Showing 18001 words to 21000 words out of 29788 words
bin shi a hankali tana faman lalumar numbern General
amma sam bai d'aga ba , Hydar ya dawo da baya ya wafce wayar daga hannun ta ya saka a
aljihu ya hankad'a ta jikin bango idon shi cikin nata yace " Young lady behave yourself!! Any
slight move here could be noticed!! " Hankade shi tayi itama tace " Toh ba se ayi noticing d'in
ba? Haka kawai zaka b'ata min mission! Ni ban san ko Kai waye ba kuma ban san me nufin ka
na Hana ni waya ba amma kaji na gayamaka if I smell anything fishy around here kana cikin
matsala!"
Tsawa Hydar ya daka Mata " toh se me? Nima ba sanin ki nayi ba kowa kuma da abunda
yazo yi nan ! Ni nazo in ga bayan su ke kuma kin zo ki bincike su! Wannan ba shine abunda
kike son ji ba!? Toh yanzu kinsan dalilin da yasa nake neman su ! Am to them like a predator!!
Ni farauta na fito ba investigation ba , minti ashirin kachal Zan baki ki gama abunda zakiyi ki bar
nan ko kuma in had'a harda ke !don duk wanda yayi niyyar shiga tsakanina da abunda nayi
niyya shima bazan barshi ba!!!!"
Duk tsoron da ya ratsa Asy bata fasa magana ba " Look who ever you are ni bazan tab'a Bari
kayi kisan Kai a nan ba! Se nayi abunda zanyi no matter what!! Do your worst!!!"
" Hmmm Asy ba laifin ki bane!! Rashin sani ne yasa kike min haka but just in case zaki
manta later on ina so ki sani kika b'ata min plans nawa you'll face the consequences!!" Tsaki
Asy taja tana gyara rolling d'in kanta da gyalen ya warware ta bi ta gefen Hydar ta wuce.............
Jeeddah ja'oí ¼í¿µ
[10/20, 10:10 AM] +234 701 661 4602: í ½í²» BURIN FANSA í ½í²»
í ½í²” NA HAUWA ISAH JA'O í ½í²”( 2016)
9⃣6âƒ£í ¼í¾ž9⃣7⃣
Wani katoton warehouse ta shiga wajen shiru kamar ba'a halicci d'an Adam a wajen ba , a
nata zaton babu kowa a ciki hakan yasa ta dinga bud'e bud'e babu abunda idanuwanta ke nuna
Mata kamar su cocaine, heroin da sauran muggan makamai , bata daddara ba ta sake bud'e
wata y'ar k'ofa ta shiga babu komai cikin sa se wata kujera a tsakiyar d'akin ita kad'ai se light
bulb me Hasken gaske ta sama , kamar daga sama ban ankara ba na hango Detective Asy a
sume , wani sangami ya ja ta kamar wata shara ya daurata a kan kujerar sannan ya d'aure da
cello tape duk hannayenta ya had'a da hannun kujeran ya d'aure haka bakin ta ma, ya dad'e
yana k'are Mata kallo kafin daga bisani ya d'ebo ruwan sanyi a bucket ya watsa Mata ,cikin
firgici ta bud'e idanuwan ta , mayafin ta ya dawo kafad'ar ta tsabar galeji gashi babu hanyar yin
self defense tunda a d'aure take.
Matsawa kusa da ita mutumin yayi yace " Kyakkyawar fuska! Amma kuma zuciyar cike da
kuruciya! Kinga Yammata da nine ke da tun daga k'ofar fari Zan juya na Kama gaba na , amma
tsabar rigima da shishigi kika cije kika shigo nan! " Yana magana yana zazzaga purse nata a
k'asa Kwatsam ID card nata ya fad'o kallon kallo kawai suke yi shi da ita wata mahaukaciyar
dariya ya kufce masa yace " Jami'ar y'an sanda! Detective Asy Khaleel! Ashe kice da biyu kika
zo nan! Kin zo neman bayanai ne akan MK ko kuma DON BK ?? Toh Bari na baki wani d'an
labari mana! Don BK baya Nahiyar ASIA baki d'aya yana Chan Nigeria ! Haka ma akwai wani
sabon labari MK ma yana nan zuwa Singapore nan da anjima kad'an !! Amma zazzafan labarin
shine yau zaki Mutu mushe babu kuma wanda zai sake jin labarin ki ! A kan gawar ki Mk zai sha
barasa!!!! " menene kalaman ki na k'arshe???! Iye fad'a min mana chika !! Ya ko kin ji tsoro
ne!!!""??
Duk wad'annan maganganu da yake yi Asy idanuwanta gam a rufe se zufa take yi kamar
daga sama suka jiyo harbi Tas!!" Asy tana d'aga Kai se gani tayi sangamin nan ya zube a k'asa
se kurma ihu yake yi , lokaci guda duk ya fita hayyacin sa , Asy dake zaune a kujerar se girgiza
Kai take kamar me son cewa "No"! Amma ina Hydar ya sake one step ya tsugunna gaban
sangamin yace " David!! Tell me yaushe zai shigo!!?" Kai David ya girgiza cikin rad'ad'in ciwo
hak'oran sa duk Jini yace " Over my dead body!!!" Wani shu'umin murmushi Hydar ya saka yace
" Don't be so stubborn David I know you wanted to live badly! Kana son rayuwar ka sosai ,
chance na baka to live , abu d'aya nake so ka sani koda MK yazo in yaji labarin ka yi sakaci har
an zo an yi lek'en sirrin ku toh lallai fa kashe ka zai yi its better ka gaya min ko Zan taimaka in
barka da rai!! Ko ba komai kaga zaka rayu zuwa lokacin da M.K zai shigo gari!!"
Kai David ya girgiza yace " Bazan sanar da kai komai ba kamun duk abunda kaga dama
amma bazan fad'a ba!!" Kai Hydar ya girgiza fuskar shi d'auke da bacin rai a take ya fitar da
wata revolver pistol ya d'aura a gaban goshin David Asy tana ta girgiza kai amma ina aikin
gama ya riga ya gama! Hydar ya harbe David har lahira a take Asy ta d'auke wuta a wajen
kwakwaran motsi ma ya gagareta ta zaro idanuwa waje numfashin ta ko k'arasawa ciki baya yi
idanuwan ta kuwa suka kafe a kan gawar David dake kwance cikin jini............
Mik'ewa Hydar yayi ya mayar da bindigan sa cikin Aljihu sannan ya nufi inda Asy take ya sa
hannu ya warware Mata cello tape d'in ya cire na bakin ta ma yayi ficewar sa, A hankali take
tafiya gyalen na rataye a wuyan ta sam ta kasa magana! Cikin motar da Hydar ya shiga itama ta
shige ya fisgi motar bai zame ko ina ba se bakin bird park yayi parking sannan suka fita sukayi
bakin ruwa a inda sukabar boat d'in nan suka sameta , Asy ko zama bata yi ba hasalima a
gaban boat d'in ta tsaya ta k'urawa ruwan ido bata ma san sun iso ba seda driver ya Mata
magana , Hydar kam tuni har ya isa wajen motarsa ko ta kanta bai bi ba balle ma yasan me
take yi!
Babu kofa a cikin falon , Uncle Junaid ya fita don haka Hydar ya ajiye wayoyin sa ya juya ya
nufi hanyar d'akin sa, wani zuciya ne ya tahowa Asy a fusace tabi bayan sa , tana shiga d'akin
ta hankad'a shi saida ya dafe hannun shi a center table d'in d'akin tukunna ya d'ago jajayen
idanuwan shi yana kallon ta.
" Who the hell are you?! Tambayan ka nake Hydar! Kai waye! How dare you kill David! Haka
ake investigation! ? Malam kaga ni ban san kai waye ba kawai an turo ni akan zaka iya taimaka
min a kan investigation d'ina amma by the look of it you are nothing but a bloody murderer !!!
Kai baka d'auki ran mutane a kan komai ba , kai dakiki ne ! Shin baka sani ba ? Ta iya yiwuwa
yana da Mata harda y'ay'a yaya kake zaton zasu ji idan har ta rasa mijin ta ko kuma suka rasa
mahaifi?!!"
Hydar da ya riga ya gama fusata musamman da tace masa shi dakiki ne bai san lokacin da
ya hankad'a ta ta bugu da bango ba cikin tsawa yace " Idan kuma hakan ta faru da yarinya y'ar
shekara biyar fa? Da yaro d'an shekara sha d'aya! ? Ina nufin idan aka kashe musu iyayen su
babu tausayi babu imani a gaban idon su , yayinda uwar ke d'auke da k'aramin ciki! Shin yaya
kike tsammani rayuwar su zata kasance?! Asy shin kin tab'a rasa wani daga cikin y'an uwanki ?
Kin tab'a fuskantar irin cin fuskar da na fuskanta a rayuwa? Da kin san waye MK da wallahy duk
abunda Zan aikata bazaki ko d'aga kai ba! Naji ni dakiki ne! Amma ina so ki sani babu wani
mahalukin da ya isa ya shiga tsakani na da wad'annan azzaluman se naga bayansu d'aya
bayan d'aya se sannan ne tukunna zan iya sauraran kalaman ki yanzu koda zaki mutu bazaki
chanza ni ba Asy! Saboda haka idan kin ga dama ki koma Chan Newyork inda kika fi wayo ki
barni nan! I was born to destroy Mk se na sa ya d'and'ana azabar da suka d'and'ana shekaru
sha biyar da suka wuce ! If you like call me names Asy but ina so ki sani I AM NONE STOP!!!! "
Da gudu Zainab ta rungume yayanta tana kuka tana fad'in " Yaya kar ka barsu da rai ka
harbesu duk! Badan su ba da yanzu ina tare da Mommy , dalilin shi na rasa kowa ,kai kad'ai ka
rage min yaya kar ka Bari suci galaba a kanka ! Kada ka kyale su yaya! Kada ka kyale su!!
Rungume ta yayi yana shafa gashin kanta , Asy dake tsaye duk sun dulmiyar da ita a duhu ta
kasa fahimtar me yake faruwa gaba d'aya ta juya da sauri ta fice daga d'akin ta nufi d'akin ta
gamida zubewa a kan gado..............
Jeeddah ja'oí ¼í¿µ
[10/20, 10:10 AM] +234 701 661 4602: í ½í²» BURIN FANSA í ½í²»
í ½í²” NA HAUWA ISAH JA'O í ½í²”( 2016)
9⃣7âƒ£í ¼í¾ž1⃣0⃣0⃣
" Dad! Nifa wannan mutumin da ka had'a ni aiki da shi yana matuk'ar bani tsoro! Ban san
waye shi ba but meyasa bashida tausayi bai damu da damuwar da wasu zasu shiga ba? Ka
duba fa d'azu ya kashe mutumin da zai bamu clue about MK amma ko a jikin sa and he have
the guts to shout at me wani wai ""I am non stop""!!! He's very dangerous! "
General yayi gyaran murya yana murmushi yace " My dear ki 'kara hak'uri kuma duk abunda
yayi ki bishi a hakan , he knows what he's doing!" Asy ta marairaice tace " Haba Dad waye shi
da zai dinga yin abu son ransa ? Who d hell is he??" Daga bayan ta tajiyo Murya yana fad'in
" N.F.S !! Nigerian force services! An undercover agent LIEUTENANT GENERAL HYDAR
ALIYU ABDOUL-RAHMAN!!!! "" juyawa Asy tayi cikinta ya dura ruwa tana d'aga kai sukayi ido
hud'u da Hydar tsaye bakin k'ofa fuskar nan tamke babu alamar fara'a tattare da ita , k'arasowa
yayi cikin d'akin ya wuce ta ya nufi wajen wani shelf dake d'akin ya ciro files guda biyu ya bi
gefenta ya fice abunsa , a hankali ta Fara mayar da wayar nata kan kunnen ta cikin murya me
rawa tace " Dddad.,., da gaske ne abunda ya fad'a?" Murmushi General yayi yace " My
daughter! Abubuwa da dama sun faru a rayuwa! Duk yanayin da kika ga mutum kar ki raina
hakan rayuwar Hydar cike take da bakin ciki ki bishi yanda yake so , bai fiye son shishigi ba ,
Anjima zamuyi magana !!"
Jiki a sanyaye ta ajiye wayar tana tuna kalaman da ta fad'a masa tace " Lallai yau na kwafsa!
Lieu gen Hydar na k'ira dakiki??" Bata kammala tunanin da take ba wayar ta sake 'kara,
Wannan Karon abokin aikinta ne Jones dake Newyork nan suka d'an tab'a hira Azeeza na gefe
tana jin su Jones ya sanar da ita zasu zo Singapore tare da Azeeza don kammala binciken
kisan da suke yi saboda haka ta nema musu waje! Bayan Ta ajiye wayar ne yayi daidai da
shigowan Uncle junaid ta zata maganar Hydar yazo yi amma to her surprise se yace " Ki sauk'o
muci abinci " Kai kawai ta girgiza masa shima ya juya , Har zai fita kuma se ya juyo " You look
disturbed Asy! Akwai wata matsala ne?" Murmushi tayi sannan ta sanar dashi cewa Su Jones
zasu zo ko zai taimaka ya basu masauk'i murmushi ya Mata yace " its ok akwai enough space ,
ba komai Allah ya kawo su lpya , Ameen ta amsa tare da bin bayan sa suka nufi dining
d'in.............
Sauk'owa yake yana Danna wayarsa kanshi a k'asa har ya iso dining area d'in ba tare da
ya d'aga kai ba yaja kujera se sannan ya ajiye wayar ya d'ago yana kallon Zainab da take ta
fama da pasta gasu dogi , dariya sosai ya Fara yana kallon ta itama ta d'ago tana masa dariya ,
ya tuna tun tana k'arama tana son abun amma kafin ta cinye se bakinta ya gaji don tsayin
pastan , seda ta gama had'iye wa sannan ta d'auki fork kamar zata choke shi ,da sauri ya matsa
yana fad'in " Dole ne se kin ci? Nan gaba bakinki se yayi tsayi! Ummmm kiyi ki gama mu fita
cikin gari ,ina son zuwa shopping " ya k'are maganar yana jefa peanut a baki , kallon sa kawai
Asy take yi kafin ta mik'e zata koma d'aki da sauri Zainab tace " Sis! Baza ki bi mu bane ? " da
sauri Hydar ya mik'e ya ce " Ke Zee ! Ki kyale ta mana Ana dole ne? Tunda kika ga ta tashi bata
da niyya ni bana son shishigi" baki zainab ta turo tace " toh kuma yaya .........." Bata k'arasa ba
yace " Shhhhh ki gama zukar pastan ki mu tafi kar ki min wasting time! Next week zamu koma
Nigeria" tsalle sosai Zainab take tana buga k'afa wai ita sam bazata koma Nigeria ba , shi kuwa
kawai ya tsaya yana kallonta yana mamaki at the same time abun ya mugun bashi dariya
,kamar bai ganta ba yayi yaci gaba da jefa peanut a bakin sa yana Danna wayarsa , Chan da ta
gaji ta matso kusa dashi a hankali tana kallon abunda yake yi a waya kafin tace " Yaya wai kai
baka cin abinci ne? Bai ko kulata ba ta sake matsowa tace yaya bani wayanka nima Zan buga
game d'in da kake yi " Nan ma bai ce Mata 'kala ba ganin bashi da niyyar magana ta wafce
wayar ta ruga a guje shima ya bi bayanta yana kiranta amma ina tak'i tsayawa ta fice Daga
falon suka fita filin gidan daga gefe ruwa ne yake zuba ga dukkan alamu bayi ake wa grass d'in
wajen da flowers ,nan ta d'auke hose (Tiyo) d'in ta yi pointing a setin Hydar duk ta jik'e shi jagaf
da ruwa ,Asy tana saman balcony tana Kallonsu with adoration , she really missed her
brotherí ½í¸˜
Jefar da hose d'in tayi ta nufi inda suke parking motoci tana fad'in come on yaya! Catch me
if you can!!!! Girgiza kai yayi sannan ya nufi inda take , Out of nowhere yaji ya ci Karo da abu ,
tun daga k'asa har sama yake kallon ta , pencil jeans trouser ne jikin ta se blue kaftan top da ya
wuce cinya da kad'an se kuma farin mayafi data yafa ba tare da tayi rolling ba , handbag nata
Sak jeans d'in jikinta ,takalman ta ma blue ne, kallon sa ya mayar zuwa kan fuskar ta wani abun
mamaki Sak take Kama da Zainab d'in sa Banbancin su tafi Maryam girman jiki kuma tana da
bulin hanci wanda ta saka masa stone fari me kyau.........
Murmushi ta sakar masa tace " Am sorry ! Am by name Azeeza MK An FBI agent Mujhe
Detective Asy Khaleel se Milne ayee"(I have come to meet detective Asy) a zaton ta Hydar
indian ne
Ba tare da ya kalli inda take ba yana matse ruwan rigar shi yace " Asy khaleel tana ciki
"amsar sa kenan a tak'aice , zaro idanuwa tayi waje tace " Oops sorry ! Nayi zaton kai d'an nan
ne , tare muke da abokin aiki na I hope ba matsala in ya shigo?" Nan ma bai kalleta ba ya juya
yana fad'in " In kinga dama !" K'ugun ta tarike tace * Lallai ma wannan mutumin shi me ya d'auki
kansa ne???"
Hydar yana shiga falo ya duba bai ga Uncle Junaid ba da sauri ya haura side nashi ,tsaye ya
iske shi yana gyara rigar sa ga dukkan alamu fita zai yi , a hankali ya juyo yace "Yaya dai
Soldier? " yana maganan yana neman wajen zama.
Hydar ya nisa sannan yace " Yar gidan MK ! Itace Uncle! Itace abokiyar Aikin Asy Khaleel
uncle idan har na barta a nan wataran Zan iya cutar da ita!! Kace ta fita! Kaje kace ta bar min
gida!!!" ..........,,,.......
Jeeddah ja'oí ¼í¿µ
[10/20, 10:10 AM] +234 701 661 4602: í ½í²» BURIN FANSA í ½í²»
í ½í²” NA HAUWA ISAH JA'O í ½í²”( 2016)
1⃣0⃣1âƒ£í ¼í¾ž1⃣0⃣5⃣