Showing 48001 words to 51000 words out of 91990 words
Chapter 17 - NOOR ALBI (Hasken Rayuwata) Writing By Mamuhgee.txt
Saida jikinsu duk yayi dumi da ruwan dake zuba akansu yasan tasamu Dan qarfi Lokacin saiya saketa tareda kallon hannuwanta Dake rufe da kirjinta ya dauke ido akai tareda bude Baki cikin wani Irin sautin daya Kuma kashe kuzarinta yace"
Zaki iya da kanki??
Kasa magana tayi sai dagowa tayi Ahankali ta zuba Masa manyan idanuwanta Dan kallon bakin dayayi maganar Dan kuwa sautin muryar Sam wani sautin ne dabam...
Shima zuba Mata nasa idanuwan yayi tsananin kunya ta rufeta ta sauke idanuwanta tana gyada Kai ahankali cikin qarfin hali,
tanaji yafice ta Tara ruwan zafi cikin bathtub tashige ciki tana rintse ido cikin wani Irin mummanan Hali na tsananin ciwon datake ji na ratsata.
Daureda towel dinsa fari qal ta fito kanta na tsiyayar ruwan dake sake nauyaya kunyarta da tsananta Mata azabar ciwon datake ciki
Tana fitowa takasa qarasowa tsakiyar dakin ganinsa tsaye gabaki daya qamshinsa ya qarasa birkita daki da sanyin AC yacika...
Qasan dakin ta kalla taga yanda komai na gadon kusan an watsoshi qasa da sauri ta dauke Kai tareda nufar kofa tana takawa a wahalce da qarfin hali
Tana Dora hannu Kan handle zata bude ya riqo hannunta daya sauka Kan handle din sai alokacin tafara Jin wani shock na haduwar jikinsu ta rintse ido batareda ta juyoba ko motsaba...
Bakinsa taji daidai kunnenta ahankali ya furta"
Zaki iya fita ahakan??
Tsikar jikinta ne Suka tashi gabaki daya sbd yanda yayi maganar ta sake rintse ido tana qanqame hannun kofar da hannunta Kai.
Bude kofar dakin yayi yaja hannunta a hankali ganin bata iya tafiya sosai har zuwa palon inda kayanta suke watse ya dauko rigarta ya Sanya Mata duk tana tsaye batareda ta iya motsawaba ko dagowa Saida yagama saka Mata rigar akan towel din ta dago ahankali ta kallesa idanuwansa na kanta....
Zame jikinta tayi daga nasa ta nufi kofa ta bude Yana tsaye gurin Yana kallonta ganin yanda take tafiya daqyar yasashi takowa ya dauketa cak fito da ita Batareda la'akarin wani zai iya ganinsu yakaita har Kan gadonta ya kwantar ya kalli fuskarta Dake Sunkuye taqi dagowa su hada ido yaja Mata bargo ya juya yabar dakin.
Bayan fitarsa zamewa tayi tashige bargo tareda zubawa kofar daya fita ido a Dan wahalce Dan take taji zazzabi Mai qarfi na taso Mata ta rufe idanuwa tana qarasa shigewa bargo.
Da asuba daqyar ta iya tashi ta lallaba ta shiga toilet tasake gasa kanta sosai da ruwan zafi kafin tayo wanka ta fito tayi sallah ta busar da kanta da hand dryer
Daqyar ta shirya kanta cikin Riga da wandon pencil jeans blue tasaka blazer akai da qaramin veil ta nada akanta ta fito su Cindy na janye da suitcase dinta hannunta handbag dintace kawai sai black fararen Balenciaga sneakers Dake qafarta...
Tea Mai zafi sosai kawai Tasha da cake biyu ta nufi dakin Ms Na'ima daketa waya tanajin kamarma Dole tana buqatan zuwa Nigeria a gaggauce taje tadawo Dan Haka har bankwanan tafiyar Mum din sukai Suka fito tare takawo Mata takardarta data baro saman ta kalleta lokacinda take kokarin Shiga mota da wani sanyin sauti tace"
Mum Zaki sanarwa abba mum wuce sbd kafin ya fito lokacin tashinmu ya wuce.
Gyada Mata Kai tayi cikin kulawa da Yar qaramar magana tace"
Daga can kisamo Min babbar tsarabar saurayi ko miji Dan Naga anan bakida alamar yin ko daya....
Murmushin rashin abin fada take kokarin saki idanuwanta suka sauka Kan Wanda ke fitowa kwarjininsa ya cika idonta da bakinta takasa fadar abinda zata fada ta dauke kanta tana maidawa Kan Ms Na'ima tace"
Good morning,
Barka da fitowa.
Kallonta yayi kafin ya kalli Ms Na'ima Data dawo gurinsa tareda riqo hannunsa cikin nata tana cewa"
Good morning Turaki.
Amsawa yayi Yana daga wayarsa da hannun daya ya Dora a kunne Yana amsa Kiran daya shigo wayarsa
Ya zare hannunsa a hankali tareda kallon Laylahn data dauke Kai tana kokarin shigewa mota Kai tsaye yace"
A Abdoul zai kira Wanda zai daukeki dakun isa....Harya gotasu ahankali ya furta"" ki kula...
Ita kadai ta iya Jin kalmar saidai Bata bi bayansa da kallonba harya shige mota suka fice da A Abdoul sbd mum Na'iman Dake gurin.
Juyawa tayi ta fada mota itama Dan tsayuwar ta isheta jiri jiri take kamar ji sbd zazzabin tun Daren jiyan datake tareda shi.
Suna Isa gidansu Sofia ta shirya ita kawai take jira Daman
suka dunguma zuwa airport dinsa sauran yan tafiyar suke can
Suna Isa ba jimawa Suka daga.
Koda suka Isa Florida zazzabine sosai a jikinta Haka ta lallaba Suka Isa gidan step sister din Sofia
Suna Isa ta kwanta Dan gabobin jikinta gabaki daya ciwo suke.
Bacci tayi Mai nauyi sai yamma sosai ta tashi lokacin zazzabin ya fada mata tayi wanka da ruwan dumi tayi sallah kafin ta shirya ta fito sanyeda half gown da doguwar socks har cinya da cardigan,
Tea Aunt siya ta hada Mata ta Bata tareda maganin zazzabin dayake Nurse ce
Saida tayi mintuna da Shan tea din suka nufi Dan dining din gidan mai kujeru hudu sukaci abinci sbd mijinta baya qasar yaje gida nijar ba yanzu zai dawoba..
Wanda zai dauketa yakirata kusan so uku tana bacci Bata dagaba Dole takirasa Dan kada yakira Abban ya fada Masa ta sanar dashi yabari sai gobe yazo ya dauketa sbd batajin Dadi yau din.
Anan ta kwana gidan, washe garin ma anan ta wuni sai yamma takirasa yazo ya dauketa tareda Sofia suka tafi zuwa apartment din da aka Kama Mata,
2bedroom ne sai Palo dasu toilet
Komai na gidan yagama tsaruwa yanda zataji dadin zaman garin fiyema da yanda tayi tunani dan kuwa dagani gidan ba qaramin kudi aka biyaba aka Kama matashi da dukkanin kayan cikin da aka zuba Mata sabbi.
Bayan tafiyar wanda yakawosu kayanta Sofia ta jera Mata a closet ita tana kwance tana waya da Anty Sa'adah har Lokacin dai ba wani qarfi ajikinta..
Sofia tayi musu order na wasu abubuwan abinci ba jimawa aka kawo musu ta gasa musu bread sukaci da kwai da hot milk sallar ishai kawai Laylan tayi ta kwanta bacci yayi gaba da ita.
Saida Suka kwana biyu a floridan tana fama da zazzabin datazo dashi kafin tasamu warwarewa bayan magungunan data samu gurin Aunt siya tasha Suka fara fita zuwa abinda yakawosu Wanda kullum da qarfe 10 suke shiga su fito 12 daganan saisu koma gidanta kokuma gidan Aunt siya danma bata cika zamaba gida tana asibiti koyaushe,
Hakan yasa Suka fara yawon shoppings da guraren bude ido a garin tunda basuda wani abin Yi dasun fito class din program nasu.
Kwanansu goma a garin suka Saba da garin sosai musamman dayake cikin abokan tafiyarsu akawi Yar garin Kuma suna Shiri sosai da Laylan gashi tanada mota Nan suka ringa yawo kala kala.
Yau pleasure beach sukaje Suka shiga water Ride daqyar ta iya shiga sbd tsoronta da ruwa Amma su Sofia suka tilasta Dan Haka tana shiga Bata jimaba a ta fito kanta na juyawa ta nema guri ta zausa Saida Suka Gama Suka fito suka nufa Cinema acan Suka qarasa wunin Suka kamo hanyar dawowa gida.
Gidan Aunt siya Suka nufa suna shiga ko tsakiyar palonta Bata Gama kaiwaba ta tsaya cak jirin datake ji tun fitowarta water Ride tana daurewa ya dibeta tayi gefe ta zube idanuwanta na rufewa.
Kiran sunanta Sofia tayi tareda yowa kanta da sauri tana qwala Kiran Aunt siya Dake Shirin fita zuwa asibiti...
Da mamakin Kiran Aunt siya ta fito tana ganin Laylah akwance da sauri ta taho tana cewa"
Meya sameta?
I dnt know....she just fainted....
Ruwa Aunt siya ta nufa fridge ta dauko da sauri tadawo tana kokarin bude robar ruwan idanuwanta ya sauka Kan jinin Dake biyo gefen Laylan ta qarqashinta Yana gangarowa ta saki robar hannunta da sauri tareda fadar"
is she pregnant Sofia????? Da mamaki Mai tsanani girma Kan fuskarta qarasa tambayar Sofia hakan.
Sai alokacin Sofia ta lurada jinin ta kalli Laylan da sauri wadda idanuwanta ke rufe da alama ta some
Tace"
She can't be pregnant Aunt,batada ko saurayi fa bare,
Wani abun ne daban just do something Aunt siya....
Da sauri taje ta daga wayarta takira motar asibiti tareda dawowa ta Kama hannun Laylan tana Jin pulse dinta tasake kallon fuskan Laylan ta bude tafukan hannunta ta duba cikeda mamaki ta miqe tana sintirin jiran motar asibitin sbd ta tabbata Inshallah Laylah is having a miscarriage...
Koda motar asibitin tazo hankali tashe suka kwasheta zuwa asibiti
Lokacin Sofia takira wayar mum Na'ima yafi so nawa baya shiga sbd ranar ta wuce Nigeria....
Shiga tashin hankali Sofia tayi sbd batasan waye zata kiraba Kuma ta sanar bayan mum Na'iman sai Abban Laylan Wanda take Jin shakkar kiransa sbd tsoron idan cikin ne da gaske karyazo yaji tajawa Laylan fitina a gida Dan Haka ta daure Bata kirasaba tafara kaida kawon jiran ganin laylan tafara samuwa tukuna.
Aunt siya tayi mamaki miscarriage a jikin Laylah saidai sbd yanda yazo Mata da matsala yasa Bata tsaya wannan ba aka duqafa ganin bata galabaita sosaiba sbd cikin duka suka baifi sati ukuba suke saka gani Dan Haka Dole Sofia takira Abban ganin jikin yazowa da Laylah da wuya.
A Abdoul takira ta sanar Masa suna asibiti Laylah batada lafiya.
Shiru yayi bayan yagama Jin abinda tafara ta dago ya saci kallon Turaki dake zaune cikin navy blue Ralph Lauren Kaftan suit fuskarsa sai sheqi yakeyi da alama Yana cikin nutsuwa.
Dan gyara necktie din wuyansa yayi tareda aje iPad Dake hannunsa
Turakin ya kallesa ganin magana yakeson fada ya dauke ido akansa alamar yanajinsa.
Ms Laylah na asibiti batada lafiya
Da alama kamar sosai ne sbd qawarta data Kira akwai sautin kuka s tareda ita.....
Dakatawa yayi iya Nan sbd Ganin cak Turakin ya tsaya daga signing dayake a takardu batareda ya dagoba ya kallesa.
Shiru ya ratsa office din kafin ya dago ya kalli A Abdoul Dake jiran umarnin abinyi.
Kallon da yayi Masa yasashi gyada Kai Yana cewa"
Zanyi booking tickets yanzu.
Juyawa yayi ya fice da sauri Yana fidda wayarsa take yayi musu booking tickets din zuwa Florida
Yakoma ya tattara sauran ayyukan Dake desk na office din Turakin yayi clearing schedules dinsa na ranar gabaki daya dama na gobe ya dawo ya sanarwa Turakin jirginsu Nan da 3 hours zai tashi.
Sai cikin dare ta farka idanuwanta jajir sun Mata nauyi hakama jikinta ba qarfi ko kadan
Ta waiwaya gefenta ahankali taga Sofia zaune tana riqeda hannunta daya idanuwa sun Dan sauya alamar harda kuka tayi
Ta lumshe ido hawayen dake ciki Suka gangaro gefen fuskarta tanaji ahankali Sofia tace"
Laylah you had a miscarriage...
Wani irin kukan da bataso zuwansa bane ya taho Mata cikin qaramin sauti da rashin kuzarin jiki na tsoro da damuwar da batasan ta halinda take ciki ko kunyar kanta datasu Sofia din.
##MAMUH#
NOOR ALBI
PAY AT +234 903 234 5899
Masu buqatan complete su duba Arewabooks.
*_Mamuhgee 28_*
Rarrashinta Sofia tahau Yi har Aunt siya tashigo dakin riqeda result na scanning din da akai Mata na tabbatarda cikin yafice gabaki daya ba wata matsala,
Kallon Laylan tayi tareda aje folder da scan din yake ciki tana hada Mata sauran allurar dazatai Mata ta kalli Sofia tana cewa ta zubawa laylan ruwan zafi tasha.
Allura Tai Mata tareda Bata magani bayan Tasha ruwan zafi.
Kamata Aunt din takaita toilet din Dake dakin tayo wankan ruwan zafi sosai ta gaso jikinta sai taji tadan ji jikin ya Dan saki kadan ta fito da Taimakon Sofia ta Sanya Riga da wando masu kauri Sosai da hular sanyi Takoma ta kwanta Suka lullubeta take bacci ya dauketa Tana sauke Ajiyar zuciyan kukan datasha.
Daga Aunt siya har Sofia Babu Wanda yayi Mata maganar cikin da abinda ya danganci waye uban cikin sbd bawai Jin cikin ajikintane abunda ya Basu mamaki ba illa sanin Laylan Batada saurayi ko daya,duk samarin Dake bibiyarta Babu Wanda ta taba kulawa bare tabasa damar soyayya da ita har wani abun yashiga tsakani..tunda su din duka tashin turaine Basu damu da wani samun cikiba ga mace rashin sanin saurayin Laylan shine yafi bawa Sofia mamaki itada sukeda kusanci Sosai.
Washe garin fayau ta farka guraren 11 na safe
Jikinta ba qwari sosai har Lokacin sai Idanuwanta dasuka sake kumbura sbd kuka dakuma bacci,
Brush tayo tareda sake shiga ruwan zafi kafin ta fito Tasha tea da liver sauce aka Bata magani takuma Sha saitaji ta sake warwarewa
Saidata Bari abincin dataci ya zauna acikinta bayan mintuna sosai kafin ta miqe tashiga wanka sbd gida zasu koma anyi discharging nata..
Ruwa masu tsananin zafi tayo wanka acikinsu kafin ta sako bathrobe da aka dauko Mata tareda Kaya a gida ta fito Rabin gaban kanta duk ya jiqe da ruwan wanka sbd qarantar hular Dake kanta...
Qafa kawai ta sako cikin dakin hancinta ya shaqa qamshin Bois elite
sai kawai jikinta yayi Sanyi ta dago ahankali idanuwanta dake kumbure har lokacin ta kalli inda yake zaune Kan kujera A Abdoul na tsaye a gefensa gabaki daya qamshinsa yagama cike lungu da saqo na dakin
Ta tsayar da idanuwanta Kan kyakkyawar farar fuskarsa Dake wani irin sheqin kwarjini da cika ido
Batasan lokacinda idanuwanta suka ciko da hawayen cikin daya bare ba Dan kuwa can qarqashin qasan ranta tanajin kamar tana qaunar cikinta saidai Kuma wanzuwarsa babban qalubale ne da tashe tashen hankulan dazasu biyo baya ta bangare daya tayaya zata iya kallon kowa da cikin Aminin Mahaifinta ajikinta bayan duniyarma ba kowane yasan itadin matarsa bace,
Hakama ta isar bulluwar ciki ajikinta na Turakin Zai iya saka wasu daga cikin dangin Momy shiga wani Halin Dan kuwa za'a kirata da irin sunan dasuke Kiran mahaifiyarta..
Shigowar Aunt siya tareda Dr Erica yasanyashi dagowa sai alokacin ya lura da tsayuwarta tana sanye da bathrobe din dukkanin Hasken fatarta yakuma bayyana tayi fari
Ya sauke idanuwansa Kan wuyanta da rigar Bata gama rufewa
Ya juyo ya kalla inda A Abdoul yake yaga baya gurin
Tuni ya Dade da fita tana fitowa sbd Ganin halinda take ciki tafito batasan dasuba Dan Haka ko dago Kai baiyiba ya fice.
Yanda ya zuba Mata mayun idanuwansa yasa jikin qarasa sakewa tana neman faduwa ya miqa hannunsa daya ya kamota tareda miqewa tsaye ya qarasa riqota dakyau da hannunsa daya tashiga gefen jikinsa har bakin gado ya zaunar da ita idanuwansa na Mata wani irin kallon mamakin ganin cikar data qara...
Kallo daya Aunt siya Taiwa Turakin da Laylah ta dauke Kai tana mamakin irin kallon Dake fita daga idanuwansu yafi sabawa uba da 'ya Dan Haka take tasan ba lallai Turaki shine ya Haifa Laylah ba
Tana cikin tunani kafin tayi yunqurin Hana Dr Erica fadar sakamakon ciwon Laylan sai Jin tayi Dr Erican na cewa Laylan had a miscarriage due to Shan magani anyhow batareda sanin cewan she was pregnant ba.........
Akaron farko tun shigowarsa daya dago gabaki daya ya zubawa Dr Erica manyan idanuwansa dasuka sata Jin fadawa sonsa lokaci daya Yana cika Mata ido....
Da muryarsa Mai shegiyar kamewa da bayyanarda mamaki yace"
Did you just said she had a miscarriage?
Kallon yanayinsa daya bayyanarda wani irin da bama zasu iya fassara meyeba Dr Erica tayi kafin ta maida kallonta Kan A Abdoul daya shigo tana cewa"
Yes,
she was pregnant and she lost th.....
Kukan da Laylah tasake ahankali yasa Dr Erica kasa qarasawa ganin wata irin kyakkyawar rungumar da yayi Mata Yana lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya take duk da baice komaiba dukkaninsu zasu iya fadar zancen ya dokesa.
A Abdoul kallon Dr Erica da Aunt siya yayi da ido yace musu"
Can we talk outside please?
Fitowa sukai batareda kowannensu ya waiwayoba sai Dr Erica Dake Dan sake waiwayowa tana kallon yanda Laylan ke cikin tsakiyar kirjinsa a rufe ya zagayeta gabaki dayanta tamkar wata babynsa da bazai iya rayuwa bata ba.
Bayan fitarsu sunjima ahakan tana tsiyayar hawaye ahankali harsaida tayi shiru kafin ya dago da ita ahankali daga jikin nasa ya kalla fuskarta data qi dagowa ta kallesa idanuwanta a qasa.
Hannu yakai batareda yasaniba ya Dora Kan fuskarta ya shafa hawayenta Yana kallon yanda suke sauka ba zato taji muryarsa dake cunkushe da nasa yanayin ya furta"
Are you sad sbd kin Rasa babyn????
Wani irin yanayi Mai tsananin girma da daukewar wuta ya sanyata da tambayarsa da shima Bai Gama tantance shine yayi tambayarba bayan dukkaninsu suna daukan abinda ya farun har aka samu cikin a matsayin kuskure da qaddara,
Saidai fitar cikinda baimasan da Allah yayi Masa arzikin samunsaba ya tabasa Amma ba zai iya nuna hakanba tunda abune da babuma Wanda ya San s ga Kuma yanayinta da alamar ita bazata iya riqe nata radadin Rasa cikinba.
Hannunta ya Kama zuwa bakin gado da kayanda zata Sanya suke Kai ya
Kalla farar _la Perla_ bra dinta Dake gefen kayan ya dago ya kalleta ta rufe idanuwanta dake da hawaye har Lokacin sbd taga abinda idonsa ya sauka akai kafin ya kalleta.
A hannu ya saka bra din kafin yakoma kujera ya zauna a hankali yace"
Ki shirya zamu tafi gida.
Kasa motsawa tayi kamar yanda takasa dagowa ta kallesa harsaida ya miqe ya fita daga dakin zuwa ganawa da Dr Erica.
Bayan fitarsa Sofia tashigo dakin tana kallonta a mamakinta a bayyane Kan fuskarta Dan takasa munafurcin boyewa
Laylah dataga hakan jikin amace tana Sanya bra murya ba Dadi Kai tsaye tace"
He is the father basai kin tambayaba.
Wani mamakin ne yakuma rufe Sofia Mai girma saidai Kuma Bata buqatan sake wata tambayar yanzu sbd yanayin Laylan
Tadai tabbata cewan Sir Turaki bashine asalin dadyn Laylan ba tunda hakan ta faru.
Riga da wandon Gucci brown ta Sanya sai cardigan akai da qaramin scarf Suka fito qafafunta sanye da slippers,
Aunt siya ce tazo ta dauki qaramar jakar kayan Laylan Sukabi Bayan A Abdoul Dake kofar dakin Yana jiransu zuwa motar Turakin Lexus.
Bude Mata bayan motar A Abdoul yayi tashiga ta zauna ahankali kafin ya kalli Sofia Dake gyarawa Laylan scarf dinta cikin kulawa
Yace"
Are you with us Ms Sofia??
Kallon inda Laylah take kalla tayi taga Turaki tafe cikin wata Irin nutsuwa da kamewa komai na jikinsa na nuni da shi din Wanda Allah yayiwa Arziki ne da sauri ta juyo ta kalli A Abdoul din tace"
No, no I will wait for Aunt siya
Allah yakaiku lfya.
Rufewa Laylah kofa tayi tareda matsawa ta juya tabar gurin gabaki daya
Yana zuwa A Abdoul ya bude Masa dayan bangaren yashige ya rufe ya zagaya yashiga gaba ya tada motar suka bar asibitin.
Suna Isa gidan ga mamakinta saitaga har ankira home cleaner tagama gyare koina a gidan sai sanyin Air-con da qamshin hayaqin humidifier Dake fita.
Daga Palo A Abdoul ya tsaya tareda kallon Mai aikin data Gama komai har abinci yace zata iya tafiya