Showing 69001 words to 72000 words out of 91990 words

Chapter 24 - NOOR ALBI (Hasken Rayuwata) Writing By Mamuhgee.txt

08 Jan 2025

4233

Ido Suka kalla juna kafin ta dauke Kai ahankali tareda qarasowa tana kallon mum Dake zaune kusa dashi sosai Sosai hakama tana riqeda hannunsa tana zuba Masa soyayya da kudin datakeson yasaka hannu A Abdoul ya Bata.


Ahankali ta Dan sauke kanta daga kallonsu cikin murya Mai taushi da nutsuwa tace"


Abba Ina wuni?
Mum barka da rana.


Yanda ya amsa Kai tsaye batareda yabar duba wayan dayakeba yasake sakata Jin wani iri ta wucewarta Dan dama ba wani tsayawa tayi ba.


Mum dakeson kudi gurin Turakin ta kalli Laylan cikin kulawan kissa tace"


Baby yau kifito kici abinci damu anjima kadan sbd munyi kewan cin abinci as happy family dukanmu.


Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa da tanajinsu akanta suke
Sai Bata waiwayoba ta gyada Kai kawai Dan batada dalilin cewa aa.


Tana shiga daki wanka tafara Yi tayi sallar la'asar da akai ta Kira Cindy a waya tace takawo Mata fruits masu sanyi.


Tana Gama cin fruits dinta waya dasu Anne tayita Yi suna debe Mata kewansu data qaru tasa Jin qasar ta isheta.
A daki tayi wuninta sai dare Bayan tagama sallar isha tayi wanka kamar bazata fitoba sbd zamanta dakin yafi Mata nutsuwa yanzu Amma sbd batada dalilin qin fitar yasata zuro slippers ta fito ta nufi dining room din.


Tun a kofar shiga ciki ta tabbatarda Yana cikin sbd hancinta daya Bata tabbacin,


Numfashi ta sauke ahankali tareda Dan rufe ido ta bude tana hadawa da Ajiyar zuciya zuciyarta na neman narkewa Amma ta daure ta qaraso ciki.


Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa Dake kokarin bada kamewarsa..


Doguwar fitted pencil gown ce a jikinta red Mai zib a gaba daga sama har Wasa,
Yanda rigar ta lafe a jikinta ta kwanta ne ya fidda asalin shape Dinta Sosai
Abin dabata lura dashiba cikinta ya Dan kumbura kadan ajikin rigar yafita saidai ba a ganewa ko kadan...
Ga wani irin Hasken gaske data qara har wani glowing takeyi.


Jin idonsa akanta yasa zuciyarta takasa hakuri ta dago ta kallesa itama
Idanuwansu suka shiga cikin na juna take taji kamar zata sakar Masa kukan tsananin kewarsa datai agurin saidai ba wannan damar Dan Haka ta dauke idonta tareda zaunawa gefen mum da taketa fama zuba Masa abinci tana Masa wasu salo salon daukan hankali duk Dan samun biyan buqatarta dataketa bi ayau din na kudin.


Murmushin yaqe tasake tana kallon mum da har lokacin Bata zaunaba tana serving dinsa da kasalalliyar murya tace"


Sannu da aiki mum.


Batareda ta waiwayo ba muryarta duk a washe tace"


Thank you baby.


Har Lokacin Bai dauke idonsa daga kantaba duk sai takasa komai ta aje cup din madarar data dauka batareda Tasha ba ta dago ta kallesa yanayi na Rasa abin Yi dakuma rashin mafita ta zuba Masa idonta Dake neman cikowa da hawaye.


Wani irin rufe ido yayi ya bude ahankali cikin Jin cin abincin ya fita kansa gabaki daya ganin hawayen idon nata,


Miqewa tsaye yayi ya juya yabar dining room din
Mum tabisa da kallo da gudu ta aje serving spoon din hannunta tabisa tana Kiran sunansa cikin firgicin karta Rasa damarta na abinda takeso.


Suna fita itama ta miqe batareda taci komaiba tabar dining room din tana share hawayenta da bayan hannunta.


Har bedroom dinsa Ms Na'ima tabisa jiki na rawa hankali tashe Dan kuwa zuwa gobe da safe idan Bata turawa Zinat kudinba akwai matsala,
Shagunan kasuwancinsu da boutiques dinsu komai na neman lalacewa kudi suke nema sosai Ido rufe Dan kila sai ta danganta da zuwa Nigeria din da kanta.


Baya buqatan hayaniya ko wace irice a yanzun Dan Haka tana shigowa tun kafin tafara Masa hayaniyar ya janyo takardarda tun safe takawo Masa take bibiyarsa ya zari pen ya saka Mata hannu akai ya miqa Mata.


Maganar dataso fada na nuna damuwar barowar da yayi baici abincinba Yana miqa Mata takardar ta shanye maganar da cewa"


Thank you my love.." ta juya da tsananin farin ciki ta tafiyarta tareda mantawa da maganar rashin cin abincinsa Dan dama kusan Dan hakan ne tazo tayi kisisinar.


Tsabar tsananin buqatan kudin da yanda take matse dasu yasa tana zuwa daki takira A Abdoul ta sanar Masa zai Bata kudi masu yawa Turaki ya saka Mata hannu,
Tanason rabi cash rabin a account Dan Haka yazo yanzu ya kawo Mata cash din.


Hakuri yabata tareda sanar da ita Yana office din turaki haryanzu wasu ayyukan masu mahimmanci yake bazai samu fitowaba ko gobe idan Bai gamasuba bazai iya zuwa koinaba gskia.


Tsoki ta sake a fili tace"


Ganinan zuwa yanzu office din na amsa tunda dama a office dinsane sbd Ina buqatan su kwana hannuna gobe tun 6 akwai inda zanbi flight din Athens.


Ok" kawai yace Mata kafin ya aje wayar.


dayake Bata Saba tambaya fitaba ko sanar Masa saidai tafiya Mai nisa Haka Dan Haka Kai tsaye ta sauya Kaya ta nufi dakin Laylah ta karbi key din motarta sbd ita Bata Jan mota da kanta Dan Haka duka motocin gidan ba wadda ba'a fita cikinta da ita Kuma sunyi Mata girma data dauka yanzu ta fita tunda itace zata tuqa shiyasa ta karba ta Laylan datake ta Yan Mata Mara girma sosai sai shegiyar tsada.


Bayan fitar mum din sbd karta dawo kawo Mata key din motar batanan yasata barin kofar dakinta bude batareda ta Sanya key ba dama Bata wani saka key a dakin sai jifa jifa sbd Cindy dake shigowa tunda safe gyaran dakin idan tana bacci kokuma wani aikin.


Tashi tayi daga kwantawar datai da rigar jikinta Dan bazata iya bacci da itaba ta nufi closet dinta ta zuge zip din rigar daga sama har qasa tana kokarin janyo Ciro pyjamas dinta ta Sanya aka bude dakin tareda shigowa Kai tsaye tanajin anrufe ta dakata daga abinda takeyi batareda ta juyoba Dan kuwa atmosphere din dakin daya sauya da sanyayyan qamshin Bois elite ya tabbatar Mata da ko waye
Dan haka sai jikinta yayi Sanyi ta kasa juyowa sai Ajiyar zuciya data sake a boye.


Qarasowa yayi Ahankali bayanta Yana tsayuwa akai knocking kofar dakin.


Ta juyo tareda kallonsa kafin ta juya ta kalli kofar
Kafin tayi wani motsi ya bude Baki Kai tsaye yace"


come in.


Bude kofar Cindy tayi tashigo daukeda qaton ceramic tray jere da noodles Mai zafi daya saka ta dafo Mata da Madara Mai sanyi sai green tea dinsa.


Aje komai taye ta juya ta fice da tray din tareda Jan kofar dakin Takoma kitchen ta dasa aikin zaman gadin dawowar Ms Na'ima duk da tasan idan tayi fitar dare irin Haka zata dauki time Bata dawoba.


Bayan fitar Cindy kallon abincin tayi zuciyarta na narkewa ta maida kallonta kansa da Ido ya nuna Mata abincin Yana kamo hannunta ya sakata jikinsa ya rungume tareda sauke boyayyan Ajiyar zuciya,


Duk kamewarsa da basarwarsa tareda riqe kansa dayayita Yi kwanakin akan rashinta sai dayayi azabtuwan zuciya Mai tsanani da har ya kame kansa a sama ya daina fita aiki sosai.


Itama tsananin kewarsa yasata sakin hawayen shagwaba tana lafewa jikinsa har sai dasuka Jima ahakan kafin ya saketa ya Kama hannunta Suka Isa qasa Suka zauna Kan center carpet Dake dakin.


Jikinsa ta zauna yaringa Bata noodles din ahankali tanaci har sai data koshi ya kalleta Yana goge Mata baki da tissue ahankali yace"


Are you sure ya Isa Haka?


Yes Abbah"" tafada tana daukan tea dinsa shima ta miqa Masa ya karba Yana Sha ahankali Yana kallon yanda take kallonsa harya shanye.


Miqewa sukai yakaita toilet tayo brush suka fito ya zauna bakin gado tareda zaunar da ita Kan qafafunsa suna fuskantar juna yace"


Fushin buya a daki da rashin fitowa cin abinci yaqare daga yau right?


Kallonsa tayi tana Hana kanta sakar Masa murmushi tace"


Ni ba buya nakeba.
Kuma ba fushi nakeba
Nigeria nakeson zuwa hutu gurinsu Anne.


Wani shegen murmushi yasake Yana kallon bakinta Dake maganar zuwa zip din rigarta Dake bude ya kalla black lace bra dinta dake jikinta kafin ya gangara da idonsa zuwa cikinta daya sani a matuqar shafe yaga ya Dan kumburo kadan yasan abincin data Gama cine yanzu
Ya kwantar da kansa kirjinta Yana cewa"


Ba yanzu Zaki ba tunda bakyajin magana kema.


Hakan daya fada yasata janye kansa jikinta tana cewa"


Kaine fa kayi fushin ko massage da kake ka dainamun
Harda rashin lafiya nayi Amma baka tambaya kaji ba..


Yanda take maganar da wata irin shagwaban daukan hankali yasa ya kamo kanta ba Bata lokaci ya zira harshensa cikin bakinta tareda matseta jikinsa sosai Suka manne.


Daga zaunen dasuke ya zare rigarta da dama a Hanya take ya jefar tareda balle bra dinta itama yayi wurgi Yana cusa kansa cikin kirjinta hannuwansa na yawo jikinta.


Bai bar dakinba sai bayan sallar asuba lokacin tuni tayi bacci sbd jigatuwan datai.


##MAMUH#
*_Mamuhgee 40_*
Da safiyar ranar dukkanin jamaar gidan da kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya kowannensu ya tashi na kwana tareda abinda zuciya da ruhi ke so fiyeda komai,


Mum Na'ima farin ciki mai tsanani take cikinsa safiyar sbd jiyan kwanan kudi tayi shiyasa Bata je kwana dakin Turakin ba data dawo da kudin dakinta tashigewarta tana lissafin tafiyar da zatai danma takasa samun flight ranar Dan Haka sai bayan kwana daya zata tafi.


Laylah kuwa shiryawarta da Abban shine asalin nutsuwar zuciya data ruhi data samu Dan kuwa zuwa yanzu da gudan jininsa ke zaune cikin cikinta yasa ta tabbatarda irin zafin sonsa daya Gama shiga jininta Bata Ankara Haka ba,


Sir ABUTURAB MUHAMMAD TURAKI kuwa baka gane yanayinsa saidai kula nutsuwar dayake tareda ita a safiyar tafi suka tsawon kwanakin Dan ko yanayin kamewarsa ta qara bayyanarda nutsuwa da kwanciyar hankalin dayake ciki.


A gurin breakfast itace tayi qarshen shigowa sanyeda doguwar pencil gown yauma data lafe jikinta wadda take har qasa Amma kuma batakai qasan sosaiba sai slippers a qafarta ta dauro qaramin gyale akai dabai Gama rufe gashintaba sbd qarantarsa,


Fuskarta fresh sai qyalli take duk da Bata shafa komaiba natural dinta ta fito kaman baby.


Qarasowa tayi ta zauna fuskarta a sake tace"


Good morning mum.


Maida kallonta tayi kansa ta sakar masa wani kallo shima Sexy rigarta daga lafe Kan fatar jikinta ta kalla tareda dauke Kai wani shegen murmushi na fita gefen bakinsa sbd Sarai tasan kunnasa takeyi.


Da wata siririyar murya tace"


Good morning Abbah.


Da wani shegen kallo ya amsa gaisuwar tata Yana daukan avocado toast din da mum Na'ima tagama zuba Masa da tea sai fries da scotch eggs yakai bakinsa ahankali Yana taunawa.


Madara tafara Sha as always kafin ta fara cin potatoe fries da ketchup batareda ta dagoba sbd Jin kallonsa na binta
Tasan tana dagowa suka hada Ido za'a iya samun matsala gwara shi
Itakam tana tsoron tashin hankali da masifar mum musamman sbd cikin jikinta datakeson abunta,
Dan Haka taqi dagowa taci gaba da cin abinta tanayi tana kallon mum daketa Masa kisisinar tafiyan da zatai washe gari.


Sama sama taci abincin tagama ta miqe zata bar gurin sbd yau Abban ko ajikinsa kallon dayake binta dashi yayi yawanda mum zata iya gano wani Abu dabam Dan Haka tana kokarin miqewane wayar mum Dake gefenta tayi ringing da sauri ta dauka Dan Kiran take jira tun safe Dan Haka daukan wayar tareda miqewa tsaye ta nufi console mirror Dake gefen dining din ta tsaya tana amsa wayar sbd da agent dintane na dubai take wayar.


Barin gurin Laylah tayi ya riqo hannunta tareda dawowa da ita baya Yana kallon shape dinta cikin rigar jikinta yakai hannunta bakinsa yayi kissing....
da sauri ta janye hannun tana satar kallon mum dake kokarin juyowa ta Isa kofa ta fice da sauri dayake kofar yake kallo tana fita ta waiwayo ta jeho Masa kisses tana murmushi....


Shima wani qayataccen murmushin ya sake ta juya da gudu ta bar gurin ganin mum na Shirin kallon kofar.


Dakinta Takoma ta miqe a gado tayi baccin Rana sai kusan maraice ta tashi tayi sallah kafin ta fito a main palon gidan ta zauna tana kallo taci abinci tasa Cindy tayata zama suna fira sbd batajin dadin kallo ita daya gashi mum Bata Nan da siddika ma ta fita da alama siyayya zata Kuma zata Dade tunda shiyasa ta fita da siddikan Dan Haka bakowa daga ita sai Cindy.


Sallar magriba tagamo ta dawo palon ta zauna suka cigaba da firarsu suna kallo tana Kuma chatting Sama sama tareda uban fruits din Dake gabanta tanaci sbd wani masifar cin fruits take fama da ita yanzu.


Qatuwar kofar palon akai taba
Cindy dake zaune ta tashi da sauri ta nufi kofar ta bude.


A Abdoul ne Yana hango Laylan zaune Palo ya miqawa Cindy qatuwar basket din fresh fruits din dayake daukeda ita yace ta shigarwa da Ms Laylah basket din ya juya yabar gurin.


Kitchen ta nufa da basket din sai gashi yashigo palon Yana amsa waya a natse sanyeda Giorgio Armani's suit black Mai duhu sosai sai haskensa ya fito sosai har takega kaman wani kyau aka qarowa Abban nata ta qarasa tura jajayen cherries Dake hannunta cikin bakinta tana kokarin miqewa tai Masa oyoyo ya rigata isowa inda taken ahankali ya zauna tareda rungumarta yace"


Bayan kinci abincin dare kike wannan ciye ciyen?


Grapes ta dauka takai bakinsa ta saka Masa kafin ta janyo fuskarsa ta qarasa tura Masa grapes din ciki da harshenta kafin ta dago tana kallon idonsa zuwa bakinsa Dake tauna grapes din cikin yanayinsa na Jan aji dayake cikin jininsa tana murmushi tace"


Sannu da dawowa abbahhhh.


Kama hannunta daya dauko Cherry yayi yakai bakinsa ya karbe Yana cewa"


Sweet cherry.


Dariya tasake Mara sauti tareda tashi tazauna jikinsa da kyau tana zare Masa rigarsa ta sama ta aje gefe tafara kallonsa tana balle maballan rigarsa tana cewa"


Harshenka zaiyi ja fa idan kanashan cherries dinnan shiyasa nabaka grapes.


Wani cherry din ya dauka jajir dashi ya Kai bakinsa ya saka tana dariya ta kai bakinta taqarasa tura Masa shi ciki da harshenta ya hada da Cherries din da harshenta ya riqe Yana tsotsa..


Ahaka suka cinye na bakinsa
Takuma dauko wani ta saka bakinta tana kallonsa da murmushi Kan fuskarta...


Murmushin yasake shima Yana Kai bakinsa yace"


Kinsan sakamakon wannan din ba???


Kafin tabasa amsa yakai bakinsa akai ya zura matashi tareda harshensa ta kame tana hadawa da Cherries din....


Kaca kaca sukaiwa farar rigarsa tas da kalar Jan cherries din har tata rigar ma Saida Suka Gama lalacewa a palon kafin suka kwasa sukai sama dakinsa acan suka qarasa babban aikin tayi wanka ta dauro towel dinsa suka fito ya rakata har dakinta ta shige ta kwanta kafin yakoma.


Bacci tayi sosai washe gari ko data tashi ko nutsuwar breakfast bataiba mum ta takurata akan takaita airport Dan Haka Tai Masa text ta sanar Masa Allah ya Taimaketa Bai hanaba sbd idan ya Hana batasan Mai zata cewa mum dinba dan Haka daga airport satar hanya tayi taje gidansu sofia ta daukota suka dawo gidan tare.


Da daddare Sofia gidan ta kwana Dan Haka da wuri Tai Masa goodnight text sukai wanka suka kwanta da sofia sunata surutunsu.


Washe gari Bai nemeta ba ya fice sanin tanada baquwa saidai ta waya sukai mgana har tasamu ta rokesa fita daqyar yabarta Dan Haka wanka sukai Suka shirya cikin dogayan pencil jeans da half ripped top gwara Laylan ita ta Dora blazer akai suka fice.


Daga can ya kwaso zazzabi Dan Haka suna dawowa magani sofia ta Bata ta wuce gida
Aikuwa daya dawo ta langwabe Masa Suka tare samansa qarshema sbd Allah yasa mum da siddika ta tafi.


Sabuwar duniya Suka bude a gidan Dan kuwa Cindy komawa tayi Bata iya fitowa koina gidan idan ta Gama aikinta ta shige Bata fitowa sbd Sir Turakin Dake gidan ba Wanda Suka sani bane
Shi kansa A Abdoul ya rungumi duka ayyukan Dake gabansu yabar Turakin ya huta a gida iyakacinsa kawo takardu a saka hannu ya koma office dasu.


Irin sabo da shaquwar dasukai yasa daqyar take iya fita school tadawo,
Idan tana waya da Anne kuwa barin dakinsa takeyi sbd ba ruwansa wani lokacin wayarsa yakeyi Annen Tasha ji Amma Bata dauka shine tunda tasan Babu shaquwa ko kusanci tsakaninsu ko kadan.


Satinsu uku suna zuba sabuwar rayuwa a gidan,
Babu inda basa soyewarsu idan Suka tashi Musamman a dining room daga cin abinci sunfi komai hargitsa dakin.


Tun Cindy na Jin tsoro da shakka harta daina sai itama gidan yafi Dadi daga ita saisu ba hayaniya ba tashin hankali,


Tareda Laylan koyaushe suke abincin Rana da dare banda na safe sbd Basa tashi da wuri.


Babban fargabar data fara kamata shine yanda cikinta yafara tasawa alamar fitowa ga Abban ya lura da tasawar cikinta Amma Bai taba tunanin ciki ajikinta ba Dan Bata Raina kanta ba Saida tafiya ta kamasa ya wuce Australia yabarta da kewa Allah yasa Cindy na Nan tana kulawa da ita sosai sbd itama tagano cikin jikin Laylan daya sakata cikin tashin hankali da tsoron ranarda Ms Na'ima zatasan cikin da uban cikin.




*********
Daga Ceddi Plaza anty Sa'adah ta fito gurin siyayyar tafiyar da zatai ganin gida Za'ayi bikin rantsar dasu Alhaji Qarami yayan Momy matsayin dasuka samu na siyasa,


Bataso zuwaba sbd tsoro da fargabar kada su Gane gaskia da aketa boye musu Dan kuwa suna ganowa tabbas batasan masifarsu ko ta Ms Na'ima wanne za'a fi Jin fargaba,


Su umma Jamila Babu abinda bazasu iya yiwa Laylah ba da dama Kawu saidun data daura auren ya wargaza dadadden burinsu,
Haryanzu alwashinsu na Kan takurawar momy dasukai tadawo Nigeria su samu su Shiga cikin arzikin Turaki da Anne tunda Sa'adah taqi bada dama umma Jamila ta tsine Mata yafi so dubu dari Akan yanda take cewan tana Amarica taqi dawowa su kutsa cikin dukiya,


Duk wasu manyan malamai da bokaye sungama shirinsu akan yanda zasu Dora Sa'adah a zuciyar Anne dashi kansa Turakin Dan samun abinda sukeso shiyasa batason zuwa Inda suken gashi yanzu Dole zata sbd ranar data dawo daga last tafiyar datai Suka hade airport da Haj Karima Dole ta sanar cewan dawowarta kenan yanzu tana Nigeria ta dawo shiyasa suka takura tazo wannan bikin da za'ai.




Motarta ta bude tasaka siyayyar datai bayan motar ta zagayo zata shiga.....


Haj Karima data Gama abinda take itama acikin gurin tana cikin motarta tana waya da Ms Na'ima da shigarta gida kenan ta koma Laylah dake fama da zazzabi Mai qarfi ta fito tana Mata sannu da dawowa....


Haj Karima ta zubawa Sa'adah Ido tana kallonta da kyau Dan ta tabbatarda ita din ce
Cikin tsananin tsana da baqin cikin ganin Sa'adahn tace"


Na'ima ga matsiyaciyar kishiyarki Nan gabana Kamar na taketa da mota...


Dakatawa Ms Na'ima tayi daga tafiyar datake zuwa daki ta miqawa Laylah handbag dinta zuciyarta na tsananin Kuna da zafi sbd da baqin cikin Turaki tadawo khairat Chiroma ta sanar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login