Showing 6001 words to 9000 words out of 29788 words

Chapter 3 - BURIN FANSA BOOK BY Hauwa M. Ja'oji.pdf

27 Apr 2025

1739

2⃣6⃣🎞3⃣0⃣


" Hanny ya meeting naku da general ya tafi ? Hope everything went smoothly? Kuma I
taught kayi amfani da maganar da na fad'a maka? " Murmushi kawai Lt Aliyu yayi ya shafa
gefen fuskar ta yace " look dear! Na fad'a miki M.K is my bro , idan babu ni ai shine who is

supposed to take Care of you and my kids I don't know why you act so different when it comes
to him ! Pls forget it! Ni ya raka kuma tare muka yi magana da General ,shida ma fita yayi ya
bamu waje tun discussion d'in bai kai ko ina ba?"

Gyara zama Fareedah tayi tace " kana nufin kun fara maganar a gaban shi se kuma ya fita?
Kenan ya ji maganar da kuka yi ,I mean yaji akan issue d'in da kuka tattauna ko?" Toh meyasa
bakayi tunanin fitan da yayi ba? Me ya fitar da shi a wannan lokacin?"
A d'an fusace lieutenant ya juyo ya kalli Fareedah yace " Look Barrister! This is not a court
issue ,wannan fa ba case bane ballantana kice zaki iya solving or something, wannan aiki na
ne! And I know exactly who to trust! M.K is my Brother ban san me ya aikata miki kika sa mishi
ido haka ba! I don't really know! Ki tsaya a matsayin ki na barrister kar ki shiga aikin soji! Ba
hurumin ki bane my dear!" Yana kai wannan ya zira jallabiyan shi ya yi waje ya barta zaune a
bakin gado , duk bak'in ciki yabi ya tokare mata wuya tana hawaye tace " That man doesn't look
to me like a true Bro! He is different ! Aliyu ya kamata ka fahimce ni ! " ta gaji da kukan ta ta
share fuskar ta sannan ta fice daga d'akin zuwa downstairs ,nan ta iske Captain Junaid tare da
su Hydar suna kallon Shaun the sheep.

Zama tayi ta sauk'e ajiyar zuciya sannan tace " Captain Junaid ina so muyi wata magana!
Pls mu je dinning table " ba musu ya mik'e suka nufi wajen ,ta ja kujera ta zauna shima haka ,

Daidai lokacin Aliyu ya shigo fuska a d'aure ya wuce d'aki, tashi tayi ta ce " Just a minute
Junaid ina zuwa pls" kai kawai Junaid yayi ya fara bubbuga hannayen sa kan table d'in. Dakin
itama ta shigo ko kallon inda yake bata yi ba ta bud'e wata drawer ta ciro wani file jacket da
briefcase ta fice , haka ya bita da kallo ,kawai yaji kuma bai yi daidai ba , maybe tana da hujjar
ta na fad'a masa hakan don haka ya bi bayanta da sauri ya rik'o hannun ta ....

" Am sorry my dear! I should have listen to you! Wata'kila kina da reason naki! Hannun ta ta
wafce ta sa kai tayi gaba ,yana biye da ita a baya! Har wajen table d'in shima yaja kujera ya
zauna , bata ko kalle shi ba ta fitar da wasu takardu tayi signing a jiki ta kalli su Hydar da ke
kallo babu ruwan su tayi murmushi sannan ta maida dubanta ga Junaid tace " Junaid wannan
file d'in yana d'auke da duk dukiyar da muka mallaka nida Aliyu! A halin yanzu nasu Hydar ne ,
wannan kuma laptop d'in yana d'auke da wasu bayanai ! A kowanne lokaci ina kwana da shi
cikin firgice ne don haka ina so ka rik'e Amana! Kar ka bari wani ya gani domin kuwa a wannan
zamanin kowa ba abun yarda bane! I believe kai kad'ai ne zaka rike amanar Mu nida Aliyu ,any
time za'a iya zuwa neman wannan system d'in kada ka sake su sameshi ! Ni nasan menene a
ciki don haka be careful ka rik'e with care!!"
Junaid ya ce " Toh amma Madame why me? " shhhhh Kaidai kawai kayi abunda tace maka
,Kaje ka Adana wannan abun tunda ta fad'a maka!! Maza tashi Kaje!!!" Aliyu ne yayi wannan
maganar , ba musu Junaid ya fice da sauri ya shiga motar sa ya fita ,bai wani bar k'ofar gidan
ba kawai ya hango wata bak'ar jeep ta nufi k'ofar gidan don haka ya kashe Wutar motar sa ya
kwanta a ciki yana lek'o wa a hankali.........
[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)

3⃣6⃣🎞4⃣0⃣


Sun gama bincika ko ina basu samu kowa ba , Motocin wasu soji ne suka fara shigowa
cikin gidan ganin haka yasa duk suka haura suka fice daga gidan ta inda su Junaid suke ba tare
da sun lura suna wajen ba , wata k'atuwar mota ce bak'a kamar bus ta zo da gudu ta daukesu
suka bar wajen cikin tsananin speed. Gaba d'aya sojojin suka bazu a gidan suna dube dube daidai lokacin Ambulance ta shigo
,baka ganin komai se walwalin sirens.

Captain Junaid ya rik'e yaran suka fito daga inda suke b'oye ,da sauri wasu Sojojin suka nufo
su tare da wasu Nurses guda biyu suna sanye da kayan soji amma kuma da lab coat a jikin su ,
yaran suka karb'a daga hannun Junaid ,Hydar ya wafce da gudu ya nufi cikin gida ,suma suka
bishi a baya , Bai tsaya ko ina ba se d'akin su Dad ,nan ya same su kwance shame shame ,
likitoci biyu suka dukufa suna duba lafiyar su , dukkan su suna Numfashi don haka aka makala
musu Oxygen mask aka fita da su , gaba d'aya unguwar cike take da sojoji. Wayar junaid ne
tayi k'ara jiki na rawa ya d'aga ya kara a kunne " Sir ! Yanzu an kaisu asibiti ! Ok se ka iso sir!!!"
Yana kai wannan ya katse wayar ya kama hannun Hydar ,Zainab kuwa tuntuni daman tana
hannun sa tayi lamo kamar mara lpya , Direct motar sa ya nufa ya sa su sannan ya d'aura ma
zainab seat belt ,ya shiga suka bi bayan Ambulance d'in zuwa Asibiti.............


Har k'arfe Hud'u na safe babu bayani akan kowanne d'aya daga cikin su, Sukayi Alwala
shida Hydar sukabar zainab tare da wasu Sargent's suka fita masallaci , Hydar babu irin adduar
da bai yi ba , Fitowan su daga masallaci basu ma k'arasa cikin asibitin ba , General ya iso ,gaba
d'aya sojoji ne a harabar asibitin tun daga waje har ciki kowa fuska a d'aure babu annuri , da
gudu Hydar ya nufi inda yake yana fad'in " Uncle !! Na gansu sune......" Da sauri General ya rufe
masa baki ya durk'usa a gaban shi yace " Keep it in your heart ,we'll talk about it later! Kar kayi
magana a nan d'ana " kai Hydar ya girgiza yana share hawayen shi , kafin k'arfe bakwai press
sun cika bakin asibitin ,kowa yana son d'aura trending story d'in nan , Captain Junaid ya fito
kenan zai yi waya yaga Press dank'are a k'ofa har ture junan su suke yi ,,bak'in gilashin shi ya
Zara ya sa a fuskar sa sannan ya fara sauk'owa daga benen ,microphone kuwa kamar zasu
chusa masa a baki kowa da tasa tambayar , wasu de fatan su Lt Aliyu is still Alive wasu kuwa
So suke suji menene ya haddasa wannan murder d'in da akayi attempting yi!!"


Dr Lloyd kwararren likita ne wajen fitar da harsashi, shi kad'ai ne kuma se wasu likitoci
guda biyu masu taimaka masa. "Anyi nasarar cire harsashin daga jikin su baki d'aya , Amma
sedai Mun rasa d'aya daga cikin su!! Am sorry " Maganar da likitan ya fad'a shi ya zaburar da
Hydar dake zaune kan kujera ya mik'e da gudu ya doke likitan har saida suka zube a k'asa , da
sauri General da Captain Junaid suka rirriqe shi yana fisgewa yana fad'in " You are lying !! Jiya
ma an harbesu basu mutu ba se yanzu!!" General ya zaro ido waje ya juya yana kallon Junaid
yace " Am afraid Yaron nan zai iya samun matsala a kwakwalwa!! Take him out of here!! "

Junaid ya rik'e Hydar da k'arfi zai fitar da shi amma ena ,ya ci k'arfin sa ya ruga da gudu ya
bud'e k'ofar ward d'in ya shiga , mutum biyu ne kwance d'aya an rufe da mayafi d'aya kuma na
kwance da drip! Hydar ya ruga da gudu gun wanda Aka rufe ya janye zanin , wani duka k'irjin
shi ya fara Nan ya fara k'ira " Dad! DAD!! DAD!!!! KA TASHI PLS PLS PLS WAKE UP!!!"
Fareedah dake sanye da drip ta fara bud'e idanuwan ta a hankali ,sannan ta juyo kanta zuwa
side d'in da take jin Hayaniyar , Dishi dishi take ganin Hydar ,da kyar sight d'in ta ya dawo me
kyau idonta ya sauk'a a kan Gawar Aliyu da ke kwance , basu ankara ba suka ji fad'uwar ta
daga saman gadon , da sauri nurses Suka zo zasu riketa ta d'aga musu hannu Da gudu Hydar
ya rungume ta Zainab ma haka ,Junaid gaba d'aya kuka ya ci k'arfin sa don haka ya fice . fuskar
Aliyu ta shafa hawaye na gangaro mata bata iya yi wani magana ba ta sulale a wajen itama ta
fad'i.................


🖊🏵 Mayjiddah jao🏵🖊
[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)
3⃣1⃣🎞3⃣5⃣


⚡FLASH BACK ⚡.......

Junaid na fita Fareedah ta mik'e ta nufi hanyar bedroom d'in ta ,Murmushi Aliyu yayi ya
girgiza kai k'asa k'asa yace " Very hard to convince" ya mik'e ya k'arasa cikin falon ya d'aga
zainab da tuni tayi bacci sannan ya cewa Hydar " Hey soldier !! Seven am tomorrow zan kai ku
schl maza gashi muje ciki" Hydar ya d'ago fuska da d'an dakile yace " Ok dad! Just five minutes
pls!!! " Aliyu yayi murmushi yace " Nooooo!!!! Tashi muje no five minutes!!! " yana maganar yana
janyo hannun Hydar bai tsaya ko ina ba se d'akin su ,nan ya iske Hindatu tana ninke kaya yace
" Haba Hindatu wannan kayan can't they wait until morning? Dare yayi Kije ki huta mana! Before
that ki rufe min k'ofar parlour yau sam babu kowa a waje nace suje su huta a gida ,so ki rufe
k'ofar da kyau. Ba musu ta fita don aiwatar da abunda ya umarceta.......

BACK TO STORY.....

Junaid yana ganin sun shiga gidan nan ya ciro wayar sa yana k'iran numbern Lieutenant
amma babu amsa , wajen fifteen missed calls don haka ya tura briefcase d'in k'ark'ashi kujeran
motar sa ya d'auko bindian shi ,unfortunately babu bullet a ciki ,ya doki motar da bindigan ya
jefar , daga nan ya d'auko wayarsa ya fara laluben numbern LIEUTENANT GENERAL YUSUF
MAINASARA , koda ya d'aga kafin Junaid yayi magana se yaji Muryar Col Aliyu yana fad'in
What exactly do. You want? , nan ya kashe da wuri ya rasa ma ya zaiyi don haka ya k'ira Major
general gaba d'aya, jiki na rawa yace " Sir this is captain Junaid speaking sir!!! We need cover
up!! Lieutenant Aliyu is in danger ,yanzu na k'ira Lt general Yusuf amma ,ba response ( Don't

really know why junaid lied dat Yousuf did not respond)

General ya mik'e a fusace ya ce what?!! I'll send my boys but you have to do something coz
it will take some time before they reach there " junaid ya amsa da Yes sir!! Copy that Sir!!!" Ya
kashe wayar ya fita cikin sand'a yana ta dube duben k'ofar gidan, Duk saida ya k'arewa position
na CCTV cameras sannan ya d'irka ta saman dogon ginin da ke wajen don gate d'in akwai
masu tsaron wajen , Cikin flowers d'in backyard d'in ya fad'o ta cikin flowers d'in ya gama
k'arewa mutanen kallo nan ya ga sun janyo Body d'in wata mace sun nufo inda yake , sake
lumawa yayi cikin flower d'in suka zo daf inda yake suka yi wurgi da ita.

Idanuwa ya zaro waje yace " Hindatu???!!! ,luckily se yaga still tana numfashi, da sauri ya fito
ya tab'a ta ,a zabure ta rik'e hannun shi tace " Ka tttaimake su yallabai!! Zzzzaaa su khkashe
y'all!!!!!a........ Daga nan bata sake magana ba ,junaid ya damk'e hannayen shi ya rumtse
idanuwan shi yace " Ya ilahi!!! Da sauri ya mik'e bayan ya rufe mata ido ya rufe fuskar ta da
jacket d'in shi , wani sangami ya hango se kai kawo yake ta wajen backyard cikin sand'a ya bi ta
bayan shi ya murd'e masa wuya sannan ya bud'e k'ofar bayan ya d'auke bindigan sangamin ,
hanyar da ya d'auka direct hanyar flat d'in su Fareedah ya d'auka daga nesa yana hango k'ofar
su lieutenant rabi a bud'e ,cikin sand'a ya je ya d'an rakab'e yana kallon abunda yake faruwa a
ciki...


Lieutenant Aliyu na hango zaune a k'asa se Fareedah dake kwance malamala cikin Jini ,
mutanen bayan su kawai Junaid ya iya hangowa , Zuciyarsa harbawa kawai take yi especially
lokacin da ya had'a ido da Aliyu , har ya yanke shawarar shigowa Aliyu ya ce ( a fakaice) A'a!!!
Wannan ba hurumin ka bane ,!!! Yara!!! " Junaid yana jin Kalmar Yara ya tuno da su Hydar,
juyawar da zaiyi su kuma sun fito daga d'aki har zainab hannun su sark'e da na juna ,Maryam
se k'ira take Mommy I can't sleep, I am having nightmare!! " Junaid ya zaro ido waje yana
waving musu hannu yana cewa su koma amma ina !! Da suka hango shi duk se suka zubo da
gudu suka rungume shi , Hydar zai yi magana da sauri Junaid ya rufe bakin su Daidai lokacin
za'a harbe Lt Aliyu , Hydar ya had'a ido da baban shi ,Aliyu ya zaro ido waje yace " No!! Pls get
out of here !! A nan ne d'aya daga cikin su ya juyo suka yi ido hud'u da su Junaid Hydar na
k'ok'arin fisgewa ya shiga d'akin zainab kuwa ta 'kank'ame Junaid tana kuka.

Captain Junaid da Hydar suka Hada baki wajen cewa ```Lt gen Yousuf mainasara?????```

Junaid ya zari zainab a kafad'a ya Fisgo Hydar suka fara gudu , da gudu wayansu katti suka bi
bayan su , kafin su iso Junaid ya koma wajen b'uyan sa na flowers shi da yaran suna kallon duk
mutanen sun fito se dube dube suke yi , Daga nesa sukaji d'aya na cewa " Babu wad'annan
files d'in a gidan gaba d'aya! Dole Mu nemi wannan mutumin ko ma waye shi!!! , Junaid ya zaro
ido yace " Files!!so they are looking for the files??" , d'ayan yana juyowa kawai Idanuwan Hydar
ya sauk'a a kan fuskar sa ,wa zai gani😳?!!

Baki na karkarwa ya fara zufa , tabbas shine wanda ya harbi Dad first kafin sauran!! Nima de

Jeeddah nayi mamaki sosai ,koda yake ba abun mamaki bane idan har akayi la'akari da take
taken Mk!!!! Readers M.K k'anin Aliyu shi Hydar ya gani!!!!!..................


🖊🏵 MAYJIDDAH JA'O🏵🖊
[10/20, 10:09 AM] +234 701 661 4602: 💻� BURIN FANSA �💻
�💔 NA HAUWA ISAH JA'O 💔�( 2016)
4⃣1⃣🎞4⃣5⃣


Stretchers biyu na hango an fito da su daga cikin asibitin , Press kam basu da aiki se
d'aukar hotuna ,wata journalist ta samu ta kutsa cikin su General ta ce

" Yallabai shin har kana da wani abu da zaka iya fad'a game da wannan aika aika da akayi da
yayi sanadiyyar mutuwar Lieutenant Colonel Aliyu Abdoul-Rahman? Wadansu na fad'in cewa
sakaci ne daga wajen ku manya ,da kuka kare kawunan ku da iyalan ku amma wad'anda suke
k'asa da ku kuma kun yi sakaci da alamarin su ,domin labari yazo mana cewa babu mai gadi ko
tsaro guda d'aya daga cikin sojoji da yake cikin gidan a lokacin da abun ya faru , while wasu
suna tunanin mak'ark'ashiya ce daga wajen ku manya idan akayi la'akari da rashin kawo agajin
gaggawa da kukayi har se bayan da aka gama aiwatar da murder d'in "

Murmushin takaici ne ya taho ya ma rasa yanda zaiyi , hawaye masu zafi suka gangaro
daga idanuwan shi ,yace " YES!! YES!! we are Selfish but not like you are!! Ku dai burin ku
kusamu labari jikin ku na rawa ku d'aura a gidan TV ,jarida magazines !! Har wawa kuke yi ya
zama kune first wanda zai fara d'aura most trending Breaking news!! Shin kun tab'a tunanin
menene muke yi kokuma wani k'ok'ari mukeyi don ganin Mun kare ku? Ku kanku baku tsira ba!
Balle kuma mu!! Duk abunda kuka ga ya faru iko ne na Allah ,haka yaso alamarin sa! Kuma
wannan itace k'addara!! Kin yi magana akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login