINAB ta shiga ta zauna tana cigaba da zubar da k'allah da ta cika mata idanu" itama RUKAIYYA bude gurin zaman driver tayi ta zauna kamar zata tayar da mota sai ta fasa ta waiwaya ta sake kallon ZAINAB da cewar k'awata ko baki dauki shawarata bane?" Da sauri ZAINAB ta d'ago runannun idanuwanta wadanda sukasha kuka, ta kalli RUKAIYAYA da cewar ko kadan wallahi ina dai tuna irin cutarwar da ake min ne" numfasawa RUKAIYYA tayi da cewar toh nagode amman dan Allah ki k'ara hakuri,sanna duk abinda zakiyi ki kalli ubangijinki shine mai yayewa bawa duk wata damuwa" godiya ZAINAB tayiwa RUKAIYYA hadi da cewa zata cigaba da hakurin da takeyi" a sarari RUKAIYYA ta nuna jin dadinta bisa ka6ar shawararta da take dauka koda yaushe." Sunyi tafiya mai nisa babu wanda yace wa kowa komai atsakanin su" sai daga baya ne ZAINAB tacewa RUKAIYYA ga wannan kudin da HAFSAT AL'AMEN ta bani ko zaki karbi wani abu daga ciki?" Murmushi RUKAIYYA ta sakarwa ZAINAB da cewa haba k'awata ko bansanki ba ace yau na fara ganinki kika sanar dani halin da kike ciki ai na tausaya miki na bar miki kudinki bare kuma ina matsayin yar uwa a gareki domin kuwa bana kallonki a matsayi k'awa sam_sam, Allah yasamin soyyayarki da tausayinki a jinana,kinga kuwa idan na karbi wani abu daga hannuki banmiki adalci ba,nifa duk abinda kika ga nayi miki daga Allah ne kawai domin nima ba iyawa ta bace". Godiya ZAINAB din ta k'ara yi mata" ta amsa da cewar ki godewa ubangiji mu baki daya" sannan ta ringa Jan ZAINAB da hira har sai da taga hankalin ZAINAB ya dawo jikinta" sanna ta shawarceta akan tayi amfani da kudin da HAFSAT ta bata wajan biyawa yaranta kudin Makaranta abinda yayi saura sai ta cigaba da amfani dasu" amsawa ZAINAB tayi da cewar kamar kin shiga zuciyata wallahi tunanin da nakeyi kenan" Ai insha Allah da zarar ANAS yaji sauki zasu koma karantarsu daga boko har islamiyya, domin bana jin dadin zaman su a gida ni kaina ai ilimi shine jigo komai" kullum sai nayiwa mahaifinsu magana akan yasan muhimmanci ilimin yarashin koda bai kula da sauran hakkoki ba,ta hanyar biyan kudin makaratarsu amman sai yayi min shiru ranar da yaso magana ne yake jefa min habaicin wai meye amfanin ka fashintar da yaran da uwarsu bamai fashintar komai bace? Ai yasan suma haka zasu zama dan shi baiga amfani bawa mara fashintar ilimi, ilimi ba, ZAINAB ta k'are zancanta da k'afa" ko kadan RUKAIYYA batayi mamakin maganar ZAINAB domin kuwa agwagwarmayar ta ta gurin aiki tasha ganin maza masu irin halin mijin k'awartata, wannan ce tasa akullum take k'ara bawa ZAINAB shawara akan tayi hakuri da halin mijinta haka zalika take kokarin taimaka mata akan duk wani abun da taka ya dace tayi mata"ko kadan RUKAIYYA bata gajiyawa da gain akin ZAINAB din domin kuwa kallon yar uwa ta jini takewa mata kamar yadda ta sanar mata tun a baya, wannan dalilin ne yasa bata Shakkar bata duk wata kulawa daga ita har 'ya'yanta,"tasha hana idonta bacci domin tashi tayi sallolin dare hadi da rok'on Allah badan kowa ba sai dan ta yar uwarta rokon ubangiji yak'ara tallafawa k'awarta ta hadi da nema mata mafita gurin ubangiji, aduk lkc da ZAINAB tazo da mtsalarta RUKAIYYA kan shiga matsanancin tashin hankali sabida tana ganin k" tana danne halin da take ciki domin gudun kar ta nuna mata damuwarta a sarari fad'awa matsala." Haka suka tafi suna tattauna al'amuran rayuwa kamar yadda suka saba a kullum" hakaki RUKAIYYA ba k'aramin dad'i take ji ba idan ta tuna irin hallicin da mijinta yayi mata a rayuwa" shi yasa a ta tuna da hakan takewa k'ara yiwa Allah godiya domin ba duka maza ne suke da hali iri d'aya ba,wani yasan abinda ya kamata na wajibinshi ga ilyalanshi wani akasin haka shi yasa hausawa suka Allah d'aya gari banban. Haka suka isa har kofa gidan ZAINAB suna hira kamar yadda suka saba a tsakanin su"guri RUKAIYYA ta samu tayi parking da motarta sanna ta bude murfi ta fito ta zagayo inda ZAINAB take zaune da ANAS a rungume a hannuta,ta bude mata karfin nata 6angaren ta mik'a hannu ta kar6i shi " ZAINAB ita kuma ta dauko leda magungunan nashi suka shiga ciki tare" ba wani dadewa RUKAIYYA tayi a gidan ZAINAB ba tayi mata sallama hadi da k'ara bata shawarwarin da suka dace akan jikin ANSA din" amswa ZAINAB tayi hadim da k'ara yi mata godiya bisa kyuatata matan da keyi" juyawa RUKAIYYA tayi ta kalli ZAINAB din sanna ta sakar mata murmushi hadi da amsa mata dacewar daga safiyar gobe aikinta zai juya morning ne kar taji shiru da zarar ta sami time zata iya zuwa duba su koda yaushe" asawa ZAINAB tayi da cewar kai haba babu damuwa" har kofar gida ZAINAB ta sake rako RUKAIYYA sai da taga tashin motarta sanan ta koma gida.
Tana komawa sake lek'awa dakinta tayi domin ganin ANAS ya farka daga baccin da yakeyi?"ko da ta duba sai taga ashe bacci yakeyi har wannan lkc hakane yasa ta fada keching da sauri ta wanke tunkuya ta daura sanwar fara shinkafa duba da babu komai a gidan sai ita kade" tana gamawa ta sake juyawa tayi waje ta shiga gidan makwafciyata Sallama ZAINAB tayi, mafkwaciyar tata da ke ta faman aiki a tsayar gida ta amsa hadi da tambayar ZAINAB sun kun dawo daman yaya ANAS din da jikin?" ZAINAB ta amsa da cewar eh yanxu muka dawo babu jimawa haba yaji sauki" masha Allah makwafciyar ZAINAB ta amsa mata da shi hadi da cewar amman dai basu da sauki sosai ko?" Amsawa tasakeyi da cewar da sauki ai dubashi sukayi sai magunguna da suka rubuta mana kuma mun saya tun a asibiti, shine ma karin jinkirin mu" itama amsawa tayi da cewar ai da naji shiru da har zan bugawa maigidana waya na gaya masa zan bi bayan ku,sai kuma na tuna ai babu waya a hannunki kema kuma bansan wanne asibiti kuka tafi ba" murmushi ZAINAB tayi da cewar karki damu tunda ba kwantar damu sukayi ba" duk maganar da sukayi MARIYA tana falon gidan tana ta kallon TV tunda duk yaran gidan sun tafi makaranta sun bayar ita kade, sai a sanna ne ta leko nacewa ZAINAB sannu da dawowa UMMA"amsawa ZAINAB tayi da cewar yawwa, sannan tace yawwa kizo gida yanxu zaki yomin cefene a bakin layi bayan ta gama gayawa MARIYA sakonta ta juya ga makwafciyar ta tayi mata godiya hadi da sallama ta koma gida" itama MARIYA komawa cikin falon ta dauko hijabinta ta bi bayan mahaifiyarta ta.Sallama MARIYA tayi shigo gidan nasu hadi da yiwa mahaifiyarta sannu da gida tak'ra da tambayar jikin kanin nata?" asmwa ZAINAB tayi da cewar yaji sauki, Sanna tayi mata umarni da tashiga d'aki ta dauko kudi ta aiketa" amsawa MARIYA tayi" ta wuce cikin hanzari ta dauko kudin tazo ta durkusa har k'asa ta mik'awa mahaifiyarta" ZAINAB tasa hannu ta kar6i kudin ta kirgo wasu daga ciki sanna ta lissafa mata duk abinda zata sayo musu na cefen miya ta mik'awa MARIYA kudin" hannu tasa ta karba ta fita da hanzari" tashi ZAINAB tayi ta cigaba da aikin da takeyi." Bayan fitar MARIYA baifi miti ashirin ba ta dawo ta kawo aikine da mahaifiyarta ta tayi mata" cikin hanzari suka hadu suka gama gyara komai tunda duk wani aikin gida tuni ZAINAB ta komawa yarta sai wanda baza'a rasa ba duk da k'aracin shekarunta" bayan komai ya kammala ZAINAB ta shiga d'aki da kanta ta taso ANAS yaci abinci sannan ta bashi magungunanshi yasha ya ko wanne, sanna ta k'ara gyara komai. Shi kuwa RABI'U bai yana chan basan a wanne hali suke ba tunda ya fita tun safiyar da ya kwashe matawa ZAINAB yan kudadenta" shi yasa ko da tadowa da kudin hannuta ta gama zarar na cefenen da tayi musu guri mai nisa ta boye sauran domin gudun komawa gidan jiya,ta sani sarai mugunta irin tashi da baya son yaganta da ko naira biyar a hannunta.


Kamar kullum yauma sai da dare ya raba sannan ya shigo gidan a fusace gudun kar ZAINAB taga fuska ta tambayeni shi wani abu shi yasa ya shigo yana tsaki hadi da mak'osanai tunda yanxu ta farga shine ya kwashe mata kudi da safe" ita kuwa ZAINAB tunda taga ya shigo yana malam zance ko kallonshi batayi ba bare ta tanka ta k'ara mayar da kanta ta kwanta kamar basan ya shigo gidan ba,bare dakinta" ganin haka yasa shi ya fara zage_zage da cewar ta rainashi tana ji ya dawo bazata kawo masa koda ruwa ba,bare tayi masa tayi abinci da zaici" k'ara gyara kwanciya ZAINAB tayi ta bawa banza ajiyarshi ganin bata da niyyar tashi yasa shi ya tafi keching da kanshi dan zubo abinci"yana zuwa ya bude tukunya yaga babu komai a ciki har an wanketa" hakan ne yasa shi ya daga tunkuyar ya maka da k'asa ya dawo d'akinya kama ZAINAB da masifa da bala'in wai ta rainashi" ita kuwa ko tari batayi masa ba bare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login