Showing 81001 words to 84000 words out of 91990 words
Chapter 28 - NOOR ALBI (Hasken Rayuwata) Writing By Mamuhgee.txt
maidata gefe ya ajiye Yana maida kansa ya jinginar jikin kujeran dayake zaune tareda rufe fararen idanuwansa dasuka kasa samun komai face ganin Laylah ta iso garesa cikin koshin lafiya Dan baisan iya abinda zai iya faruwa idan Na'ima ta Isa qasar ta taba lafiyarta Dana cikin jikinta.
Ms Na'ima ma data Isa gidan Haj Zinat kasa Shan Koda ruwa tayi sai data Kira Laylah Dake fama da kanta ta ringa jeho Mata tambayoyin dasuka sakata shiga fargaba da shakka saidai duka amsoshin data bawa momyn basu gamsar da itaba Dan Haka ta kashe wayarta tana cewa"
Dama nasan ba wani amfani ne da Laylan ba kikace sai ankirata gashinan na batawa kaina lokaci da Rai abanza.
Da qyar da dabara Haj Zinat tasaka Ms Na'ima Shan tea kafin ta banka Mata maganin qwaqwalwan datake akai aikuwa tana shansa ba jimawa baccin Dole ya dauketa ta zube a gadon Haj Zinat Dake cikin lafiyayyar bedroom dinta tana baccinda ba shiri.
Bata farka ba sai yamma wanda daman Haka maganin yake wani irin mugun bacci yake sanyata harsai qwaqwalwanta ya dawo Yana Dan aiki daidai,
Hakama da mutuwar jiki zatai kusan wuni biyu sbd bazata samu qarfin wani tashin hankalin ba shiyasa batason maganin idan tanajin masifarta Amma so da yawa Zinat ke yaudararta tabata gashi yanzu Bata iya wani dogon tashin hankali sai bayan kwana biyu kuma Dan Haka ta tattara Fahad babban Dan Haj Zinat din ya dawo da ita gida.
Tana Shiga bangarenta tun a Palo siddika dake Mata sannu da zuwa tana karban handbag dinta ta fahimci maganintane ke aikinsa Dan Haka wani dadi ya mamayeta tana Jin kwanakin duka na Sa'artane Dan kuwa yanzu rayuwar Jin Dadi da kwanciyar hankali takeyi a gidan tunda masifar gaban Ms Na'iman ta isheta da Bata lokacinta
Dan Haka daki takaita ta kwanta ta fito tareda janyo Mata dakin ta wuce kitchen tana cewa"
Faduwar wani tashin wani.
Kwananta biyu Bata tako ko kofar fita Dana bangarentaba tana fama da kanta sai data cika kwanan biyu cif tadawo daidai ta nufa Sashen Anne ta gaidata Kamar Dole ta fito Takoma bangarenta tana wayoyinta da Zinat data dagawa hankali akan ita ta tafi Ta binciko musu sbd zaman Nan a baibai bazai kaisu koinaba sai gurin baqin ciki da bacin Rai sbd suna Bata lokaci cikin Yana da uwar cikin suna sake samun qarfi tunda ciki zaina cigaba da girma.
*****
Qarfe 5 na asuba jirginsu ya sauka a Murtala Muhammed International airport dake Lagos,
Sanye take da _Moja majka_ Abaya maroon Mai shaking material
Kanta nade cikin Marron veil qarami na Abayar sai black Gucci suede loafers a qafarta da qaramar _Bottega veneta_ small shoulder bag Dake rataye a kafadarta,fuskarta tayi haske sosai ta yanda ko kafin idonka ya sauka a cikinta zakasan tana daukeda juna biyu dayayi Mata kyau matuqa,
Bata qara wata qiba ba hakama Bata rameba shiyasa cikin ya fito sosai iya watanninsa...
Wani numfashi ta sauke lokacinda ta shaqi iskar Nigeria ta lumshe ido cikin gajiya da Yar yunwar Dake damunta ta fito Ana biyeda ita da luggages dinta.
Tana fitowa Wanda idonta yafara sauka akansa ne tsaye Yana waya cikin black Rugby's Riga da wando da jacket Mai girma datakai Masa har gwiwa...
Duk da Yana sanyeda face mask black da hular sanyi,
kallo daya tayi Masa tagane shine duk koina nasa kusan a rufe yake Kuma Bata taba tunanin zai iya zuwa airport da kansa tarbonta ba
Da haka wani sanyi ne ya mamaye zuciyarta har batasan idonta Yana cikowa da hawayen kewarsa dataiba da farin cikin ganinsa...
Ahankali take takowa idonta cikin nasa daya zuba matasu cikin kallo Mai wuyar fassarawa,
Akan cikinta daya turo Ana ganinsa da kyau ya sauke idanuwansa kafin ya ware Mata hannuwansa ahankali Yana cewa"
Finally.
Ahankali tashige jikinsa tareda rungunmesa da sauri hawayenta suka sauko tana cewa"
Abbahhhh.
Hannunta ya Kama A Abdoul ya wuce gaba tareda kayanta aka shigar mota kafin ya bude motar Turakin da kansa ya bude Mata motar yana riqeda hannunta ta shiga kafin shima ya Shiga A Abdoul yaja motar suka bar airport din.
Hannunta na cikin nasa a sarke yake kallon cikinta Yana kallon fuskarta Dake glowing tana daukan idonsa da hankalinsa..
Wani malalacin murmushi ya saki Mara sauti ko kadan alokacinda idonsa yagama shawagi Kan cikinta Kuma maganar Abbanta ya fada Masa alokaci daya.
Dagowa tayi ta kallesa ganin murmushin daya sake,
a hankali ta bude Baki zatai magana ya Dan rufe Ido Yana girgiza Mata Kai alamar Bata buqatan magana.
Lumshe fararen idanuwanta tayi tareda Dora hannunta daya Kan hannuwansu dake sarqe cikin kulawa da son abun Dake ranta ta bude Baki ba sauti tace"
I love you Abbahh.
Wannan karon murmushinsa sai daya bada sauti kadan sbd shigarsa da kalmar Tayi da dagashi sai itane bazata hadiye yawun datake bakinta lokacinda tafada Masa wannan kalmar saiya shanyesu tas Dan kuwa sauran zaqin kalmar na cikinsu...Dan Haka sai kawai ya sake damqe hannunta cikin nasa cikin kulawa Yana Dan dauke Kai daga kallonta ya maida Kan wayarsa da aka sake Kira.
Lafiyayyan gidansa Dake Lagos din suka Isa Madam sarat Dake gidan tareda sabuwar Mai aiki daya da aka kawo Ruky sungama gyare koina a gidan sai qamshi da Sanyi ke tashi koina
Ga aikin breakfast dasuke Yi cikin qwarewa da mutsuwa...
Hannunta cikin nasa Suka shigo palon bayan A Abdoul ya miqawa Madam sarat akwatinan Laylan ya juya ya nufi sashensa dake gidan dan komawa baccin Dake cinsa.
Madam sarat kallo daya tayiwa hannuwansu dake sarqe ta dauke Kai tana neman Yar rudewa dai kafin ta Kama nutsuwarta sukai ciki da kayan itada ruky tana kyafta idonta Dan tabbatarda cikin Dake gaban Laylan da alama da Turakin ne tunda ga hannuwansu a sarqe...
To kodai Ms Na'ima ta rasu ne?
Da wannan rudadden tunanin Suka kai kayanta duka makeken bedroom dinsa daya Dake palonsa na sama Suka sauko.
##MAMUH.
*_Mamuhgee 46_*
Lafiyayyan wadataccen Master Bedroom dinsa suka Isa sai alokacin ya sake hannunta tareda waiwayowa suka fuskanci juna ya kalli cikinta da yayi Mata kyau,
Ya dago da mayun idanuwansa ya kalli fuskarta da ita shi take kallo jiki amace da gajiya..
Murmushi tasaki tana juyawa ta nufi sofa ta zauna tana warware nadin gyalen kanta ta ajiye gefe,
Gashinta dayake a gyale tsaf Yana qamshin hair oils masu tsadar gaske.
Gefenta ya zauna yana riqo hannunta ya shinshina kanta Yana Dan lumshe ido sbd ya tabbatar idan tana kusa da inda yake koinane qamshin da komai nata keyi yasa baya iya Dauke hancinsa da idonsa akanta.
Da kansa ya tayata cire kayan jikinta sbd gajiyan datakeji dakuma yanda take sake sake jiki cikin shagwaban ganinsa,
Duk wani motsinta idonsa daya kalli fuskarta saiya kalla cikinsa Dake jikinta....jin yake kaman zaiyi boyonta har saita haihu lafiya kafin ya bayyanawa duniya ita da 'dansa ko 'yarsa sbd zai Basu kariya da kulawa fiyeda komai daya mallaka a duniyan.
Cikin Towels dinsa masu Dan girma Dake jere a nade cikin qaramar open closet Mai zaman kanta cikin toilet din ta daura jikinta kafin ta nufi Brushes din zina45 Sonic toothbrush dasuke jere sababbin ta dauka daya tayi brush a natse kafin tanufi qaton jacuzzi Dake toilet din tashige tareda rufewa ta sakarwa kanta ruwan zafi tareda lumshe ido sbd Jin dadin saukan ruwan zafin jikinta.
Wanka tayi tareda alwala tafito daureda towel tana qamshin Hermes Eau D'orange verte body shower gel...
Baya dakin Dan Haka kamai nasane na dakin tayi amfani dashi,su sprays dinsa da body oils dinsa ta saka farar long sleeve dinsa ta Dora abayarta Dake aje akai tafara sallolin dake kanta ko gani batayi sosai sbd tsabar gajiya da baccin dayake cinta Dan Haka tana gamawa ko jiran dawowarsa dakin bataiba ta Haye gadonsa tareda shigewa farin bargonsa Mai Taushin gaske take bacci ya daukeba ba Bata lokaci.
Bacci sosai tayi mai nauyi bata farka ba sai bayan karfe daya da kusan arbain,
Dan Haka tana farkawa toilet takuma komawa tayi wani brush da alawala tafito tayi sallar azahar yunwa na cinta,
Tana idarwa cire Abayar jikinta tayi tareda fitowa palonsa Dake saman tana nemansa Dan yunwa takeji sosai gashi bazata iya saukowaba tunda batasan waye da waye a gidanba...
Dayan bedroom din Dake palon inda aka Kai kayanta nufa ta shiga
Dakin babbane komai na cikinsa golden ne sabanin na Abban dayake komai na cikinsa fari ne,
Handbag dinta Dake rataye jikin wata kyakkyawar golden hanger ta nufa ta Ciro jakar tana budewa ta dauko wayarta dake ciki da niyar kiransa taga batada layin Nigeria Dan Haka ta maida wayar ciki tareda jefar da jakar Kan gadon dakin tana fitowa.
Tana fitowa Yana hawowa saman sanye da Armani's navy blue idonsa akanta da rigarsa datake sanye da ita fararen cinyoyinta a bayyane
Ya maida kallonsa yayi cikin idonta dasukai laushi da yunwa ya qaraso Yana Kama hannunta cikin nutsuwa da kulawa da qaramin sauti yace"
Yunwa right?
Gyada Kai tayi tana cewa"
Sosai Sosai nakejinta...
Slippers Suka koma daki ta zuro na Burberry masu taushi da hula Mara nauyi Suka sauko qasan Kai tsaye Suka nufa dining.
Zama yayi tareda zaunar da ita Kan qafafunsa yana kallon fruits data zubawa idon suke take buqatan fara ci ya janyo Mata suna saka hannu akai tare..
Yana Bata tana bawa kanta sbd yunwar datake ji Haka akecin abincin sbd shi baya buqatan cin komai sbd ba yunwa taredashi.
Madam sarat data fito kitchen daukeda madarar dayasa A Abdoul ya Nemo a wani babban super store aka bawa Madam sarat umarnin dumama Mata kullum itace ta dumamo Jin motsinsu ta kawo dining.
Tana sako Kai idonta ya sauka kan Mace 'dare dare akan qafafun Sir Turakin take ta Dan gwalo Ido ta sake kalla kafin ta dauke ido Yana jinjina al'amarin lallai babbane,
Wlh kwashe arzikin data Tara a gidan zatai takai gidanta Dan ranarda Ms Na'ima ta sauka garin ta tadda wannan babbar harka Kona gidan zatai su asare
Gwarasu basuda asara tunda da arzikinsu suke, ita wahalartane na shekaru masu yawa zata Rasa.
Dayake ita Kam ba baturiya bace Kamar Cindy Yi takeyi tana satar kallonsu musamman 'dan cikin dayake qara tabbatarda su din couples ne.
Murna ta taya Sir Turakin Mai girma sosai ta wani bangaren,
Wani bangaren Kuma tunanin meyake faruwa take.
Ajewa tayi ta juya ta fice tareda komawa kitchen tana sakin murmushi ita kadai Dan kuwa yanda Laylan ke narke Masa ajiki yasata Jin Kai love na musamman ne.
Lokaci Suka Bata sosai gurin Cin abincin sbd zabin da Tai tayi tunda abincine data Dade rabonta data cisu.
Baro dining din sukai Suka koma sama ta zauna jikinsa a Palo tana cewa"
Abbah idan nakoma gurin Anne wlh bansan me zance Mata ba...
Kallon cikinta da hannunsa daya yake Kai tayi tana marairaice fuska tace"
Idan taga wannan wlh banzan iya hada Ido da itaba..
Wani malalacin murmushi ya sake Yana janye hannunsa Kan cikin ya shafa kanta a hankali Yana cewa"
Idan kinje kiyi kaman bakisan Ana ganin meye a jikin naki ba...
Musamman idan kin hadu da Abbanki.
Abbanta daya ambata yasata Shiga wani yanayin Mai girma,
Ta kwantar da kanta jikinta tana cewa"
Abbana Zan Shiga halin mafi girman kunya idan yaganni shi da Anne,
Saidai mum idan ta ganni Abba Zan Shiga.....
Kissing din bakinta yayi ahankali tareda hanata qarasa zancenta.
Kallonsa tayi Jin taushin lips dinsa Bai bar nata lips din ba,
Ta saki murmushi ahankali tana cewa"
I love you.
Wani matsiyacin kallo ya zuba Mata idanuwansa Yana Mata sbd batasan tasirin kalman datakeyi akansaba,
Kunna takeyi tako Ina musamman sautin datake amfani dashi gurin fadar.
Ganin irin kallon dayake Mata yasata Kai hannuwanta ta sarkafo wuyansa tareda Kai fuskarta daf da tasa ta hura Masa iskar bakinta a hankali cikin idon kafin ta Dora bakinta Kan NASA tana zira harshenta cikin bakinsa ahankali ta laso harshensa tareda lumshe ido tana qarasa zira harshenta cikin bakin nasa.....
Cirata yayi ya Dora Kan qafafunsa da kyau yanda zataji daidai sbd cikin ya kama fuskarta da kyau tareda bude bakinsa ya cafke nata bakin Yana Bata wani irin deep kiss daya tada tsikar jikinta duka ta saki wani wahalallen numfashi tana sake sarkafo wuyansa da kyau.
Hannuwanta ta gangaro dasu ta bude maballan rigarsa gabaki daya tana zura hannu cikin rigar tana yawo da hannunta Kan lafiyayyar fatarsa...
Take taqarasa Kunnasa yasa hannu ya balle gabaki daya botiran gaban rigar jikinta ya zare rigar ya jefar gefe ta fada Kan wani tsadadden flower vase Dake Kan wani glass table set ta Fadi kasa tasaki wata irin wara tareda fashewa.
Madam sarat Dake palon qasa tana bawa Ruky umarnin wani aikin tajiyo qarar fashewar Abu kamar Kuma daga saman ne.
Kallon hanyar Hawa saman tayi cikin Dan mamaki da wasi wasi tace"
Lafiya kuwa?
Dan takawa tayi ta Isa bakin stairs din tana jiran Jin sake jiyowa Idan lafiya sai takuma Jin fashewar Abu da sauri ta waiwayyta kalli Ruky da itama hanyar saman take kalla.
Sanin Sir Turakin na Nan yasa bazata hau ta duboba,
Da bayanan ne da zata iya Shiga palon ta dubo ko wani abun ne ya fashe Dan Haka suka bar gurin tana cewa Ruky"
Jeki kiyi aikin gabanki.
Duk yanda sukai tunanin sunyi kewan juna abun ya wuce Nan Dan kuwa wani irin love suke zubawa kalman "I love you" na tashi cikin sautikan da basama fita sai iya su kadai sukejin abarsu.
Duk da cikin dake jikinta sakewa tayi sukai abunda sukeso musamman dataga Abban yagama mutuwa a duniyarta Dan Haka ta sake Masa suka Gama hargitsa palon Kuma Suka koma daki suka qarasa sauran aikin.
Sai dare suka sauko cin abinci Yana riqeda hannunta Suka sauko stairs din tana sanye cikin guntuwar free doguwar Riga red Mai kyau sai slippers dinsa da sukai Mata yawa..
Shima sanye yake da Balenciaga shirt da wando sai slippers din.
Wannan karon taci abincin fiyeda fruits Tasha Madara shima yaci macaroni salad da Potato kababs.
Sama Suka koma madam sarat Bata Kuma ganinsuba ko Jin motsinsu sai washe gari,mamakin duniya yagama kasheta Amma ba damar nunawa tunda ba huruminta bane saidai ko daga kallo daya tasan Sir Turakin su a hannun wannan Yar qanqanuwar yarinyar yake.
Tunda tada iso qasar Bai Kuma fitaba sai dayayi kwana biyu cif a gidan sallah kawai ke fiddasa tukuna...
Wani mahimmin aiki ya taso Masa a Abujan Dan Haka badan yayi Shirin tafiyarsu a kusaba Dole Suka shirya A Abdoul ya siya musu tickets suka nufo Abujan.
Tunda Suka Shiga jirgi zuciyarta ke harbawa,
Takasa samun nutsuwar zuciya data ruhi,
Hannuwanta har Yar rawa sukeyi duk lokacinda ya riqo hannunta,
Sunan mum kawai idan ya fado ranta zuciyarta harbawa takeyi Dan kunyar Anne ma daga bayane zatazo idan sukai Karo da mum Na'ima idan ta Isa...
Duk dokinta da farin cikin zuwa Nigeria data Jima tana fata gushewa yayi sbd fargaba da rashin kwanciyar hankalin datake ciki.
Lura da yanda hankalinta ya tashi yasa yayi kokarin kwantar Mata da hankali Amma sam Bata ganewa Haka ya lallabata tayi bacci jikinsa saidai ba baccin tayiba kwanto kawai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa.
Suna sauka airport din Abuja motaci biyu sukazo daukansu sbd da ruky sukazo da zata ringa Mata komai.
Dan Haka suka shiga motocin Suka nufi gidan.
##MAMUH#
_Mamuhgee 47_*
Parking motocinsu sukai a harabar gidan,
A Abdoul ne yafara fitowa motar dayake ciki zaune a gaba sai Ruky a sit din baya,
Motar da Turakin suke ciki ya nufa da niyar bude Masa sai gashi ya bude da kansa tareda zuro qafafunsa Dake sanye da black Camilo Italian leather loafers ya fito motar.
Hannu ya miqa Mata ahankali ta Kama zuciyarta na bugawa ta fito motar sanyeda Ash turkish abaya da light Ash gyale akanta nade.
Handbag dinta ma qarama ce sosai sbd yanzu batason masu girma suna damunta,
Ahankali ta zare hannunta daga nasa Bayan fitowarta motar sbd tasan yanzu Kuma ita dashi sai kallo daga nesa tunda suna gida daya da mum Na'ima gakuma Anne.
Kai tsaye Sashen Annen Suka nufa Ruky da A Abdoul tuni sukai gaba da Suitcases dinta zuwa bangaren Annen,
Ahankali jiki a matuqar sanyaye take tafiya gashi kamarma yanzu tafi ganin girman cikin nata,
Dan Haka duk tabi ta sake shiga halin firgici da damuwa...
Suna gap da Isa su shige babbar kofar dazata sadasu da babban palon bangaren Annen motar Ms Na'ima ta sako Kai harabar gidan ita ke tuqawa da kanta Haj Zinat na gefenta zaune
Kowaccensu cikin Shiga ta alfarmar manyan Mata Kuma matan masu abin duniya...
Motacin Turakin da aka daukosa daga airport dake sarari a pake ta kalla kalla batareda idonta yakai Kan gabansuba hanyar Sashen Annen
Tana kokarin parking tace"
TURAKI ya dawo kenan¿Amma dazu da mukai waya baicemun yau zai dawo din ba,
Zinat shiyasa nake fada Miki Turaki ya......
Haj Zinat da tun shigowarsu idonta ya sauka kansu Laylan dake kokarin Isa kofar bangaren Anne
Batareda ta dauke idontaba akansu cikin zallan mamaki da shakkar abin datake gani a idonta tace"
Na'ima Kamar fa mace Mai ciki ce tareda turakin gasu can zasu shige gurin Anne......
Baammmmm.....wata irin qara Mai qarfi ta tashi na buga motar gabansu da Na'ima tayi ba shiri sbd zancen Zinat...
Ware idonta tayi a bangaren daidai sun sunshige lokaci daya atare....
Bata kashe motarba barewa tsayawar ta bude kofa tana kokarin fita Zinat cikin tashin hankali biyu da biyu ta riqota tana cewa"
Tsayar da motar ki kashe tukuna kafin ki kashemu da sauran kwananmu a gaba..
Tsayar da motar tayi Amma Bata tsaya kashewaba ta fito
Tana cewa"
Zinat wlh itace ya kawo gidan,
Anne ta sane kenan,
Aikuwa yau za'ayi budaddiyar wasika kowa ya dauki sakamonsa....
Gaba tayi har tana tuntube saura kiris ta kife,
Haj Zinat da sauri ta fito tabiyo bayanta batareda itama ta tsaya kashe motarba sbd Ganin ko ganin gabanta Na'iman batayi,
Tasan Sarai Yau mahaukaciyar hauka zata buga idan tayi Ido biyu da Matar Nan,
Yau Babu maganar aro hauka koina original tata din zata buga abarta,
Itakuma bazata yarda ba Na'iman tayi abinda zaisa agane lalurarta gwara ta bita ta danneta duk da itama dazata samu damar idonta idon Matar data rigasu daukan cikin Turaki da hannunta zata halakar da cikin kafin ita Daga baya sayi lokacinta.
Anne ce zaune a Palo tana Amsa wayar Sa'adah cikin kwanciyar hankali nutsuwa,
Palon sai qamshin Turaren wutar YERWA INCENSE yake tashi tareda sanyin Ac da hayaqin Oud Dake fita ahankali daga qatuwar humidifier Dake can gurin hanyar kofar shigowa palon.
Shigowar A Abdoul da ruky Dake janye da set din akwatinan Louis Vuitton guda hudu yasata kallonsu da mamaki akan fuskarta,
Ruky data gefe tana gaidata cikin tsananin girmamawa ta kalla kafin ta kalli A Abdoul din shima tace"
Abdoul-Hameed baqi mukayi ne da Kaya Hakan?
Fara gaidata yayi cikin girmamawa da sakewar Dake tsakaninta dashi yace"
Ms Laylah ce ta dawo..
Da sabon mamaki Mai girma ta Kuma kallonsa murmushi na