Showing 3001 words to 6000 words out of 54429 words

Chapter 2 - JIDDAH Heartbeat Book Complete By Nimcyluv.txt

24 Jan 2025

4477

tare da faɗin.


"Anty duk tsuran kar kije ƙasane yasa kika ruɗe"


Ɓata fuska tayi tare da gyara mayafinta tace"bana son shiririta Aryan wato na zama abokiyar wasanka ko?,kana ganin yadda abokinka ya hulaƙan tani shine kayi shuru"


Murmushi yay mata tare da neman wajan zama ya zauna yace"aikam Allah ya suki dan hadda kwalba a tsakiyar bayanki nima ta yanke shine yasa ki kaji na bigeki a baki ban sani ba am sorry Anty"


Ƙara ɓata fuska tayi ba tare data amsashi ba tace"Aryan pls take care of him shi kaɗai nake da,banson komai yay a pecting lafiyar kasa ido a kansa a matsakinga na best frnd ɗinshi ka daina bari wannan shegiyar budurwar tasa Jessica tana zuwa wajansa gaba ɗaya bana sonta da Irfan kasan yadda za'ai su rabu"


Kai Aryan ya jinjina mata tare da faɗin"insha Allah i will try my best naga komai yay dai²"


Hand bag ɗinta ta ɗauka tayi hanyar waje tare da faɗin"yauwa ka lallai ɓashi anjima yaje library ya duba novels masu kyau"


Da "ok"kawai ya amsa bata tare da zubawa ɗan fafaffaɗan waist ɗinta wanda ya zauna a duguwar rigar jikinta,harta fice a parlour'n ba mutsa ba jin ana ƙoƙarin data sallah yay saurin tashi tare da nufar saman benen cikin sauri yake haɗa 2steps na benen yana hucesu,ƙofar ɗakin ya murɗa tare da shigewa ciki a zaune ya ganshi akan wata kyakkyasar paryer mat jikinsa sanye da farar jallabiya sai kuma farar hula irin wacce ake kira da tashi ka fiya naci da alama ya iddar da sallar amma still yana zaune da casbawa a hannunsa ya sunkuyar da kansa ƙasa yana ja,huceshi Aryan yay ba tare daya kulashi ba yana zuwa bathroom ya fara ɗaura alwala bayan ya gama ya fitu daret hanyar fita daga ɗakin yay hanyar fita daga gidan gaba ɗaya,second kaɗan suka ƙarasa dashi masallaci jam'i yabi ana idarwa akai addu'a nan limamin masallacin ya fara sanarwa kamar haka.


"ya kamata mu kula da yaranmu sosao susan irin abokanan dasu ke mu'amala dasu da kuma kula da yaranmu mata,naga alama akwai ɓata gari a wannan anguwar tamu da idona naga wasu a mota ɗasu banbancinsa da arne kaɗanne dan haka musa ido sosai bissalam"


yana gama faɗin hakan Abuyazeed tashi yay gida,Aryan ya daɗe a wajan yana tunanin maganarsa kafin ya tashi ya fita daga masallacin garasawa gidansu yay wanda yake kallon masallacin tafiya kaɗan yay ya ƙarasa gidan,a parlour ya samu Ifran wannan karonma ya sauya kayan jikinsa zuwa blue ɗin yadi the same dana ɗazun amma wannan karan haryafi karɓar jikinsa kasan cewarshi baƙi shi kuma yadi blue hakan ya bawa kwayar idon damar sajewa yadin jikinsa,yana zaune akan sofa ya lumshe idonsa sai ƙarar A.c data cika parlour,kallo ɗaya Aryan yay masa ya shige zuwa flat ɗinsa domin yin wanka yasan jiransa yake da ace ya fita shi ɗaya kwara ya zauna.


Cikin sauri² yake shiryawa bayan ya fitu daga wanka irin yadin jikin Irfan ya ɗauka ya saka a jikinsa sunyi masa kyau sosaai domin shi farine a gurguje ya fesa turare ya fice daga ɗakin yana fituwa yaga Irfan harya miƙe tsaye wajansa ya nufa tare da faɗin"legs go"kai ya jinjina baice komai ba,ficewa sukai daga gidan suka nufi compound suna zuwa yay wajan wata ƴar ƙarama motar me kyau dan kaf wajan tafisu kyau,buɗewa yay ya shiga side ɗin drever ya zauna kallonsa Aryan yay fuskarsa ɗauke da mamaki yace"kana nufin kaine zakai dreving namu kennan" ya faɗa yana zubawa Irfan ido shima kallonsa yay ba tare daya ce komai ba ya shiga yiwa motar key hakan yasa Aryan saurin faɗawa cikin motar da gudu yaja motar zuwa get nan me gadin ya wangale get ɗin gidan da gudu Irfan ya cilla hancin motar waje idonsa a lumshe amma hakan dreving yake"a'a stop it pls yaza kana dreving kana rufe ido nidai banshirya mutuwa yanzu ba sai nayi aure ato"cewar Aryan kallon kawai ya ɗauke kai bai tanka masa ba saima ƙara giyar motar yay sam bai iya dreving a hankali ba.


30min ya kawosu wani ƙaya taccen Resturest kashe motar sukai suka fitu a hankali suke tafiya har suka ƙarasa cikin wajan iya haɗuwa ya haɗuwa wajan,shiga sukai wajan da manyan mutane suke zama (VIP)waiter tace ta kawo masu wani ɗan ƙaramin littafi Aryan ne ya karɓa ya fara dubawa tick yay a wanda suke su,wajan 10second waiter ta dawo ɗauke da babban tray na abincinsu jera masu komai tayi sannan ta huce ta basu waje,abincin Aryan ya fara ci dan dama yunwa yake ji,zuba masa ido kawai Irfan yay yana kallon yadda yake cin abincinsa hankali kwance,murmushi kawai Aryan yay dan yasan idan ba abincin nan aka bawa Irfan ba ko shekara sukai a wajan bazai taɓa ci shi kaɗai ba,saida ya gama cin abincinsa tass sannan yaja kujerar wajan Irfan abincin ya jawo zuwa gabansa sannan ya ɗauki spoon ya ɗebo abincin ya miƙa masa zuwa bakinsa ya mutsa face yay sannan ya buɗe bakinsa a hankali aka zura masa spoon bakinsa sosai Irfan yake cin abincin da Aryan yake bashi sai zuba masa shagwaɓa yake wani yaci wani ya fitu dashi ruwa ya ɗauko mai sanyi ya miƙa masa kafin yasa Aryan ya ɗauke cup ɗin da sauri ya shanye ruwan kwaɓe fuska Irfan yay hannu yasa a hankali ya daki shoulder Aryan yace"stop it boddy" dariya Aryan yay yana kafa mashi cup ɗin a baki saida ya shanye ruwan tas sannan ya miƙe tsaye shima Irfan miƙewa yay tare da faɗawa jikin Aryan yana murmushi ɗan bubbuga bayansa Aryan ya shigayi wajan 3second ya cire jikinsa yay waje mota suka shiga tare da barin wajan wannan lokacin Aryan ne ke dreving kallonsa Irfan yay da alamun tambayar inda zasu ganin ya ɗauke kan motar fuskantar hakan yasa Aryan cewa"library zamu"




*jidda pov*


Zare jikinta tayi daga jikin mama ta shige ɗaki tana zuwa taga mimi na rera kuka kallonta tayi sannan ta ɗauke kai taji gaba da picking hand bag ɗinta da kuma lapton ɗinta saida ta gama komak sannan tyi facing mimi tace"what happen now?"harara mimi ta zabgawa jidda tare da faɗin"are you aking me meke faru to kinfi kowa sanin abinda yake faruwa meyasa bakya son farin cikina da kuma kwanciyar hankali na Yaya,kifi kowa sanin abinda yake faruwa meyasa ba zaki nemu mutumin da zai aureki ba ko nima na samu nayi aure kinsan idanba aure kikai ba Abu bazai taɓa bari na nayi aure ba"takai ƙarshan maganar tana ƙara sautin kukanta.


Harɗe hannayenta tayi saman brest ɗinta ta zuba mimi ido domin tabbatar da abinda take gaya mata tnx God kowa ta ganu gsky domin mimi har zuciyarta take gaya mata hakan,murmushi kawai tayi tare faɗin.


"kada ki damu mimk as soon as sameer ya dawo evertin will be fine zanyi aure kodan farin cikinki ok"tana faɗin hakan tayi waje abinda a parlour ta tadda mama da kuma abu wanda ya dawo daga masallaci murmushi tayi tace.


"mama zan tafi" kallonta mama tayi taga sai yawo fake cikin wani ƙaton hijab kafin fa ɗauke idonta tace"where"au kin manta yau nice keda library fa"hannu tasa ta dafe forehead ɗinta tace"i almost forged wlh Allah ya tsare kuma ya kiyaye ki kula sosai kinsan after 6kuna da karatu da Abu kada kiyi late"insha Allah cewar jidda.


ɗago kai Abu yay ya kalleta yana mai jindaɗin shigarta yace.


"nikam wannan aikin yana ragemun jin daɗi baga barina zama da abinda nafisu a rayuwa take care my luv a kula da irin mutane da za'a dinga mu'alama"


Murmushu tayi tace"insha Allah my luv"sunkuyawa tayi ta ɗanyi hug ɗisa tare dayi masa peak a kumatu kanta yasha fa yace"Allah yay maki Albarka my luv"Waiving tayiwa mama sannan fa fice a gidan tana zuwa waje ta gyara glass ɗinta drever ta kwalawa kira cikin sauri ya ƙarasu ya shiga mota itama ta shiga da sauri yaywa motar key ya jata da sauri suka fice daga gidan.


Kasan cewar babu wani nisa sosai hakan yasa 10min suka ƙarasu kallon drever tayi tace.


"basai ka dawo ɗauka na ba kaje kawai i take care of my self"tana faɗin hakan ta shige ciki nan ta fara gaisawa da mutane daret ɗan ƙaramin office ɗinta ta shige ta zauna wajan 5second ta fitu ta fara jera sabbin littafai cikin library ɗin tana kallon yadda mutane suke ta neman novels masu daɗi dan karantawa.


Wani sihirintaccen ƙamshi taji ya daki hancinta hakan ya haddasa mata wata kasala ci gaba tayi da jera littafan hannunta kamar daga sama taji ance"hy"a hankali ta juyo nan idonta ya sauka akan samarin wa ƴanda sukai shiga iri ɗaya like twints ɗaya fari ne sosai ɗaya kuma baƙi amma black ɗin haryafi farin kyau da D is C banbancin a baiyana yake,ɗan murmushi tayi wanda ya haddasa lumawar dimples ɗinta guda biyu gyara tsaiwa tayi tace"ur wlcm me kukeso"ta faɗa cikin harshan turanci"what the you want?"shuru gaba ɗaya sukai mata sun rasa bai zasu ce can yaɗan gyara zama tare da mutsa bakinsa cikin maganarsa mai daɗi da kuma sanyi Irfan yace.


"listen..can you recommend me a book?"


Book itama ta ƙara mai maitawa a zuciyarta kafin tace "like what?"


Aryan ne yay saurin cewa"like if someone's been released from jail after 8years"


Kai kawai ta jinjina ta tafi nemu masu littafin,Aryan ne ya kalli Irfan wata uwar harara ya zabga masa mai ɗauke da warning,kawo masu tayi sannan ta nufi wajaɓ lifter tana zuwa ta danna ta shiga ciki wajan wani ɗan saurayi taje sukai magana akan littafan da basu dashi sallama tayi masa sannan tabar wajan,ɗaya lifter ta koma ta danna buɗewa tayi ta shiga kafin fa rufe ya shigo hannunsa ɗauke da wata kwalaba bata kallesa ba tana jiran lifter ta tsaya,kwalbar ya buɗe ya fara kwankwaɗar abinda yake cikinta saurin daga kansa sama yay jin lifter ta tsaya cak nan da nan zafi ya fara damunsa tsaki yay ya ciro wayarsa ya fara neman layin Aryan amma yaƙi tafiya lokacin ya gaba shanye giyar dake cikin kwalabar jin zafi yay yawa yasa ya cire rigar jikinsa yayar a gefe kallonta yay yaga ko mutsi batai ba hakan yasa ya nufi inda take. *~Comment ɗinku shine kaɗai zai bani damar ci gaba da rubuta wannan littafin na (JIDDAH) wlh wlh wlh Sau uku kenan idan har ba'a comment to zan ajjiye rubuta wannan littafinne domin nima ina da abinyi🤗bazan ɓata lokaci nayi abu ba kuma comments ya gagara,kuma WATTPAD ina sane daku zan dai nai muku update ne wlh babu ruwana gwamma na kwanta nayi bacci abina idan kuma kun ceci kanku ta hanyar comments shikenan🥰~*


```Maman muqaddis grop naga comments ina gdy sosai,Nimcy luv hausa novel na facebook kuma ina maku gdy sosai🥰😍aci gaba da comments kona daina posting👌🏻```




Comments
Vote
Share




Sarauta ce👑








*note*


Ciwon infection yafi saurin shiga jikin mace wata tun tana karama take samunsa Amma baya bayyana har saita fara al ada shiyasa ya kamata iyaye mata su tabbatar suna kula da gaban yaransu mata kamar makarantar kwana yanada kyau kina kula da lafiyarta domin mafi yawan mata anan suke kamuwa da cutar dalili kuwa toilet dinsu yanada yawa ko wajen yin fitsari idan bazakina zuba ruwa kafin kiyiba Zaki iya kamuwa da cutar
Barin jika bayan kin gama ya kamata ki goge kafin saka pant kada kuma kiyi amfanida kayan wata kamar abinda yashafi kayan al aura
yin toilet shima kisamu wani Abu kinayi aciki yafi lafiya akan tsuguno wari tareda cututtuka suna shiga jikin mace
wanke gaba da Sabulu me kamshi shima yana kawo shigar cutar
musamman masu saka yatsa suna wankowa ya kamata kisamu Sabulu gashi ayanzu sabulai na liquid suna nan barkatai Wanda guda daya Sai kiyi wata daya
Lokacin Al ada bayan kin kammala ki gyara sosai kiwanke da ruwan dumi da magarya tana amfani sosai ga yan mata




nimcyluv
08119237616
[12/9, 5:41 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*


```MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```


CHAPTER 4
```THE LIZARD


```Wattpad@nimcyluv```


👇🏻wanda suke gruop na ɗina guda uku pls kada suyi join


https://chat.whatsapp.com/LvXakfYhIUsLs839jHMjUR




Dedicated to my luv HASSENATU AUTAR MANYA😍wannan page ɗin nakine ke ɗaya ƙaunarki a raina ba zata faɗu kina raina koda yaushe,kada ka manta alkairin mutum duk girman sharri ina sonki sosai fiye da sosai pls come back soon😭







*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*YA AL'WAJUDU👏🏻😭*





Chapter 4






a hankali ya taka ya isa inda take, kasan cewar ta sadda kanta ƙasa yasa bai gane ko wacce ba musamman idonta data mannashi a glass ɗin,ba tayi aune ba taji saukar tattausar hannunsa mai tuƙar laushi da kuma tsantsi gaba ɗaya gargasar gashi ne kwance a hannunsa hakan ya ƙarawa batarsa baƙi amma tayi kyau sosai,zare glass ɗin idonta yay yana ƙara kallonta,still bai gama ganin face ɗinta ba hakan yasa ya tallafu haɓarta,saurin sakinta yay ganin yadda idonta yay wani fari tas har shaning yake sabida haske kwayar idonta baƙa ce sosai saɓanin tashi blue,juya mata baya yay gaba ɗaya zafi ya isheshi 2second ya ƙara juyowa tare tasa hannu ya taɓa dukkan shoulders ɗinta girgizata yay a hankali ya kusantu da fuskasa wajanta numfashin bakinsa ya fesa mata lumshe ido tayi sabida yadda wani daddaɗan ƙamshin bakinsa ya daki hancinta,ƙaramin bakinsa ya mutsa dai² kunnanta yace"4 eyes"ya faɗa yana maida mata glass ɗin daya cire mata ganin idonta ya fara kawo ruwa.


Mamakin shurunta yake duk rashin maganarsa yaga alama ta fishi gashi duk miskilancinsa yau shike neman magana,koda yake da ai ba haka yake ko a school an sanda zamansa faɗa babu da uban wanda ba yayi shiku baka yi masa magana saiya tsukaneka faɗa ko ba nashi ba saiya ara🤔.




Jidda kam a zuciyarta ji take kamar ta zunduma ihu sabida zafi,ga wani abu dake mata yawo a jiki kamar snake dauriya kawai,amma duk abinda Irfan keyi mata tana jinsa kuma tana kula dashi babu abinda ya bata mamaki sai sunnan daya kirata dashi 4EYES so sweet ta faɗa cikin ranta wato idonta da kuma glass ɗinta shine ta zama 4Eyes wonderfull,zamura tayi jin abin ya shige mata cikin riga gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa lokacin harya cire dugwan wandon jikinsa ya rage daga shi sai boxer da kuma farar t.shirt,hannu yasa ya jawota zuwa gabansa yay hakan bada wata manufa ba danshi a rayuwa babu abinda ya tsana illah yaga mace cikin wani hali shiyasa yake mutuwarsa yayarsa Amrah,kallonta yay sosai ganin ta fara shassheƙar yay saurin mannata a faffaɗan ƙirjinsa cikin raɗa yakai bakinsa dai² kunnanta yace"4eyes lifter ne ko?oya shuru zansa acireta a sauya wata stop cry i don't like it"ya faɗa yana jan numfashu rabunsa da yay magana kamar haka tun dawowar daga U.S.


Ƙara zabura tayi haɗe ƙanƙame Irfan ta rushe da kuka jin abin na neman zautar da ita,hannu yasa ahankali ya shiga bubbuga bayanta,tsayar da hannunsa yay a tsakiyar bayanta jin tudu da kuma huci wani abu,ƙara jidda ta saki jin abin ya karceta cikin muryar kuka da kuma shagwaɓa tace"pls help bafiii"ta faɗa tana ƙara shigewa jikinsa,lumshe ido yay domin muryarta ba ƙaramin daɗi tayi masa,hijab ɗinta ya ɗaga a hankali tare da zura hannunsa cikin rigarta,cije lips yay tare da tsotsar lips ɗinsa na ƙara a hankali ya furta"lizard" kuka taci gaba da rerawa jin abinda ya faɗa tu yaushe ƙadanƙare ya shiga jikinta,dariya mai sauti yay tare da faɗin "yarinya saidai ki hakuri kawai ya shige cikin jikinki nima am scared banson sa"da sauri tasa hannu zata zare hijab ɗin yay saurin riƙe hannun tare da murzawa kaɗan ɓata rai yay kamaninsa suka dawo kamar bazai magana ba sai kuma yace"laifinki ubanwa yace kina yawo babu rigar mama,ni kuma ban shirya taɓa jikin kwaila ba"sadda kanta ƙasa tayi taci gaba da rera kukanta ta najin mutuwar tace tazu babu abinda take tsoro sama da ƙadanƙare da kuma ruwan sama musamman mai tsayawa yanzu zata fita hayyacinta,a haukace ya ƙara mannata a ƙirjinsa tare da faɗin"sorry nine ko?" gyaɗa kai tayi kai tsaye ya zura hannunsa cikin rigarta hakan ta yake mata sai taji kamar yana shafa tane nan da nan ta fara jin wani iri a jikinta,da sauri ya kamu ƙadangare amma ya ƙara zillewa ɗaya hannun yasa ya juyata ya zamana shine yay hug ɗinta ta baya ita kuma ta kallon gefe,ɗan tsaki yay jin yayi wajan da baya son taɓawa runtsa idonsa yay ya kaiwa ƙada ngaren cafka ya ƙara zillewa ƙara matseta yay a jikinsa ya ƙara damƙar ƙadangaren nan yay nasarar cafkoshi fitu dashi yay daga jikinta idonsa ya zubawa ƙadangaren ganin yadda yake kumbura kai tare da huci bugashi da jikin lifter yay tare da faɗin "fuck you" tsayawa yay yana maida numfashi bai ƙara kallonta ba har lifter ta buɗe cikin sauri ta fita daga ciki gaba ɗaya mutanan wajan da masu gyara suka zuba mata ido ganin ta fita da sauri ga kuma kayan Irfan a yashe a gefe.


Haɗe rai Irfan yay tamau ya koma a salin Irfan,dan haka kowa yasha jinin jikinsa hannu Aryan yasa ya kamashi tare da faɗin "kayanka"harara ya manna masa baice dashi komai saima gaba da yay abinsa,da sauri Aryan yabi bayansa yana dariya ƙasa² har suka kawo wajan motarsa buɗe motar yay ya faɗa mazaunin drever shi kuma Aryan ya zauna a ɗaya side ɗin,da gudu Irfan yaja motar yay waje a tsaye ya ganta tana jiran napep,taɓe baki yay tare da ƙarawa motar key Aryan ne yaci aikam baka isa ba saika rage mata hanya bayan ka gama lalube masu yarainya shine yanzu ba zaka taimaka mata ba,tsaki ya ƙarayi sanna ya juya kan motar zuwa inda take tsaye,wayarsa ya shiga dannawa hakan ya nuna bazaice komai ba,zuge glass ɗin Aryan yay sosai yadda jidda zata iya ganin Irfan murmushi yay

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login